https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

Daga


         Umar Aliyu Bunza


Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato


aliyubunzaumar@yahoo.com


07063532532, 08095750999https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Tsakure


Aikin samar da rubutaccen adabin Hausa wata hikima ce da Allah ya ba wad’ansu mutane cikin bayinsa. Wasu cikin marubutan sun yi fice, an ji su har ana nazarin ayyukansu a ilmance wasu kuma ba su sami wannan gatancin ba. Isa Rasco Dangoma na cikin marubuta da ba a san da ayyukansu ba a fagen ilimi duk da yawan rubuce-rubucensa da ya fara daga shekarar 1994. Daga wannan shekarar zuwa yau, ya samar da wak’ok’i da k’agaggun labarai da fim masu yawa, amma ba a sami wani da ya yi nazari kan adabin nasa ba. Ba shakka, adabin nasa na buk’atar nazari domin a fito da hikimomin da ke ciki, ya kuma bi sahun takwarorinsa. Manufata a wannan mak’ala ita ce sharar fage a nazarin adabin Isa Rasco Dangoma.

Gabatarwa


Nazarin rayuwa da adabin wani mutum abu ne da manazarta suka dad’e suna yi. Manazarta da yawa (‘Dangambo, 2002 da Usman, 2008 da Maiyama, 2008 da Malumfashi, 2009 da Adamu, 2009 da Bunza, 2009, da Bunza, 2012 da da Isah, 2013 da Bunza, 2014 da sauransu) sun yi ayyuka kan adabin d’aid’aikun mutane. Wannan ya nuna aiki kan wani adabi da adabinsa abu ne mai muhimmanci. Isa Rasco Dangoma wani matashi ne mai shekaru 41 da Allah ya yi wa hikimar shirya rubutaccen adabi. Ya rubuta wak’ok’in Hausa da k’agaggun labarai masu yawa, ya kuma shirya finafinan Hausa. Adabinsa ya kasance kan fannonin rayuwa masu yawa kamar fad’akarwa da kishi da soyayya da siyasa da sauransu. Duk da yawan ayyukan adabin Hausa da Isa Rasco ya rubuta a iya k’ok’arina ban ci karo da wani aikin bincike ko nazari da aka yi kansa ba bale a san da shi a ilmance.[1] Na rubuta wannan mak’alar ce domin nazarin adabin nasa a tak’aice. Na tak’aita mak’alar kan tarihinsa da rabe-raben adabinsa da nazarin wasu ayyukan nasa a tak’aice domin yin haka ya kasance somin-ta’bi, kuma sharar fage don ci gaba da nazarin taskar adabin nasa. Ba shakka ci gaba da nazarin zai ba da damar fito da hikimarsa da kuma ganin irin tasa basirar. Haka kuma nazarin zai k’ara fad’ad’a binciken da ake yi na adabin Hausa.

 

2.1       Tak’aitaccen Tarihin Isa Rasco Dangoma


Sunansa na yanka shi ne Isa. Sunan mahaifinsa Abdullahi Dangoma.An fi sanin sa da Isa Rasco Dangoma. Ya sami lak’abin ‘Rasco a makarantar boko.[2]  An haifi Isa Rasco a shekarar 1975 a wani gari da ake kira Dangoma. Dangoma wani k’aramin gari ne da ke cikin k’aramar Hukumar Mulki ta Kalgo cikin Jihar Kebbi, Nijeriya. Garin yana gabas ga titi a bisa hanyar Bunza kafin isa wani gari mai suna Sabon Birni. A cewar, Bunza (2016), garin Dangoma yana da tarihi. Na farko a garin ne wani Buzu ya fara ya da zango da littafin ‘Jawahirul Ma’ani’ na tafsirin Alk’ur’ani mai girma.[3].

Lokacin da Isa yake k’aramin yaro mahaifinsa ya sa shi makarantar allo ta Malam Muhammadu Dangoma. A wannan makaranta ya sauke Alk’ur’ani mai girma kuma ya fara shiga cikin littattafan sani na fik’ihu da hadisai kamar K’awa’idi da Ahalari da Arba’una Nawwawi da Majamu’ul Baharaini da sauransu.

Bayan makarantar allo, an sa Isa Rasco makarantar firamare a garinsu na Dangoma (Dangoma Model Primary School). Bayan da ya kammala sai ya wuce ta gaba da Firamare a Government Secondary School, Gwandu (GSS Gwandu) daga shekarar 1989 zuwa 1994. A wannan shekara ce (1994) ya fara gabatar da adabinsa da wata wak’ar Hausa ta Madahu mai suna ‘‘Dan Aminatu’ inda ya yi yabo ga Manzon Allah (S A W).

Isa Rasco ya yi karatu a makarantar Kimiyya da K’ere-k’ere, (Birnin Kebbi Polytechnic) inda ya kammala a shekarar 1997. A nan ya sami takardar shaidar kammala k’aramar Diploma ta ND a Sashen Sanin Yanayin Ruwa Da K’asa (Soil and Water Conservation). A shekarar 2006 ya sake komawa makarantar ya yi babbar Diploma (HND) ya kammala a 2007 a wannan fannin da ya kar’bi takardar shaida ta k’aramar Diploma.

A gwagwarmayar rayuwa, Isa ya fara aiki bayan kammala Diplomarsa a wani Kamfanin ‘Dab’i mai suna Mubel Printing Press da ke Birnin Kebbi a shekarar 1999. Shiga wannan kamfani sai Allah ya sa ya zama k’wararre a aikin na d’ab’i (Rubutu a Injimin Rubutu). Da yake tun lokacin da yake matashi ya zan yana sha’awar  aikin jarida, da karatun k’agaggun labarai, sai ya yi amfani da damarsa ta aikin kamfanin na d’ab’i ya fitar da littafin k’agaggen labari na farko mai suna ‘Wasik’a Abin Ado Ga Masoya’. Tun daga wannan lokaci Isa Rasco ya ci gaba da zurfafa ga rubuce-rubuce na wak’ok’i da littattafai da kuma shiga harkar samar da fim yana kuma samun yabo da godiya ga wasu masu karanta adabin nasa.

 

3.1       Isa Rasco Dangoma Da Rayuwar Adabin Hausa


Isa Rasco Dangoma mutum ne da Allah ya ba hikimar sarrafa tunaninsa a rubuce domin isar da sak’o ga al’umma. Wannan ya sa ya yi rubuce-rubuce masu yawa. Shi kansa rubuce-rubucen nasa sun yi tasiri sosai ga ci gaban rayuwarsa. Da rubuce-rubuce Isa ya san mutane masu yawa, su ma suka san shi. Ta wannan  hanya ya gina gidansa, ya sayi mota. A halin yanzu, adabi ya kasance sana’a gare shi, kuma yana d’aya daga cikin hanyoyin rayuwarsa. Adabin nasa ana iya kasa su gida uku: wak’a da k’agaggen labari da kuma fim.

3.1.1    Wak’a


Isa Rasco ya rubuta wak’ok’in Hausa masu yawa daga shekarar 1994 lokacin da ya fara wak’arsa mai suna ‘Dan Aminatu. Wak’ar ‘Dan Aminatu wak’a ce ta madahu wadda ya yabi Manzon Allah (S A W) a cikinta. Ya rubuta wak’ar bisa tsarin ‘yar k’war hud’u, kuma cikin baituka 40. Babbar k’afiyar wannan wak’a ita ce ga’bar kalmar ‘ba’ da ke zowa a k’arshen kowane baiti. Dan a tambaye shi dalilinsa na fara wak’ar Madahu. Ya nuna cewa, bai san wani tsayayyen dalili ba domin yana yaro ya rubuta ta. Abin da kawai yake cewa, shi ne shi Musulmi ne mai son Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Tun bayan wannan wak’a, Isa ya ci gaba da rubuta wak’ok’i kan fannonin rayuwa daban-daban. A hirar da na yi da shi ya nuna cewa, ya rubuta wak’ok’i sama da d’ari biyu tsakanin na madahu da siyasa da yabo da aure da kuma ilmantarwa. Ga wasu kad’an daga cikin wak’ok’in nasa:

 

‘Dan Aminatu, Manzo Muhammad, Sayyadil Anbiyyah, Nana Aisha, Sayyadi Abubakar, Dan Khad’d’ab (Umar), ‘Dan Attanna, Sayyadi Ali, ‘Yar Manzona Fatima, Yak’in Uhudu Nana Khadijat, Ya Muhammadu Manzon Allah (SAW), You Are Prophet (Saw), Sayyadi Hamza Zakin Allah, Uwar Mummunai A’isha, Mu Yo Soyayya, Tafi Tafiya Za Ni Yi

Kofi-Kofi, Ehl Lallai Soyayya, Sahibata, Sahibina, Uwar Gida Ran Gida, Naf Studio. Mu Ne Fa ‘Daliban, Tsadar Rayuwa, Duniya Ho!     , Illar Talla, Bangar Siyasa, Mu Yo Ilmi, Kishin K’asa, Dogara Da Kai, An Sa Ta Lalle (‘Dan Alhaji), Auren Soyayya, Auren Sunnah A Yau An Ka ‘Daura, Aure Yau Fa An Ka ‘Daure, Arzika Zaki Ango, Zayyanu Da Zainab Auren Sunnah, Atiku Ya Share Ga Amarya, Matar Mutun Kabarinsa, Rangwad’a Amarya Yau Ranar, ‘Yan Uwa Da Masoya, Marhaban Marhaban (‘Dakin Gari), ‘Dan Baiwa, An Had’e An Zamo ‘Daya, PDP Sak (‘Dakingari), CPC Ce Muke Shiga (CPC).[4]

3.1.2          Rubutaccen K’agaggen Labari


Rubutaccen k’agaggen labari wani fad’ad’d’en labari ne, watau labari ne na zube wanda ake rubutawa da yake bayani game da mutum da yanayin zamantakewa, tare da kawo wani abu da yake faruwa a rayuwar al’umma. Haka ma abin yana iya kasancewa ko bai faru ba, amma ana hasashen faruwarsa (Bunza, 2011). Shi wannan nau’in rubutaccen adabin Hausa an fara samar da shi ne daga shekarar 1933. Adabin ya bunk’asa a tsakanin shekarar 1984-2010 lokacin da aka k’iyasta akwai littattafai sama da 3,500 (Malumfashi, 2010). Daga wannan lokaci 1984 –yau matasa masu yawa sun yi rubuce-rubucen k’agaggen labarin Hausa kan fannonin rayuwa masu yawa aka kuma sami masu nazari da suka ba adabin nasu sunaye daban-daban. An kira rubuce-rubucen adabin da sunaye kamar Adabin Kasuwar Kano da Littattafan Soyayya da Adabin Hausa Na Zamani da Hadisan ‘Yan Kano da Rayayyen Adabin Hausa (Malumfashi, 2002 da Adamu, 2013). Isa Rasco ya kasance d’aya daga cikin matasan da suka samar da wani ‘bangare na wannan adabi.

Isa ya fara rubuta k’agaggen labari ne da wani littafi mai suna ‘Wasik’a Abin Ado ga Masoya’ a shekarar 1999. Shi wannan littafi ne da ke kan jigon soyayya da yadda ake samun shigar soyayya tsakanin ‘ya’yan talakawa da ‘ya’yan masu kud’i. Ya rubuta littafin ne saboda a daidai wannan lokaci ne lamarin soyayya ya fara shiga rayuwarsa. Ya fara karanta littattafan soyayya da aka rubuta. Tun daga wannan lokaci Isa Rasco ya ci gaba da rubuta littattafan k’agaggun labarai inda zuwa yau ya rubuta littattafai masu yawa wad’anda kuma aka buga su a mad’aba’arsa mai suna Nabila Printing Press, Birnin Kebbi. Ga jerin littattafan nasa:

Wasik’a Abin Ado Ga Masoya 1 Da 2 (1999)

Gayun Zamani Ga Gida Ga Naira (2001)

Balkisu Koka-Kola (2002)

Maza Allurar Guba 1 Da 2 (2002)

Shafin Zuciya (2002)

Komai Saurin Narba Tana Barin Talata Ta Wuce (2005)

Zama Da Kishiya Riba Ce

‘Yar K’walisa 1 Da 2 (2001)

Alk’awari Da Macce Aikin Banza 1 Da 2 (2008)

Hattara ‘Dan Tsako Shaho Na Kallon Ka (2008)

‘Dan Duniya Hayak’in Taba 1 Da 2 (2013)

K’arya Linzamin Shaid’an. Da dai Sauransu.

 

3.1.3    Fim


Fim wani ‘bangare ne daga kafar sadarwa ta lantarki wadda take samar da gani da ji da motsi, domin amfanin mutane masu yawa. (Gidan Daboni da Yakasai, 2004). Fim wani nau’in wasa ne da ake shirya wasu abubuwa na yanayin rayuwa a aiwatar da su zahiran, kamar dai wasan kwaikwayo. Tarihi ya nuna an fara samar da fim na Hausa a tsakanin shekarar 1980-1984 a garin Kano lokacin da wasu k’ungiyoyi suka fara aiwatar da shi. A wannan lokaci ne wata k’ungiyar wasan kwaikwayo mai suna Gyaranya ta samar da wasu finafinai biyu; d’aya ya k’unshi sigar fim na k’asar Sin na fad’ace-fad’ace. ‘Daya kuma sigar fim irin na k’asar Indiya na yadda suke rawa da wak’a (Chamo, 2004). Al’amarin fim na Hausa ya ci gaba ya bunk’asa daga shekarar 1999 lokacin da marubuta matasa da dama suka mai da hankali ga shirya finafinai da aiwatar da su (Malumfashi, 2002). Wannan ya sa aka sami finafinan Hausa masu yawa kan jigogin rayuwa daban-daban.

Isa Rasco Dangoma ya kasance d’aya daga cikin marubutan Hausa da suka taka rawa ga samuwar fina-finai ko bayan rubuce-rubucen da suka ci gaba da aiwatarwa. Isa ya kasance yana shirya fina-finansa ne ba tare da amfani da juya wani littafinsa zuwa fim kamar yadda wasu marubuta suke yi ba. Ya fara shiga harkar fim ne a shekarar 2004 lokacin da ya samu fitar da wani fim mai suna ‘Baya Da K’ura’. A halin yanzu ma yana kan shirya wani fim mai suna ‘Bokon Zamani’. Dukkan fina-finan nasa yana shirya su ne tsakanin garuruwan Birnin Kabi da Kalgo zuwa Kamba. A wad’annan garuruwa yake samun yawancin taurarin fina-finansa, ya k’ara da wasu daga Kano kamar Ahmed Tagge. Kowane fim nasa ya warware jigonsa cikin kaset na CD guda d’aya. A kamfaninsa mai suna Rasco Fim Production da ke Birnin Kebbi yake tsara su tare da had’in guiwar Tagge Production Kano. Wad’annan su ne fina-finan da ya fitar zuwa yau. Ga finafinan kamar haka:

Baya Da K’ura

Bokon Zamani

 

4.1       Rabe-Raben Jigogin Adabin Isa Rasco


Jigo shi ne manufar ko mak’asudi yin wani abu, ko k’aga wani abu, ko tsara yin wani abu (Bunza, 2009). Isa Rasco ya rubuta ayyukan adabinsa da manufar isar da wasu sak’onni daban-daban ga al’umma. Jigogin na adabin nasa sun had’a da soyayya da yabo da madahu da siyasa da aure da fad’akarwa da kishi tsakanin mata da sauransu. A nan za a raba ayyukan nasa ta fuskar jigoginsu.

4.1.1    Soyayya


Soyayya hanya ce ta nuna k’auna tsakanin mutane musamman tsakanin maza da mata. Soyayya ta kasance wani muhimmin jigo da marubutan adabin Hausa suka yi rubuce-rubuce da dama kansa. A irin wannan jigo ne ake nuna yadda mace ke son namiji ko namiji ke son mace. Haka kuma ta wannan hanya ake bayyana matsayin masoyi a zuciyar mai son sa. Ana bayyana wasu abubuwa da soyayya ke haifarwa masu kyau ko marasa kyau da kuma bayyana gurin da masoya suke da shi na yin aure. Rubuce –rubucen jigon soyayya sun taka rawa ga bunk’asa adabin Hausa da kuma ta’bar’barewar wasu sassan tarbiyyar al’ummar Hausawa.

Isa Rasco ya samar da wasu ayyukan adabi kan jigon soyayya wad’anda a cikinsu ya fad’i abubuwa da dama kan abin da yake hasashe kan soyayyar zamani. Ga wasu daga cikin adabinsa na soyayya:

Wak’ok’i

Mu Yo Soyayya

Tafi Tafiya Za Ni Yi

Kofi-Kofi

Eh! Lallai Soyayya

Sahibata, Sahibina

Uwar Gida Ran Gida

Muna Fa ‘Daliban

Tsabar Rayuwa

 

Littattafan Zube

Wasik’a Abin Ado Ga Masoya (1999)

Gayun Zamani Ga Gida Ga Naira (2001)

Balkisu Koka-Kola (2002)

Shafin Zuciya (2002)

Komai Saurin Narba Tana Barin Talata Ta Wuce (2005)

‘Yar K’walisa Sarauniyar ‘Yan Mata

4.1.2    Madahu


Madahu jigo ne na yabon Annabi (S A W) ko sahabbansa ko iyalansa. Rubuce-rubucen madahu abu ne da aka dad’e ana yi, musamman wak’ok’i. Marubuta wak’ok’in Hausa da dama sun rubuta wak’ok’i inda suka yabi wad’annan fiyayyun mutane don nuna k’auna gare su. A wad’annan wak’ok’i ana bayyana gudummuwar da wad’annan mutane suka ba da wajen ci gaban addinin Musulunci ta fuskar jihadi da karantarwa. Daga baya an sami wasu masu madahu da suke yi kan waliyyai da shaihunnai da wasu magabata malamai.

Isa ya shiga cikin wad’annan marubuta da suka yi madahu ga Annabi (S A W) da wasu sahabbansa kamar Abubakar da Umar da Aliyu da kuma iyalan gidan Annabi (S A W) kamar Khadija da A’isha da Fatima (A S) da sauransu.Ya nuna ya yi wad’annan wak’ok’i ne domin neman lada ga Ubangiji ba don wani abin duniya ba. Ya kai wasu kaset-kaset guda shida na wasu wak’ok’in nasa na madahu a gidan Radiyon Jihar Kebbi inda ake sa su don watsawa ga jama’a. Ga wasu daga cikin wad’annan wak’ok’in.

 

‘Dan Aminatu

Manzo Muhammad

Ya Muhammadu Manzon Allah (SAW)

You Are Prophet (SAW)

Sayyadil Anbiyyah

Nana Khadijat

Nana A’isha

Uwar Mummunai A’isha

Sayyadi Abubakar

‘Dan Khad’d’ab (Umar)

Sayyadi Ali

‘Yar Manzona Fatima

Yak’in Uhudu

Sayyadi Hamza Zakin Allah

 

4.1.3      Yabo


Yabo na d’aya daga cikin muhimman jigogin da aka yi rubuce-rubucen Hausa kan su.Yabo na nufin fad’ar wata kalma mai dad’i game da wani wadda idan ya ji ta zai ji dad’i, ta kuma sa mutane su so shi, su kuma k’ara ganin girmansa. A wannan jigo ne marubuci kan kawo wasu muhimman abubuwan gwarzanta mutum domin dad’ad’a masa rai da kuma jan ra’ayin mutane don su so shi. Ire-iren abubuwan da ake yaba mutum da su yawanci sun had’a da hali na gari da rik’on addini da taimakonsa da kyauta da ilimi da sauransu.

Daga cikin adabin Isa Rasco akwai wak’ok’in da ya shirya kan wannan jigo. Su wad’annan wak’ok’i, Isa ya rubuta su ne bisa nufin yaba wasu mutane da yake jin sun cancanci ya yaba su saboda arzikinsu da kuma yadda suke sarrafa shi ko kuma saboda mulkinsu da sauransu. Ga kad’an daga cikin wad’annan wak’ok’i nasa:

‘Dan Bauran Gwandu (Sadiq Marafa)

Kabiru Kamba Zakin Fama

Chairman Ciyamomi (Hannu ba ka da tsoro)

Duk Jama’ar Kalgo (Ali Diggi)

Ibrahim Basaura Sadauki (Chairman Jega)

Mazan Jiran Maza (Hannu Ba ka da tsoro)

Chairman Maiyama Zakin Fama (UU)

Sarkin Gwandu (Iliyasu Bashar)

Magayak’in Kebbi

 

4.1.4       Kishi


Kishi na nufin rashin jituwa da nuna k’yashi wanda matan da ke auren mutum d’aya ke yi wa juna (CNHN, 2006).  Shi kuma Bakura (2014) ya bayyana ma’anar kishi da cewa tsananin son da mace ke yi wa mijinta ko neman ke’bancewa zuwa ga mijinta ko wanda take son ta aura, da take nuna k’auna, da kyakkyawar fata gare shi, tare kuma da nuna k’iyayyarta ga duk wata da take son sa da aure ko kuma shi yake son ta da aure. Kishi wani abu ne sananne a rayuwar matan Hausawa wanda wannan ya sa ake kiran sa kumallon mata. Da wuya a sami wata mace da ke son kishiya bale ta goyu bayan mijinta ya k’ara aure.

Marubuta adabin Hausa da dama sun yi rubuce-rubuce kan lamarin kishi. Wasu sun kalle shi a matsayin mugun abu. Wasu kuma sun kale shi a matsayin abin dole ga mata. Akwai wad’anda kuma suka yi rubutu don daidaita zaman kiyoshi da sauransu.

Isa Rasco ya kasance d’aya daga cikin marubutan da adabinsu kan kishi shi ne na k’ok’arin gyara a zaman kishiyoyi. Littafinsa na Zama Da Kishiya Riba Ce ya tabbatar da mace ba ta son kishiya domin tsoron yanayin zaman da ake yi maras aminci. A wannan littafi Isa ya nuna akwai hanyoyin kyautata zaman kishi har mata su zama ‘yan uwa. Wannan littafi shi ne kad’ai adabinsa kan jigon kishi

 

4.1.5       Siyasa


Siyasa ita ce tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu (CNHN, 2006). Siyasa k’ok’ari ne na kafa ko d’abbak’a wani abu, ko kuma neman rusa wani abu, ko neman samar wa wani abu ‘yanci, ko matsayi, ko kuma tallata wani abu ya samu shiga da kar’buwa da kafa gwamnati domin tafiyar da lamarin mulkin jama’a kan wanda suka za’bar wa kansu.

Al’amarin siyasa ya kutsa cikin al’amurran rayuwa mutane na yau da kullum da yawa. Neman matsayi a gwamnati ko kafa gwmanati abu ne da koyaushe yake buk’atar marubuta adabi musamman mawak’a domin farfaganda da kuma watsa manufar jam’iyya ko d’an takara cikin zukatan mutane. Marubuta wak’a a fagen siyasa suna cikin masu tallata d’an siyasa, su kai shi inda k’afafunsa ko hotonsa bai riga ya isa ba. Wannan ya sa kowace jam’iyya da kuma kowane d’an takara suke amfani da mawak’a a matsayin wata kafa ta watsa manufofinsu da kuma mai da martani ga wanda ke suka ko k’alubalantar su.

Isa Rasco ya taka rawa wajen rubuta wak’ok’in siyasa. Ya rubuta wak’ok’i don tallata wasu jam’iyyu da wasu ‘yan takara musamman na jihar Kebbi bias ga nemansa da aka yi ya rubuta, wasu kuma don ra’ayinsa ga d’an siyasa. Dukkan wak’ok’in yakan rubuta su, ya kuma rera su da kansa, wani lokaci tare da masu amsa masa. Ga wasu cikin wak’ok’insa na siyasa.

An Had’e an Zamo ‘Daya

PDP Sak (‘Dakin Gari)

CPC Ce Muke Shiga (CPC)

A Kasa A Tsare (CPC)

Buhari Mazan Fama (CPC)

Kainuwa Dashen Allah (‘Dakin Gari)

‘Dan Tsiron Da Allah Ke So (Shatima)

Nasamu 2 Terms (Nasamu)

7 Point Agenda

Sakkwatawa Muna Murna (Alu Wamakko)

Sauyin Zamani

2007 Nasamu

2011 CPC

ANPP Muke Shiga (ANPP)

Ibrahim Bande Jarumi (‘Dan Majalisa)

Yanzu Kebbi Ta Lek’o Ta Koma (‘Dakin Gari)

 

4.1.6      Aure


Aure na nufin halartaccen zaman tare tsakanin namiji da mace da aka shirya bisa hanyar da al’umma ta amince da ita. Aure ya kasance jigo muhimmi da ya kawo samuwar wasu ayyukan adabin Hausa masu yawa. Marubuta da dama sun yi rubutu kan lamarin aure. Wannan kuwa ya shafi ko dai taya murna ko kuma hannunka mai sanda kan wasu matsalolin aure. Ta wannan hanya wasu marubuta ke watsa shawarwari kan yadda ya kamata ma’aurata su zauna don samun natsuwa da kyakkyawar rayuwa a tsakaninsu. Wasu marubuta kuma a cikin rubutu suke bayyana wa ma’aurata hak’k’ok’in da suka rataya kan su. Mata sau da yawa cikin adabi sukan tsinci bayanan da ke nuna musu matsayinsu na masu kula da gida da bayyana ayyukan tafiyar da gida da kula da miji da tsabta da sauransu. Shi ma namiji ana bayyana masa hak’k’ok’in kula da matarsa da kawo abinci da sauransu. A yau rubuce-rubuce kan jigon aure musamman wak’a sun zama wata hanyar rayuwa ga wasu da ke da hikimar wanda har akan gayyace su daga gari zuwa gari a d’auki d’awainiyarsu, a kuma biya su.

Isa Rasco ya rubuta adabi kan jigon aure musamman wak’ok’i. A cewarsa, yana rubuta wak’ok’in aure ne idan wani cikin ma’aurata ya buk’ace shi da yin haka. Ya rubuta wak’ok’in aure masu yawa. Ga kad’an daga cikinsu.

 

An Sa Ta Lalle (‘Dan Alhaji)

Auren Soyayya

Auren Sunnah A yau Anka ‘Daura

Aure Yau Fa An Ka ‘Daure

Arzika Zaki Ango

Zayyanu da Zainab Auren Sunnah

Atiku  Ya Share Ga Amarya

Matar Mutun Kabarinsa

Rangwad’a Amarya Yau Ranar

‘Yan uwa da Masoya

 

4.1.7      Fad’akarwa


Fad’akarwa na nufin tunatar da mutane da fahimtar da su wani abu muhimmi da zai taimaki rayuwarsa ta hanyoyi masu yawa. Usman (2008), ya nuna cewa, fad’akarwa hanya ce ta waye wa mutane kai kan wasu al’amurra da yake ganin suna da alfanu gare su. Ana yin haka ne don nuna wa mutane muhimmancin wani abu domin su ji’binci aikata shi saboda muhimmancinsa. Wani lokaci ana fad’akar da mutane illar wani abu domin su nisantar da kansu daga gare shi. Lamarin fad’akarwa abu ne muhimmi da ya ja hankalin marubuta suka yi rubuce-rubuce kansa. Marubuta da dama sun yi rubuce-rubucen fad’akarwa kan kyautata tarbiyya da gyaran al’umma kamar illar jahilci da shaye-shaye da zaman banza da talla da kuma muhimmancin ilimi.

Isa Rasco ya bi sahun wasu marubuta inda ya rubuta adabi domin fad’akar da mutane wasu muhimman abubuwa da suka ji’binci kyautata rayuwar Hausawa da ci gabanta. Ga wasu ayyukan adabinsa na fad’akarwa.

 

Wak’a

Illar Talla

Bangar Siyasa

Mu Yo Ilmi

Kishin K’asa

Dogara Da Kai

 

Littattafan Zube

Maza Allurar Guba (2002)

Alkawari Da MacceAikin Banza (2008)

Hattara ‘Dan Tsako Shaho Na Kallon Ka (2008)

‘Dan Duniya Hayak’in Taba (2013)

K’arya Linzamin Shaid’an

 

Fim

Baya Da K’ura

Bokon Zamani (Bai riga ya fito ba)

5.1       Tak’aitaccen Bayanin Wasu Ayyukan Adabin Isa Rasco

Da yake an ga ayyukan adabin Isa Rasco, a nan nake son in yi bayani tak’aice kan k’umshiyar wasu ayyukan adabin nasa. Na za’bi littafi d’aya mai suna Zama Da Kishiya Riba Ce da kuma fim d’aya na Muhimmancin Ilimi.

 

5.1.1    Zama Da Kishiya Riba Ce


Zama da Kishiya Riba Ce littafi ne da aka shirya kan jigon kishi. Yadda labarin yake shi ne, wani mutum ne mai suna Dr. Halliru ya auri wata Ba’indiya mai suna Mirsiyya. Dr. Halliru d’an wani hamshak’in mai kud’i ne a garin Kano. Ubansa ya rasu ya bar masa dukiya mai yawa. Ita kuma Mirsiyya can farko Kirista ce ana kiran ta Bolgat. Da ta Musulunta sai iyayenta suka kore ta ta koma garin New York da zama. A can New York shi kuma Dr. Haliru yake a wannan lokaci yana karatu.

Wata rana ya je wani hotel mai suna New York Hotel sai ya had’u da wannan mata, kuma ya ji yana son ta. Ya je ya yi mata magana, aka yi dace suka daidaita maganar aure. Suka je wajen wani k’anin babanta wanda yake Musulmi ne aka canza mata suna daga Bolgat zuwa Mirsiyya. Daga nan bayan wata biyar aka d’aura musu aure. Suka ci gaba da zama har lokacin da ya k’are karatu ya d’auko ta suka koma Kano da zama. A nan suka ci gaba da zama cikin daula har tsawon shekaru goma sha d’aya. Tsawon wannan lokaci ba abin da ke damun su illa rashin haihuwa.

Ana nan wata rana Dr. Halliru ya fita yawo da yamma sai ya had’u da wasu ‘yan mata biyu; d’aya ana kiran ta Hajaru, d’aya kuma Lanti. Da ganin wad’annan ‘yan mata sai ya ji yana son Hajaru. Bai tsaya ba ya je wajen su ya gaisa da su, ya kuma nuna soyayyarsa ga Hajaru har ya d’auke su da mota ya kai su inda za su je. Hajaru ta amince, ta kuma nemi ya je wurin iyayenta. Dr. Halliru ya aika magabatansa aka shirya maganar aure aka kuma sa lokaci. Wannan ya sa Dr. Halliru da Hajaru suka ci gaba da soyayya. Duk wannan abu bai gaya wa Mirsiyya ba.

Wata rana ya shigo gida sai ya sami Mirsiyya cikin damuwa.Ya tambaye ta ba ta ce komai ba. Daga nan ya gabatar mata da maganar k’ara aure ita kuma ta nuna rashin yardarta. Ga yadda suka yi kan maganar:

‘A gaskiya ina ganin ya fi kyau na karo mata mugani ko Allah zai ci da mu…’

Ita kuma ta ba shi amsa da cewa;

‘Ba za ni yarda da kishiya ba har iyakar raina. Kuma komai ya faru tsakanina da kai to kai ne ka jawo shi. Ka kuma tuna na bar iyayena, na bar daula, na bar kasarmu don kawai in aure ka in yi maka biyayya. Shi ne ya sanya ni barin kasarmu da duk dangina. Amma ga shi kana son ka yi mini sakiyar da ba ruwa’ (shafi na 29).

 

Jin wannan magana ta sa Dr. Haliru ya ji tsoron gabatar da maganar aurensa ga Mirsiyya. Ana nan wata rana sai wata mata mai suna Malka mai haja ta je talla wajen Mirsiyya. Suna cikin magana sai Malka ta gaya mata cewa, mijinta na nan yana maganar aure har ma an yi kusan sa amarya lalle. Wannan magana ta tayar da hankalin Mirsiyya, ta shiga damuwa sosai.

Bayan an d’aura auren Dr. Halliru da Hajaru da kuma tarewar amarya d’akinta, sai Mirsiyya ta shiga kishi. Bayan wani lokaci zaman nasu ya yi kyau saboda Hajaru na ba Mirsiyya girmanta da kuma kare mutuncinta koyaushe. Haka zaman ya ci gaba har su duka suka haihu. Hajaru ce ta fara haihuwa aka rad’a wa yaro suna Mas’ud. Ita kuma Mirsiyya bayan wata shida ta haihu aka sa wa yaro suna Fahad. Yaran suka tashi suna son juna, iyayen nasu suka zauna lafiya.

 

5.1.2      Baya Da K’ura


Baya Da K’ura fim ne da Isa Rasco ya shirya A Rasco Fim Production Birnin Kebbi a k’ark’ashin umurnin Ahmad Tagge. An shirya wannan fim ne kan jigon fad’akarwa kan muhimmancin ilimi da kuma illar talla ga d’iya mace. Yadda wannan fim ya gudana shi ne wasu mata ne kishiyoyi su biyu. ‘Daya sunanta Rashida, d’aya kuma Hauwa’u. Ita Rashida ita ce uwar gida tana da ‘ya’ya uku duka mata. Ita kuma Hauwa’u (Amarya) tana da d’iya d’aya.

Uwargida Rashida babban burinta shi ne yaranta su sami ilimin addini da na boko. Wannan ya sa kowace rana takan tabbatar da yaran sun tafi makaranta ko da kuwa tana da wani abu da take son su yi mata. Da wannan tsari na karatu akoyaushe yaran nata suka taso har suka girma.

Amarya ita kuma babban abin da ta sa gaba shi ne ‘yarta ta nemi kud’i ta tara kaya domin aurenta. Wannan ya sa kowace rana sai ta shirya wa yarinyar wani abu da za ta je talla a kasuwa ko tasha ko filin wasa. Duk lokacin da uwargida ta ja kunnenta kan yadda take hana d’iyarta zuwa makaranta da aza mata talla, sai ta yi cikin ta da fad’a tana fad’in ita ba za ta bari su yi kunyar ‘yan wari ba. A tashi aure ba su aje komai ba sai tarin takardun banza da biro. Haka ita kuma wannan yarinya ta ci gaba da rayuwarta.

Wata rana yarinyar ta fita talla a gareji wurin kanikawa sai ta sami wani saurayi mai suna A- Sa- Ni- A- Layi. Bayan da ya kira ta suka gaisa, sai ya saye dukkan abarbar da take d’auke da ita kan kud’i naira dubu da d’ari biyar. Daga nan ya yi mata alk’awalin duk lokacin da ta biyo zai saye mata sana’arta don ba ya son ganin ta tana wahala. Sannu-sannu yarinya ta ci gaba da zuwa har ya ja ta d’akinsa har ya kai ya yi mata ciki. Da ciki ya bayyana amarya ta yi da –na- sani da bak’in cikin d’ora d’iyarta ga tallace-tallace.

 

 

6.1       Kammalawa


Idan aka yi nazarin abin da ya gabata a wannan mak’ala za a ga cewa, Isa Rasco Dangoma ya kasance d’aya daga cikin matasan zamani da suka ba da gudummuwa kan ci gaban adabin Hausa. Ya yi rubutu a dukkan fannoni uku  (wak’a da zube da wasan kwaikwayo) na adabin Hausa. Da yake an tak’aita nazarin adabin nasa, an yi haka ne domin nazarin ya zama shimfid’a ga fito da shi da kuma matashiya ga ci gaba da nazarin taskar adabinsa.

Mak’alar ta gano cewa, akwai d’imbin abubuwan nazari a fannin harshe da al’ada da ma cud’ed’eniyar adabi cikin adabin Isa Rasco Dangoma. An lura akwai salon sarrafa harshe da aron kalmomi da tasirin karin magana da bak’ar magana da kirari masu yawa cikin adabin nasa. Wannan na buk’atar fad’ad’a nazarin adabin nasa ga manazarta da d’alibban ilimi domin fito da wad’annan abubuwa.

Wani abu kuma shi ne, lura da aka yi cewa, Isa Rasco Dangoma bai karanci Hausa a matakin gaba da sakandare ba bale ya san tsare-tsaren rubutun Hausa. Don haka ci gaba da nazarin zai ba da damar jawo shi kusa ga masana don kyautata aikin adabinsa, ya d’ora shi bisa k’a’idodjin rubutun Hausa don inganta shi. Da haka sai y azan an kyautata tunaninsa da rubutunsa don a gudu tare, a tsira tare.

Daga k’arshe mak’alar na tabbatar da cewa, ba shakka idan aka ci gaba da nazarin adabin Isa Rasco Dangoma za a tsinto muhimman abubuwan da suke k’unshe cikin hikimar da Allah ya yi masa ta rubuta adabin Hausa. Don haka akwai buk’atar manazarta su san da haka, su kuma sa wannan cikin tunaninsu.

 

Manazarta


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

[1]. Shi kansa ya tabbatar min cewa, bai san da an yi wani aikin ba. Ya ce ba wani da ya ta’ba tuntu’barsa kan rubutunsa. Wannan ne karo na farko.

[2] . Duk aikinsa na adabi da wannan sunan Isa Rasco Dangoma yake fitowa. Wannan sunan ne yake rubutawa, kuma da wannan sunan aka fi saninsa.

[3] . Bunza shi ne Aliyu Muhammad Bunza wanda malami ne a Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato. Ya ba da wannan bayani ne a wajen taron da aka gabatar da wannan mak’ala.

[4] . Na sami sunayen wak’ok’i 67. Wad’annan sunayen kad’an daga cikinsu ne na kawo.