https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

Daga

         Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya

Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato

aliyubunzaumar@yahoo.com

07063532532, 08095750999

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Abstract


Hausa literature is a channel through which Hausa people’s life is studied. The literature was highly developed as a result of means of writing Hausa either in Ajami or Boko that is, Roman scripts. Boko was introduced by the White men since before colonialisation. Through ‘Boko’ scripts the White men preserved Hausa folklore and started writing fiction and drama in order to achieve their hidden agenda. The aim of this paper is to discuss some of the hidden agenda of the White men’s-missionaries so-called helping hand in the introduction of ‘Boko’ scripts and the Hausa literature in Boko system of writing, that is, the Roman Script.

 

1.0       Gabatarwa


Adabin Hausa wata kafa ce muhimmiya da ake hangen dukkanin rayuwar al’ummar Hausawa daga cikin ta. A cewar ‘Dangmabo (1984), adabi shi ne madubin ko hoton rayuwa na al’umma. Al’ummar Hausawa al’umma ce da ta dad’e da kasancewa ma’abociya zirga-zirga da yawace-yawace na kasuwanci da neman ilmi da ci rani da sauransu. Dalilin wannan ya sa adabin Hausa ya bazu a sassan duniya masu yawa musamman a nahiyar Afirika da wau k’asashen Larabawa kamar Libiya da Tunisiyya da Moroko da sauransu. Ta hanyar samuwar hanyoyin rubuta Hausa na Ajami da Boko sai lamarin adabi ya k’ara fad’ad’a. A maimakon taskace adabin baka kad’ai, sai aka sami wanzuwar rubutaccen adabi na wak’ok’i da zube da kuma wasan kwaikwayo tun lokaci mai tsawo. Manufar wannan mak’ala ita ce nazarin wasu ‘boyayyun manufofin da suka sa Turawa suka shiga cikin aikin samar da adabin Hausa na Boko da kuma inganta shi. Wannan zai ba manazarta na wannan lokaci wani haske na abin da ya gudana a baya da kuma sanin yadda za a daidaita adabin Hausa a yau.

 

2.1       Saduwar Turawa Da Adabin Hausa


Turawa sun fara saduwa da adabin bakan Hausa ne tun lokaci mai tsawo ta dalilin yawace-yawacen Hausawa na kasuwanci da neman ilmi da bauta da sauransu. An nuna cewa, Turawa sun fara samun labarin Hausawa ne tun a wajajen shekarar 1535 lokacin da aka sami wani Balaraben Afirika ta Arewa mai suna Al-Hassan ibni Muhammad Al-Wizas Al-Fasi wanda ya sauya sunansa zuwa Leo Africanus da ya rubuta littattafai bakwai cikin harshen Larabci a lokacin da ya yi zaman kurkuku a k’asar Italiya inda ya bayar da labarin tafiye-tafiyensa cikin daulolin Afirika. A cikin littafi na bakwai ne ya kawo ziyarar da ya kai k’asar Borno da wasu dauloli na k’asar Hausa a tsakanin shekarar 1513 zuwa 1515. Ya nuna k’asar Borno na da nasu harshen magana, ita kuma k’asa d’aya (da bai ambaci sunanta ba wadda ita ce k’asar Hausa) ya nuna suna amfani ne da harshen Gobir (Yahaya, 1988 da Hair, 1994). Duk da wannan tsawon lokaci da Turawa suka share da samun haske game da al’ummar Hausawa, sai a wajajen shekarar 1841 aka sami wani abu na adabin Hausa ya sadu da Turawa.A yawace-yawacen da J. F. Schon da Henry Barth da Kolle suka yi a sassan k’asashen Afirika ne suka rubuta wasu batutuwa na adabin bakan Hausa da suka tsinta a lokuta daban-daban.

Karo na farko da sassan adabin Hausa masu yawa suka sadu daTurawa shi ne lokacin da aka je da wani yaro d’an k’asar Hausa mai suna Dorugu a k’asar Jamus da Ingila. Dorugu ya isa Ingila ne tare da wani Bature mai suna Henrich Barth (Abdulkareem da Hausa) wanda ya yi yawo a sassan k’asar Hausa da wasu k’asashe masu mak’wabtaka da k’asar. A shekarar 1855 Barth ya sauka London tare da Dorugu mai shekaru kamar 16-17 da wani d’an k’abilar Margi mai suna Abbega ( Schon, 1862). A wannan tafiyar ce J. F. Schon ya kar’bi aron matasan biyu inda ya yi amfani da hikimar Dorugu ya tatsi rassan adabin bakan Hausa biyu (zube da wak’a) ya samar da muhimmin ‘bangaren fitaccen littafin adabin Hausa na farko na Bature mai suna Magana Hausa a shekarar 1885.

Idan aka yi la’akari da gudummuwar Dorugu za a ga cewa, ita ce ta kasance zuciyar littafin. Gudummuwarsa ce ta fi birge Schon abin da ya sa har ya ke’be wani sashe na gudummuwar zuwa babi na musamman. Haka kuma Schon ya jinjina wa Dorugu tare da yaba masa a wasu kalamai inda ya ce,

‘Dorugu Bahaushe ne na tsintsa, ya iya magana da harshen sosai. Ba a ta’ba samun d’an Afirika da ya shigo k’asar nan ba wanda yake da amfani kamar sa ba; yana da cikakken bayanin rayuwarsa, d’an shekaru kamar 16 ko 17, amma kuma koyaushe shirye yake ya yi magana. Ya ba ni labarai daban-daban, ya ba ni bayanin rayuwarsa da tafiye-tafiyensa cikin Afirika cikin harshensa. Ya zauna sa’o’i yana ba ni labarai, wani lokaci har cikin dare. Da haka na samar da littafin Hausa mai shafuka d’aruruwa’ (Schon, 1862).

 

Shi kuma rubutaccen adabin Hausa ya fara saduwa da Turawa ne daga wajajen shekarar 1891-1896. A wannan lokaci ne C. H. Robinson ya yi wa K’ungiyar Church Missionary Society aikin lek’en asiri a wasu sassan k’asar Hausa, musamman a tsakanin k’asar Kano da Zazzau. A lokacin wannan aikin ne, C. H. Robinson ya samar da wasu wak’ok’in Hausa 6 da wani tarihi da ya nuna fassara ne daga Larabci ya wallafa littafinsa mai suna Specimens Of Hausa Literature.  A cewarsa, ya wallafa littafin ne domin musanya abin da Schon ya gabatar na cewa, shi ne ya fara samar da rubutu cikin Hausa (Robinson, 1896).

Littafin Specimens Of Hausa Literature ya k’unshi ‘bangarori biyu. Ɓangare na farko shi ne na rubutun Ajami Hausa. Ɓangare na biyu shi ne na rubutun Hausar Boko da kuma fassara a harshen Ingilishi. Daga k’asan wannan ‘bangare ne ke da sharhi na matanin adabin. Wannan littafi ne ya kasance na rubutaccen adabin Hausa da Turawa suka fara samarwa.

Idan aka dubi k’unshiyar wannan littafi, za a ga cewa, ko bayan kasancewarta cikin harshen Hausa, ta yi kama k’warai (musamman wak’ok’i) da na malaman k’asar Hausa ta fuskar jigo da zubi da kuma salo.

Wanzuwar mulkin mallaka ne ya kasance mataki na k’arshe kuma mafi girma da yalwa da ya ba Turawa damar saduwa da adabin Hausa da kuma yin tasiri kansa. Daga shekarar 1900 ne Turawa mabambanta suka zauna cikin k’asar Hausa. Zaunawarsu ta sa suka cud’anyu da adabin Hausa tun daga na baka zuwa rubutacce. Da wannan suka k’ara samar da wasu littattafan adabi na taskacewa da kuma juyawa. Haka kuma suka samar da wani sabon aji na rubutaccen adabi na k’irk’ira littattafan labarai da kuma na wasan kwaikwayo. Haka kuma suka koyar da ‘yan k’asa da kuma kula da dabarun samar da adabin.

3.1       Wasu Manufofin Turawa Ga Samuwar Adabin Hausa


Idan aka dubi zamanin da Turawa, suka fara aiki kan adabin Hausa na taskace shi da aza harsashin nazarinsa za a ga cewa, abu ne mai muhimmanci ga tarihin ci gaban lamurran adabin. Kowane abu ana tsara shin kan manufa wadda tana iya kasancewa a bayyane ko ‘boye. Manufa ta bayyane ita ce wadda ake gani ko ji ta la’akari da wasu abubuwa kamar samar da littattafai da kundaye. Manufar ‘boye kuwa ana fitar da ita ne daga nazari da sharhi da kuma lura da wasu abubuwa da suka biyo bayan wanzuwar wani lamari kamar sauya ainihin abin ko gur’bata shi da sauransu. Aikin Turawa ga adabin Hausa yana k’unshe da wasu ‘boyayyun manufofi. Wad’annan manufofin su ne lek’en asiri da gur’bata tarihi da sauya akalar adabin Hausa da suka taras.

3.1.1                Lek’en Asiri


Tun kafin saduwar Hausawa da Larabawa da Turawa Hausawa suke da shimfid’ad’d’en tsarin rayuwa da kyakkyawar zamantakewa kamar gaskiya da amana da sauransu. Ire-iren wad’annan halaye da tsare-tsare suka samar wa Hausawa yanayin walwala da tsaro da tattalin arziki yalwatacce. Dukkan wad’annan tsare-tsare an taskace su cikin adabin bakan Hausa.

Kasancewar adabi madubi na rayuwar al’umma sai Turawa suka shiga taskace shi domin ya kasance musu wata kafa ta lek’o lamurran rayuwar Hausawa don sanin yadda za su shigo cikinsu cikin sauk’i ta kowane mataki. Turawa masu yawa sun nuna wannan ce manufarsu ta farko, kuma k’wak’k’wara da ta sa suka rubuce adabin bakan Hausa. Ga misali, J. F. Schon ya bayyana irin wannan manufa ga aikin da ya yi na taskace adabin, ya samar da littafinsa da shi na Magana Hausa. Ga yadda ya bayyana manufarsa ga adana labaran cikin littafin nasa,

Labarin rayuwa da tafiye-tafiyen Dorugu ya fito da sirruka masu yawa kan yanayin k’asa kuma za a ji dad’in karatunsa. Sa idonsa da dafuwar abincin Ingilishi zaman kalaci da al’adu ya nuna wayo da rayuwarsu kulawa. Su kuma labarai sun nuna hanyar tunanin ‘yan k’asa da na ja-in-jansu, sun ba mu haske kan sirrukan zaman iyali da rayuwar jama’a, mun karanci wani abu na bauta, da na k’asa, da fad’ace-fad’ace da rikice-rikice da ke aukuwa saboda al’adar auren mace fiye da d’aya, da yadda suke k’in al’adar cikin fitattun wak’ok’i da adabinsu; da tunaninsu kan lamarin sama da wuta, da rana da wata da taurari; haka kuma da son kud’i, abin da yake ruwan dare ga bak’in mutum; da yawan hanyoyin yaudararsu musamman cikin mata. Haka abin sha’awa ne a san cewa duk wani ilmi da ya wanzu cikinsu suna watsa shi ne ta ire-iren wad’annan labarai (Schon , 1862).

Shi kuma Rattray (1913) ya bayyana manufarsa ga littafinsa inda ya ce,

‘Ga sauran, na d’auke shi cewa, nazarin adabin bakan Hausa na ba d’alibai sha’awa matuk’a saboda kawai kira da ake yi na rairaye shi da auna shi kan mafi tsattsauran nau’i. Al’adun Hausawa ta kowace fuska ba su kasance masu yawan abubuwan wulak’antarwa, ko duhun kai ba. Sun sha samun kutsawa daga ‘bangaren Fulani da sauran bak’in haure. Wasunsu sun kar’bi Musulunci. Suna harakokin kasuwanci wanda shi ne ya ba su damar huld’a da mutane da yawa na yammacin Afirika. Tattare da wannan, sun yi nisa k’warai daga halin kad’o maras laifi wanda kai tsaye yake sa koyaushe al’ada na k’ara ciyar da kanta gaba ta hanyar labarai wad’anda yawanci ta fatar baki ake ba da su, ba su sa’ba tsarin fasalinsu ba, sun bambanta da masu shigo su da cud’anya da su.

Shi kuma M. G. Smith a shimfid’ar da ya yi wa littafin Neil Skinner (1969) wanda ya fassara daga littafin da Frank Edgar ya rubuta na Hausa Tales and Traditions an English translation of Tatsuniyoyi na Hausa, ya kawo manufa da muhimmancin adanawar inda ya ce,

Abu na farko shi ne tanadar wa jami’an mulkin mallaka abubuwan nazarin Hausa. Abu na biyu shi ne k’ara wa jami’an ilmi game da halin zaman Hausawa da al’adunsu ta hanyar kawo musu wad’annan tatsuniyoyi da al’adu. Dukkan ra’ayin Gwamnatin Ingila shi ne fasalin tsarin mulki kaikaice wanda take fatar mulkar wannan babbar k’asar Hausa-Fulani da shi ta hanyar sarakunansu na gargajiya. Irin wannan tsarin mulki na buk’atar jami’an Ingila su sami ingantaccen ilmin harshen ‘yan k’asa’ (Sa’id, 1997).

Idan aka yi la’akari da wad’annan bayanai za a ga cewa kowane littafi na adabin bakan Hausa da Turawan suka rubuta, yana k’unshe da tsare-tsaren rayuwar Hausawa cikin adabinsu na tatsuniyoyi da labarai da sauransu. La’akari da wad’annan bayanai ya tabbatar da cewa, ta hanyar taskace adabin Hausa ne Turawa suka sami haske dangane da tsarin rayuwar Hausawa masu yawa tun kafin zamansu na dirshan cikin Hausawa. Akwai ire-iren wad’annan tsare-tsaren rayuwa cikin littattafan adabin da Turawan suka rubuta. Ga misali, a cikin littafin Magana Hausa akwai dabarun kusantar Sarakuna da magani da zaman iyali da tsaron k’asa da tattalin arziki da sana’o’i da yanayin k’asa da sauransu.

