Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi A Cikin Litattafan Kulu Muhammad Bello Tambuwal (6)

NA

ABBAS MUSA

KUNDIN NEMAN DIGIRI NA D’AYA (B.A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NAJERIYA JAMI`AR USMANU D’ANFODIYO SAKKWATO
www.amsoshi.com

BABI NA BIYAR


KAMMALAWA


5.0 Shimfid’a


Hausawa na cewa komi ya yi farko tabbas zai yi k’arshe a wannan ga’bar na kawo Babi na Biyar cikin aikina inda zan yi Magana a kan abubuwa biyar. Bayan wannan shinfid’ar da na ke yi zan dubi sakamakon abin da na yi inda zan bayyana sakamakon abin da na gani kuma na fahimta game da kishi musamman a d’an bincike na game da tunanin mata wajen fahimtar Kalmar kishi cikin rubuce-ruubcensu na was an kwaikwayo ko zube. Daga nan kuma a matsayin d’alibi zan bayar da wasu shawarwari da nake ganin za su d’an yi maganin wani abu da mata keji cikin zukatansu na kishin junansu domin ko da akwai kishi a sauran d’aid’aikun mutane to ga mata ya fi muni idan ba a yi shi yadda ya dace ba. Saboda an sha samun labarai daban-daban yadda mata ke d’aukar mumunan mataki a kan kishiyoyinsu, a k’arshen babin zan rufeshi da kammalawa inda zan tak’aita abubuwan da na tattauna a cikinbabin gaba d’aya sai kuma manazarta.

5.1 Sakamakon Bincike


A sakamakon binciken na fahimci galibin abin da ke rubuce a litattafan marubuta mata da ke maganar kishi wasu daga cikinsu labarin rayuwarsu suke bayarwa   a rubuce, wasu kuma suna bada labarin wani abu ne da ya faru ga wani nasu; kodai ya kasance ‘ya’ya ko ‘yanuwa; kamar Hajiya Kulu Muhammad Bello Tambuwal a cikin dukkanin litattafanta da a ka yi nazari; labarin K’alubalen rayuwarta take bayyanawa da ta ‘ya’yanta.

Babu ko shakka so da dama wasu mutane kan buk’aci su bayyana wani abu da ke ci masu tuwo a k’warya, amma saboda gurguwar fahimtar da za a yi musu sai su mayar da shi a rubuce ko ta wata hanyar isar da sak’o ta daban; masanana cewa “Rubutunka kamanninka”

5.2 Shawarwari


Kafin ba da shawarwari ya kamata a fahimci shin mene ne kishi tun farko; sannan me yasa ake kishi?

Kishi: yanayi ne da mutum kan tsinci kansa a ciki na son mallakar wani abu ko zuciyar wani shi kad’ai ba tare da wani ya samu wannan abin ko kulawar wannan mutum ba.

Babu shakka Mata na nuna kishi ne domin su samu kulawa ta musamman sa’banin abokan zamansu; ya yin da amfanin kishi ga Mata ya ta’allak’a ne a kan amfanin da za su samu cikin zamansu da mazajensu na duniya da ‘ya’yan cikinsu.

Abu na farko da ya kamata kowace Mace ta nema don samun kyakkyawar rayuwa a gidan Miji, shi ne ilmi; duk Mace mai ilmi za ta kasance abin sha’awa kuma abin koyi ga kowa. Ilmin da nake Magana a nan ya k’unshi ilmin addini da na zamani; da ilmin addini ne za       ta tausasa zuciyarta ta hanyar tunanin ayoyin Alk’ur’ani da Hadissan Annabi (S.A.W) a kan fahimtar magabata nagari, sai ta sanyawa zuciyarta linzame kan d’aukar duk wani mataki mai muni, a maimakon haka sai ta yi amfani da k’issoshin magabata nagari wajen zama da Maigidanta da abokiyar zamanta cikin kyautatawa don samun iyalai masu farin ciki da walwala; manisanta daga mummunan kishi.

Sai kuma lmin boko da za ta yi amfani da shi wajan iya jan hankalin kowa a gidan Mijinta da salailai daban-daban na samun dauwamammen zaman lafiya mai d’orewa. Hausawa na cewa “Idanka san halin mutum, to sai ka ci maganin zama da shi”

Haka kuma zaman da kike yi da kishiya kada ki yarda ta had’a ki fad’a da mijinki, za a samu a wani gida ana zaman lafiya amma sai kishiya ta rik’a shirya mak’ark’ashiya don ta ga ta haddasa fitina tsakanin abokiyar zamanta da mijinta; duk abin da kishiya za ta fad’a miki duk yanda kika yanda kike da ita kada ki yarda ta ga ‘bacin ranki matuk’ar abin ya shafi zamantakewarku a gidan miji.

Bugu da k’ari ki rage zargi a cikin zuciyarki sannan ki yi rik’o da addu’o’i na neman tsari safe da yamma lokacin kwanciya da dukkan sha’anin rayuwarki; sannan ma’aurata su kasance masu yawaita kyauta a tsakaninsu musamman ke da abokiyar zamanki, domin kyautatawa na saye zuciyar wanda ake wa ita yau da gobe.

Lallai Mata su nisanci duk wata k’awa wadda ke sanadiyyar had’a su da wani malami mai d’abi’a irin ta bokaye ko ‘yan bori.

A k’arshe lallai hak’uri yana da matuk’ar amfani a rayuwa musamman gamatar da ke da abokiyar zama. Domin dole sai an gani an kauda kai a ji a yi kamar ba a jiba.

5.3 Kammalawa


Bahaushe na cewa “komi ya yi farko, lallai zai yi k’arshe”. A nan ne na zo k’arshen wannan aikin da na fara na bincike a kundin digiri na farko wanda na yi babi-babi har guda biyar. A babi na farko an yi gabatarwa; na biyu kuma aka bada tarihin marubuciyar litattafan da aka yi nazari a babi na uku aka yi bayani a kan k’umshiyar kishi; sai a babi na hud’u inda aka yi nazarin litattafan marubuciyar; sai babi na k’arshe uma na biyar inda aka rufe da kammalawa.

 

MANAZARTA


https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments