Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Alhaji Musa Lumu (Alhaji Musa Ɗanba’u Gigan Buwai)

Wannan ɗaya ne daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai.
Rubutawa: Shehu Hirabri 
08143533314

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Mu tafi Gwadabawa,

Musa ciyaman ya kiran,

Yara:  Ina a gida na don ban zuwa sai an kiran.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Ƙasar Gwadabawa,

Mu mun yi babban arziki,

Don mun ije kunkuru mai idanu kakkahe,

Yara:  Kai bari ɗan tulluƙi ba a yin komai da kai.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Wane an kashe shi sai ya tcira min tcegumi,

Mai babban gaba mig gami na ni da kai,

Yara:   Ka isko ni gida ka ce za ka tungatci da ni.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Mutan Gwadabawa akwai tambaya ni da ku,

Mutan Gwadabawa akwai tambayata ni da ku,

Don Allah raƙumi na garin ko ba ya nan,

Sai suka ce raƙumi ai yana nan zumbuge,

Yara:  Bai iya tahiya cinai sun kare sai rarrahe.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Baƙa akuya wance ke ad da ƙallalen ƙaho,

Ban layya da ke kuma ba mu yin suna da ke.

Yara:  Mu ba mu sayen labari masu yin tsahi su sai.

Jagora: Umaru sarkin maguri babban baƙo kake,

Yara:  Maza ba su kamakka ko su ishe wa ba su ja.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Ina Alhaji Audu Ɗanhwaransi ya taimaka man,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ina Ɗan Nakaduna Audu babban baƙo kake,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A sarkin rwahii abin da ka yi mani ka biya ni,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Baba sarkin rwahi ubanmu na gode ma ƙwarai,

Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Mai tasa Haji Umaru Ghana da godiya,

Yara:  Ban rena maiba haira yakai ya taimaka.

Jagora: A na gode ma ciyaman Haji Sani a ka

Ubangidana ‘ya taimaka man,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Alhaji Sani a ka nidai kai ƙoƙari,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ana gode Zubairu S. Magori yai taimako,

Yara: Ban Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Mu je magina in ga maigidana,

Mamman uban gidana ya san da ni,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A Mamman Ɗanbarno za ni magina in gai da shi,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Yaro: Haji Ɗanba’u akwai tambaya ta ni da kai,

Yaran Musa akwai tambayata ni da ku,

Maroƙan Musa akwai tambayara ta ni da ku,

Shin don Allah ina mai hwaɗin sai ya bugan?

Wani ɗan kutu’bi baƙi mai idanun raguna,

To na zage ka.

Yara: Komai kakai man sai ka yi.

Jagora: Wane yau na zage ka,

Yara:  Komai kakai man sai ka yi.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Mu je Gwadabawa Musa ciyaman ya kiran,

Yara:  Ina a gida na don ban zuwa sai an kiran.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: A ɗan Amadu baba jikan Alu namijin tsaye,

Yara:  Riƙa a sakamma duk masu ja sun barkace.

Jagora: Ina Bello Magaji na yaba maka kai ƙoƙari,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ciyaman na Tangaza ina Musa Ausa

Koyaushe ba kuɗi yakai,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ina Haji Aminu Garkuwa ka kyauta ƙwarai,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Inda sai godiya nikai ma injin niƙa,

Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A Bashiru Gigane uban gidan Ɗanba’u kake,

Yara:  Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A na gode Mairi Turɗa tanai man ƙoƙari,

Yara:  Ban rena mar ba hairan takai ta taimaka.

Jagora: A na gode Bara’atu ‘Yar Audu da godiya,

Yara:  Ban rena mar ba hairan takai ta taimaka.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Akwai magana yara sai na faɗi na jaddada,

Kai Ɗanba’u halan ka yi gwajen A’isha?

A’isha tawa ni na yabamat tabiya,

Yara:  Ban rena mar ba hairan takai ta taimaka.

Jagora: Sanusi Wali Sanusi ka taimaka ƙwarai,

Yara:  Ban rena mai ba hairan taƙaita tamaka.

Jagora: A A ɗan Amadu baba jikan Alu namijin tsaye,

Yara:  Riƙa a sakamma duk masu ja sun barkace. ×3
 
Jagora: A gyare-gyare Mu’azu,

Yara:  Allah daɗa mai arziki,

Jagora: A bara har jaki ya ban yai tuma sai ni sakai.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments