Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Hada-Hadar Kudi A Tattalin Arzikin Hausawa: Duba Ga Wasu Littattafan Kagaggun Labaran Hausa

Daga

Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
aliyubunzaumar@yahoo.com
07063532532, 08095750999

www.amsoshi.com

Money is one of the most important things that hve direct and indirect impact on the life of people. It is with money that people buy, sale as well as paying taxes etc. In Hausa society, money plays important role in changing the minds of many people. Many Hausa people change their decision for the purpose of money. It is in view of the above, that the paper aimed at studying the role of money in some Hausa novels which include Ruwan Bagaja, Tura ta Kai Bango, Fitsarin Fak’o Mallakin Zuciyata, ‘Yartsana etc. The method used for this study, is the reading and analysing of some portions of the novels in which the role of money is found.

1.0       Gabatarwa


Dukkan lamurran tafiyar da rayuwar d’an Adam a yau sai tare da kud’i suke tafiya yadda ya kamata. Da kud’i ake hada-hadar kasuwanci mafi sauk’i. Da kud’i ake nuna isa da neman girma da alfarma da sauransu. Ganin irin matsayin kud’i a al’amurran duniya ya sa wasu mutane suke neman kud’i ido rufe. Mutum kan sauya tunaninsa don ya ga kud’i, ko don a ba shi, ko kuma don an ba shi. Wannan ya zama ruwan dare har cikin adabin Hausa.

K’agaggen labari nau’i ne na rubutaccen adabin Hausa, kuma wata taska ce ta musamman da ake iya tsintar kowane irin abu da ya shafi rayuwar d’an Adam. La’akari da kusancin rayuwar mutum da kud’i ya sa wasu marubuta labaran suke sakad’a yadda kud’i ke sauya tunanin mutane cikin wasu sassan labaransu. Manufar wannan mak’ala ita ce, nazarin hada-hadar kud’i a tattalin arzikin Hausawa daga wasu littattafan k’agaggun labaran Hausa.

2.1       Dangantakar d’an Adam Da Kud’i


Tun da Allah (SAW) ya halicci mutum ya k’awata masa son wasu abubuwa guda 7 cikin zuciyarsa. Kud’i na d’aya daga cikin wad’annan abubuwa. Allah ya ce:

An k’awata wa mutane son sha’awoyi daga mata da d’iya da dukiyoyi abubuwan tarawa daga zinariya da azurfa, da dawaki  kiwatattu da dabbobin ci da hatsi. Wannan shi ne dad’in rayuwar duniya. Kuma Allah a wurinSa kyakkyawar makoma take (Surah ta 3: 14).

Kud’i sun kasance abokan rayuwar mutum ta yadda kowane irin abu na rayuwa da su ake yi. Neman biyan buk’atar rayuwa ya sa wasu mutane ke neman kud’i ta kowace hanya. Wasu mutane kan rasa rayukansu wajen neman kud’i. Wasu kuma sukan halaka wasu don su sami kud’i. Wasu kuma sukan bi kowace irin hanya ta gaskiya ko rashin gaskiya don kud’i kawai. Lamarin kud’i ya sa tunanin mutane da yawa yakan sauya daga fari zuwa bak’i, ko daga bak’i zuwa fari. A yau mutane da yawa ba su da tsayayyen tunani, ba su da tsayayyar magana ko za’bin rai saboda kud’i kawai.

3.1       Kud’i A Adabin Bakan Hausa


Adabin bakan Hausa (adabin gargajiya) shi ne adabin da Hausawa suka gada daga kaka da kakanni. Wato adabin da yake asalinsa, in ma daga wani wuri ya zo, to, yana da nisa (‘Dangambo, 1984: 9). Shi wannan adabi fage ne mai fad’i da ya k’unshi lamarin rayuwar mutane ta kowane gefe. Cikin adabin bakan Hausa akan sami abin da ya shafi zamantakewa, tsarin mulki, addini, da sauran abubuwan da mutane suke so, ko kuma suke k’i. Lamarin kud’i na d’aya daga cikin abubuwan da ake hangowa cikin adabin. Wannnan ya k’unshi tasirin kud’i cikin rayuwar mutane ta hanyar fa’ida da illa. Da yake adabin baka na da rassa daban-daban zan dubi karin magana da wak’ok’i da labarai don ganin tasirin kud’i a rayuwar mutane.

3.1.1    Karin Magana


Karin magana na d’aya daga cikin muhimman rassan adabin bakan Hausa da ke k’unshe da lamarin rayuwar Hausawa. Shi dai karin magana  wata ‘yar gajeruwar jimla ce ta hikima wadda ta k’unshi ma’ana mai yawa in za a tsaya a yi bayaninta (Muhammad, 2005: 59). Karin magana fili ne babba da ke k’unshe da darussa masu yawa da suka shafi rayuwar mutane. K’imar kud’i a rayuwar mutum na cikin darussan da ake iya gani cikin karin magana. Ga misali:

Kud’i abin zaman duniya

Kud’i ba ku son k’azamar buk’ata

Kud’i na gwamna masu gida rana

Kud’i tushen jin dad’i

Yaro nemi kud’i tun abin saye bai zo ba

Kud’i maganin wata magana

Yaro da kud’i abokin tafiyar manya

Yaro ba kud’i abin tausayi

Nazarin wad’annan karuruwan magana ya nuna cewa, Hausawa na kallon kud’i da wani matsayin na musamman a lamurran rayuwarsu ta duniya. Wannan ya k’unshi yadda kud’i ke mai da yaro babba da wurin neman kud’i da yadda kud’i ke iya kashe kowace irin magana da yadda mutum ke zama abin tausayi don rashin kud’i da sauransu. Daga wad’annan karuruwan magana ana iya ganin hoton yadda kud’i suka zan komai da ruwanka cikin rayuwar mutane.

3.1.2    Wak’ok’i


Wak’a magana ce mai k’unshe da sak’o da ta shafi za’ben kalmomi da tsara su cikin tsarin da ba lalle sai ya dace da maganar yau da kullum ba (Yahya, 1997). A cikin wak’ok’in bakan Hausa, mawak’a kan sanya abubuwa masu yawa don ilmantar da al’umma da nishak’antar da su, ko yin zambo da sauransu ko da kuwa ba kan wannan jigon suka shirya wak’a ba. Da yawa akan sami lamarin da ya shafi amfanin ilimi, kiyon lafiya, sana’a, tarbiyyar yara, kula da addini, da sarrafa kud’i ta kashe su inda ya dace da kuma nuna had’arin kud’i a wasu lokuta. Fitacciyar wak’ar Hausa da tafi nuna matsayin kud’i a rayuwar mutane ita ce ta Abdu Wazirin ‘Dan Duna mai gindin wak’a kamar haka:

Uban wak’a: Tsakanin d’an Adam da kud’i

A cikin wannan wak’a Abdu ya fad’i abubuwa da yawa da kud’i ke sa mutum ya aikata kamar sawa da hanawa, shiga kunya da fita kunya, kowace irin huld’a, d’ebo rigima, zare ido, lumshe ido da sauransu. Ga kad’an daga cikin d’iyan wak’ar:

Yanzu ba wata haraka sai kana da kud’i

Saboda ba ka sawa sai kana da kud’i

Kuma ba ka hanawa sai kana da kud’i

Zamani ya zo sai kana da kud’i

Ba ka komi sai kana da kud’i

Ba a yi maka komi sai kana da kud’i

Kuma kakan gaza komi in kana da kud’i

Kana iya komai don saboda kud’i

Akan shiga kunya ma saboda kud’i

Akan fita kunya ma saboda kud’i

Ana shanye hud’d’a saboda kud’i

Ana d’ebo rigima saboda kud’i

Ana yajin aiki saboda kud’i

K’aramin yaro saboda kud’i

Ka ga anai masa ban girma saboda kud’i

Ana son mummuna saboda kud’i

Ka ga ana k’in kyakkyawa saboda kud’i

 

Idan aka yi la’akari da wad’annan baituka za a ga cewa, mawak’in ya nuna rayuwar mutune a yau ta kasance ta kud’i inda kud’i ke sa mutum ya aikata kowane abu ko mai kyau, ko maras kyau.

3.1.3    Labarai


Labari wani zance ne da akan shirya shi a gargajiyance na hikima da yake zuwa kai tsaye a kan wani abu da ya ta’ba faruwa ko ma wanda ba a ta’ba yin sa ba a sakamakon huld’a da jama’a (Gusau, 1984). Labari adabin baka ne da ya taskace lamarin rayuwar mutane na abubuwa da yawa. Da yawa akan sami labarin mutuwa, haihuwa, aure, kasuwanci, kishi da sauransu. Ba wani labari da ba ya d’auke da wani abu na rayuwar mutane da aka shirya don wani darasi da nishad’antarwa. Akan ci karo da wasu labaran baka da ke nuna lamarin hada-hadar kud’i da tasirin kud’i a cikin rayuwar mutum. Ga misali, labarin Matafiya Biyu yana k’unshe ne da irin yadda hada-hadar kud’i ke sauya tunanin mutum. Wasu matafiya ne su biyu Abdu da Ali suna cikin tafiya za su wani gari sai suka hangi k’unshi a gefen hanya. Ali ya d’auka ya bud’a sai ya ga kud’i ne. Abdu ya ce ‘Kai, mun taki sa’a’ Ali ya ce’A’a! Mun taki sa’a, ko dai na taki sa’a?’ Abdu ya ce ‘To Allah ya ba mu lafiya’

Suka ci gaba da tafiya. Sun yi nisa cikin wani bak’in daji sai ‘yan fashi suka ‘bullo musu. Suka ruga da gudu, ‘yan fashi suka bi su. Can Ali saboda nauyin kayansa sai ya kasa gudu, ya ce, ‘Wayyo! Yau za mu yi hasara’ Shi kuma Abdu da yake can gaba sai ya ce, ‘A’a. Za mu yi hasara, ko dai kai zaka yi hasara’ (Sudan Interior Mission, 1938: 10-11).

Wannan labari ya nuna yadda mutum ke yin butulci ga abokinsa saboda kud’i. Ali wanda yake tare da abokin tafiyarsa Abdu komai bai shiga tsakaninsu ba, sai da ya sami kud’in tsintuwa sannan ya san kansa kad’ai. A wannan wuri an nuna son kan Ali ya fito fili saboda dalilin kud’i.

Shi kuma labari Mai take Maci Amana Yana Tare Da Kunya  labari ne na wasu aminai biyu; Ali da Tanko. Wata rana Ali zai yi tafiya sai ya sa kud’insa cikin wani bango ya d’ura zuma ya lik’e. Ya je ya kai wa Tanko don ya aje masa har ya dawo. Bayan shekara biyu, sai Tanko ya bud’e don ya ga ko zumar ba ta lalace ba. Ko da ya zubo sai ga kud’i. Nan da nan ya kwashe, ya nemi wata zuma ya lik’e, ya aje. Ana nan Ali ya dawo ya tambayi Tanko ajiya. Tanko ya kawo ya ba shi. Ko da Ali ya bud’e bango ba kud’i. Nan suka ta yin rikici har suka isa kotu. Alk’ali ya sa aka kirawo dillalan zuma ya tambaye su ko tsohuwar zuma ce wannan. Suka ce a’a. Nan Alk’ali ya sa Tanko ya biya kud’in Ali, aka kuma yi masa hukuncin zamba cikin aminci. (Sudan Interior Mission, 1938: 28).

Wannan labari ya nuna kud’i ne suka sauya tunanin Tanko daga aminci zuwa zamba. Tanko ya yaudari abokinsa ta yadda ya musanya masa ajiyarsa da abin da ba ita ba bayan ya kwashe masa kud’i.

Yanayin kowane d’aya daga cikin wad’annan rassan adabin baka ya nuna tasirin kud’i wajen sauya tunanin wani mutum. An ga yadda kud’i suka ‘bata zaman aminci da kuma tafiya tare.

4.1       Hada-Hadar Kud’i a Tattalin Arzikin Hausawa a Wasu Littattafan K’agaggun Labarai


K’agaggun labaran Hausa wasu littattafai ne wad’anda wasu mutane da Allah ya yi wa baiwar hikimar tsara tunani da shirya shi don isar da wani sak’o da suka rubuta. Su wad’annan littattafai an fara samar da su ne daga shekarar 1933 lokacin da Hukumar Talifi ta shirya gasar k’aga labari. Tun daga wannan lokaci zuwa yau, an samar da littattafai masu yawa da ba a tantance adadinsu ba. Malumfashi (2010) ya nuna a wajajen shekarar 2010 akwai littattafai sama da 3,500. An shirya littattafan kan jigogin ilmantarwa, soyayya, zaman aure, da sauransu.

Tasirin kud’i wajen sauya tunanin mutum ya kasance d’aya daga cikin muhimman k’ananan jigogin da suke taimakawa wajen warware manyan jigogin wasu littattafai. Wannan kuwa ya shafi yadda kud’i ke sa wani ko wasu su aikata wani aiki kamar na kisan kai, ko sata, ko fashi, tona asiri ko rufa shi, fyad’e, zina ko sauya akalar shari’a. Ga misali a littafin Ruwan Bagaja na Alhaji Abubakar Imam (1934) an kawo yadda kud’i suka sa wani Alk’ali ya sauya akalar shari’a. Ga yadda aka kawo batun a shafi na 12:

‘Na ce, ‘Malam ‘Dalhatu da d’an’uwansa sun shaida. Malam Sule da d’an k’anensa malam Hashimu sun shaida. Bari ta su ma, har autansu Malam Muhtari yana nan aka yi. Wad’ansu mutane ma kamar d’ari masu zuwa da tsakad dare duk za su shaida!’

Ko da malam ya ji haka sai ya fahimta da maganata. Malam  ‘Dalhatu da d’an’uwansa dala biyu ke nan. Malam Sule da Malam Hashimu kuwa sule da sisi ke nan. Malam Muhtari kuwa taro ke nan, mutane d’ari ke nan masu zuwa da tsakad dare kuwa sule d’ari ke nan.

Watau da tsakad dare zan kawo masa sule d’ari da shida ba taro idan ya ba ni gaskiya. To, yanzu zamani ne dai na wanda ba mai gaskiya sai mai sule. Nan da nan mai bakin cin rashawa ya birkita maganar, ya ba ni gaskiya. Aka d’aure bak’auye wata uku don ya sa mini sata. Da dare na kawo wa Alk’ali wad’annan, na koma na shiga shagali da sauran.’

 

Idan aka dubi yadda aka kawo wannan batu ya nuna yadda kud’i ke sauya tunanin mutane. Alhaji Imam ba ya da gaskiya a shari’ar, shi kuma bak’auye ba ya da kud’i. Lokaci guda Alhaji Imam ya gabatar wa Alk’ali zancen kud’i sai aka ba shi gaskiya. Ba don kud’in da ya gabatar da zancensu ba, da Alk’ali ya tabbatar wa bak’auye gaskiyarsa.

 

A littafin Tura Ta Kai Bango marubucin ya kawo yadda kud’i suka sauya tunanin wasu mutane suka aikata wani abu da ake son su aikata ba tare da nazarin sakamakon abin ba. A shafi na 45 an nuna yadda aka yi amfani da kud’i aka had’a wata mata fitina da d’anta. Wani mai suna Alhaji Kaukai ya je wajen matar tare da wani yaronsa mai suna Karen ‘Buki inda bayan sun gaisa da ita suka gabatar da buk’atarsu, daga nan Alhaji ya kawo kud’i ya ba ta. Ga yadda aka kawo batun:

‘Alhaji ya ce, ‘To kin ji dai abin da muka gaya miki. Muna fatan ki sami shawo kansa. Ga kuma wannan ki sayi nono’ Ya kawo naira ashirin ya ba ta. Ita kuma ta yi ta sa musu albarka har suka fita. Na farko dai tana ganin ga shi sun zo sun fad’a mata gaskiya game da d’anta. Na biyu kuma ga naira ashirin ta samu haka tun da sassafe. Abin da rabon da ta sami masu yawansu tun wata shekarar da sulu ya yi tsada.’

Idan aka yi la’akari da wannan batu za a ga cewa, samun wannan kud’i ya sa matar ta sa wa Alhajin albarka, kuma ta gaskata abin da ya gaya mata tun kafin ta bincika. Wannan ya faru saboda ta dad’e ba ta sami kud’i masu yawan wad’anda ya ba ta ba. Haka kuma abin da ya nemi ta yi na jan kunnen d’anta Hassan, haka ta yi lokacin da ya dawo gida. Ga yadda aka kawo abin da ya biyo baya a shafi na 49:

Zuwa can ta nisa ta ce, ‘Yanzu d’an nan irin sakamakon da za ka yi wa mahaifinka ke nan? Yana kwance k’asa maimakon ka dinga yi masa addu’a sai ka je ka shiga cikin kahurai?...’

Wannan ya  nuna tunanin matar ya sauya domin tsawon zaman ta da Hassan ba ta ta’ba jin irin wannan zance ba sai wannan karo. Haka kuma wannan karo ne na farko da ta yi sa-in-sa da shi. Shi ma shafi na 69 an kawo yadda kud’i suka sauya tunanin wata yarinya har aka ci kanta, aka biya buk’atar da ake so kanta. Ga yadda aka kawo batun:

Ruga ya d’an ja ta waje guda suka gaisa. Bayan da za su rabu sai ya kawo naira d’ari ya ba ta, ‘yan Murtaloli guda biyar. Shi ma Taiki ya yi wa tasa yarinyar kyauta, kana suka yi ban kwana da su da cewa za su dawo kwanan nan..

Ashe kuwa wannan kyauta ta Naira d’ari, ta rikitar da ita, ta kuma ba ta mamaki. Ita da za ta dawo hutu daga gida bai fi a ba ta Naira ashirin ba, sai ga naira d’ari, Murtala ko canzawa ba a yi ba. Ta kwana tana mamaki da murna. Don haka yau da aka ce ta zo, da rawar jiki ta zo, ta gaishe da su cikin harshe na girmamawa. Kuma da aka ce su je su shirya za a d’an je yawo da su, ba ta tsaya wata-wata ba, ta je ta shiryo.’

 

Idan aka yi la’akari da wannan wuri za a ga cewa, kyautar kud’i da aka ba wannan yarinya ya yi tasiri k’warai wajen sauya tunaninta har aka yi nasara kanta. Kud’in suka rikita ta, ta yi d’a’a da girmama wannan mutum da ba ta san shi ba, kuma karo na farko ta gan shi ke nan. Daga k’arshe ya d’auke ta ya je ya biya buk’atarsa kanta. Irin haka yake faruwa kan wasu mata da yawa.

Shi ma marubuci littafin Fitsarin Fak’o ya kawo irin wannan tasiri na kud’i da sauya tunani da suke yi na mutane. Wani mai suna Tahir Hassan ne ya yi amfani da kud’i don binciko wasu bayanai, kuma ya yi nasara. Ya yi amfani da kud’i a wani Hotel inda ya sami bayanai na farko daga wani ma’aikacin Hotel duk da hana fitar da bayanan da Hotel ya yi. Bayan kashe Faruku wani abokinsa ya je Hotel na Daula da can ne aka ce ya sauka. Da yake Hotel d’in na da tsaurin mataki kan kar’bar cin hanci, kuma yana son bayani kan wani d’aki da ya lek’a cikin dare, sai ya yi amfani da kud’i ta wata dabara ga d’aya daga cikin ma’aikatan wurin ya sami bayani.  Ga yadda abin ya wakana.

‘Na dubi saurayin nan, muka had’a ido, na yi murmushi. Na ce, ‘Da za ka yarda, da mun d’an zanta da kai. ....na sa aka kawo mana lemun kwalba, muka sami wuri muka zauna. Na sa hannu a aljihu na zaro ‘yar Murtala sabuwa fil na aje a k’ark’ashin kwalbar  lemuna. Idanunsa suka shiga karakaina tsakanin Naira ashirin d’in da fuskarsa. Duk ya k’osa ya ji abin da zan ce....Amma kuma saboda yabawa da kirkin da ka yi mini, nake so in ba ka wannan ka sayi goro. Take na ga ya saki jikinsa. Na mik’a masa Naira ashirin d’in nan, ya kar’ba, ya rik’e ya k’i sa ta a aljihu. Ya ce wane tsegumi kake so in yi maka?’ (shafi na 24).

La’akari da yadda wannan bayani yake, ya nuna ma’akacin ya amince ya bayyana sirrin ne bayan da ya kar’bi kud’i. Ba don da ya kar’bi naira ashirin ba, da bai amince ya ba da bayanan ba. Shi Tahir ma yana sane da yadda kud’in za su iya sauya masa tunanin ma’akacin, wannan ne ya sa ya fitar da su.

Tahir Hussaini a ci gabansa na binciko lamarin mutuwar Faruk ya had’u da Madam Vera a gidan Yashi Kulob inda ya yi amfani da kud’i don samun biyan buk’atarsa. Lokacin da ya tattauna da ita bai sami kanta ba sai da ya had’a da kud’i. Ga yadda aka kawo batun a shafi na 59-61:

...ta yi ‘yar dariyar jin dad’i, ta ce, ‘wace ni?’

Na yi dariya na ce, ‘Ashe  kin ji Hausa kamar jakin Kano.’

Ta ce, ‘A’a kad’an dai’

Na fitar da kud’in da ke aljihuna na d’an yar da su. Na lura Madam Vera ta k’yalla ido ta gan su. Na mayar cikin aljihu. Na ce, ‘ban sani ba, ko zai yiwu ki ba ni d’an lokaci mu tattauna...’

‘Ka san ni ne da ma?’

Na ce mata ‘Ina jin na san ki, sai dai ba zai yiwu mu ci gaba da magana a nan ba. In dai kin yarda to mu ke’be kad’an’ Na sake fito da kud’in na ware Naira dari biyu na ajiye bisa tebur. Sai fuskarta ta canza....’

Ta ce, ‘Shi ke nan, za mu iya zuwa d’aya daga cikin d’akunan manyan bak’i da ke sama..’

Biya na aka yi in sa ido a kan Faruk, ko da zan same shi da wasu takardu da aka aiko daga Afrika ta Kudu in kai rahoto.’

 

A nan Tahir ya sauya tunanin Madam Vera ne da kud’i. Ya yi amfani da dabarar da ya yi amfani da ita a Hotel, ya fitar da kud’i ya sami kanta, ta saurare shi har ta sanar da shi abin da ya faru kan abokinsa Faruk. Ba don tasirin kud’in da ta k’yalla ido ta gani suka sauya tunaninta ba, da wata k’ila ba ta saurari Tahir ba.

Shi ma Sulaiman Ibrahim Katsina a litafinsa na Mallakin Zuciyata ya kawo yadda aka yi amfani da kud’i aka sauya tunanin mahaifiyar wata yarinya kan maganar aure. Ga yadda ya kawo labarin a shafi na 118-119:

 

‘Alhaji ya sake d’aukan naira d’ari ya ba wa yaronsa. Can hantsi na yi ya je ya iske uwar yarinya ya gaya mata abin da ya kawo shi. Ya kuma kawo naira hamsin ya ce, Alhaji ya ce a kawo mata. Ta amshi kud’i, ta ce a gaya ma Alhaji in dai wajenta ne ba damuwa. Sai dai wajen yarinya da ubanta...

Da Sakina ta dawo daga cikin gari, kud’in suka sa uwar ta gaya mata cewa, ‘Zo nan zauna kusa, yau abin arzikk’i ya same ki. In kin yarda kin dace ainun..’

Uwar ta ce, ‘Yau ga zancen banza. Alhaji ne mummuna? Je ki ki ga matansa mana. Ga shi kuma da arzik’i.’

 

Abin da ya faru a wannan wuri tsakanin Alhaji Garanhotsami da mahaifiyar Sakina ya nuna kud’in da ya aika mata ne suka sa ta bijere wa yaron da ta san yana tare da d’iyarta tun da dad’ewa. Da wannan ta sauya tunaninta, ta shiga jan hankalin Sakina ta hanyar nuna mata matsayin Alhaji don ta amince ta so shi.

Shi ma Ibrahim Sheme a littafinsa na ‘Yartsana ya kawo tasirin kud’i da yadda suke sauya tunanin wasu mutane su aikata wani abu. Ga yadda ya kawo yadda wani mai suna Alhaji Maidogonsoro ya yi amfani da kyauta ya sauya tunanin wata tauraruwa mai suna Zainab da kakarta Kandala:

‘Nan fa ya dinga ba Zainab kyaututtukan kud’i da kayayyaki, ya na kuma ba Kandala. Da fari Zainab na jin tsoro, ganin cewa akwai igiyar aure a wuyanta, kuma ga shi Alhaji sa’an tsohon ta ne ...To amma Kandala ta k’arfafa mata gwiwa, ta ce ta rik’a kar’bar duk abin da ya ba ta. Ba a jima ba ta rik’a kar’bar duk abin da ya ba ta. Ba a jima ba ya rik’a d’aukar Zainab ya na kai ta wani gidan sa na shak’atawa a bayan gari...’ (shafi na 91).

La’akari da wannan wuri, ya nuna kud’i ne kan gaba wajen sauya tunanin mutane domin a nan kud’i ne aka kawo kan gaba ga kyautar da Alhajin ke ba Zainab. Da wannan kyauta Kandala ta k’arfafa wa Zainab k’afa, ta ci gaba da huld’a da Alhaji har ita ma ta saba, ta cire tsoro. Wannan ya nuna irin tasirin kud’i wajen sauya tunanin mutane a yau.

A littafin Turmin  Danya akwai yadda wani mai kud’i mai suna Alhaji Gabatari ya je neman wata kwangila a wajen wani shugaban ma’aikata. A k’a’idar wurin ba a barin masu son yin aikin su san sirrin tsare-tsaren aikin. Shi Alhajin ya yi amfani da kud’i inda kai tsaye aka karya k’a’idar. Shi Alhaji Bagatari bayan ya je wajen cayaman sun gaisa ya gaya masa ya sami labarin sun fitar da kwangila. Ya ba cayaman kud’i don ya sami haske kan tsarin aikin. Ga yadda aka kawo batun yadda suka yi da shi:

Alhaji ya ce, ‘To’ Sa’an nan ya sa hannu aljihu ya d’auko kud’i Nera dubu ya ba shugaba. Ya ce, ‘Ga wannan a saya ma yara cakuleti’

Kai har da d’awainiya. Ka bari man....’

Cayaman ya kar’ba ya ce, ‘Na gode k’warai. Sai ka biya wajen Sakatare ya baka istimet d’in kwangilar ka gani.’

