Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi A Cikin Litattafan Kulu Muhammad Bello Tambuwal (3)

NA

ABBAS MUSA

KUNDIN NEMAN DIGIRI NA D’AYA (B.A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NAJERIYA JAMI`AR USMANU D’ANFODIYO SAKKWATO
www.amsoshi.com

BABI NA BIYU


TARIHIN KULU MUHAMMAD BELO TAMBUWAL


2.0 Shimfid’a


Kowane aiki na adabi kamar rubutaccen wasan kwaikwayo da labarun zube da wak’ok’i rubutattu ko na baka na da muhimmanci dangane da irin gargad’i na gyara kayanka da suke wa al`umma. Saboda haka ya kamata a san tarihin marubucin da irin abin da ya sa shi ko ya sa ta shiga wannan aikin wanda kan kasance fad’akarwa ko nishad’antarwa ko ilmantarwa ga al`umma. Shi ma wannan rubutaccen wasan kwaikwayo na Kulu Muhammad an dubi abubuwa k’ark’ashin tarinhinta bisa matakan rayuwa da haihuwa da k’uruciya, neman iliminta da kuma shiga rayuwar aurenta, sai kuma sana`o`inta. An kuma dubi ayukkan gwamnati, k’alubalen rayuwa sai kuma rubuce-rubucenta da kuma kyaututtukan da ta samu na karramawa.

2.1 Haihuwar Kulu Muhammad Bello Tambuwal


An haifi Kulu a garin Tambuwal ta Jihar Sakkwato. An haife ta ne ranar Talata biyu ga watan Nuwanba 1961.

Kulu ta tashi a garin Tambuwal tare da mahaifanta da `yan uwanta biyu kamar haka: Atiku, Nasara, sun tashi k’ark’ashin kulawar mahaifinsu Malam Mamman Likitan Dabbobi har zuwa lokacin da Allah ya yi masa rasuwa, wanda ba za ta iya tuna shekarar ba. Duk tsawon rayuwarsa sun kasance ne a garin na Tambuwal.

2.2 Neman iliminta


Kasancewar mahaifan Kulu masu son ilimi da k’ok’arin yi wa `ya`yansu tarbiyya. Sun sanya `yarsu makarantar allo kamar yadda aka al`adanta a k’asar Hausa da k’uruciyarta inda ta yi karatun Alkur`ani a hannun Malam Yawale Illela a garin Tambuwal har zuwa lokacin da Malam Yawale ya tashi ya koma Sakkwato da zama. Daga nan ne kuma ta koma hannun Malam Umar har zuwa lokacin da ta sauke Alkur`ani.

Kazalika Kulu ta shiga makarantar Faramare a Tambuwal. Bayan kammalawa sai ta koma makarantar Sakandaren `yan mata a Sakkwato mai suna (G.G.C) Sokoto wato go’bernment girl’s college. bayan kammala sakandare ne sai ta wuce Kwalejin Koyon Mulki ta Sokoto (College of Administration, Sokoto) inda ta yi karatu a kan harkokin koyon mulki. Bayan kammala wannan makaranta sai ta wuce Jami`ar Bayero da ke Kano (B.U.K) a can Jami`ar ne kuma ta samu takardar kammala digirinta na farko.

2.3 Aure da Iyali


Kulu ta yi aure kuma Allah ya albarkace ta da haihuwar `ya`ya bakwai. Daga cikinsu akwai maza biyar da kuma mata biyu, ga jerin `ya`yan kamar haka:

 1. Aisha

 2. Muhammad Maigari

 3. Abdurrazak’

 4. Bukhari

 5. Sadik’

 6. Khadija

 7. Saifullahi


2.4 Sana`o`inta na Rayuwa


Kamar galibin matan Hausawa, Kulu akwai sana`o`in da Allah ya sa ta k’ware a kansu. Daga cikin sana`o`inta akwai sarrafa albasa a yi gari da ita da kuma yadda ake fitar da mai daga albasa don a yi amfani da ita wajen cin biredi ko masa da ita. Kuma ta k’ware kan yadda za a yayyanka albasa a aje ta har tsawon shekaru ba ta yi komai ba.Bugu da k’ari Kulu ta samu k’warewa a kan yadda ake sak’ar suwaita da kayan Jarirai. Sana`ar da ta koyo a Kano.Haka kuma tana sana`ar yadda ake had’a Dettol, Izal, sabulun wanka, sabulun wanki; duk ta samu k’warewar sarrafa wad’annan abubuwa ne a Sardauna Memorial Foundation.

Kasancewar Kulu mai ilimin Zamani ta sami k’warewa a fannoni daban-daban. Kulu ta samu aiki a Ma`aikatar watsa labarai ta tsohuwar Jihar Sakkwato. Bugu da k’ari ta yi aiki a Hukumar Shiga da Fice ta K’asa (Nigerian Immigration Ser’bice) na wani lokaci amma ta bari ta koma aikinta da Gwamnatin Jihar Sakkwato.Hajiya Kulu ta yi rik’on k’warya na kansila a Tambuwal daga shekarar 1993-1995. Daga nan kuma sai ta aje aikin Gwamnati.

2.5 K’alubale


A ‘bangaren k’alubale ko gwagwarmayar rayuwa kuwa, Hajiya Kulu ta ce ta fuskanci jarabawa kala-kala a rayuwar aure da kuma na aikin gwamnati da sauran huld’od’i na rayuwa. Daga cikin abin da ya tsaya mata a rayuwa na k’alubale shi ne akwai lokacin da ta zauna da wata kishiya wadda ta yi azamar ganin bayanta, take cewa:

“Wata rana muna zaune da wata mata a k’ark’ashin miji d’aya, sai kawai ta d’auki wata sara ta k’i yin miya ta k’i yin tuwo. Sai dai a sayo ‘bula (tuwon ruwa) shi kowa zai ci. Ashe wai wani magana ake sakawa, wajen had’a shi na mallake dukkan iyalan gidan ita kuma ta yi nasara domin ta raba ni da mijina, amma daga baya an gano bayan lokaci ya k’ure.

 

Haka kuma na zauna da wata kishiya mai matuk’ar hassada. Wata rana ina kiyon saniya sai kishiyar ta daddaka gwalaf na k’wan lantarki ta had’a da dusan dabbobi da niyar saniyar ta ci ta mutu. Sai Allah ya kawo ni wajen, na duba dusan sai ga daddak’ak’k’en k’walaf a ciki. Da na tambaye ta sai ta yi shiru. K’arin damuwa shi ne, da mai gidan ya dawo na bashi labari sai Ya hauni da masifa wai sharri na ke mata. Har ma ya yi min barazana idan ina son zama lafiya in san inda zan kai saniyar kiyo amma ba gidansa ba.”

 

Hajiya Kulu ta ci gaba da cewa, bayan ta bar aiki da Go’bernment Printing Press, wata rana ta je gwajin d’aukar aiki (inter’biew) da hukumar sojan ruwa (Nigerian Na’by) aka yi jarabawa duk ta ci amma daga k’arshe sai sakamako ya fito wai tsayinta ya yi kad’an.

2.6 Fara Rubuce-Rubucenta


Kamar kowane marubuci idan aka tambaye shi dalilinsa na fara rubutunsa zai bayyana ko kuma ya ‘boye dalilin. Hajiya Kulu ta fara sha`awan rubutu tun makarantar Sakandare (ba ta bayyana tana aji nawa ba), sannan a shekarar 1988 ta rubuta littafinta na farko. Lokacin da wani abin bak’in ciki ya same ta a kan rabuwar aurenta da mijinta wanda tana da gaskiya amma mutane suka kasa fahimta dole ta sa ta koma fad’akarwa ta hanyar rubuta littafinta na farko mai suna Nawaibul Yak’een wanda ke da jigon fad’akarwa da wa`azi a kan mutuwa da hisabi da kuma zaman k’abari.

Daga shi sai littafi na biyu mai suna Rashin Uwa Hasara ne. Shi wannan littafin yana da jigon fad’akarwa ne ga mata da maza masu barin `ya`yansu a hannun miyagun kishiyoyi masu gana musu azaba. Duk ko da sun fahimci ana cutar yaran nasu.

Littafin ta na uku mai suna Mata Masu Duniya shi kuma yana fad’akarwa ne a kan yadda mata ke rasa imaninsu da mutuncinsu sakamakon zuwa wajen bokaye da Malaman Tsibbu don dai kawai su mallaki mijinsu ko da zai k’i Allah ya yi watsi da `yan uwansa. Wad’annan sune jogogin littattafan Hajiya Kulu Muhamad Bello Tambuwal na wasan kwaikwayo da kuma na wa`azi da fad’akarwa.Kulu Muhammad Bello duk da kasancewar tana fuskantar kalubalen lokaci na zamanta ma`aikaciyar gwamnati da hidimomin gida da na sana`o`inta, ta yi k’ok’arin wallafa littattafanta a matsayin na ta gudummawa ga magance matsalolin rayuwar aure.

Daga cikin rubuce-rubucenta akwai:

 1. Nawa`ibul Yakeen (1988)

 2. Rashin Uwa Hasara ne (1988) • Fad’akarwa ga Mata (2012) 1. Amfani Kanki da Kanki (2014)


2.7 Kyautukan karramawa


Babu ko shakka idan mutum Ya yi aikin k’warai ya cancanci a saka masa ko kuma a yaba masa, domin wasu su kasance masu kwaikwayo aikin kirki, kamar yadda duk wanda ya yi kishiyar aikin k’warai ya cancanci a gargad’e shi wani ma a yi masa uk’uba dan ya zama darasi ga na baya. Hajiya Kulu ta yi ayyuka na taimakon mutane don horar da su da kuma fad’akar da su domin haka ne ma aka samu wata k’ungiya ta Gizago ta karramata da:

 1. Award of Ed’cellence Presented to Hajiya Kulu M.B Tambuwal, First Female Author of Hausa Books in Sokoto 2012


Kyautar karramawa da aka gabatar ga Hajiya Kulu M.B Tambuwal, a matsayin marubuciyar farko ta Hausa a Jihar Sakkwato, a shekarar 2012.

 1. House of Representati’be Committee of Labor Employment and Producti’bity in Collaboration With Federal Ministry of Agriculture and Rural De’belopment and Go-getter consulting Limited.


Kwamitin Na `Yan Majalisa Akan Harkokin `Yan Kwadago, Ma`Aikata Da Masana`Antu da Had’in Gwuiwar Ma`aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Ha’baka Karkara da Kuma da K’arfafa Mutane don Samun Nasara.

Sun karramata da “National Co-operati’be Merit Award on Onion and Food Processing Co-operati’be Society, Sokoto State in recognition of your Outstanding contributions to co-operati’be de’belopment in Nigeria” 2015

Sun karrama K’uniyar su da Lambar girmamawa ta k’asa saboda sarrafa albasa da suke yi da sauran kayan masarufi ta Jahar Sakkwato saboda yabawa da gudummuwar ku wajen ci gaban k’asa a shekarar 2015.

2.8 Nad’ewa


Mutane da dama kamar Kulu muhammad Tambuwal suna da tarihin Rayuwa mai cike da darussan da za a koya domin samun cimma matakin nasara a rayuwa. Domin dacewa da manufar binciken wannan babi na biyu ya fara ne da shimfid’a. Daga nan kuma sai aka kawo tarihin Hajiya Kulu Muhammad Bello Tambuwal wanda ya had’a tun daga haihuwa neman iliminta da aure da iyalanta da sana’o’inta da aikin gwamnati da kuma k’alubalen rayuwa da ta fuskanta.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments