Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Aliyu Magatakarda Wamakko Mai Suna Gwamnanmu Mun yi Mun Kare (Alhaji Musa Danba’u Gigan Buwai)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Rubutawa: Shehu Hirabri
08143533314

 
Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Wasƙar ga tamu mun soma ta,

Mun fara ta da roƙon SAllah,

In Allah ya so ya yarda,×2

Yara:    Gwamnanmu mun yi mun ƙare.

 

Amshi:   Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora:  Baba in dai kana shirin yaƙi ka fito,

In ka ga ba ka yi ka gaya min,

Siyasar jahar ga in bar ta,

Yaƙi sai da uwa ɗan Barade ×2

Yaƙi babu uwa banza ne,

Yara:     Har ƙara ma zaman karta.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 
Jagora: Ni na tabbata kana da basira,

Na sani kana da tunani,

To amma fa ka ƙara kulawa,

Angulu munahukin Allah ne, ×2

Yara:   In ka ganai wurin yaƙi,

Shi ba da gaske ya zo ba.

 

Amshi:  Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

Jagora: Mun san masu takarar gwamna,

‘Yan takara zama mun san su,

‘Yan shaye-shaye mun san su,

Mun bar wane ɗan wiwi ne, ×2

Yara:  Can nig ganai cikin lungu,

Ya la’be ana yi mai moli.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Tun sadda wane yai gwamna,

Martaba jaharmu ta hwaɗi,

Mai ilimi da marar ilmi,

Dole ne a samu bambanci,

Ku Sakkwatawa albishirinku,

Ga ɗan uwanku nan ɗanku,

Shi za ya takarar gwamna,

Ku daure ku ba shi goyon baya,

Yara:   In Aliyu ya zamo gwamna,

Martabar jaharmu ta tashi.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Yanzu kowa ka cin amanar jama’a,

A kwan a tashi ‘Danba’u,

Sai ka ganai cikin tarko,

Tarkon da ba  ya hishshe shi,

Ji wanda a cikin jama’atai,

Sai ga shi yanzu ya bar su,

Waɗanga nan da ya samu,

Ya biɗo abarba don ya raba musu,

Yara:   Sai ga abarba tai tsutsa.

 

Jagora: Da ya biɗo abarba don ya raba musu,

Yara:    Sai ga abarba tai tsutsa.

Jagora: Sakkwato mun canza masu suna,

Ba ‘yan abarba a sunansu ba,

Yara:  ‘Yan tukuwa ɗiyan ɗiɗi.

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,

Birnin da ƙauye na duba,

Kuma manya da yara na duba,

Yara:    Duk inda ka ishe ɗan abarba,

Ya iya shirin munahucci.

 

Jagora:  Wannan,

Yara:     Ya iya shirin munahucci.

 

Amshi:  Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

 

Jagora:  Ni ‘Danba’u hamdullahi,

Na yi godiya wajen Allah,

Siyasar su wane ta watce,

Yau shekara takwas suna mulki,

Girman sakarakuna sun kasai,

Ga ɗan talakka ya sha ƙwaya,

Wai za ya kori sarkinmu,

Kahin ya kori sarkinmu,

Allah ya biya buƙatunmu, ×2

Yara:    Sai ga sakamako ya yi,

Shi ya rigaye hisshe shi.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora:  A yanke mutum a yanke dabba,

Don tattalin baƙin tsahi,

Don ɗai a hau kujerar mulki ×2

Yara:    In lokacinka  ya ƙare,

Tsahinka duk na banza ne.

 

Jagora: Wawa,

Yara:    In lokacinka ya ƙare,

Tsahinka duk na banza ne.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora:  Ga magatakrda ga Muntari,

To amma fa ku ƙara kulawa,

In dai abin rabo ya samu,

A damƙa ma masu imani ×2

Don kada a baiwa kuraye shi ya,

Yara:    In sun haɗe shi an huta.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

Jagora: Mu Sakkwatawa sannu da aiki,

A gaishe ku Sakkwatawan Shehu,

Na gaishe ku Sakkwatawan Shehu,

Na tabbata kuna da ɗiyauci,

Domin abarba kun ƙi ta,

Sai yawo sukai suna ƙarya.

Yara:    Sun rikirkice musa,

Sai hwaɗa sukai da junansu,

Harkarsu ta yi dameji.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora:  An tsaida wane takarar gwamna,

Kare mai baƙin jini da yawa,

Yara:    Du inda ya bi ya hurce,

‘Yan yara na yi mai yihu.

 

Jagora: Yihu kare.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Ina ɗan buga-buga wane,

Ya leƙa Gabas ya leƙa Yamma,

Ya leƙa Gusun ya leƙa Arewa,

Kullum wurin muna hucci,

Ba Sakkwato noz ba da Sakwkato,

Yara:   Ko isa mun hi ƙarhinsa.

 

Jagora: Wawa,

Yara:    Ko Isa mun fi ƙarfinka.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Kowa tasu tare da manya,

Ka san yana da tarihi,

Don haka manya sunka gaya mini,

Yara:   Danginsu Maguzawa ne.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Na iske wane na ta jawabi,

Ya ce Sakkwato duk kaji muke,

Shi bai biɗar mu sai ran za’be,

Nan take za ya jawo mu,

Yara:   Yanzu talakawa sun gane,

Nerarka ba ta jawo su.

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Ku ƙara shiri in za ku shirawa,

Ku ja ɗamara in za ku shirawa,

An ce mahaukaci ya ratce,

Ya shedi ba ya kaffara,

Sai ya yi gwamna Sakkwato binni,

In kunka yarda yai gwamna,

Yara:   Irinta dauri ta dawo,

Har yau muna cikin ƙangi.

 

Jagora: Idan ka gane ni da manyan kuɗɗi,

Aljihuna ya cika damfam,

Yara:   To kar ka tambaya Malam,

Tambarin Tahida yab ba mu.

 

Jagora: Idan ka ga babura sababbi,

An lodo an kai Illela,

Har ana biɗar gidansu ‘Danba’u,

Yara:   To kar ka tambaya malan,

Yahaya Buhari yab ba mu.

 

Jagora: Idan ka ga riguna sabbi,

Aska biyu ɗunkin Zazzau,

Yara:    To kar ka tambaya malan,

Ladan na Shuni yab ba mu.

 

 

Jagora: Na gaishe ka ciyaman fati,

Arzika Tureta ɗan girma,

Ka taimaka ma ‘ya’yan bunni,

Ka taimaka ma ‘ya’yan ƙauye,

Gulbi babu jira sai kwalhwa,

Yara:   Kowa ishe ka ya samu.

 

Jagora: Baba,

Yara:    Kowa ishe ka ya samu.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau walaƙanci.

 

Jagora: Idan ka gane ni da babba mota,

Kuma motar nan tsadadda ce,

Kuma motar nan mai tsada ce,

To Muntari ka sai mini mota,

Yara:    To kar ka tamaya malam,

Na ishe mataimakin gamna.

 

Jagora: A gaishe ka mataimakin gwamna,

Ga jikan Mahmadu Gummi nan,

Ɗan malam kake jikan Malam,

Yara:   Yaƙinka ya yi rinjaye.

 

Amshi: Ɗantakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka ɗau reni,

Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.

Jagora: Na gode wa Haji Muntari ɗan Bello,

Yara:    Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A Ɗalha Sidi Uban ‘Danba’u,

Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora Alu A.A. Alu ɗan boko,

Yara:   Duk yanda ya yi ya kyauta.

 

Jagora: A gaishe ka mai matasan bunni,

A gaishe ka mai matasan ƙauye,

Nasiru Itali na gode ma,

Yara:    Duk yanda ya yi ya kyauta.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments