Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi A Cikin Litattafan Kulu Muhammad Bello Tambuwal (5)

NA

ABBAS MUSA

KUNDIN NEMAN DIGIRI NA D’AYA (B.A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NAJERIYA JAMI`AR USMANU D’ANFODIYO SAKKWATO

www.amsoshi.com

BABI NA HUD’U


CUD’ANYAR KISHI A LITATTAFAN WASAN KWAIKWAYO NA “GARGAD’I GA MATA”  DA KUMA “RASHIN UWA HASARA NE” NA KULU MUHAMMAD TAMBUWAL


4.0 Shimfid’a


A wannan babi na hud’u za a yi nazari da sharhin litattafan Gargad’i ga Mata da kuma Rashin Uwa Hasara ne ta dubin jigo, salo, zubi da tsari, da kuma cud’anyar kishi a cikin litattafan.

  • Gabatar da Littafin “Rashin Uwa Hasara Ne”


Wannan littafin mai suna Rashin Uwa Hasara ne Kulu Muhammad Bello Tambuwal ta rubuta shi a shekarar 1988. Littafin yana da jigon gargad’i ga maza (magidanta) wad’anda ke barin ‘ya’yansu ga kishiyoyin uwayen yaran. Bayan Allah ya yi rabuwarsu da uwayen yaran mata. Sai su wad’annan matan su rik’a cutar da yaran ta hanyar gallaza musu da barinsu cikin tsumma da yunwa a wulak’ance. Kuma abin mamaki wasu magidanta sun sani amma kash! Sai su kasa d’aukar matakin da ya dace.

4.2 Jigon Littafin “Rashin Uwa Hasara ne”


          Wannan littafin da Kulu Muhammad Bello ta rubuta domin ta isar da wani sak’o dake cikin zuciyarta.

Littafin yana da jigon gargad’i musamman ga maza masu barin `ya`yansu ga hannun kishiyoyin uwayen yaran duk ko da sun fahimci ana cutar yaran.

Wasan kwaikwayon yana magana a kan labarin rayuwar wani magidanci mai suna Baban D’angata da matansa biyu masu suna Basaraka mahaifiyar D’angata da Mardiyya da kuma d’an Amarya. Sai kuma d’aya matar mai suna Zumbai mai ‘ya’ya kamar haka: D’angata, Dija da Bebi.

A wasan an nuna Baban D’angata yana zaune gida d’aya da mahaifiyarsa mai suna Zango. Sai kuma yayansa mai suna Maigero. Da kuma ‘yar uwarsa mace mai suna yaya.

4.3 Halayen Taurari


Malam Ruwa: Magidanci mai mata biyu wanda matarsa ke ganin asiri aka masa halayensa suka canja daga mai son matansa zuwa son d’aya kawai.

Basaraka: Uwar gidan Malam Ruwa marar son zama lafiya.

Zumbai: Mace mai hak’uri mai tawakkali wadda Malam Ruwa ya saka.

Maigero: D’an`uwan Malam Ruwa mai d’aukan komai cikin sauk’i.

Dangana: D’a ne ga zumbai da k’annensa biyu; Bebi da Dija wad’anda aka tsangwama saboda uwarsu bata gidan.

D’angata: D’an Basaraka da `yan`uwansa biyu da aka sangarta wato Mardiyya da D’an Amarya.

Yaya: `Yar`uwar Malam Ruwa marar son zama lafiya.

4.4 Zubi da Tsari


Littafin wasan kwaikwayo ne da aka bud’e shi da farko a gidan Malam Ruwa, k’arshe an rufe shi da maganar Maigero d’an uwan Malam Ruwa. A littafin akwai babi-babi har guda bakwai.

4.5 Salo


A littafin an samu salailai kamar haka:

  1. Salon Zayyana


“M. Ruwa: Ya shigo cikin gida ya tarar da `ya`yan Zumbai suna kuka a k’ofar d’akin uwarsu.”

  1. Salon karin magana


“Maigero: Gamu gani dai saniya da auren runji, sai munga inda akuya za ta da kayan taiki.”

  • Salon kamancen daidaito


“Zumbai: Ta sunkuyar da kai kamar za ta yi kuka.”

  1. Salon habaici


“Maigero: To ai kaga abin da ake gudu, anyi gudun gara an fad’a zago, Bunsuru ya je barbara ya dawo da ciki.”

  1. Salon Zambo


“Zumbai: Kin haifi ‘Barawo, kin haifi D’andaudu, kin haifi `yar iskar yarinya shekara sha uku amma gidan k’atti ta ke kwana.”

 4.6 Cud’anyar Kishi a Littafin “Rashin Uwa Hasara ne”.

A cikin wannan littafi ta marubuciyar ta kawo matsalolin kishi da dama domin nuna gargad’i ga Mata da su yi hattara da gallazama `ya`yan kishiyoyi musamman marigaya, ta kawo matsalolin kishi nau`i-nau`i kamar haka:

  1. Nau`in Kishin Mata da `Ya`yan Kishiyarsu


A Rabo na d’aya shafi na farko basaraka ta yi wata magana mai nuna tsantsar kishi kamar haka:

Basaraka: (a fusace) ba shakka da haka ka so, me ya sa ka yi wa uwarsu saki uku? Ai sai ka je ka mayar da ita ta yi wahala da ‘ya’yanta. Ni ba zan iya wahala da d’an kowa ba. A nan Basaraka tana mayar da raddi ne ga maigidanta Malam Ruwa (Baban D’angata) a yayin da ya kawo mata k’orafin halin da ‘ya’yan kishiyarta suke ciki na takura.

       Nau`in Kishin Mata da `Ya`yan Kishiyarsu:

A shafi na biyar cikin rabo na biyu, Zumbai ta yi wata magana mai zafi da ke nuna kishinta ga Basaraka kamar haka:

Zumbai: wa ma ya san irin ‘ya’yan da Basaraka ta haifa, tun da alhakin kwana na ne ya d’auka ya kai mata.

A nan Zumbai tana wajen Zango ce ana neman a yi sulhu a kan a ba ta ‘ya’yanta ta rene su da kanta. Shi ne take yin wannan bayani mai nuna tuhumar ‘ya’yan kishiyarta da yadda aka haife su.

ii.Nau`in Kishin Uwar Miji.

A rabo na biyu shafi na hud’u zango mahaifiyar Malam Ruwa ta yi wata magana mai nuna tsantsar kishi ga matar D’anta Basaraka kamar haka:

Zango: ko kud’i nake so, sai na nemi alfarma daga Basaraka sa’in nan ta je ta nemo mini a wurinsa. To ko ni da nike uwarsa ya wulak’anta ni a kan Basaraka balle ke?

A nan Zango mahaifiyar Malam Ruwa tana bayani ga Zumbai matar Malam Ruwa da ya saka, a lokacin da ita Zumbai ta zo tana neman a ba ta ‘ya’yanta ta kula da su har su fara wayo. Inda Zango ke nuna cewa ai Basaraka ta riga ta fi k’arfinta. Ko ita da take uwar mijinta balle ita da ke tsohuwar matarsa. Bugu da k’ari a shafi na bakwai Zango ta koma wata magana mai zafi da nuna kishinta a kan yadda zaman Malam Ruwa da Basaraka ke ci gaba da zama k’alubale gare ta.

Zango: Ni kan na kusa mutuwa in huta da masifar ruwa da basaka.

iii. Kishin `Yan`Uwan Miji.

A shafi na bakwai an nuna irin yadda Maigero ya yi wata magana mai zafi ta bayyana tsantsar kishinsa a kan abin da Basaraka ke yi. Kalli abin da yake cewa:

Maigero: Kai ne da ka fi kowa sanin dad’in karuwa ko? Wai ka ga kishiya na murna don an saki wata saboda ita. Kai! Mata na cikin jahilci.

A nan Maigero yana mai da jawabi ne ga Malam Ruwa a kan irin yadda matarsa Basaraka take wahalar da ‘ya’yan kishiyarta Zumbai. Amma kuma ya kasa ta’buka komai a kai. Saboda haka yake zaginsa da aibata matarshi, da ce mata karuwa.

A shafi na goma a rabo na uku an bayyana irin yadda yayar Malam Ruwa ta je har gida da niyyar kar’bo ‘ya’yan Zumbai, amma ta buge da cin mutuncin Zumbai kamar haka

Yaya: (ta tsaya tana yatsinar Zumbai) ba kin je kina cewa ‘ya’yanki yunwa ce da su ba? to sai dai yunwar ta kashe su, ba za mu bar su a hanunku ba.

A nan saboda kishin da ke tsakinin yayar Malam Ruwa da tsohuwar matarsa Zumbai ta same ta har gidan iyayenta tana gaya mata magana saboda kishi.

 Nau`in Kishin `Yan`Uwan Miji. (I)

A shafi na sha-d’aya ita ma Zumbai ta mayar da martani abin da yayar Malam Ruwa ta yi mata da magana mai zafi kamar haka:

Zumbai: Kin haifi ‘barawo kin haifi d’an daudu mai kwaikwayon halayen mata, kin haifi ‘yar iskar yarinya shekara tara amma a gidan k’atti take kwana. To in Allah ya so ‘ya’yan nan nawa da ikon Allah za su zama mangarta in dai ina da rai.

                        A wannan waje Zumbai ce ke mayar da raddi ga yayar Malam Ruwa a kan abin da take gaya mata a cikin gidansu bayan sa-in-sa ta kaure a tsakaninsu har ta kai ga suna wa juna tonon silili a bainar jama’a.

Nau`in Kishin `Yan`Uwan Miji (II)

A shafi na talatin da d’aya a rabo na bakwai an bayyana yadda Maigero ke cike da jin Haushin irin rayuwar k’unci da su Dangana suka shiga a hannun kishiyar mahaifiyarsu Basaraka, har yana mayar da jawabi ga malam Ruwa kamar haka:

Maigero: Komai aka gani tsakaninku ko a tsakanin su D’angata wallahi ba abin da za a ce illa amanar ‘ya’yan Zumbai ne, ka tuna irin ramar da suka yi. Ga ka da kud’i ga abinci, amma duk a banza yunwa ta kama su.

A nan Maigero yana yin zance ne da Malam Ruwa a kan irin yadda yake ganin ya yi watsi da sha’anin yaransa a lokacin yarintarsu, amma lokacin da suka fara kai wani matsayi a ‘bangaren karatu sai ya nuna wai ‘ya’yansu ne. shi ne Maigero ke ce masa duk abin da yaran nan suka yi masa ko suka wa ‘ya’yan kishiyar mahaifiyarsu, ba abin da za a iya cewa. Sai dai a ce, amanar su ce, suke fitarwa, da aka ci lokacin k’uruciyarsu. A nan Maigero yana taya ‘ya’yan Zumbai kishi ne.

  • Nau`in Kishin `Yan`Uba


A shafi na goma sha biyar na Rabo na biyar an bayyana irin yadda yaran ke taya iyayensu mata kishi kamar haka:

Mardiya: (ta nufo Dangana, ta share shi da mari) jeka uwarka ta sayo maka duniyar nan duka d’an iska.

A nan yaran sun nuna cewa lallai sun fahimci tsakanin mahaifansu ba sa ga maciji saboda kishi. Don haka ne su ma suka ara suka yafa. Har da kai duka da kuma zagi duk don a bayyana tsabar kishi.

Nau`in Kishin `Yan`Uba.

A rabo na shida, shafi na goma sha tara an bayyana irin yadda su D’angana suka fahimci lallai Basaraka ita ta sanya Malam Ruwa ya saki Zumbai mahaifiyarsu, kamar haka:

Dangana: (ya shure ta da k’afa) ke shegiya don ubanki ki yi karatu kin ji ko?

                        A nan an bayyana Dangana saboda kishi da jin haushin abinda aka yi wa mahaifiyarsu na korar ta daga gidan har ma yake kiran ‘yar uwarsa da shegiya. Sannan ya koma gargad’inta kamar haka da cewa:

Nau`in Kishin `Yan`Uba.

Dangana: In kin k’ara maganarsu sai na dake ki. Halan ba ki ji an ce uwarsu ce ta sa ubanmu ya kori uwarmu ba?

            Duka dai maganganun na nuna yaran Malam Ruwa ke kishi a tsakaninsu a matsayin masu taya mahaifansu mata kishi.

  • Nau`in Kishin Mata Masu Auren Miji D’aya


A rabo na bakwai a shafi na ashirin da bakwai an bayyana yadda Zumbai ke ba da labarin abin da ya sami ‘ya’yan Basaraka na k’ask’anci, kai ka ce abin ya yi mata dad’i kasancewarsu ‘ya’yan kishiyarta:

Zumbai: E, baba ya ce wai Mardiyyar Basaraka tana Gusau ta kama d’aki su kuma su D’angata suna nan suna shiririta sun zama zauna gari banza.

Mhm! Saboda kishin da ke cikin zuciyar Zumbai, duk da ta bar gidan Malam Ruwa, amma tana neman labarin wani abin assha da ya sami ‘ya’yan kishiyarta Basaraka, don dai kawai ta bayyana shi ga duniya ta ji dad’i a matsayin wani abu na huce takaicin kishin da take nuna wa a kan Basaraka.

4.7 Gabatar da Littafin “Gargad’i ga mata”


Littafin “Gargad’i ga mata” Littafi ne na wasan kwaikwayo da ke jan kunnen mata game da halayen kishi mai zafi musamman irin yadda ake gallazawa irin wad’anda ba su san hawa ba balle sauka.

 4.8 Jigon Littafin “Gargad’i ga Mata”


Littafin Gargad’i ga Mata Kulu Muhammad Tambuwal ta rubuta shi da manufar fad’akar da mata a kan biyar malaman tsibbu da bokaye. A tak’aice dai littafin yana da jigon fad’akarwa.

Wannan littafi mai suna “Gargad’i ga Mata” da aka rubuta a shekarar 2012 yana da jigon fad’akarwa musamman ga matan da suka d’auki zuwa wajen malaman tsibbu da bokaye domin su mallake mazajensu na aure. Kana su kori kishiyarsu ko su kawo rashin zaman lafiya a gida.

A littafin an bayyana labarin wani magidanci mai suna Lumu da yake da mata d’aya mai suna Tallu. Rana d’aya ya ce zai k’ara mata abokiyar zama. Abokiyar zaman kuwa sunanta Mangu, wadda bayan shigowar amarya duk ta rikita zaman gidan har aka kai matsayin da aka yi mata saki uku amma saboda asiri miin ya ce saki biyu ne ya yi.

A wasan akwai taurari kamar Mai Anguwa wanda shi ne dagacin gari da fadawansa. Sannan akwai yaron mai gida Lumu mai suna D’anmowa, sai kuma malaman tsibbu uku masu suna Mai Barahaza, Malam Maiwake sai kuma Boka. Wad’annan su ne ‘yan wasan da suka fito a littafin Gargad’i ga Mata.

4.9 Zubi da Tsari


Littafin yana da tsarin wasan kwaikwayo sannan an tsara wasan kwaikwayon  da fitowa daga d’aya har zuwa biyar.

4.10 Halayen Taurari


Lumu: Magidanci mai mata biyu da ke rigima tsakaninsu, kusan sun fi k’arfinsa.

Tallu: Uwargidan Lumu wadda ke ganin an tauye mata hak’k’i a koyaushe.

Mangu: Amaryar Lumu marar son zama lafiya.

Malam Maiwake: Malamin tsibbu ne da abokan aikinsa Maibarhaza da kuma Boka.

Maigari: Sarkin gari mai sasanta rikici a gari a tsakanin talakawansa.

D’anmowa: Yaron gidan Lumu.

4.11 Salo


A littafin an samu salailai kamar:

  1. Salon Zayyana


“A cikin gidan su Mangu tana yi wa yaranta wankin tufafi, tana hira da mak’wabciyarsu Hure.”

  1. Salon kamancen daidaito


“Mangu: Don nima in shiga cikin matan zamani, bani zama kamar `yar aiki.”

  • Salon karin magana


“Mangu: Kai shege har da kai. Ai tsafi gaskiyar mai shi.”

  1. Salon kirari: Mangu: Ba dai kunyar duniya ba, sai dai Lahirar maza ta yi k’ura wallahi. Bamu kunya biyu, ina? Duniya sai tsaye, barzahu sai imani.” Da kuma inda ake cewa:


“Malam Maiwake: Babban, ka buwaya ko ga mazan jiya balle mazan yau mata.”

  1. Salon habaici


“Tallu: Gwara ayi mana gorin yawan aure da a ce ni karuwa ce.”

4.12 Cud’anyar Kishi Littafin “Gargad’i Ga Mata”

Babu ko shakka a wurare da dama an yi maganar kishi a littafin, don shi ne ma aka za’bi a yi nazarin wad’annan wuraren.

  1. Nau`in Kishin Mata A tsakaninsu


A fitowa ta biyu shafi na uku Mangu ta yi wata magana mai nuna tsabar kishi kamar haka:

Mangu: Ni ai wallahi so ni kai da an d’aura aure in tare (tana kallon hure) don an gaya mani yana ji da matar nan ta shi. Son ni ke da na shiga kada ta yi wata d’aya don ‘yar duniya ce. Ina son ko dai ta wulak’anta ko ta bar gidan.        .

A wannan waje an bayyana yadda Mangu ke tsananin kishin Tallu tun kafin ta shiga gidan, har ta sha alwashin sai ta kori matar da ta iske a gidan ko kuma ta wulak’anta ta. Duk dai saboda tsabar kishi.

 Nau`in Kishin Mata a Tsakaninsu. (I)

A fitowa ta uku a shafi na shida an nuna yadda sa’insa ta kaure a tsakanin Tallu da Mangu har Mangu ta yi wata magana kamar haka:

Tallu (tana kallonta) ke, ki ji tsoron Allah. Kin ci amanar mijina, saboda kin halaka shi kin halaka kanki don da ganin wannan halin da yake ciki mun san asiri ne kika yi mashi. Allah sai ya tona asirinki mushrika.

A wannan wajen an bayyana saboda tsabar kishi har Tallu ke ganin take-taken Mangu a matsayin lallai asiri take yi har ma ta kira ta da suna mushurika.

Nau`in Kishin Mata a Tsakaninsu (II)

A fitowa ta hud’u a shafi na goma sha d’aya a fadar mai unguwa ga wata magana da Tallu ta yi mai nuna tsabar kishi ga wani abu da ta fahim ci Lumu yana aikatawa Mangu, sa’banin ita, kamar haka:

Tallu: Ranka ya dad’e da ranar girkinta da ba ranar ta ba, duk Luma na d’akinta, na biyu duk abin da ta ce masa ko gaskiya ko k’arya yarda yake, sannan komai ta ce tana so, ko yana da kud’i ko baya da su sai ya je ya ciyo bashi muna kallo sannan an saka masa mugun tsoranta (ta nuna Lumu) ka gan shi in abu ya had’a ni da ita ko ‘ya’yana sai ya aza mana laifi ita har abada cikin gaskiya take. Tsoronta yake kamar me, jikinsa har rawa yake in tana masa magana.

A wannan wajen an bayyana saboda tsabar kishi har Tallu ta fahimci Lumu yana tsabar tsoron Mangu, sannan komi take so ko da kud’i ko ba kud’in lallai sai ya je ya ciwo bashi ya yi mata shi. Sannan idan ana rigima ko yaya ne, to ita ake ba gaskiya.

Nau`in Kishin Mata A Tsakaninsu(III)

Bugu da k’ari a fitowa ta hud’u a shafi na goma sha biyar an bayyana wajen da Tallu ta koma fad’in wata magana mai nuna tsantsar kishi. Duk dai a wajen dagaci:

Tallu: (ta sunkuyad da kai) in na yi mishi magana a kan zaluncin da yake mani da ‘ya’yanmu sai ya ce kishi ne ba komai ba, ni na shaida har ga Allah wannan mata asiri take mashi da tsafe-tsafe. Don akwai lokacin da take dafa mishi wata tantabara da magani ta tsare shi ya cinye har ran nan da ta sake dafa mishi ya k’i ci yasa d’an sa ya ce ya jefar cikin bola kuma wallahi ita da ‘yar uwarta duk karkarar ga sun san gidan kowane boka da malami. Da kowannmu abu ya had’a ta mu ne da laifi ko da shi take fad’a shi ke rok’onta gafara. Ita kullum ita ce mai gaskiya.

            A wannan wajen an bayyana yadda Tallu har ta yi rantsuwa da Allah a kan duk abin da ake yi lallai dai Mangu asiri take had’awa kuma duk wani gidan boka ko malami ba wanda ba ta zuwa. Sannan ta bayar da labarin har yadda ake had’a wata tantabara a sanya magani a ciki duk dai domin juyar da hankalin Lumu ya kama ganin abin da ba daidai ba a matsayin daidai.

  1. Nau`in Kishin Yaran Gida da Matan Mai Gidansu.


Harwa yau a fitowa ta uku an nuna inda D’anmowa ya yi wata magana mai nuna yana taya Tallu kishin da take yi wa Mangu kamar haka:

D’anmowa: (yana dariya) har kin tuna min wak’ar Malam Muhammadu Sani D’angani inda yake cewa: “Akwai d’ibgau mai d’ibge mijinta ba ta bari ga fad’a ya taya ta “. ita ce d’ibgau. To ashe kin ga wannan ita ce d’ibgau don k’arfi ta ke ji baki ganin jikinta ai k’irar k’ato aka yi mata.

A nan siffanta Mangu da D’anmowa ya yi da mai siffar k’ato lallai ba k’aramin kishi ya bayyana ba a matsayinsa na yaron gida mai taya tallu kishi, sannan yana kushe Mangu.

A tak’aice wad’annan su ne nazarin da aka yi na kishi a cikin littafin Gargad’i ga Mata na Kulu Muhammad Bello Tambuwal.

4.13 Nau’o’in Kishi a Cikin Littattafan


A cikin littattafan an samu nau’in kishi daban-daban. Amma za a fara da bayyana na littafin Gargad’i ga Mata kamar haka:

  1. Kishin mata a tsakaninsu; wato tsakanin Mangu da Talle.

  2. Yana bayyana kishin mata a tsakaninsu kamar yadda Tallu ke nuna wa Mangu.

  3. Yana bayyana yadda yaran gida ke kishin wasu daga ciki saboda watakila ba su kyautata musu inda aka bayyana D’anmowa yana kishin Mangu.

  4. An bayyana yadda Tallu ke kishin Mangu saboda tana ganin duk wasu abubuwa da Maigidansu ya ke yi ba a cikin hayyacinsa yake yi ba. yana yi ne saboda asiri. Shi ma wannan kishin mata ne a junansu.

  5. An bayyana tsananin kishin Tallu a kan mijinta don tana ganin ana ba shi wani naman tantabara yana ci. Da ita Tallu ke zargin akwai lauje cikin nad’i. Kishi ne na mata a tsakaninsu.


Wad’annan wurare su ne aka samu tsattsafin kishi a littafin Gargad’i ga Mata. Maganar farko ta zo a shafi na uku, ta biyu kuma a shafi na shida, magana ta uku a shafi na takwas, magana ta hud’u a shafi na goma sha d’aya. Sai kuma kuma maganar k’arshe a shafi na goma sha biyu.

Wannan abin da ya shafi littafin Gargad’i ga Mata kenan. Sai kuma littafi na gaba da za a bayyana ire-iren kishin.

 

A littafin “Rashin Uwa Hasara ne” an sami nau’o’in kishi daban-daban kamar haka:

  1. An bayyana yadda Basaraka ke tsananin kishin ‘ya’yan Malam Ruwa da ba ita ta haife su ba. kishi ne na ‘ya’yan miji.

  2. An bayyana yadda Zango ke matuk’ar kishi da matar d’anta Malam Ruwa, wannan kishi ne na uwar miji.

  3. An bayyana yadda Zumbai ke tsananin kishin Basaraka har tana tuhumar ‘ya’yan Basaraka a matsayin halastattu. Kishi ne na mata a tsakaninsu.

  4. An nuna yadda Maigero yake tsananin kishin da matar k’anensa malam Ruwa. Wannan kishi ne na ‘yan uwan miji.

  5. An bayyana yadda Zango ke kishi da matar d’anta Malam Ruwar har tana fatar ma ta mutu ta huta da bak’in cikin matar d’anta. Wannan kishi ne na uwar miji.

  6. An bayyana yadda yayar Malam Ruwa ta je har gida ta yi fad’a da tsohuwar matar d’an uwanta. Wannan kishin ‘yan uwan miji ne.

  7. An yi bayanin yadda Zumbai ta mayarda martani mai zafi a kan ‘yan uwar Malam Ruwa. Wannan kishi ne ne na ‘yan uwan miji.

  8. An yi bayanin yadda ‘ya’yan malam Ruwa ke kishi a tsakaninsu har da duka da kuma zagi. Wannan kishi ne na `yan`uba.

  9. An k’ara bayyana irin yadda ‘ya’yan ke kishi, sannan su taya uwayensu kishi ko da ba su kusa. Kishi ne na ‘yan`uba.

  10. An bayyana yadda Zumbai ke kishin’ya’yan kishiyarta har tana bayyana abin da ya same su na lalaci cikin jin dad’i. Kishi ne na mata a kan ‘ya’yan mijinta.

  11. An bayyana yadda Maigero ke bayanin irin yadda ‘ya’yan da yake so na Malam Ruwa za su kasance a gaba cikin jin dad’i. Yayin da yake fatar lalaci ga ‘ya’yan da ba ya so saboda mahaifiyarsu ba sa shiri da ita. Kishi ne na ‘yan uwan miji.


Wad’annan su ne wuraren da tsattsafin kishi ya fito a littafin Rashin Uwa Hasara ne. sun fito ne a shafi-shafi kamar haka:

Maganar farko a shafi na farko magana ta biyu a shafi na hud’u, magana ta uku a shafi na biyar, a shafi na bakwai ma an sami irin wannan magana ta kishi. Sai magana ta biyar a shafi na takwas. Magana ta shida a shafi na goma sai magana ta bakwai a shafi na goma sha-d’aya. Sai magana ta takwas a shafi na goma sha biyar. Sai magana ta tara a shafi na goma sha tara. Sai kuma magana ta goma a shafi na ashirin da bakwai sai kuma maganar k’arshe ta goma a shafi na talatin da d’aya.

4.14 Falsafar Marubuciyar a Cikin Rubutunta


Kulu Muhammad Bello Tambuwal tana fahimtar Kishi a matsayin wani abu da ke faruwa tsakanin ma`aurata wanda ta fahimci ba yadda za a yi a samu birbishin kishi sai an samu lallai d’aya daga cikin mata tana duk wani abu mai yiyuwa wajen kawar da hankalin maigidansu daga jikinsa sannan ta shuka abin da ta shirya. Kuma kulu tana kallon kishi abu ne da za a magance shi ta hanyar hak’uri da juriya domin kuwa duk a litattafanta da aka nazarta guda biyu ta nuna yadda aka yi amfani da bokaye da `yan tsibbu wajen cimma nasara. Sai dai wad’anda aka zalunta suka yi hak’uri a k’arshe su suke samun nasara.

 

 

4.15 Kammalawa


Wannan shi ne k’arshen babi na hud’u inda a ciki aka tattauna abubuwa masu muhimmanci kamar haka: An yi nazari jigon littafin Gargad’i ga Mata dangane da salo, zubi da tsari, halayen taurari. Sannan aka yi bayanin jigon littafin Rashin Uwa Hasara ne. Sai kuma aka bayyana salo, zubi da tsari, halayen taurari. Sai kuma cud’anyar kishi a cikin littattafan guda biyu inda aka zak’ulo kishi ko kuma inda aka yi maganar kishi har waje goma sha biyar. A k’arshe an bayyyan nau’o’in kishin da suka fito a cikin littattafan. Daga nan kuma aka rufe babin da kammalawa.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments