Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi A Cikin Litattafan Kulu Muhammad Bello Tambuwal (4)

NA

ABBAS MUSA

KUNDIN NEMAN DIGIRI NA D’AYA (B.A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NAJERIYA JAMI`AR USMANU D’ANFODIYO SAKKWATO

www.amsoshi.com

BABI NA UKU


KISHI DA RABE-RABENSA


3.0     Shimfid’a


Lamarin kishi abu ne da ya shafi rayuwa ba ta mutane kawai ba har ma da aljannu da dabbobi da k’wari da tsuntsaye da dai sauran halittun Allah (SWT). Allah (SWT) ya halitta wad’annan halittun da son kasancewa su kad’ai kada a had’a su da wani. Wanda wata sifa ce da ta kad’aita ga Allah mad’aukaki shi kad’ai. Kamar inda Al’k’ur’ani yake cewa “Lallai Allah ba ya gafarta a had’a shi da wani a wurin bauta, sai dai yana gafarta zunubin da bai kai shirka ba ko shi ga wanda ya so”. (4:48).

Sai dai a rayuwa ta yau da kullun Bahaushe a ‘bangaren aure yana kallon kishi nau’i-nau’i har zuwa nau`i kamar kishin mata tsakaninsu masu auren miji d’aya, kishin uwar miji, kishin k’annen miji, kishin mace da ‘ya’yan mijinta, kishin samri, kishin ‘yan uba. Kuma idan aka koma a sauran ma`amaloli na rayuwa ana samun kishi kamar a fadodin Sarakuna a kasuwanni da Makarantu da wuraren aiki da ma a gidajen Karuwai kamar yadda aka nazarta a cikin littafin `yartsana na Ibrahim Sheme.

3.1     Ma’anar Kishi


Bayan Ubangiji ya halicci sammai da k’assai, da kuma abin da ke cikin duniya, sai kuma ya zuba d’inbin haittarsa iri daban-daban a cikin ruwa da k’ark’ashin k’asa da bayan k’asa da sararin samaniya. Ya kuma halicci Annabi Adamu domin ya aje shi a doron k’asa don ya mik’a masa jan ragamar mulkin dukkan halittarsa da ke cikin duniya baki d’aya.

Irin yadda Allah ya d’aukaka Annabi Adamu da kuma fifikon da aka nuna masa a kan Mala`iku  da kuma Iblis abin bai yi wa shi Iblis dad’i ba wajen ba sa shi da aka yi da ya yi sujada ga Annabi Adamu k’arshen lamari dai ya yi girman ga Umarnin Allah ya yin sujadar.

Allah Mad’aukaki ya ce “Ya Ibisu! Me ya hana ka ka yi sujada ga abin da na halitta da hannaye na biyu? shin ka yi girman kai ne?”. (Alk’ur`ani, 38:75). Shi Iblis d’aya ne daga cikin Aljannu wanda aka halitta daga wuta saboda tsananin kishi har ya kai Iblis ba ya ganin girman Ubangijinsa wanda ya haifar masa da yin Magana cikin hushi da nuna rashin ladabi da bayyana k’iyayya ga Annabi Adamu (A.S) dubi abin da ya ce “Ni mafifici ne daga gare shi, ka halitta ni daga wuta, shi kuma halicce shi daga yun’bu”. (Alk’ur`ani 38:76).

Saboda haka Allah Mad’aukaki ya kore shi daga cikin gidan Aljanna wanda ya k’ara rura wutar kishinsa ga Annabi Adamu da zuriyarsa inda ya d’auki Alwashi na d’aukar fansa, wanda abu na farko da ya fara yi shi ne sanadiyar fitar da shi Adamu da matarsa Hauwa`u daga masaukinsu wato Aljanna.

Lamarin kishi abu ne dad’ad’d’e tun a zamanin Annabi Adam (A.S) ‘ya’yansa sun nuna wani abu da ake ganin kishi ne wanda har ya haifar da zubda jinin d’an uwansa. Annabi Adam(AS) ya kasance yana haihuwar tagwaye mace da namiji idan an yaye su sai kuma a sake haihuwar wasu namiji da mace da zarar sun isa aure sai a d’auki namijin farko a had’a su da macen tagwaye na biyu, haka kuma macen tagwayen farko a had’a su aure da namijin tagwaye na biyu. Yayin da K’abila da Habila suka girma sai Habila ya nemi ‘yar’uwar haihuwar K’abila da aure, sai K’abila ya bugi k’asa ya ce, shi allambaram bai san wannan zance ba.

Yayin da husumar ta tsananta sai suka kai k’ara gun mahaifinsu, ya umurce su da su gabatar da sadaka duk wanda aka kar’bi tasa shi zai auri mai kyau, k’arshe dai aka kar’bi sadakar Habila, sai K’abila ya ce sai ya kashe Habila haka kuwa aka yi saboda tsananin kishi Allah mad’aukaki ya ce “A lokacin da suka bayar da baikon sai aka kar’bi na Habila amma ba a kar’ba daga K’abila ba, sai ya ce lallai zan kashe ka”(Al’k’ur’ani 5:27).

Wannan k’issa mai cike da tausayi tana bayyana laifi na biyu da aka fara yi wa Allah a bayan k’asa shi ne kisan kai wanda kuma ya faru ne sanadiyar matsanancin kishi.

Bargery, (1934) a k’amus d’insa ya bayyana ma’anar kishi da cewa: “shi ne ganin k’yashi da ke tsakanin kishiyoyi”. A k’amusun Hausa na jami’ar Bayero, (2006) sun bayyana ma’anar kishi kamar haka: “Rashin jituwa da nuna k’yashi irin wanda matan da ke auren mutum d’aya ke yi wa juna.

Bakura, (2003) a kundin digirinsa na biyu ya bayyana ma’anar kishi da: “kishi: wani nau’i ne na k’auna da fatar alheri ga wani abu da ke haddasa wa d’an adam aiwatar da gwagwarmaya da za ta taimaka masa wajen kare mutunci kansa da kansa da martabarsa da d’aukakar darajarsa da d’orewar wanzuwar abin da yake so da k’auna

Wad’annan su ne ma’anar kishi daga wasu litattafai da kundayen bincike duka dai sun dubi kishin a mahanga biyu wato k’yashin wani alheri ga wani da kuma son alherin a ke’bance. Wannan a fahimta ta kenan.

Ni kuwa a tawa fahimta kishi yanayi ne da mutum kan tsinci kansa a ciki na son mallakar wani abu ko zuciyar wani shi kad’ai ba tare da wani ya samu wannan abin ko kulawar wannan mutum ba.

 

3.2 Rabe-raben Kishi


Kishi kamar kowane fagen nazari za a samu rabe-rabensa kamar haka:

 1. Kishi tsakanin mata


Kowane aure a kan k’ulla shi ne domin zama na din-din-din ko kuma a ce mutu-ka-raba, to amma duk da haka a kan samu matsaloli tsakanin kishiyoyi na rashin fahimta ko son kai da kan jawo rashin zama lafiya da kwanciyar hankali a cikin gida, wanda zafin kishi ne ke kawo shi. A lamarin kishi wani lokaci ya kan jawo rabuwa tsakanin ma’aurata wanda ko bayan sun rabu da wata mata matuk’ar akwai ‘ya’ya tsakani ko kuma wadda ke gida ta fahimci lalle wadda ke waje tana yin duk wata mai yiyuwa don dawowa gidan ko maigida na da ra’ayin dawowa da wadda aka saka lamarin kishi kan k’ara ta’azzara a lokacin.

Wani abu da ke k’ara haifar da irin wannan kishi shi ne sakin wata bayan an yi amarya, a nan za a tarar cewa matar da aka saka kullum tana ganin k’yashin matar da ke gidan miji kuma za ta yi duk mai yiyuwa don ganin itama ta yi waje, ita kuma wadda ke gidan kullum aka tayar da zancen wadda aka saka sai a ji tana ambaton aibobinta, kuma idan aka fahimci maigida na k’ok’arin yi mata wani alheri ko dan saboda zuriyyar da ke tsakaninsu sai a hana, saboda tsabar kishi.

 1. Kishin uwar miji


 Daga cikin abin da ake kira kishi shi ne rashin jutuwa a tsakanin mata da uwar miji musamman idan ana zaune a gida d’aya, a wasu gidajen Hausawa, matar D’a kan d’auki mahaifiyar maigidanta a matsayin abokiyan gaba, hasali ma sai a tarar ta d’auki tsanar duniya ta d’ora a kan uwar mijinta har ma sukan kira su da sunaye na banza irinsu hawan jini, bairos, k’anjamau da sauransu. Wasu uwayen mijin kuwa suke d’aukar matan ‘ya’yansu a matsayin kishiyoyinsu saboda wani dalili na su, irin wad’annan abubuwa suke jawo rashin jutuwa da k’iyayya a tsakanin uwar miji da matar d’anta, yayin da ita uwar kan fahimci ga wata ta zo da rana tsaka tana k’ok’arin k’wace mata d’an cikinta, ita kuwa matar na ganin wannan tsohuwa da ta ci na ta zamani sannan tana k’ok’arin cin zamanin wasu, daga nan sai a samu abin da ake kira kishin uwar miji.

Irin salon da wannan kishi ke d’auka wanda shi ya sa ya fad’o a nan shi ne uwar miji za ta yi k’ok’ari ta mallake d’anta ta hana shi ya yiwa matar da take kishi da ita wani abu sai abin da ta ce haka uwar ita ma matar za ta so ta mallaki mijin sai abin da ta ga dama zai yi wa uwarsa kowanne daga cikinsu (matar da uwar miji), za su yi k’ok’ari wurin mallakar hanyoyi daban-daban don ganin sun yi nasara ga wanda suke kishi

 1. Kishin `yan`uwan miji


Kasancewar galibin gidaje Hausawa ana zaune ne da ‘yan’uwa kamar kawunnai da yannai da k’annai da ma kakanni a wani wajan, a kan samu matsanancin kishi tsakanin matar aure da k’annan maza ne ko mata wanda kan ha’baka saboda wasu dalili mabambanta.

Wasu magidanta  kan wakiltar da k’annensu wajen gudanar da lamurran dukiyoyinsu da kuma tafiyar da wasu lamurran da suka shafi irin sutura da abinci da sauran kayan masarufi daga haka sai a samu kishi tsakani saboda tunanin k’anen miji ya kar’be musu fada a wajen maigidansu; a wani lokacin za a ga cewa matar ita ke da fada fiye da ‘yanuwan maigida sai ta yi amfani da wannan dama wajan hana wa maigidanta tallafawa ‘yan’uwansa, hasali ma wasu daga cikinsu idan suna son wani abu sai sun yi kamun k’afa a wajenta wanda ke Haifar da kishi a tsakani.

A ra`ayin Malama Ruk’ayya Hussaini ita tana ganin kishi ya rabu kashi biyu:

 1. Kishin hankali: Shi ne tsakanin mata biyu ga mai gida, idan d’ayar matar ta yi wani abu da ya burge mijin har ya zama hankalinsa ya karkata zuwa wannan matar sai ita kuma d’ayar ta shirya wata kyautatawa tsakaninta da maigidan wanda ya wuce na abokiyar zamanta domin jawo hankalinsa da natsuwarsa a gare ta.

 2. Kishin hauka: Shi wannan kishin mata ne guda biyu sa’banin na farko domin su kullum suna cikin fitina da tadawa mai gidansu hankali.


3.3 Kishi a Ra’ayoyin Malaman Addini


Talatar mafara (2000) Kishi shi ne canzawar zuciya da motsuwar jini domin nufin ramuwa, saboda dalilin tarayyar wani ga wani abu da ba ya kar’bar tarayya.

Rijiyar Lemo (1987) yana ganin kishi: na da ma’anar sosuwar zuciya da ‘bacin rai, a dalilin tarayya da wani ya yi da wani a kan abin da wanin ya ke’banta da sonsa ko mallakarsa.

Al’furaih: (ba shekara) Kishi halitta ce ta asali kuma d’abi’a mai tushe ga mace kuma kishi bai kasancewa sai akwai soyayya a koyaushe mace ta zama mai son mijinta to za ta yi kishinsa sosai sai dai kishi yana iya jan ta zuwa wuta ko kuma sanya ta aljanna idan ta ji tsoron Allah.

Jarjani (ba shekara) ya ce “Kishi shi ne k’in kar’bar tarewa da wani ga bin abun da yake hak’k’i na mutum.”

Ruk’ayya Husaini (2017) ta ce “Kishi wata halitta ce da ke cikin zukatan bil`adama sai dai kowa da irin yadda yake nasa kishin.”

Fatima Alti (2017) ta ce “Kishi wani hali ne na mata da duk mace tana da shi sai dai na wata ya fi na wata.”

3.4 Kishi a Mahangar Malaman Al’ada


Zulai ingawa (1987) “Kishi a Hausa na nufi wata hanya ta tsokana don nuna fifikon kare abin so dangane da irin matuk’ar son da ake wa wannan abu”.

Gobir (2017) “Kishi shi ne nuna damuwa a kan wata ni’ima ko baiwa da Allah ya yi wa wani mutum, tare kuma da fatan ni’imar ta gushe ko kuma ta dawo gare shi, ko jin cewa ni’imar ba ta dace da kowa ba sai shi”.

Kontagora (2017) “Kishi shi ne kamar kana da mata sai ka k’aro d’aya sai su kama k’eta a tsakaninsu.”

D’und’aye (2017) “Kishi shi ne k’arfin hali da kasada da mata kan shiga don nuna suna son mazajensu.”

Dogon Daji (2017) “Kishi shi ne zafi ko haushin da mutum ke ji idan aka had’a shi da abokin rayuwa.”

Kalgo (2017) “Kishi shi ne sanya damuwa a rai ko zuciya ta hanyar nuna damuwa da wani abu ko rashin sonsa.”

Isa (2017) “Kishi shi ne mutum ya zama yana da zuciyar yin wani abu da ya sa a rayuwarsa kamar taimakon addininsa in kuma ‘bangaren mata ne yana nufin hassada.”

K’ofar Mazugal (2017) “Kishi d’abi`a ce ko hali da yake tsakanin mata sai dai kishin wata ya d’ara na wata zafi.”

Zoromawa (2017) “Kishi shi ne hassada”

Tudun Wada (2017) “Kishi duk abin da kake so a ranka kuma ya d’aid’aita gareka kai kad’ai ba tare da abokin gwami ba

3.5 Abin da ke K’ara Haddasa Kishi


A lamarin kishi kamar wuta ce mai ruruwa idan aka zuba mata wani makamashi, shi kan shi kishi akwai abubuwan da ke k’ara hasbud’ashi ko motsar da shi, a gani na kishi halitta ce da ke cikin zuciya da ake samun abubuwa da dama da ke hasbud’a shi.

Kishi kusan ko wace halitta yana da shi illa Alhanzir (Alade) kamar yadda nassi ya nuna, saboda haka wani dalili kawai ya ke jira sai ya motsa.

Daga cikin abubuwan da ke motsar da shi akwai:

 • Nuna fifiko da mazaje ke yi a tsakanin matansu ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwa.

 • Yunk’urin k’ara mata,

 • Neman mata a tsakanin mazaje masu aure

 • Neman maza a tsakanin matan aure.


 • Samun wata ni’ima ko d’aukaka. 1. Nuna fiifiko da mazaje ke yi a tsakanin matansu ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu


Nuna fifiko a tsakanin ma’aurata abu ne da ya zama ruwan dare, musamman idan aka samu d’ai daga cikin matan ta fi d’ayar iya wasu huld’od’i na hila a wajen huld’a da maigida ta kowace irin hanyar zamantakewa ko kuma tsarin halittar da Allah ya sanya wa magidanci kan son d’aya daga cikin matansa a kan d’ayar ko kuma `ya`yansa ko `yan`uwansa, bugu da k’ari, ba komi ne zai tafi har abada ba domin duk yadda wasu ke son su ‘boye, wata rana za`a gane daga nan sai kishi ya motsa.

 1.  Yunk’urin K’ara Mata


A zaman aure ba abin da mata ke matuk’ar k’i da k’yama kamar kawo masu abokiyar zama. Daga lokacin da matar gida ta fahimci maigidanta na k’ok’arin k’ara mata to duk wasu halaye da za ta nuna don bayyana kishin za ta fito da su a fili don bayyana abin da ke cikin ranta daga lokacin za a samu sauyin fuskar matar gida ko sauyin ma’amalar aure ko k’in yin girki a gida ko ta hanyar k’ok’arin illata mai gida, kamar k’ok’arin kashe shi don duk kowa ya rasa, ko ta raba shi da wata ga’ba ta jikinsa kamar mazakutarsa kamar yadda duk ya faru a wannan zamani da muke ciki ko kuma idan duk wad’annan hayoyi ba su yiyu sai ta shiga bokaye da malaman tsibbu don a illata wadda ake k’ok’arin shigowa da ita ko kuma a sauya ra’ayin maigidan duk dai kar abun ya tabbata.

 • K’arya Kafin Aure


A adabin Hausa masana sun dubi k’arya a matsayin abin da ake k’yama, Hausawa kan ce k’arya fure take ba ta ‘ya’ya, marar gaskiya ko cikin ruwa ya yi ji’bi.

A yau an samu mutane musamman matasa da suka d’auki k’arya a matsayin hanyar da suke bi wajen sace zuciyar ‘yan mata kafin aure wanda ya had’a da hayar kayan sawa da kayan lehe irin wad’annan matasa su kan samu matsanancin kishi ga matansu da rashin fahimta domin su matan za su d’auka kamar suna taskance kud’in ne a wajen matan waje, ya yin da su kuma samarin ba su da kud’in ne daga nan sai a samu abu na biyar da ke k’ara haddasa kishi wato zargi.

 1. K’aryar Iyaye


Wasu iyaye mata kan yi hayar kud’in d’aki a kai a jera a d’akin ‘yarsu bayan sati biyu ko wata d’aya a kwashe a bar d’aki wayam. Wannan kan zubar da kimar amarya ga idon ango har ya kai ga rashin arziki da mutuwar aure.

 1. Zargi


Babu ko shakka bayan aure a kan samu sauyin zama a wasu daga cikin gidaje saboda tun asali an gina auren ne a kan tubalin toka wanda zai rushe a kurkusa daga wannan waje sai a fara sai zargin juna ya biyo baya kamar zargin ma’amala da matan banza ko mazan banza ga matan, wanda idan d’ayan ya fita daga gida hankali ba zai kwanta ba, kan abin da yake yi a waje har dai ya dawo gida.

3.6      Matakan Kishi Bisa Nazarin Wannan Bincike


A wannan wajen zan yi bayani kan matakai uku da mutane kan tsinci kan su game da lamarin kishi kamar haka:

 1. Matsanancin Kishi


Mataki ne na kishi wanda ke faruwa tsakanin mutane wanda mutum zai nuna zuwa ga iyalansa ya kuma nuna himmarsa da damuwarsa dangane da halayyar zamantakewarsu tare da k’ok’arin kiyaye su daga kowane irin abu da ka iya cutar da su domin tabbatar da kariyar mutuncinsu, a k’ok’arin tabbatar da wannan k’uduri a kan d’auki mataki kowane iri don a nuna lalle ana kishin da gaske, kamar hana mata fita sai da k’wak’k’warar lalura irin ta shari’a ko kuma hana ‘ya’yansa na cikinsa shiga wajen matansa musamman Amare sai dai buk’atar da suke da ita su aika a kira mahaifiyasu su ganta.

Bugu da k’ari irin wanan mataki na kishi za a samu mai yin sa a kowane lokaci yana k’ok’arin kare mutuncinsa da na addininsa a idon mutanen da yake zaune da su. Daga cikin halayen masu irin wannan kishin za a ga matan wasu da hijabi har k’asa, sannan basu cika yarda likita namiji ya duba lafiyar matansu ba; a ‘bangaren mata kuwa duk wadda suka fahimci tana k’ok’arin lik’ewa mijinsu tofa sai inda k’arfinsu ya k’are. Daga lokacin wasu ke shiga bokaye da malaman tsibbu, wasu kuma su d’auki matakin hallaka rayuwar abokin kishinsu ta hanyar makamai da duk wani abu da za su iya don cimma manufarsu.

 1. Matsakaicin Kishi


Wannan nau’i na kishi shi ne mutum zai nuna kishinsa ga matansa amma ba zai kai kamar wancan matsanancin ba, domin shi ya kan bar matansa su kama huld’a da k’annensa da sauran ‘yan uwan zumunta.

 1. Rashin Kishi


Irin wannan mataki na kishi, shi ake samu a yau ga wasu daga cikin wad’anda su ka yi boko mai zurfi ko kuma wad’anda al’adun bak’in al’ummu suka yi tasiri a kan rayuwarsu kamar dai Turawa ko wasu daban, anan ne za a ga wasu daga cikin shuwagabanni suna barin matansu suna cud’ed’eniya da maza manisantansu, kamar halartar biki da galibi maza ne ke wajan ko yawace-yawace zuwa k’asashen k’etare domin ta buk’ata ta su ta k’ashin kansu. Babu shakka idan aka dubi lamarin kishi a yau za a ga cewa yana da matakai uku game da halayen al’ummarmu a yau da ake wannan bincike.

Daga cikin misalan labaran da suka faru na kishi, akwai kamar haka:

 1. Wata mata ta shigar da k’arar mijinta wajen alk’ali Musa dan Ishak’ a garin Rayyi, shekarar hijira 286. Wakilinta ya yi da`awar cewa “lallai wadda ya ke wakilta tana bin mijinta dinari d’ari biyar na sadakinta.” Sai mijin ya yi musun kud’in, sai alk’ali ya ce da wakilin matar “ko akwai shaida akan da`awarku?” yayin da aka zo da shaidu sai d’aya daga cikinsu ya ce wa matar ta tashi tsaye, sai mijin ya ce “ta yi maka me?” sai wakilinta ya ce “domin ya kalli fuskarta sosai da sosai domin ya tabatar shin ita ce wadda ya sani koko?..


A lokacin mijin ya ce inko hakane sai ya kalli fuskarta za ya bada shaida to alk’ali ya shaida lallai a kaina akwai bashin da ta ke da`awa ba sai ta bude fuskarta kowa ya gani ba.

A lokacin ita kuma matar ta ce “ni kuma alk’ali ya shaida lallai bashin da nake bin mijina na yafe masa kuma na ku’butar da shi a da`awar da na ke yi a kansa duniya da lahira. A karshe saboda kishinsu ya yi matuk’ar burge alk’ali ya ke cewa lalle a rubuta wannan labarin cikin littafin halaye mafiya girma.

 1. Wata mata ta shiga mota da mai gidanta za su je anguwa, sai jami`an shige da fice (immigration) suka tare su, ana cikin bincike, sai d’aya daga cikin jami`an ya mari mijin a gaban matar, da jami`an suka k’are bincikensu, sai matar ta ce wa mijin “fau-fau ba za ta bi mijin ba sai ya rama marin da aka yi masa, da mijin ya fahimci ba sauk’i cikin zancen matar tasa, sai ya yi k’arfin hali ya kife jami`in da mari, da jami`in ya tashi zai d’auki mataki, sai shugabansu ya tsawatar da shi.


 

 

3.7 Kammalawa


A wannan babin an ga irin yadda kishi ya fara tun daga farko wato matsalar Iblis da Annabi Adam (A.S) da kuma matsalar K’abila da Habila da ra`ayoyin Masana da Malaman addini da na al`ada a kan yadda suke kallon kishi da kuma shi yadda mai binciken ke kallon lamarin kishi inda za a fahimci Babu ko shakka lamarin kishi abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya a tsakanin mutane da sauran halittun Allah.

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Post a Comment

0 Comments