 

 

3.1.2               Gurɓata Tarihi


K’asar Hausa k’asa ce mai yawan fad’in k’asa da yawan jama’a tun lokaci mai tsawo. K’asar ta kasance mai k’unshe da abubuwan tarihi mai yawa. Babban abu na tarihi, kuma wanda ya kafa harsashin adana ingantaccen tarihi shi ne bayyanar addinin Musulunci cikin k’asar. Shigowar Musulunci ya bud’a wa Hausawa wata kafar wayewar kai da ci gaba a ilmance. Wannan ci gaba ya ba Hausawa damar sarrafa bak’ak’en Larabci suka rubuta harshen Hausa. Fasahar rubutu ta ba Hausawa d’aukaka suka kasance kad’an daga cikin al’ummun Afirika da suka rubuta harshensu tun kafin shigowar Turawa (Robinson,  1896). Adabin Hausa ta hanyar sarrafa bak’ak’en Larabci ya k’ara bunk’asa a lokacin rayuwar malamai masu jihadi. Jihadin ya sa addinin Musulunci ya kafu sosai a k’asar Hausa, ya kuma mamaye rayuwar Hausawa, ya kuma zaunu a muhallan mulki da shari’a a lokacin jihadin Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo.

Rubuce-rubuce da malamai suka samar cikin Larabci da kuma Ajami sun kasance wata kafa ingantacciya ta adana tarihin k’asar Hausa da al’ummar cikinta. Rubuce-rubucen sun had’a da littattafai da wak’ok’i da hud’ubobi da wasik’u da sauransu.

Ko da Turawa suka shigo k’asar Hausa sun sami al’amurran k’asar na gudana bisa tsari na addinin Musulunci daidai gwargwado. Irin wannan yanayi na watsuwar Musulunci da cigabansa cikin k’asar Hausa ya zama wani tarnak’i babba ga rukunin Turawa Mishan da ke k’ok’arin dasa addinin Kirista cikin k’asar (Miller, 1936).

Charles Henry Robinson ne d’an Mishan na farko da ya sami zagaya wasu sassan k’asar Hausa har kuma ya wallafa littafin adabin Hausa. Littafinsa Specimens Of Hausa Literature ya k’unshi wak’ok’in Hausa 6 da zube guda. Wak’ok’in 6 Robinson ya jingina asalin rubuta su ga wasu malaman k’asar Hausa uku.[1] Ya jingina wak’ok’in ga malaman ba kan kowace hujja ba. Idan aka yi la’akari da k’unshiyar littafin Specimens Of Hausa Literature ana iya tabbatar da cewa, Robinson ya shirya littafin ne saboda wasu manufofi da yake son ya cimma.

Gur’bata tarihin shigowar Musulunci da watsuwar sa cikin k’asar Hausa na cikin ‘boyayyun manufofin Robinson ga wallafa wannan littafi. Ana iya gane haka idan aka yi nazarin bayanin da ya rubuta a sharhin wak’a ta 5 (E) da ya jingina wa Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo. Ga abin da ya ce,

Manufarta ita ce zuga mutane su shiga yak’in da ya fara da Hausawa, shi Shaihu Usmanu wanda yake Bafillace ne. Sakamakon k’arshe na yak’in shi ne Shaihu ya ci yankuna masu yawa na daular k’asar Hausa, da kuma tilasta su kar’bar addinin Musulunci (Muhammadu) ( Robinson, 1896: 60).

 

Idan aka yi nazarin wannan batu aka kuma kwatanta shi da tarihin shigowa da watsuwar Musulunci k’asar Hausa za a ga cewa, bayanin yana gur’bata gaskiyar tarihin ne kawai. Malaman tarihi sun yi sa’bani dangane da farkon shigowar Musulunci k’asar Hausa. Akwai masu ganin cewa, Musulunci ya fara shigowa k’asar Hausa ne tun a zamanin sahabban Annabi (SAW). Wasu kuma sun nuna a wajajen k’arni na10 ko na 11 ne ya fara shigowar k’asar Hausa (Yahaya, 1988:8-9 da Gada, 2010: 3). An k’arfafa zaton fara samuwar rubutaccen adabin Hausa cikin Ajamin Hausa tun a wajajen k’arni na 17 daga wasu ‘yan k’asa da suka sami zurfin ilmin Musulunci irin su Sheikh Ahmad Tila da Sheikh Abdulk’adir Tafa da Abdurrahman Tajuddin da sauransu (Yahaya, 1988: 31).

Shi kuma Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo an haife shi ne a ranar Lahadi 15 ga watan 12 shekarar 1754 (miladiyya). Ya yi karatunsa daga wurin mahaifinsa da wasu malaman k’asar Hausa kamar malam Jibrila. A shekarar 1804 ya k’addamar da jihadi kan wasu daulolin k’asar (Bunza da wasu 2009). Wannan ya kawo tabbatar da Musulunci a matsayin tsarin gudanar da mulki da shari’a da sauransu. Haka kuma aka assasa daula mai cikakken tsarin Musulunci mai suna ‘Daular Usmaniyya’.

Idan aka dubi tarihin rayuwar Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo za a tabbatar da cewa, tun kafin haihuwar sa addinin Musulunci ya watsu cikin k’asar Hausa, kuma har an sami malamai da rubuce-rubuce na ‘yan k’asa. Ke nan a nan, bayanin da Robinson ya kawo a wannan littafi nasa (Specimens Of Hausa Literature, 1896 , 60) wanda ya nuna jihadin Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo ne abin da ya sa mutanen k’asar Hausa suka kar’bi Musulunci wani abu ne da ke gur’bata ainihin tarihin watsuwar Musulunci cikin k’asar. Musulunci ya watsu k’asar Hausa tun kafin wannan jihadi na Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo.

3.1.3                Sauya Akalar Rubutaccen Adabin Hausa Zuwa Na Turawa


Rubutaccen adabin Hausa abu ne da aka fara samarwa tun zamanin shigowar Musulunci da watsuwarsa cikin k’asar Hausa. Rubutaccen adabin da ya fi zama ruwan dare a lokacin shi ne wak’a. Wak’ok’in Hausa da aka samar a lokacin suna rubuce ne cikin Ajamin Hausa saboda ita ce kad’ai ingantacciyar hanyar da Hausawa ke rubuta Hausa kafin mulkin mallaka. An sami malamai masu yawa da suka yi rubuce-rubuce cikin Ajami tun kafin jihadi da kuma bayansa.

Adabin Hausa (wak’a da sauran littattafai) da aka samar a wancan lokaci suna k’unshe ne da jigogin addinin Musulunci. Rubuce-rubucen an yi su domin a karantar da mutane al’amurran Musulunci daban-daban tun daga tauhidi da ayyukan ibada da zamantakewa da yabon Annabi (SAW) da siyasa da sauransu. Bisa irin wad’annan jigogi Turawa suka sami rubutaccen adabin Hausa.

Daga shekarar 1900 ne Turawan Ingila suka k’addamar da aniyarsu ta mulkin mallaka a k’asar Hausa. Muhimman batutuwan mulkin da tsaro da kuma ilmi ne Turawa suka fi mayar da hankalisu a kansu, musamman a farko-farkon shekarun mulkin nasu. Wannan ya sa Turawan suka shiga kiran taruka na ganawa a k’ark’ashin shugabansu Gwamna Lugga (Lugard). A wannan shekara Likita Miller ya nuna shawarar musanya hanyar karatun Hausawa ta Muhammadiya da ta boko domin ta haka ne masu tasowa a gaba za su tashi da tunani irin na Kirista –Turawa a maimakon na cikin adabin Musulmi wanda yake na addinin Musulunci (Miller 1936: 200-201).

A shekarar 1901 Gwamna Lugga ya kira wani taron ganawa da jami’an mulki da ilmi da addini. A wannan taron aka sami halartar Manjo Burdon da Likita Miller da wasu jami’ai inda suka tattauna batun bayar da ilmi ga Hausawa. Abin da ya dami taron shi ne sautukan da za a za’ba (Larabci ko Ingilishi) don rubuta adabin Hausa. Ga abin da likita Miller (wakilin k’ungiyoyin addini) ya rubuta game da zaman nasu,

Lokacin farko-farkon shekarun mulkin mallaka muhimmiyar matsala da ake neman walwalewa ita ce ta ilmi. Cikin wane tsarin rubutu za a samar da adabi nan gaba; cikin Larabci, ko Ajami, ko kuma Romanci? Masana  gaba d’aya da wasu da yawa daga cikin jami’an mulki-musamman Manjo Burdon da saura gaba d’aya saboda la’akari da alak’ar da ke tsakanin k’asar Hausa da k’asashen Gabas, wato Musulunci da suke jin ya fi kyau a kiyaye, sun yi fatar a ci gaba da amfani da Larabci. A wajena wannan babbar matsala ce, na ji cewa sosai akwai buk’atar d’aukar matakin da ya dace. K’warai akwai k’wararan dalilai masu yawa na za’ben Larabci: shi ne wanda ake amfani cikin dukkan makarantun Musulunci na k’asar; shi ne hanyar da ake rubuta adabi cikin k’asar; uwa-uba, shi ne hanyar rubutu da dukkan Musulmi suke girmamawa saboda asalinsa, da kuma zamansa sautukan da aka rubuta Alk’ur’ani mai girma da su. ‘Dabbak’a wani zai zan kamar an yi batali (watsi) da dukkan wad’annan dalilai masu k’arfi da kuma cin fuska ga addini, domin Hausawa Musulmi ne na sosai. Da wannan na tsabbace gefe, na kuma gamsu sosai cewa, in nuna k’yama ga wannan in za’bi nasu in kuma yi fafutuka don shigo da tsarin rubutun Romanci. Wannan ya fi sauk’in koyo ga yara bisa ga Larabci. (Miller, 1936: 200).

Idan aka yi la’akari da wannan bayani za a ga cewa, Likita Miller ya nuna k’yama ga adabin da suka sami Hausawa kansa. Ko da suka shimfid’a tsarin mulkinsu sun sami Hausawa sun gwane  ga rubuta Larabci da Ajami na wa’azi da sauransu wad’anda suke yi ta hanyar amfani da ayoyin Alk’ur’ani da hadisai. Fannonin addini da mu’amala masu yawa malamai sun yi rubutu kansu cikin Hausa da Larabci. Shi kuma Likita Miller wanda shi d’an Mishan ne na k’ungiyar CMS gurinsa shi ne samun wata hanya da za su shiga su yi tasiri cikin rayuwar Hausawa cikin ruwan sanyi. Sanin ta hanyar ilmi ne kad’ai za su sami haka, ya sa ya jajirce kan musanya sananniyar hanyar ilmin Hausawa da wata sabuwa ta Boko (Romanci). Ta wannan hanyar Hausawa za su nak’alci ak’idojinsu da al’adunsu da ke rubuce cikin sautukan Romanci. A wani littafin nasa ya fad’ad’a bayanin taron nasu inda ya ce,

...cikin tsarin ilmi wanda da ma H. E ya fara tunani kansa, wa ne abu zai zama k’a’ida ta rubutu? Shin za mu d’auki sautukan Larabci wad’anda da ma su ake amfani da su a dukkan yankin Arewa, rubutun adabin Musulmi, da Alk’ur’ani da hadisai ko kuma bak’ak’en Romanci wad’anda wata rana za su mayar da matasan Arewacin Nijeriya magada ga adabin Girkawa da Romawa da Yahudu (Judea) da ma sauran k’asashen duniya da suke da wayewar kai. Daga cikin manyan mutane da jami’an mulki wad’anda Lugga ya za’bo tare da shi, kusan duk sun goyi bayan Larabci ne. Na yi fafutuka sosai na kawo muhawarori masu zafi a tsare don goyon bayan bak’ak’e da rubutun Romanci. Na ga dukkanin alamu da ke nuna shi kansa gwamna yana goyon bayana, sai dai ya yi shiru ne tukuna... Kafin wani lokaci buk’atata ta biya, ina cikin farin ciki sosai ganin an amince da amfani da bak’ak’en Romanci. Na ga alamu sosai da suka nuna shi ma Gwamna yana goyon bayana, sai dai ya saurara ne kawai (1949: 28-29).

Adabin Girkawa da Romawa da sauran k’asashen Turawa su ne wad’anda Turawa ke ganin su ne na wayewar kan duniya. Likita Miller na sane da irin yadda lamurran adabin Hausawa ya ci gaba ta fuskar wak’ok’in wa’azi da ilmantarwa wanda yake na tsintsar addinin Musulunci ne. Idan gwamnatin mulki ta goya wa adabin baya, zai k’ara k’arfafa, ya hana wanda Turawan Mishan suke son bazuwarsa kar’buwa ga Hausawa. Wannan ya sa ya yi wa Turawan nuni ga abin da shi ne k’asashensu suke kansu. Da yake bori d’aya suke wa tsafi, sai shugaban taron ya bi bayansa, sauran su ma suka mik’a wuya.

Bayan k’are tattaunawarsu sai suka shiga lalaben wanda za a d’aura wa alhakin jagorancin fito da hanyar da za a bi don nasarar lamarin nasu. Wannan ya sa aka d’auko Hans Vischer (‘Dan Hausa). Hans Vischer ya fara shigowa k’asar Hausa ne a 1901 don aikin Mishan. A shekarar 1902 ya sauya riga zuwa mulkin mallaka. A shekarar 1908 ya gabatar wa gwamna rahotonsa kan lamarin bayar da ilmi ga Hausawa. A cikin rahoton ne ya bayyana ra’ayin musanya tsarin rubutun Ajami da na Boko. Ya yi haka ne domin a sami hanyar da za a sauya akalar adabin Hausa daga na Musulunci zuwa na duniya. Ga yadda ya tak’aita manufar tasa a lambar rahoton ta 2 b.

Ta hanyar k’arfafa karatun sautukan Larabci, hak’ik’a Gwamnati za ta taimaka watsuwar addinin Musulunci.

 

Idan aka yi nazarin wad’annan bayanai za a ga cewa, tunanin Turawa na samar da hanyar rubuta Hausa da sautukan Romanci (Boko) shi ne, sauya akalar manufar marubuta adabin Hausa cikin Ajami daga na addinin Musulunci zuwa na sharholiyar duniya cikin Hausar Boko. Wannan zai sa rubuce-rubucen Hausawa su dace da irin wad’anda Turawan suke so kamar na Girkawa da Farisawa da sauransu.

Bayan daidaituwar ra’ayin Turawa ga manufar sauya akalar adabin Hausa, sai suka shiga hidimomin bud’a makarantun boko da samar da littattafan koyon karatu cikin Hausa. Burdon ya bud’a tasa a Sakkwato a shekarar 1905. Miller ya bud’a ta CMS a Zariya a 1906. Hans Vischer ya bud’a ta yankin Arewa cikin birnin Kano a 1909 (Ozigi da Ocho,1981 ). Haka kuma a shekarar 1901 Miller ya wallafa littafin koyon Hausa mai suna Hausa Note. Shi kuma Hans Vischer a shekarar 1911 ya wallafa nasa littafin k’a’idojin rubuta Hausa mai suna Rules For Hausa Spelling. A makarantun na Boko aka ci gaba da koyar da yaran Hausawa karatu daga labaran da aka fassara na littafin Linjila da kuma littattafan tatsuniyoyi don kau da hankalin d’aliban da shagaltar da su daga adabin Musulunci da suka saba da shi da kuma gina wani sabon tunani cikin zukatansu. Haka Turawa suka ci gaba da koyar da Hausawa karatu da rubutu cikin Hausar Boko.

A shekarar 1919 Hans Vischer ya aje aikin mulkin mallaka. Wannan ya ba shi dama ya had’u da wasu Turawa da suka yi ayyuka daban-daban a sassan nahiyar Afirika suka kafa wata cibiya. Tunanin kafa cibiyar ya taso ne a lokacin taron Mishan da wasu Turawa da aka yi a High Leigh cikin Satumba 1924. A watan Satumba 1925 jami’an cibiyar suka amince su yi wani taro a School of Oriental Studies, London. A wajen taron aka samar da wani kwamitin gudanarwa, aka kuma ba Mr. Hans Vischer sakatare. A watan Yuni 1926 aka sake ba shi muk’amin mataimakin Darakta, aka kuma amince da kafa wannan cibiyar hukumance daga 1-7-1926. Daga cikin manufofin wannan cibiyar akwai kafa hukumar da za ta tattara bayanai don hukumomi da d’aid’aikun mutanen da ke da sha’awa ga ilmin harsuna da bincike-bincike da kuma aikin ilmi a cikin Afirika. Akwai kuma taimako don buga littattafan adabi na ilmi cikin harsunan Afirika. Domin a k’arfafa ‘yan Afirika su rik’a rubutu cikin harsunansu, a watan Disamba 1928 kwamitin ya yanke shawarar sanya gasar rubuta adabi cikin harsunan Afirika kuma daga ‘yan asalin Afirika. A shekarar 1931, aka za’bi harshen Hausa, aka kuma gabatar da wasu littattafai guda 5.[2] (Smith, 1934: 1-6). Abin da Turawa suka gani a wad’annan littattafai ya nuna hak’arsu ta kusa cimma ruwa domin Hausawa sun fara sarrafa fasaharsu su rubuta adabin da ba na Musulunci ba.

A nan cikin k’asar Hausa kuwa, tun a shekarar 1929 aka kafa Hukumar Fassara don a fassaro labarai daga wasu harsuna zuwa cikin Hausa. A shekarar 1932 wannan hukumar ta aza gasar rubuta k’agaggun labaran Hausa don ‘yan k’asa[3]. ‘Yan k’asa suka gabatar da littattafansu na hira da ba su danganci addinin Musulunci ba kai tsaye, aka za’bi guda 5 daga cikin su aka buga. Likita Miller ya bayyana sha’awarsu ga yadda hukumar ta fara samar da irin adabin da suke son Hausawa su rubuta. Ya ce,

Mr East na Hukumar fassara da ke Zariya ya fara wani aikin gwaji kuma ya cancanci goyon baya tare da sa idon k’ungiyoyin Mishan. Yana k’arfafa guiwar fitattun yara ‘yan makaranta da matasa da ke cikin manyan azuzuwan makarantu da kwaleji na gwamnati da ke Arewacin Nijeriya don su rubuta littattafai cikin Hausa. Tuni an fara samar da k’ananan littattafai a kan tafiye-tafiye da tarihi da k’agawa da kuma adabin baka, kuma suna ba mu mamaki ganin irin k’warewarsu da ingancin littattafan (Miller, 1936: 204).

Ta fuskar rubutattun wak’ok’in Hausa wad’anda kafin shigowar Turawa da shimfid’a manufofinsu cikin k’asar Hausa, dukkan wak’ok’in ana rubuta su ne kan jigogin addinin Musulunci, sai aka sami rukunin wasu Hausawa suka rubuta wak’ok’i kan jigogin al’amurran duniya daban-daban. Malam Alk’ali Haliru Wurno ya rubuta wak’ar Honda. Malam Aliyu Na Mangi ya rubuta ta Keke. Shi kuma Alk’ali Bello Gid’ad’awa ya rubuta ta Railway, inda Shehu Usman Aliyu Shagari ya rubuta wak’ar Nijeriya. Malam Abubakar Ladan ya rubuta wak’ar Had’in Kan Afirika. Tun daga wannan lokaci lamarin wak’ok’in Hausa ya d’auki wani sabon salo da jigo. Ana rubuta na addini tsantsa, ana kuma samun na duniya da soyayya da yabon wani mutum da siyasa da sauransu.

Idan aka dubi yadda lamarin rubuta adabin Hausa ya taso daga hannun Turawa da ire-iren abubuwan da suka shiga adabin , za a ga cewa, sauya akalar adabin ne babbar manufar Turawan. Sun sauya sautukan rubuta Hausa suka d’abbak’a wa Hausawa nasu, suka koyar da ‘yan k’asa rubuta adabin sharholiya, suka kuma fifita shi da kyautuka a maimakon na Musulunci. ‘Yan k’asa suka nak’alci dabarar rubuta adabi kan kowane abu na duniya. Wannan ya sa wasu masu yawa musamman matasa ‘yan boko suka karkata tunanin rubutunsu daga addini zuwa wani abu daban. Da yawa wasu kan shirya adabin nasu don neman abin duniya ko neman suna ko bayyana wani abu sabon shigowa k’asar Hausa da dai sauransu. Haka yanayin adabin Hausa ya ci gaba har zuwa yau.

4.1       Kammalawa


Saduwar Turawa da Hausawa da kuma shigarsu cikin samar da adabin Hausa tun kafin mulkin mallaka da bayansa ya sa adabin ya k’ara fad’ad’a da k’ara watsuwa cikin duniya. Ayyukan da Turawa suka yi na koyar da Hausawa wasu sababbin hanyoyin rubuta adabin Hausa da kafa hukumomin inganta shi wani muhimmin abu ne da ya taimaka ga taskace adabin da kuma ci gaba da wanzuwar rayuwarsa. Manufofin da suka ja Turawa ga wannan aiki, manufofi ne da ba za su yi nasarar su ba in har ba da shiga cikin adabin Hausa da aiki kansa ba. Shigarsu cikinsa ya sa manufofinsu suka wanzu, suka kuma kai ga nasara. A tak’aice, mak’alar nan ta tattaru ne kan bayanin wad’annan manufofi da yadda Turawa suka yi amfani da wasu hanyoyin amfani da adabin Hausa suka cimma nasara. Wannan zai ba wasu manazartan wannan k’arni na 21 haske dangane da yadda Turawa suka inganta adabin Hausa don kai ga muradinsu. Sun cimma manufofinsu  na sauya tunanin wasu marubuta cikin Hausa daga abin da suka taras na rubuce-rubucen Musulunci tsantsa zuwa ga rubutu irin na tunanin duniya. Da wannan sai a shigo da wata sabuwar kafa da tunanin daidaita akalar adabin Hausa na yau don ya dace da muradun al’ummar Hausawa a wannan k’arni.

 

 

Manazarta


 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

[1] . Malamai uku da Robinson ya jingina wa wak’ok’in su ne, Muhammadu na Birnin Gwari da Malam Halilu da ya ce shi ne Limamin Ced’iya da Shaihu Usmanu ‘Danfodiyo.

[2] . Littattafan su ne, Hausa Stories na H. B. G. Nuhu da Hausa Stories na Malam Dodo da Zaman Dara na Malam Ahned Mettenden da Takobin Gaskiya na Malam Nagwamatse da Littafin Karatu na Hausa na Malam Bello Kagara.

[3] . An sauya sunan Hukumar Fassara zuwa Hukumar Talifi ne daga ranar 2 ga watan Afrilu na shekarar 1937. Don ganin cikakken bayanin a dubi Usman, L. R. (2011) mai taken Hukumar Talifi: Tsettsefe Tarihi Da Gudunmuwarta Wajen Ha’baka Rubutaccen Adabin Hausa. Kundin digiri na biyu, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.