Ticker

6/recent/ticker-posts

Adabin Wayo A Tantance Bahaushen Asali (Duba Cikin Adabin Abubakar Imam)

Daga

Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
aliyubunzaumar@yahoo.com
07063532532, 08095750999

Da

Abdulbasir Ahmad Atuwo
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07032492269, 08084298903
Kibdau: atuwoaa@yahoo.com

www.amsoshi.com

Tsakure


Adabi fage ne babba da ake iya hango kowane abu da ya shafi rayuwar Bahaushe. Wayon Bahaushe na cikin muhimman batutuwan da suka zama ruwan–dare cikin wasu sassan littattafan adabin Hausa, musamman littattafan  adabin Abubakar Imam. Wannan wayo ya k’unshi ko dai dabara don fitar da kai, ko ceton wani ko wasu jama’a, ko cutar wani, ko wani hali na girma don birgewa da samun kar’buwa ga wasu mutane. Dukkan wad’annan nau’o’i ko matakan wayo ana amfani da su domin a tantance Bahaushen asali a muhallin zamantakewa da wasu k’abilu. Manufar wannan mak’ala ita ce duba cikin adabin Abubakar Imam don sharhin yadda Bahaushe ya nuna kansa ta hanyar wayo ga wasu k’abilu da suka yi tarayya ta wani lamari.

1.0       Gabatarwa


Wayo hikima ce da mutum yake amfani da ita don ya fitar da kansa daga wata matsala ko ya sami wani abu na amfani ko kuma wani lokaci ya yi zamba ga wani. Bahaushe mutum ne da Allah ya yi wa arzikin wayo cikin rayuwarsa. Duk inda Bahaushe ya sami kansa a zamantakewa, wayo na kasancewa kan gaba da ake iya gane shi kai tsaye. Wannan ya sa wani lokaci har wayon nasa kan zamar masa wauta, ya jefa kansa cikin matsala da sai ya sake shiri, ya kintsa wani wayo, sannan ya samu wata mafita. Da yawa a sassan adabin Hausawa akan ci karo da yadda suke kallon wayo cikin hikimarsu.[1] Marigayi Abubakar Imam fitaccen marubuci adabin Hausa ne da masana da manazarta suka yi rubuce-rubuce  masu yawa kansa.[2] Alhaji Imam marubuci ne da yake sakad’a lamurran wayo cikin adabinsa. Hasali ma, wayo kan kasance ruhi ko k’ashin bayan warware jigogin wasu labaran nasa. Yana amfani da hikimar wayon Hausawa ga wani tauraronsa domin ya nuna yadda Bahaushe ya kai gaya ga hikima fiye da sauran k’abilun da yake huld’a da su na kusa ko nesa. A wannan mak’alar muna son duba yadda wayon Bahaushe ya fito cikin adabin nasa.

2.0       Ma’anar Wayo


Kalmar wayo na d’aukar ma’anoni daban-daban gwargwadon yadda aka sarrafa ta cikin zance.[3]  Akwai masana da manazarta da suka bayar da ma’anar wayo ta fuskoki da dama.

 

Skinner (1999) ya fassara kalmar  wayo da:

 

‘Hankali, ko kangado, ko fahimta, ko basira.’ [4]

 

A cikin K’amusun Hausa (2006), wallafar Cibiyar  Nazarin Harsunan Nijeriya,  Jami’ar  Bayero  Kano, an kawo ma’anar  wayo da cewa:

‘kyakkyawan shiri, ko hikima, tsari.’ [5]

 

Hornby, (2006), shi kuma sai ya bayar da ma’anar   kalmar da cewa:

 

‘Gane, ko fahimta, ko hasashe, da tunani a kan wasu abubuwa, ana danganta wannan ga mutum ko dabba.’[6]

 

Mish da Promila (2010), su kuma su kuma cewa suka yi:

 

‘Fita, ko ku’buta, ko iya warware matsaloli da aka shiga, ta hanyar  yin amfani da ilmin yau da kullum, ko kuma goguwa da harkar rayuwa’.[7]

 

Shi kuma  Mu’azu (2014), ya kawo ma’anar wayo da cewa:

 

Wayo na nufin dabara, ko basira, ko sanin makamar al’amurra, ko samar wa kai mafita (ku’buta) idan an shiga wani bak’on yanayi

 

Ta la’akari da wad’annan ma’anoni, ana iya fahimtar cewa, wayo yanayi ne na rayuwar Bahaushe da ke zo masa kai tsaye cikin sauri don tattara hankalinsa da tunaninsa wuri d’aya, ya cimma wata manufa da ya sa a gabansa cikin sauk’i. Da wannan yake ceton kai ko yaudara ko kuma neman matsayi. Kishiyar wayo ita ce wauta. Ba wani wuri da za a nuna wayo face sai an sami wauta ta bayyana. Sau da yawa Bahaushe kan  nuna wayo don ya fito da wautar wani a fili. Bari mu dubi ma’anar wauta don daidaita wannan nazari.

3.0       Ma’anar Wauta


Wauta kalma ce da Bahaushe ke k’yamar a danganta masa. Kalma ce da ke nufin shashanci ko rashin hankali ko rashin natsuwa (CHCN, 2006). Bunza (2014), ya nuna wauta a matsayin kalmar da ba ta daidaitu d’aram ga sikelin hankali ba, kuma ba ta hau buzun hauka sosai ba. [8]k’a rashin girma ko rashin kyautatawa. Wauta ta k’unshi dukkan wani hali na rashin kirki da rashin girma ko rashin kyautatawa.

Hausawa mutane ne da ke kallon kowace k’abila da wani abu na wauta. Wannan ya sa kusan kowace k’abila akan ci karo da wani abu na adabin Hausa da ke nuna wautarta a fili ko da kuwa tana riya wayewar kai a duniya. Akwai k’abilun da Bahaushe ya had’a zamantakewa da su, kuma ya nuna wautarsu cikin wasu labaransa. K’abilu kamar Fulani da Buzaye da Nufawa da Yarbawa da sauransu duka akwai wasu labaru daban-daban da ke nuna wautarsu. Kowace k’abila akwai wani abu da Bahaushe ke kiyayewa game da d’abi’arta wanda ta kansa yake fitar da wautarta.[9]

Idan aka yi la’akari da wannan, yana nuni yadda Bahaushe yake kallon wasu al’ummu wawaye. Wannan ya sa yake k’ok’arin nuna kowace al’umma yana da basirar da zai iya yi mata wayo don d’ayan abu uku: ko ceton kai, ko zamba, ko kuma ya sami wani matsayi.

4.0       Wayon Bahaushe A Mahangar Adabin Abubakar Imam


Abubakar Imam marubuci ne da yake sakad’a halayyar Hausawa da yawa cikin rubuce-rubucensa. Wayon Bahaushe na cikin muhimman abubawa da yake amfani da su domin warware wasu jigogin labaransa. A wannan wuri muka duba irin matakan wayon Hausawa da ya yi amfani da su domin cimma wata manufa ta warware jigon labarinsa. Wad’annan su ne ceton kai ta cikin dabara, da cuta ta hanyar zamba cikin aminci da kuma neman matsayi ta hanyar halin girma.

4.1       Dabarun ceton Kai


Wayo ne da Bahaushe yake yi ya ceci kansa ko wani daga cikin wani hali na matsuwa da ya shiga. Ta wannan ceton ne akan yi amfani da wasu dabaru da masu ban mamaki da kuma nuna wayon Bahaushen asali.

4.1.1   Iya Ruwa Fid Da Kai


Wannan wata dabara ce da Bahaushe ke amfani da ita ya ceci kansa daga cikin wata matsala. Ta wannan wayo ne mutum kan yi amfani da hikima don ya taimakin kansa, ya fitar da kansa ko wani daga wani hali na k’ak’a-ni-ka-yi da ya shiga. A wannan hali mutum kan yi amfani da dabara ko hikima ko fasaha cikin ruwan sanyi. Wannan dabarar na iya kasancewa ta magana ko wani aiki da za a iya gani ko jin samatarsa. Bahaushe mutum ne da Allah ya yi wa dabarar da yake sarrafa tunaninsa, ya samar da wata mafita a wani halin matsuwa da ya shiga. Wannan ya sa yake ganin mutumin da ba ya da dabara bai cika mutum na hak’ik’a ba. Dabarar Bahaushe ta iya ruwa fid da kai ta kasance wani muhimmin ado ga adabin Abubakar Imam. Ga misali, a cikin littafin Ruwan Bagaja, akwai wurare da dama da Bahaushe ya yi amfani da dabara ya ceci kansa kamar a shafi na 13 inda Alhaji Imam ya shiga hali mawuyaci wanda sai da dabara zai iya ceton kansa da abokin tafiyarsa. Mahaukacin rak’umi ya bi su suka haye ice, ba ruwa, ga rana, ba kowa da zai taimake su. Ga yadda aka kawo batun:

...Muna cikin tafiya a daji, sai wani mahaukacin rak’umi, amale, ya biyo mu baki bud’e. Muka shek’a wurin wata itaciya muka hau. Shi kuwa rak’umin ya tsaya nan gindin itaciyar yana jira wai sai mun sauko, ya tasam mana. Muka rasa yadda za mu yi tun safe har azahar, ga shi kuwa cikunammu suna ta kiran ciroma. Can zuwa la’asar sai na ga wad’ansu Filani za su yawon sharo. Da dai na hange su kan hanya, sai na ce, ‘Kai masu tafiya, uwaku.’

          Ka san Bafillace kan bak’in rai, daga can kuwa sai suka nufo mu da gudu, wai su ji dalilin da ya sa na zage su. Da dai rak’umin nan ya k’yalla ido ya gan su, bai sake komawa ta kammu ba, sai ya ce da ku aka gama mu. Kowanne ya ranta, suka yi dawa! Mu kuwa muka sauko, muka yi tamu hanya..’

 

Rak’umi dabba ce abin tsoro bale ma mahaukaci. Ba yadda za su yi da shi, dole suka haye ice. A can saman ice suka d’auki lokaci ba wanda ya biyo ta wurin bale ya taimake su. A irin wannan hali suka ga Fulani. Fulani mutane ne da Hausawa ke dangantawa da rashin wayo da zafin rai, ga kuma saurin fushi. Sanin wannan hali nasu ya sa ya yi amfani da basirarsa ya zage su. Idan ya nemi ceto Fulanin za su zo ne cikin natsuwa. Wannan zai sa su lura da mahaukacin rak’umi su yi ta kansu. Wayon da ke nan shi ne ya husata su, su zo ido rufe, shi kuma rak’umi ya bi su. Wannan ya nuna dabarar Bahaushe ta kira wa wani ruwa, shi kuma ya bi ta kai ya gudu.

4.1.2   Ba A San Maci Tuwo Ba...


Wani nau’in wayo ne da Bahaushe ke amfani da shi domin fito da hikimarsa a fili. A irin wannan wuri ne ake samun wata gaggak’a tsakanin mutum biyu kan wani abu d’aya wanda dole mutum d’aya zai tsira da shi, ko kansa. Bahaushe na son shiga irin wannan gaggak’a domin ya nuna basirarsa, ya tsira ta hanyar da ba a zaton ku’buta daga gare ta. A cikin Littafin Ruwan Bagaja, a shafi na 16-17 Abubakar Imam ya kawo irin wannan gasar, ya kuma yi amfani da zurfin wayon Bahaushe ya yi wa tauraronsa mafita, ya ceci kansa daga wani taliki mai suna Zadoro d’an Zotori. Alhaji Imam ya had’u da wannan taliki ne a wani gari mai suna Baku kusa ga teku. Zandoro d’an Zantori wani mutum ne d’an k’abilar Iwaja d’an Unk’a wanda ya yi zamani da Annabi Nuhu (AS). Yana da tsawon zira’i saba’in. Wannan mutum ne Alhaji Imam ya yanka sansa da alkawarin zai ta’ba kansa, ya kuma san hakan ba ta yiyuwa sai da wani wayo dole. Ga yadda batun yake:

...Can an yi kwana biyar sai wata dabara ta fad’o mini. Rana ta bakwai tun da jijjifi, sai ga shi zalam-zalam, na dube shi na ce, ‘Wai Zurmi!’

Mutane sun dafo shi don su ga yadda zai canye ni. Da ya zo, ya ce, ‘To, fito, alkawari ya cika.!’

Sai na ce masa, ‘Dakata kad’an, in gama lallabce bangon d’akin nan da ya tsage da damina.’

Ya ce, ‘Kai, yaya ake d’inkin bango?’

Na ce, ‘Ai ba wuya a garinmu, lek’o ka gani.’ Sai ya cuso kai don ya gani.

Sai na yi farat na ta’ba kansa, na ce, ‘Ah, na ta’ba!’ Mutane suka ce, ‘I, ya ta’ba! I, ya ta’ba!’

 

Idan aka dubi yadda lamarin yake za a ga cewa, Alhaji Imam ya sha ta fi cikinsa. Ba wani abu da ya rage masa sai tunanin dabara. Da ma Bahaushe na cewa, dabara k’afa. Wannan ya sa ya shigo da dabarar lallabce bango. ‘Dinkin bangon d’aki abu ne da ba a san shi ba duk da yake an yarda bango na tsagewa kamar yadda k’warya take tsagewa. Abin lura a cikin zancen shi ne, Alhaji Imam ya danganta aikin d’inkin bango da garinsu kad’ai domin kada wani ya yi musun yin haka domin duniya fad’i ke gare ta. Abin da yake a nan, sau da yawa ba shi yake can ba. Shi kuma Zandori jin d’inkin bango ya sa shi mamaki har ya manta da ta’ba kansa, ya nemi ya ga yadda ake yi. Shi kuma Alhaji Imam ya san ba a gani sai tare da sunkaya kai domin idanu a ‘bangaren kai suke. Wannan ya sa Alhaji Imam ya nemi Zandori ya sa kansa cikin d’aki don ya gani. Idan aka yi la’akari da wannan wuri za a ga cewa, wayon da ya nuna a nan shi ne na k’irk’ira abin da ya sa’ba wa hankali don ya ceci kansa. Wannan ya sa Zandori ya yi hasarar sansa, shi kuma Imam ya ci banza.

4.3       Shigo-Shigo Ba Zurfi


Wayo ne da Bahaushe yake amfani da shi domin cimma wata manufa da ya sa a gabansa. A wannan wayo Bahaushe kan yi maraba da wani da ke nufin cuta masa ta yin amfani da dad’in baki da shimfid’ar fuska. A shafi na 28 an nuna irin wannan wayo inda Alhaji Imam ya ceci kansa daga ‘barawo. Ya sauka a wani gari Miska a gidan wani malamin addini. Wata rana da dare ‘barawo ya shigo d’akinsa. Ganin ‘barawon ya sa ya yi tunanin dabara, ya kuma ceci kansa da ita:

              Da ya matso kusa da ni sai na tashi, na ce, ‘Maraba, maraba. Ga tabarma nan ka zauna. Ashe za ka zo ka k’i gaya mini tun da rana da muka gamu kasuwa?’ Na yi ta yi masa magana kamar na san shi.

              Da ya ga haka, sai ya zauna yana tuna inda ya san ni. Ya juya wajena ya ce, ‘Ina ka san ni?’

              Na ce, ‘A! Ai tun tuni na san ka, bari ta kai ma duk danginka na san su, duk kuwa ma sun san ni. Na sha gamuwa da ‘yanuwanka k’warai har sun tambaye ni labarinka, ina cewa ban sani ba. Yau da dare Allah ya nufa sai mun sadu.’

              Ya sake dubana daga k’asa har bisa, ya ce, ‘Kai in ka san ni ina sunana?’ Sai na d’aga kai sama. Na yi ihu k’warai na ce, ‘Ai sunanka ‘barawo!’

 

A nan Alhaji Imam ya lura da had’arin da ke gabansa. K’ato, kuma ‘barawo da bai san wane shiri yake da shi ba ya shigo masa d’aki. Wannan ya sa ya k’i kowace irin kiza-kiza ko barazana. A maimakon haka sai ya bi ta dabara cikin ruwan sanyi ya kori ‘barawon. Bahaushe ya san dad’in baki abu ne da ke sa jikin kowane mutum sanyi. Wannan ya sa ‘barowan da kansa ya bud’a wa Alhaji Imam kafa ta yin kuwa da sunan fad’ar sunansa. Da wannan ana iya tantance wani wayon Bahaushe na dad’in baki don yi wa kai mafita da ceto a yanayi mawuyaci.

4.2       Dabarun Sata


Sata wani wayo ne ko wata dabara ce ta raba mai abu da abinsa ko dasaninsa ko ba da saninsa ba, amma ba da son ransa ba bale yardarsa (Bunza, 2014). Bahaushe mutum ne da ke amfani da dabaru don yin sata idan ya sami damar yin haka. Akwai Hausawa da yawa da suka d’auki sata wata k’awa ko sana’a. Wannan ya sa wasu k’abilu masu yawa suke tsoron sake jiki da Hausawa da kuma ba su amana. Akwai dabaru da Bahaushe ke amfani da su domin ya yi sata ga wani ko wasu. Dabarun sun had’a da shigar burtu da wayon wayo da sauransu.Wad’annan dabaru ana samun su wurare da dama cikin adabin Abubakar Imam.

4.2.1   Shigar Burtu


Wata dabara ce da ake amfani da ita domin a yi sata. A irin wannan shigar ce Bahaushe ke sanya sutura irin ta wasu mutane da aka sani da wani hali ko yanayi. Akan yi wannan shigar ce domin a amince masa, ad’auke shi cewa shi ma d’aya ne cikin wad’ancan mutane masu wannan shigar. Wannan zai sa a kar’be shi, a sakar masa jiki kamar wad’ancan mutane, sai daga k’arshe ya yi sata, ya gudu. A cikin littafin Ruwan Bagaja, a shafi na 7an kawo irin wannan dabara inda aka ce:

              Bayan na yi kwana saba’in ina tafiya, sai na isa Tamtubu. Na yi shiri irin na fatake, na isa gun Sarki, na ce ni falke ne, kayana suna baya, za su zo bayan kwana uku...Kullun da yamma sai in sami taro, in sayo miya, in bi k’ofar gidan da na sauka, in warwatsa ko’ina. Abin da ya sa nake haka, don ina da wani aboki ne attajiri’

 

Alhaji Imam ya isa Tambutu ba ya da komai, kuma bai bar komai a baya da yake zuwa ba. Isarsa wurin Sarki, maganarsa ta farko ya saka cuta (k’arya). Sarki Haka kuma kai tsaye ya shirya wa abokinsa zamba cikin aminci. A nan ma k’arya ya shirya, ya yi wa wanda ya amince da shi wayo, ya kar’bi dukiyarsa. Abin da ya sa ya sami wannan amincewa shi ne, shigar fatake da ya yi, ya kuma yi ik’irarin shi falke ne. Ganin wannan shiri nasa ya sa Sarki da attajirinn suka ba shi amana. A hankali ya kwashi kud’in attajiri da sunan jiran shanunsa a matsayin shi falke ne. Wannan na nuna Bahaushe mutum ne da ya nak’alci wayon shigar burtu, ya shirya yaudara da cuta bayan an amince masa cikin zamantakewa, kuma idan aka ba shi amana zai yi amfani da wayonsa na zamba cikin aminci ya yi cuta cikin amanar.

4.2.2   Wayon Wayo


Wata hanyar sata ce da Bahaushe ke amfani da ita ya yi wa wani mai jin wayo cuta. A duk lokacin da aka sami wani mutum da ke jin wata baiwa ta wayo, to akan sami Bahaushe ya bi ta wannan wayo nasa, ya yi masa wani wayo cikin ruwan sanyi. Ta wannan wayon wayo ne Bahaushe kan rungumi aradu, ya kutsa kansa cikin wata kasada, daga k’arshe ya yi sata cikin wannan hali. A shafi na 32 an kawo irin wannan wayo  inda ya ce,

Dare na yi, sai na sayi wata shar’be’biyar wuk’a na shiga gari yawon sata, sai na kawo ga wani babban zaure, na tarar da wad’ansu samari sun kunna fitila suna k’irgar dukiya, don gobe Salla, sun kuwa rufe k’ofar gidansu. Ko da na ga haka, sai na k’wank’wasa k’ofar, wani daga cikinsu ya ce, ‘Wane ne nan?

Sai na ce, ‘barawa ne.’

Suka ce, ‘barawo?’

Na ce, ‘I’

Suka ce, ‘To, da wacce ka zo?’

Na ce, ‘Na zo ne don in yi muku sata.’

Sai wani daga cikinsu ya ce, ‘To, zo saci!’

Ni kuma na ce, ‘Ku bud’e k’ofar zaure mana ku gani in ban sata ba.’

Sai babbansu ya tashi da fushi, ya bud’e zauren. Ni kuwa da ganin ya bud’e sai na fad’a ciki fagagam, na kashe fitilar, na dubi bangon na karta da wuk’a, na koma gefe guda na fad’i ris, na ce, ‘Wayyo Allah, ya kashe ni. Ko da suka ji haka, sai suka yi tsammanin wani d’an’uwansu ne na soka. Sai na ga duk sun yi cikin gida da gudu. Na tashi na nad’e kayansu sarai, na bar garin.’

 

Idan aka dubi wannan jawabin, Alhaji Imam ya yi amfani da wayon wayo ne ya yaudari samarin, ya yi musu sata. Asali an yi masa sata ne, kuma samarin nan ba su da labari. ‘Daukar fansa a kansu ba daidai ba ne. Wayon su samarin shi ne yawansu da suke ganin za su rinjayi ‘barawon da k’arfi. Wayon da shi kuma Alhaji Imam ya yi na gaggauta kashe fitila da karta yuk’a ga bangon d’aki da fad’ar wayyo ya kashe ni ya sa samarin suka tsorata, suka bar kud’insu, shi kuma ya kwashe. Yana sane cewa, kowane mutum yana tsoron mutuwa. Ya san da ya bari samarin suka gan shi, ko kuma ya tsaya kokawa da su da bai kai ga buk’atar da ya je da ita ta yaudarar samarin, ya yi musu sata ba. Falsafar da ke nan tana nuna Bahaushe mutum ne mai fasahar gaske da yake sarrafa ta ya yi nasara ko da cikin taron jama’a ne.

4.3       Wayon A Ci


          Wayon a ci wani nau’in wayon Bahaushe ne da yake amfani da shi domin ya yi wa kansa wata kafa ta samun abinci da wani matsayi cikin mutane. Domin nasarar wannan wayo, Bahaushe yakan yi amfani da dabaru irin na halin girma da kum ci da addini.

 

4.3.1   Halin Girma


Halin girma na nufin karimci ko kyauta ko shimfid’ar fuska ko kuma duk wani abu na sadaukar da kai don amfanar da wani ko wasu. Halin girma wayo ne da ke sa a amince da mutum a ja shi ga jiki, a ba shi amana da yarda. Duk lokacin da mutum ya yi wani abu na halin girma za a kyautata masa zaton zama zarumi, kuma abin yarda. Irin wannan wayo abu ne sananne cikin rayuwar Hausawa.

Hausawa mutane ne da ke nuna halin girma cikin zamantakewarsu da kowa. Bahaushe na ba abu baya ko da yana son sa don tsammanin ya sami wanda ya fi shi a can gaba. Wannan ya sa har karin maganar Hausa ke cewa, ‘Aje alheri bayanka, ka tsince shi gabanka.’ Abubakar Imam ya yi amfani da irin wannan wayo don cimma nasarar warware zaren labarinsa a wurare da dama. Ya yi amfani da halin ga tauraronsa Alhaji Imam da ke cikin littafin Ruwan Bagaja a shafi na 10 inda ya kawo cewa:

Ina tafiya sai ga wani yaro yana gudu za shi wurin biki. Na kira shi na ce, ‘Kai samari, yau garin lafiya?’

Yaron ya ce, ‘Dan’mori? Sarki aka kawo wa mata yau.

Na ce, ‘Daga ina?’

Yaron ya ce, ‘’Yar Sarkin K’aryatun Ni’am ce aka gama su.’ Ko da na shiga garin, ban ko zauna ba sai k’ofar fada wajen da ake biki. Na shiga biki, na yi ruwa, na yi tsaki, kamar k’anena aka sa a lalle. Nan da nan duk na shahara ga marok’a, suka tambayi sunana. Na ce, ‘Alhaji Imam.’ Ana biki da dala dala. Amma ni da fam guda guda, nake yi.

Wannan shagali da na yi ya sa Sarki ya yi maraba da ni. Muka yi abota da d’an Sarki, dare kad’ai ya ke raba mu.

Gaisuwa ko ina daga gidajen fadawa, da attajirai, da malamai da sauran manyan gari. Da haka fa duk na azzama cikin k’asar. Saboda haka wurina masu laifi ke kamun k’afa. Masu son sarauta gare ni suke nemanta.’

 

Idan aka yi la’akari da abin da Alhaji Imam ya aikata sai a ga wani nau’in wayon Bahaushe ya nuna k’arara. Yana cikin wayon Bahaushe ya yada abu don ya tsince shi gaba. Alhaji Imam ya kau da kai ga kud’insa, ya yi bikin da ba a gayyace shi ba, bai kuma san kowa ba ciki. Ya watsar da kud’insa ga marok’a. A maimakon ma ya yi yadda kowa yake yi, sai ya yi abin da ya fi na kowa don a san da shi. Wannan wayon ya sa ya sami farin jini da kar’buwa ga sarki da d’ansa har ya shiga cikin manyan fada da ake kamun k’afa da neman alfarma wurinsu. Haka ne da ma gurinsa.

4.3.2   Ci Da Addini


Wani wayo ne da wasu Hausawa suke amfani da shi su nemi abinci. A irin wannan wayo ne wani ke sake kamannunsa da halayensa, ya d’auki na wani mai addini. Yawanci masu irin wannan dabara idan suka sauka wani wuri, suka kuma lura mutanen wurin sun damu da addini, sai ya tattara kansa, ya koma kamar wani salihin bawa ko da kuwa shi ja’iri ne. Kintsa kai da zama kamili mai addini wani nau’in wayo ne na Bahaushe idan yana son ya sami matsayi ga wani ko wasu. Bahaushe mutum ne mai fasahar sauya kamanninsa ya yi irin na wasu mutane don cimma manufa. Hausawa da yawa sukan yi irin wannan sauya kama, su yi shiga irin ta mutanen Allah domin su sami kar’buwa da amincewa ga wani da sunan su mutanen Allah ne. Wannan ke sa a amince da su, su nemi abinci da wannan hali. Da irin wannan kamar sai mutanen wurin su girmama shi, su rik’a neman fatawa kan lamurran da suka shafi addininsu. Idan aka ci karo da su masu k’arancin sani ne, sai ya zan duk abin da ya gaya musu, da shi za su dogara. Abubakar Imam ya kawo irin wannan wayo lokacin da Alhaji Imam ya sauka garin Nasarawa ya shiga rigar malamai waliyya kamar haka:

..Na tafi wurin Sarki na sauka, na bid’i wani masallaci na kame, ba ni kome sai jan tasbaha. Duk garin aka yi ta kawo mini sadakar abinci iri-iri, sai na ta’ba ko loma biyu in k’i ci. Da ma na yiwo guzurin k’aton buhu cike da nakiya da gurasa, shi nake ci kullun. Abin da ya sa ba ni cin abinci da ‘yan garin suka kawo mini sadaka, so nake su mai dani Waliyyi ne, su rik’a girmama ni. Bayan kwana kad’an kuwa suka soma tsammanin haka nan. Kowa ya kawo abincinsa sai ya ce in sa masa ko loma don ya sami tabarrukin hannuna.

Haka na yi zamana garin nan abin girmamawa.Idan za a yi wani abu na addini kamar su salla, sai su ce in shige gaba. Ni kuwa ka san inda jahili duk ya kai na kai, saboda haka ko sun yi juyin duniyan nan sai in k’i. Kowane malami kuwa aka sa, sai ya rik’a nonnok’ewa, don yana tsoron kada ya yi d’an ‘bata, ga kuwa masu abin watau ni’ (shafi na 30-31).

 

Alhaji Imam a wannan wuri ya yi kama ce irin ta masu tsoron Allah. Ya tare Masallaci ga tasbaha yana ja koyaushe. Irin wannan siffa ce ta mutanen da ke da gudun duniya (zuhdu) da neman kusanci kawai da Allah. Da wannan wayo ake amincewa da su, aja su jiki, daga k’arshe su yi yaudara, wato abin da aka fi sani 419. A nan da wannan wayo ya sami kan mutanen garin har suka d’auke shi wani mutumin Allah, suka rik’a kawo masa sadakar abinci don neman albarka. Don ya tabbatar da wayonsa ya sa ba ya cin abinci mai yawa don ya k’ara tabbatar da waliyantakarsa. Wannan nau’in wayo na ci da addini sananniyar d’abi’a ce ga Hausawa masu yawa.

4.4       Kafin Ka Ga Biri...


Wani wayo ne na sanin dabarar mai dabara. A irin wannan wayo ne wani mutum ke shirya wata dabara ko don ya cuci wani, ko kuma ya kama shi, shi kuma wanda aka shirya wa dabarar ya san dabarar, ya kuma nak’alce ta. Bahaushe mutum ne da yake da hikimar hangen nesa da d’aukar hannu a duk lokacin da ya sami wani mutum ya shirya dabararsa. Da wannan wayo ne yake kintsa kansa, ya aje hankalinsa, ya yi wa wani lamari dogon nazari kafin ya auka masa.

A shafi na 10, Abubakar Imam ya kawo tauraronsa,  Alhaji Imam ya yi nasarar ku’buta daga tarkon K’wara. K’wara (farar fata) mutum ne da ke jin yana da wayo. Duk wayon K’wara Bahaushe na iya yi masa wayo cikin ruwan sanyi don ya yi wa kansa mafita, ko kuma ya yi yaudara.[10] Ga yadda aka kawo wayon Alhaji Imam ga K’wara;

A kwana a tashi, sai na yi gaba zuwa Sasa. Da shiga garin sai Allah ya yi mini gamo da katar, na sauka gidan wani K’wara mai sule. Na kama kaina sai ka ce wani mummini. Da K’wara ya ga halina, sai ya fara jana a jika. Bayan ‘yan kwanaki kad’an ya mai da ni yaronsa, ya sakan mini al’amuransa duka, na shiga cikin dukiyar ina bundum bundum, ba ni aikin fari balle na bak’i, sai dai ko da yaushe in wanke goma in tsoma biyar!’

..... Da K’wara ya ji haka, sai ya fara k’ok’arin da zai kama ni, ya sa a d’aure, ya hak’a mini wannan tarko nan in ku’bce nan, ya hak’a nan in ku’bce nan. Da ya ga haka, ran nan sai ya aiko a gaya mini ya mutu. Aka zo aka gaya mini, aka rarrashe ni in je in gani, don ba shi da d’a ba shi da jika sai ni. Ni kuwa na san halin K’wara da wayo. Ban dai k’i ta mutane ba, sai na tafi. Aka ce ga d’akin can, ko rufe shi ba a yi ba, sai na zo don ni ne d’ansa. Na lek’a ta taga, sai na gan shi kwance baki bud’e. Shi kuwa abin da yake so in shiga d’akin ne ya kama ni.’

Ko da na dube shi da kyau sai na yi sai na yi sansanar mutuwarsa, sai na ce, ‘Allah Sarki! Amma ban yi tsammani ya mutu ba.’

Wanda ya kira ni ya ce, ‘Subhana lillahi! Don me?

Na ce, ‘Don na ji an ce K’wara ba su mutuwa da baki bud’e sai a rufe. To, ga wannan K’wara nasa a bud’e.!’

Da K’wara ya ji jawabina, sai ya rufe baki wai don in yarda ya mutu; sai ka ce ni gaula ne. ‘Ashe, wanda ya mutu ya ta’ba motsi, balle har ya rufe baki?’ Ko da na ga haka, sai na yi waje.’

 

Idan aka dubi labarin za a ga cewa, Alhaji Imam ya riga ya cuci K’wara, kuma ba shakka ya san idan aka kama shi zai fuskanci hukunci. K’wara ya shirya masa tarko iri-iri yana tsallakewa. Wannan ya sa ya rik’a nisa da duk inda zai had’u da K’wara. Yana cikin haka sai aka gaya masa mutuwar K’wara wanda shi ne mak’urar wayon K’wara na kama Alhaji Imam. Tilas ta sa ya yi dogon tunani. Ya kar’ba kira, ya kuma amince ya je ya gani, amma a cikin shakku. Wannan ya sa ya k’i shiga d’akin da mamacin yake kwance sai dai kawai ya kula da yanayin da ya sami mamacin. A tunanin K’wara, Alhaji Imam ba zai tsallake wannan tarko ba. Shi kuma Alhaji Imam ganin bakin K’wara bud’e sai ya kawo zancen K’wara ba ya mutuwa baki bud’e. Idan aka dubi wannan zance sai a ga cewa, Imam ba cewa ya yi ba a mutuwa baki bud’e ba, cewa ya yi ‘K’wara ba ya mutuwa baki bud’e’. Abin lura a nan shi ne, ambaton K’wara ba ya mutuwa baki bud’e wata dabara ce ta kod’awa ya yi amfani da ita wadda ya san za ta iya yi masa mafita. Shi K’wara ya d’auki batun kamar wani ban girma, sai ya rufe bakinsa. Rufe bakin sai ya bayyana wautarsa a fili, domin ya k’aryata kansa, shi kuma Imam ya gudu. Wannan ya nuna hikimar Bahaushe ta kowane abu yana yi masa duba cikin tsanaki, sannan ya yi amfani da hikimarsa don nuna wayonsa da yi wa kansa mafita.

Ita ma wata yarinya mai suna Jamilatu da irin wannan wayo ne Alhaji Imam ya yi nasarar auren ta. Ya shiga neman ta ne tare da wasu samari biyu, suka zama su uku. Yarinyar ta rasa wanda za ta za’ba, saboda haka ta shirya mutuwar k’arya don ta tantance mai son ta na hak’ik’a. Mahaifinta ya je ya gaya wa sauran samarin biyu cewa Jamila ta mutu, suka nuna rashin damuwarsu har suka ce ‘Gwai’ Shi kuma Alhaji Imam da aka same shi sai ya nuna bak’in cikinsa. Ga yadda aka kawo wannan batun;

Tsoho ya sa kai ya fita, ya nufi gidana. Ko da na ji wannan jawabi, sai na yi shakkar mutuwan nan, ko da ya ke na san ikon Allah ya fi da haka. Nan da nan sai na ‘barke da kukan k’arya. Na ruga na sawo tufafi, na nufi gidan, ina matse-matsen k’arya. Da na isa gidan, na tarad da ita a kwance. Sai na rungume ta, ina salati. Da ta ji haka sai ta bud’e ido, ta ce a d’aura mana aure ta yi miji!Nan da nan aka d’aura mana aure da ita. Aka sa ranar biki, aka yi shagali aka gama’ (shafi na 14).

 

Abin lura a nan shi ne, dabarar Jamilatu ita ce ta sami mai son ta da gaske. Wannan ya sa ta shirya mutuwa wadda ba kasafai ake k’aryar ta ba. Shi kuma Alhaji Imam zamansa Bahaushe ya san kowace mace namiji d’aya yake auren ta a k’a’ida. Ya san dole a nemi yadda za a sami mutum d’aya da zai doke sauran mabid’anta, ya aure ta. Wannan ya sa da aka gaya masa mutuwarta ya ‘boye hankalinsa da shakkunsa, ya shirya kukan k’arya.

Kukan k’arya wani wayo ne da Bahaushe yake amfani da shi don cimma wata buk’ata. Kukan mutuwa wani hali ne na Bahaushe. Yana kuka don nuna tausayi da kuma jin ciyo na rashin da aka yi. Idan mutuwa ba ta zan kusa sosai ga Bahaushe ba, yana shirya kukan k’arya don a zaci shi ma ya ji ciyo kan wannan rashi. Wannan wayo na sa dangin mamaci su yarda da mai kukan a matsayin mai k’aunarsu. A nan Alhaji Imam ya shirya kukan k’arya har da rungumar gawar don ya nuna tsananin jin ciyo ga mutuwar Jamilar. Wannan wayo ya sa dabarar Jamilatu da mahaifinta ta tashi, da ita da danginta suka amince shi ne kad’ai mai k’aunarta cikin masu bid’anta. Don haka aka aurar masa da ita shi bak’o, aka bar ‘yan gari. Wannan yana nuna wayon Bahaushe na sanin dabarun rayuwa da zamantakewa.

5.0       Kammalawa


Idan aka yi la’akari da yadda wayo ya game littafin Ruwan Bagaja sai a ga cewa, shi ne ya zan k’ashin bayan jan zaren labarin. Idan aka auna yadda zaren wayon yake da rayuwar Hausawa, sai a ga cewa, wayo da aka yi amfani da shi cikin adabin, wani abu ne da yake da ainihin sila da rayuwar Hausawa ta zahiri. Wayon ceton kai da dabarun sata da wayon neman abinci abubuwa ne da Bahaushe ya yi suna da k’warewa kansu. Kasancewar Alhaji Abubakar Imam Bahaushe, ya sa ya yi wa adabin nasa zobe da wayo don ya nuna Bahaushe ne na hak’ik’a. Ya fito da yadda Bahaushe ke shigar burtu ya sauya kama da dad’in baki da halin girma da kasada da ba wani abu baya don ya kai ga buk’atarsa ta ceton kai ko cuta, ko wani matsayi da yake dubi. Wannan ya sa marubucin bai yarda ya kawo wani mutum daga wata al’umma da ya yi wa Bahaushe wayo ba komai kururuta wayewar kan wannan al’umma.

 

                                      Manazarta


 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

[1] .  Akwai karin magana masu yawa da ke nuni ga hikimar wayon Bahaushe. Misali, wayon mutum abinsa na hannunsa.

[2] . Alhaji Imam an yi rubuce –rubuce da dama kan adabinsa tun daga matakin digiri na farko har zuwa na uku da ma littattafai da aka riga aka wallafa. Kad’an daga cikin wad’annan ayyuka sun had’a da Pweddon, (1977), da Abdullahi, (1988), Buhari, (1988), da Nafi’u (2012).  Don ganin wasu rubuce- rubuce a dubi Bunza da Noofal (2013), Humanities in The Sub-Saharan World Ruwan Bagaja in Perspectives. UNICAIRO/UMYUK Special Research in Humanities.

[3] . Kalmar na d’aukar ma’anar hikima, Hausa, basira, ko fasaha da sauran kalmomin da ke nuna hazak’ar mutum.

[4] Skinner (1999)K’amus na Turanci da Hausa. Northern Nigeria Publication  Company,  Zaria. shafi na 91.

[5] K’amusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006), shafi na 82

[6] Hornby.A.S (2006) Oxford Advanced Learner’s Dictionary University Press NewYork shafi1688: Wisdom- the ability to  make sensible decisions  and give  good advice because of experience & knowledge  that you have.

[7] International Encyclopaedia  of  Education, Philosophy of  EducationVol.4.2010:  Consist  of the ability to solve problems & to adapt to learn  from everyday  experiences.

[8].  Bunza (2014), ya k’ara kawo wasu kalmomi da ya nuna suna fad’ad’a ma’anar wauta. Kalmomin ‘Iyani, Nad’ad’d’e, Ji’bananne, Kwashikwaram da kuma Fand’ararre da ya nuna dukkaninsu suna nuna ma’anar wauta

[9] .  K’abilar Buzaye Bahaushe na kallon wautarsu ta kan son banza, da son dukiya da raganci da k’arancin wayo. Su kuma Fulani ana kallon wautarsu ta hanyar saurin fushi, da saurin yarda, da k’arancin wayo. Su kuma Yarbawa da Inyamurai ta kan kud’i wautarsu ke bayyana.

[10].  Akwai wani labari da aka nuna wani Bahad’eje ya tafi Ingila sai kashi ya matse shi. Ya rasa yadda zai yi, sai ya shiga cikin wata fulawa, ya tsuguna ya shibga kashinsa. Yana tsugunne sai wasu ‘yan sanda suka hange shi, kuma suka lura ya dad’e tsugunne. Suka yanke shawarar su je su tambaye shi ko lafiya. Shi kuma da ya lura da su, sai ya yi wuf ya cire hular kansa ya rufe kashin. Da ‘yan sanda suka zo, suka tambaye shi, sai ya ce tsuntsunsa ne ya gudu daga cikin keji, shi ne ya kife cikin hula, kuma bai san yadda zai yi har ya je ya d’auko kejinsa ya mayar da shi ciki ba. Jin haka sai Turawan ‘yan sandan nan suka ce ya yi sauri ya je ya d’auko kejin su za su tsaya masa. Da ya wuce, suka ga ya dad’e bai dawo ba, sai suka yi shawarar su kama tsuntsun su tafi da shi ofishinsu in ya dawo sai ya je can ya kar’ba. Daga nan d’ayan ya ce d’ayan ya d’aga hular a hankali, shi kuma ya yi hanzari ya danne tsuntsun. Haka kuwa suka yi, d’aya ya d’aga hular. Ko da shi kuma d’ayan ya buga rida a k’ark’ashin hular da nufin kama tsuntsun sai ya ca’ba hannunwansa cikin kashi. (Filin Mu Sha Dariya a Jaridar Aminiya ta ranar 21 ga Maris, 2014).

Post a Comment

0 Comments