Tauhidi A Bakin Makadan Baka Na Hausa

    Daga
    Umar Aliyu Bunza
    Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
    aliyubunzaumar@yahoo.com
    07063532532, 08095750999
    www.amsoshi.com

    1.0  Gabatarwa


    Tauhidi shi ne kad’aita Allah Ta’ala da bauta tare da amincewa da dukkanin abin da ya jingina wa kansa na sunaye da siffofi da ayyuka. Tauhidi ne abu na farko da ke tabbatar da kasancewar mutum Musulmi. Kad’aita Allah (tauhidi) shi ne ginshik’i na farko mai k’arfi da addinin Musulunci yake kansa. Don a kad’aita shi (Allah) ne ya aiko Annabawa da manzanni masu yawa daga zamanin Annabi Adamu (AS) zuwa Annabi Muhammadu (S A W). Bayan tauhidi sai sauran ayyukan ibada kamar Sallah da Azumi da Zakkah da Hajji da sauran al’amurran zamantakewa.

    Al’ummar Hausawa mutane ne da suka kasance Musulmi, kuma masu rik’o da tauhidi cikin kowane lamari nasu. Wannan ya sa kowane abu ya faru mai kyau ko maras kyau, Bahaushe kan danganta kasancewar abin daga Allah (S W T). Mawak’an baka wani rukuni ne cikin Hausawa da ke da cikakken tasirin Musulunci cikin rayuwarsu. Wannan tasirin ya kasance wani muhimmin abu har cikin wak’ok’insu. Kasancewar tauhidi ginshik’i babba cikin rayuwar Musulmi, ya sa mawak’an bakan suke tsarma tauhidi cikin wak’ok’in. Suna yin haka ne saboda wani lokaci su yi wa al’umma wa’azi da fad’akarwa. Wani lokaci kuma suna yi saboda tasirin Musulunci da kuma k’arfin imaninsu ga kasancewar Allah mai iko kan komai da kowa, kuma mai aikata abin da ya so, da kuma kasancewar Allah abin dogara da neman biyan buk’ata da kuma kariya.

    Manufata a wannan mak’ala ita ce nazarin tauhidi da ke k’unshe cikin wasu d’iyan wak’ok’in mawak’an baka na Hausa. Duk da yake daga cikin wak’ok’i ne zan duba tauhidi, na kauce  wa kawo ma’anar wak’a da tarihinta domin wasu masana da manazarta (‘Dangambo, 1981 da 2007 daYahya, 1997 da  Gusau, 1993 da 1996 da Ibrahim, 1983 da Isma’ila, 1998 da Lere, 1987 da Gumel, 1992 da sauransu) sun riga sun yi rubuce-rubuce kan wannan. Don haka wannan mak’alar ta fara da duba tauhidi.

    2.1       Ma’anar Tauhidi


     

    Sanin ma’anar tauhidi abu ne mai muhimmmanci ga kowane Musulmi. Idan Musulmi suka san tauhidi, suka kuma kiyaye shi, zai zama mataki na farko na kiyaye tanade-tanaden Ubangijinsu da kuma bauta masa bisa hak’ik’a. Wannan ya sa wasu masana lamurran Musulunci suka dubi matsayin tauhidi a Musulunci da kuma k’unshiyarsa suka fito da ma’anoni daban-daban gwargwadon fahimtarsu. Ga kad’an daga cikinsu. A cewar Wazirin Kano (1980: 8):

     

    “Tauhidi shi ne tabbatar da samuwar zati, k’adiri, mai siffofin kamala, tsarkakakke daga kowace irin tawaya da kowace irin nak’asa wanda bai yi kama da komi ba, kuma babu wani abu da ya yi kama da shi ta kowace fuska da kowane hali”

     

    A tak’aice, idan aka yi la’akari da wannan ma’ana ana iya cewa tauhidi shi ne tabbatar da samuwar Allah Mad’aukakin Sarki mai kowa mai komai tare da bauta masa shi kad’ai ba tare da tarayya da komai ba a cikin kowane nau’i na bauta masa ba da kuma sakankancewa ga samun sakamako ga yi masa bauta da kuma azaba ga yi masa tarayya a bauta.

    3.1       Rabe-Raben Tauhidi A Musulunci


    Tauhidi ya mamaye dukkan rayuwar Musulmi wanda hasali ma shi ne k’ofar da ake shiga addinin Musulunci daga gare ta. Wasu malaman Musulunci kamar Asimina (1980) ya karkasa tauhidi zuwa gida uku kamar haka:

    1. i) Tauhidur-Rububiyyat (kad’aita Allah da ayyuka) wanda shi ne tauhidin kad’aita Allah da ayyuka misalin halitta, da azirtawa, da rayuwa, da kashewa, da juyar da al’amurra, da kawar da cuta, da makamancin wad’annan. Wannan nau’in hak’ik’a kafirai sun yi ik’irarinsa tun bisa lokacin manzon Allah (SAW) amma bai shigar da su  cikin Musulunci ba.

    2. ii) Tauhidul-uluhiyyat (kad’aita Allah da bauta) shi ne na kad’aita Allah da bauta misalin, addu’a, da yanka, da alwashi, da neman taimako, da neman tsari da wanin wad’annan. Wannan nau’i na tauhidi shi ne wannan da kafirai suka yi musun shi, kuma jayayya ta kasance a cikin shi take tsakanin mazanni da al’ummunsu tun daga Nuhu amincin Allah ya tabbata gare shi har zuwa ga Annabibimmu Muhammadu sallalahu alaihi wasallam.


    iii)       Tauhidul-Asma’u was-siffat. (kad’aita Allah da sunaye da siffofi) wannan na nufin mik’a wuya (imani) ga dukkan abin da ya tisgo (ya zo) a cikin Alk’ur’ani mai girma da hadisai ingantattu na daga sunayen Allah da siffofinsa wad’annan da ya  siffanta kansa da su, ko manzonsa ya siffanta shi da su a kan hak’ik’an (tabbaci). Wad’annan su ne muhimman kashe-kashen tauhidi da malaman Musulunci suka yake kansu.

    4.1       Tauhidi A Bakin Makad’an Bakan Hausa


    Tauhidi abu ne da ya zama ruwan dare cikin wak’ok’in makad’an Hausa saboda tasirin Musulunci a zukatansu.  An yi k’ok’arin  kawo misalan tauhidi ta hanyar bijirowa  da d’an wak’a da ake ganin akwai tauhidin a ciki tare da bayanin sa domin hak’a ta cim ma ruwa. Ga misali, Alhaji Musa ‘Dank’wairo yakan sanya tauhidi a cikin wak’ok’insa a wurare da dama. A wak’arsa ta Ado Bayero wadda ake yi wa amshi da ‘Barkak ku da taurin gaba, na yarda da Sarki Ado’  akwai tauhidi kamar haka:

    ‘Gaskiya na nan ga wurinta,

    Mutane mu yarda da Allah,

    Wanda duk yay yarda da Allah,

    Ka san wannan bai ta’bewa’

     

    Al’amarin yarda da Allah, tauhidi ne da ya game duk kashe-kashen tauhidi.  Wannan d’an wak’an ya game yarda da samuwar Allah, da kad’aita shi da bauta, da ayyuka da duk wani abin da ya k’unshi mik’a wuya ga Allah.  Haka kuma, makad’in ya bayyana sakamakon duk wanda ya tsai da k’afa ga yarda da Allah a d’ango na k’arshe na rashin ta’bewa koyaushe.

    A wak’arsa ta ‘Mai dubun nasara garnak’ak’i Sardauna’ nan ma ‘Dank’wairo ya shigo da tauhidi inda yake  cewa:

    ‘Tun da Allah shi ya hukunci bawa nai,

    Shi ka ba shi komai,

    Kuma shi ka hana mai,

    ‘Yan uwa ku rik’a,

    Ba k’arfi nai na ba,

    K’arfin Allah ne’

     

    Wannan d’an wak’a ya k’unshi tauhidi na kad’aita Allah da ayyuka. Hukunta kowane lamari ya wanzu, ya tabbata abu ne da ya kad’aita ga Allah kawai. A nan mawak’in ya bayyana Allah a matsayin mai hukunta komai ta hanyar bai wa bawansa komai, ko hana mashi.  Haka kuma ya nuna ko da mutum na da wani abu ya san ba k’arfinsa ya ba shi ba, sai dai k’arfin Allah wanda imani da haka tauhidi ne tsayayye, kuma ingantacce.

    Bayan ‘Dank’wairto, shi ma Narambad’a sanannen makad’i ne da ke amfani da salon wa’azi da fad’akarwa a cikin wak’ok’insa. Wannan ya sa al’amarin tauhidi ya zama abu mai sauk’in gani da yawanci ake tsinta cikin wasu wak’ok’insa. Ga misali, a wak’arsa ta Sarkin ‘Burmin Moriki Muhammad, Narambad’a ya sanya al’amarin tauhidi a inda yake cewa:

    ‘Jahilci rashin sanin Allah,

    Abu dai in ya taho,

    Ga Allah aka mai sai’

     

    Wannan d’an wak’a babu shakka ya bayyana al’amarin tauhidin kad’aita Allah da bauta ne. Mai da dukkan abin da ya zo ga Allah al’amari ne na kad’aita Allah da bauta ta hanyar imani da k’addara mai kyau, ko maras kyau duka abu ne daga Allah.

    A wak’ar Gamda’are Sarkin Kudu Ali, nan ma Narambad’a cewa ya yi:

    ‘Batun Allah mu shi muka biya,

    In Allah ya za’bi abin da kash shukka,

    Ka san shina hita.’

    A cikin wannan d’an wak’a an samu tauhidin kad’aita Allah da ayyuka ta inda makad’in ya bayyana Allah a matsayin mai za’ben abu da kuma tabbatar (fitar) da shi.  Bayan wannan ma akwai kuma tauhidin nan na kad’aita Allah da siffofinsa. Hakan zai inganta ganin yadda makad’in ya bayyanar da bin maganar Allah wanda magana na cikin siffofin Allah Mad’aukaki.

    Shi ma Aliyu ‘Dandawo fitaccen makad’in fada ne da ke k’ok’arin fito da tasirin addininsa na Musulunci a cikin wak’ok’insa da dama. Saboda haka, ba zai zama abin mamaki ba a ga lamarin tauhidi ya fito a cikin wak’ok’insa. A wak’arsa ta Tukur Sarkin Yauri Aliyu ‘Dandawo ya kawo lamarin tauhidi yana cewa:

     

    ‘Tukur ka yi don Allah,

    Shi ka bari don Allah,

    Halinka ba d’ai da halin na yau ba tun can hwarko,

    Abin da duy yas same shi bai cewa wani yay yi mai,

    Ga Allah shi ka dogara,

    Shi ko tuban mai,

    Abin da duy yas samu shi tabbata,

    Allah yan nuhwai shi tun farko.’

    Ilimin tauhidi ne ya mamaye wannan d’an wak’a kuma ya k’unshi tauhidi na kad’aita Allah da bauta ne. Tun farko, ana iya fahimtar tauhidin ta inda mawak’in ya bayyana duk abin da ya samu ba maganar wani ya yi sai dai ya mai da lamarin ga Allah. Ya kuma nuna cewa, Allah ne ya nufa tun farko hakan ya kasance. Haka lamarin tauhidin kad’aita Allah da bauta yake. Bawa ya san Allah yake hukunta masa komai, ba wani halitta daban ba.

    A wani d’a na wannan wak’ar ga yadda Aliyu ‘Dandawo ya sake fito da tauhidi a inda yake cewa:

    “Ka ga komi tsananin hwari,

    kana ishe tohwahiya da kunnuwa na d’anya,

    Cikin sarautar Allah ta rayu ba da ruwa ba,

    Allah bai yi sarautad da za a koyo nai ba.”

     

    Rayawa da kashewa abu ne da ke hannun Allah Mad’aukakin Sarki. Allah yakan raya abin da ya ga dama koda kuwa a muhallin da ba a al’adanci rayuwar abin ba. Yakan kuma kashe abin da ya ga dama duk da irin tanade-tanaden da aka yi masa na d’orewar rayuwarsa. Yarda da haka ga mutum, tauhidi ne na kad’aita Allah da ayyukansa. Ke nan wannan d’an wak’a ya taro sha’anin tauhidin kad’aita Allah ne da ayyuka. Hakan ya tabbata ne bisa ga la’akari da yadda ya k’unshi al’amarin ikon Allah na raya wani tsiro ba tare da ruwa ba wanda ko shakka babu yana daga cikin ayyukan da Allah ya kad’aita a kansu. Idan fari ya tsananta, kowane tsiro na mutuwa, amma ita tunfafiya koyaushe tana d’anyar ta kamar babu fari. Wannan k’arfin iko na Allah ne kawai kamar dai yadda ya halicci Annabi Adamu (AS) ba uwa ba uba, ya kuma halicci Annabi Isah (AS) da uwa kawai ba uba.

    Mamman Shata shi kuma makad’in jama’a ne da ya yi fice sosai a wak’ar Hausa. Mamman Shata yakan sanya tauhidi a cikin wak’ok’insa a wajen k’ok’arin warware jigon wak’arsa. Ga misali, a wak’arsa ta Ado Bayero wadda ake yi wa amshi da ‘Ado na Kano ‘Dan Abdu’  Yana cewa:

    ‘Ka ji birnin Kano har daji,

    Allahu wanda ya yi ta,

    Ado na Kano yab baiwa.’

     

    A wanna wuri, ana iya fito da tauhidin nan na kad’aita Allah da ayyuka inda mawak’in ya yi bayanin cewa, Allah ne Mahaliccin da ya halitta Kano, kuma shi ne mamallakin mulki mai ba da mulki da ya ba da sarautar Kanon ga Ado Bayero.

    Wani makad’in jama’a da ake samun tauhidi cikin wak’ok’insa shi ne Sani ‘Dan-Indo. A wak’arsa ta ‘Mai mai da tasha sabuwa’ ‘Dan-Indo cewa ya yi:

    ‘Sani nay yi tunani na sani,

    Mai tunani na sani,

    Shin wa ka baje ma wuri,

    Allah d’ai ka baje ma wuri.’

     

    Tauhidin da yake  k’unshe cikin wannan d’an wak’a shi ne tauhidin kad’aita Allah da ayyuka.  Tauhidin zai tabbata ta kallon yadda makad’in ya bayyana Allah ne kad’ai ke iya wa mutum wuri, ya ba shi dama ya yi abin da yake so. Yarda da wannan tauhidi ne tsayayye a addinin Musulunci. A wata wak’ar tashi ta Garba Abu kuwa cewa ya yi:

    ‘Na ji abin mamaki a’a Garba Abu,

    Ka ji abin tarihi a’a Garba Abu,

    Wasu ‘ya ‘ya sun ce da Aljani nika aikin ga,

    Wasu ‘ya ‘ya sun ce da malamai nika aikin ga,

    Wasu ‘ya ‘ya sun ce da ilimi nika aikina,

    Wasu ‘ya’ya sun ce da boka nika aikina,

    Su san da komi Allah ya ce,

    A yi shi don ya zan ba illa.’

     

    Babu shakka, za a iya hango tauhidin nan na kad’aita Allah da ayyukansa a cikin wannan d’an wak’a. Al’amarin tauhidin zai iya tabbata ganin yadda mawak’in ya mik’a lamarin fasaharsa ta w ak’a ga hukuncin Allah. Yarda da cewa, duk abin da Allah ya ce shi ke tabbata da kore kowane abu kan haka, tauhidi ne tabbatacce a Musulunci.

    Bello ‘Dan Sha-biyu na cikin makad’in Hausa da ke sanya lamarin tauhidi a wak’ok’insa. Ga misali, a wak’arsa ta motar siyasa cewa ya yi:

     

    ‘To Allah shi ka canza mutum,

    A in bai canza mutum ba,

    Na san kowa ba ya canza shi.’

     

    Lamarin canza mutum abu ne wanda ya tak’aita ga ikon Allah kawai. Yarda da haka abu ne da ke kyautata imanin Musulmi da kuma inganta tauhidinsa. Ke nan wannan d’an wak’a yana d’auke ne da tauhidin kad’aita Allah da ayyuka, inda makad’in ya tabbatar da Allah ne kad’ai mai canza mutum. Allah ya kad’aita ga wannan domin shi ne muk’allabil k’ulub kuma mudabbirul amri. Haka kuma duk wanda Allah bai canza ba, hak’ik’a ba wani wanda zai iya canza shi.

    Shi kuma ‘Dan’anace sanannen makad’in maza ne da ya yi fice sosai a k’asar Hausa musamman a wak’ok’insa na dambe.  ‘Dan’anace mawak’i ne da ke shigowa da tauhidi a cikin wak’ok’insa musamman saboda tauhidi shi ne ginshik’in addininsa na Musulunci.  Ga misalan tauhidi a cikin wasu wak’ok’insa.

    ‘Bismillahi Alhamdu,

    Mun gode ma Allah

    Kyawon d’an Musulmi

    Ya san Allah guda na.’

     

    Sanin Allah d’aya ne da sakakancewa kan haka shi ne k’ololuwar tauhidi. Wannan d’an wak’a ‘Dan’anace ya kawo tauhidin kad’aita Allah da sunayensa da siffofinsa ta inda ya bayyana ingantacciyar siffar nan ta Allah Guda (Ahad) wanda ba ya da abokin tarayya ta kowane gefe. ‘Dan’anace  har kuma ya bayyana cewa, yin imani da kasancewar Allah shi kad’ai shi ne daidai ga d’an Musulmi. A wani d’an kuma ‘Dan’anace na cewa:

    ‘To Allah shi ad da mutane,

    Allah shi ad da iyawa,

    Kuma Allah shi yay yi sarki,

    Yay yi talakka,

    Yay yi makafi, yay yi guragu,

    Yay yi talakawa, yay yi matsaci.’

     

    Babu shakka, wannan d’an wak’a ya ginu ne a kan tauhidin kad’aita Allah da ayyukansa ta la’akari da yadda makad’in ya bayyana Allah a matsayin Mahalicci, kuma mai cikakken ikon halitta abubuwan halitta daban-daban. Da ikonsa ya halitta mutane aji daban daban kamar sarakai da makafi da guragu da talakwa da sauransu.

    Shi ma makad’a Muhammadu Gambo makad’in maza ne da ya yi fice musamman a wak’ar ‘barayi.  Ko da ya ke makad’in ‘barayi ne, akan sami tauhidi a cikin wak’ok’insa wanda zai tabbatar muna da cewa, komai munin wak’a in dai daga bakin Musulmin Bahaushe ta fito, to ba za a rasa tsarmin lamarin tauhidi ba a cikin ta. Tasirin Musulunci a rayuwar Gambo ya sa wani lokaci yakan yi amfani da salon wa’azi da fad’akarwa a wak’ok’insa.  Ga misali, a wak’arsa ta Inuwa ‘Dan Mad’aci, Gambo cewa ya yi:

    ‘Wanga ba wada Allah bai iya ba,

    Ko mis same ka a filin duniyag ga,

    Kak ka kuka da kowa wanga dangana,

    Halik’u Allah ke matsama.’

     

    A nan Gambo ya fito ne da tauhidin kad’aita Allah da ayyuka ta inda ya bayyana Allah a matsayin mai ikon aikata komai.  Haka kuma ya bayyana cewa,ba wani a fad’in duniya da zai iya sa wani abu ya sami mutum face Allah kawai.  Saboda haka, duk wani abin da ya sami mutum, ya dangana ya bar wa Allah kawai. Samuwar irin wannan tunani a zucci na tabbatar da kad’aita Allah da yarda da k’addarorinsa. A wani  baitin da ke cikin wak’ar Jibirin Mugun Tsoho a gunduwoyin k’arshe da ke d’auke da mai da jawabin wata mata ga ‘barawon da ke yi mata barazanar kashi, Gambo ya kawo tauhidi inda yake cewa,

    ……………………………….

    ‘In ya yi tunani sai ya dangana,

    Don ba wani kuka za shi yi ba,

    Ya ce haka Allah yah hukunta,

    Kowa ajali nai na tahowa.’

     

    A nan ma Gambo ya sake bayyana tauhidin kad’aita Allah da ayyukansa ne ta hanyar bayyana dangana da abin da Allah ya hukunta. Mik’a wuya da ga abin da Allah ya k’addara ga bawa, tauhidi ne da ke kan kad’aita Allah da ayyukansa.

    Shi kuma Amali Sububu makad’in sana’a ne da ya yi fice a wak’ok’in noma kuma wanda a cikin wak’ok’in yake sakad’a lamarin tauhidi. Ba wani abin mamaki  ba ne ganin Amali Sububu na sanya tauhidi a wak’ok’insa saboda akwai tasirin Musulunci tare da shi.  Ga abin da ya ce a wak’arsa ta Isah Mai Kware mai amshi kamar haka:

    ‘Allah Ubangijinmu hiyayye mai sama,

    Jabbaru Mai dare Mai rana Halik’u,

    Na gode mashi,

    Da yai man lafiya,

    Da hura ta yah had’a,

    Sutura ta mai sama,

    Kud’d’ina Halik’u,

    Mui ta zaman duniya,

    Kahin lahira ta ce musu,

    Ta amshe musu,

    Jatau duniya,

    Ba komi ba ce.’

     

    Idan aka yi la’akari da abin da ke cikin wannan d’an wak’a, za a iya ciro nau’in tauhidi biyu a cikinsa.  Na farko shi ne tauhidin nan na kad’aita Allah da sunayensa da siffofinsa inda makad’in ya jera siffofin Allah a d’angaye uku na farko.  Daga nan kuma sai makad’in ya juya akalarsa zuwa ga fito da tauhidin nan na kad’aita Allah da ayyukansa inda makad’in ya bayyana Allah a matsayin mai baiwa ga kowane abu kamar ba da lafiya da abinci da arziki da sutura da sauransu. Ya kuma tabbatar wa Allah siffarsa mai halitta (halik’i).

    Haruna Uji shi kuma fitaccen makad’i ne a fagen sha’awa. Kasancewar sa Musulmi ya sa ake samun tauhidi a wak’ok’insa.  Ga misalin tauhidin a wak’arsa ta Bak’ar Rama inda ya ce:

    ‘Komi da ka duba,

    Sha’anin Allah ne,

    Arziki da karatu,

    Wannan nufin Allah ne,

    Da dukiya da hak’uri.’

     

    Idan aka yi nazarin abin da yake k’unshe a wannan d’an wak’a za a ga cewa Haruna Uji ya yi kawo tauhidin kad’aita Allah da ayyuka ne ta inda ya bayyana duk abin da mutum ya duba ya gani, ya san sha’anin Allah ne. Yarda da kasancewar komai cikin yarda da k’udurar Allah abu ne da ke tabbata tauhidin Musulmi. Allah cikin k’udurarsa ya halitta komai. Ba wani abu zai kasance idan ba da k’udurar Allah ba. Wannan kuwa ya had’a da dukiya, da karatu, da arziki da hak’uri da ma sauran abubuwan da bai kawo ba.

    Da yake a nan ne aka cimma k’arshen misalan tauhidia cikin wasu wak’ok’in makad’an Hausa, ana iya cewa, misalan tauhidi da aka samu a rukunan wad’annan makad’an sun yi k’ok’arin fito da nau’o’in tauhidi wanda idan aka yi nazari za a ga ba tauhidi ne manufar, ko sak’on wak’ok’in ba, sai dai don kasancewar sa tauhidi abu ne wanda tun farko muka nuna yana tafiya da rayuwa gaba d’aya ya sa suka shigo das hi cikin wak’ok’in nasu. Wato abu ne mai wuya Musulmin mawak’i Bahaushe ya bud’e baki ya yi wak’a har ya k’are bai ambaci wani nau’i na tauhidi ba.

     

     

     

    5.1      Kammalawa


    Idan aka yi la’akari da misalai da bayanai da mak’ala ta zo da su, za a ga cewa, lamarin tauhidi abu ne babba, kuma mai tasirin gaske cikin rayuwar Hausawa. Wannan ya kasance ne ganin cewa, ko da yake ana kallon wak’ok’in bakan Hausa matsayin sharholiya, kuma na raha, amma kuma sai ga shi ana tsintar batutuwan tauhidi masu yawa cikin wak’ok’in. Haka na k’ara tabbatar da cewa, lamarin tauhidi ta kowace fuska aka dube shi, abu ne da ya yi kaka-gida cikin rayuwar mawak’an bakan Hausa. Irin wannan kaka-gidan ta sa ko da ba don Musulunci kai tsaye suke shirya wak’ok’insu ba, amma kuma tauhidi na shiga da fice da kuma giittawa cikin wasu d’iyan wak’ok’in nasu.

     

    Manazarta


     

     

     

    https://www.amsoshi.com/contact-us/

     

     

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.