 

Da ya isa ofishin Sakatare suka tattauna, sai sakatare ya ba shi tsarin kwangilar abin da kuma ba a haka a k’a’idarsu ba. Ga yadda suka yi:

...Ya kulle kabod d’in sa’an nan ya zo ya mik’a ma Alhaji wannan takarda. Ya mayar da makullan cikin aljihun teburinsa, ya ja kujerarsa, ya zauna.’

Ya ce ma Alhaji, ‘Ka duba ko? Ofisoshi uku ne za’a gina. Guda mai ciki biyu, wato kamar ofisoshi hud’u ke nan. Kuma za a yi su ne kan Nera dubu d’ari. Ina jin yau zaka rubuto ko? (shafi na 36-38).

 

Da aka taru wurin bitar takardun masu neman kwangila, kwamitin ya amince da takardun Alhaji Bagatari ba don cancanta ba, sai dai don kud’in da ya ba su. Ga abin da marubucin ya nuna:

‘Da fad’in haka su sauran sun fahimce shi sun kuma gane wanda ya kamata a baiwa, sun kuma amince. Domin kuwa ban da Cayaman da Sakatare, babu wanda Alhaji bai kaima Nera d’ari biyu a gidansa ba, ko kuma ya aika masa’ (shafi na 44).

 

Wannan dogon bayani ya nuna kud’i ne suka sa wad’annan mutane masu alhakin kula da kwangilar suka sa’ba k’a’idarta. Ciyaman da ya kar’bi kud’in Alhaji, sai ya ba shi dama ya je ya ga Sakatare. Shi kuma Sakatare da ya ji ta kan Ciyaman Alhaji ya biyo, shi ma sai ya mik’a wuya, ya nuna wa Alhaji takardun asirin kwangilar har da yi masa bita. Nan shi ma ya kar’bi nashi rabon. ‘Yan kwamitin ba da kwangilar su ma da yake kowanensu ya kar’ba, dole suka amince  a ba shi. Wannan duk ya faru ne saboda tasirin kud’ad’en da suka kar’ba, tunaninsu na kiyaye k’a’ida ya sauya, suka aikata wani abu daban.

A wani wurin a wannan littafi an nuna yadda lamarin kud’i ya sa Alhajin bai yarda da kowa ba. An nuna mahaifiyarsa ma ba ta tsira ba domin koyaushe lamarin kud’i ya shiga tsakaninsu sai ya zarge ta. Ga yadda aka kawo batun:

‘Akwai ma labarin da ya bazu cikin Karaini, musamman ma wurin na kusa da shi Alhajin, game da uwarsa da shi, game da kud’i. In har ya bata don a yi wani abu, to sai yayi ta zarginta ko ta saci wani abu daga ciki. Duk wanda zai yi tu’ammali da kud’insa, gani yake sata yake yi masa. Sanin yadda ma yake ma uwarsa yasa mutane basu faye damuwa da halinsa ba.’

Bansuwai ne kuwa yaji shi wata rana yana cema uwar, wai ya bata kud’i game da haihuwa duk ta kashe, bata yi abin da ya ce ayi da kud’in ba. In ba kashewa tayi ba, ya ya za’a ce har wad’annan kud’i sun k’are. Shi in tana haka bai k’ara sa kud’in duk da za’a yi wata hidima hannunta, sai ya sa hannun amarya’ (shafi na 47-48).

 

Lamarin kud’i abu ne da ya kai gaya ga wasu mutane. Alhaji irin mutanen nan ne da kud’i kan mantar da su komai. A bayanin da ke sama ya nuna kud’i kan sa Alhaji ya fita hayyacinsa, ya ci zarafin kowa. Bai aminta da kowa ba cikin sha’anin kud’i. Mahaifiyarsa ma wadda ak’alla ta ci a ce ta tsira, ba ta tsira ba. Zargin da yake yi mata ya tabbatar da cewa, kud’i suka sauya tunaninsa gaba d’aya, ya manta da girma ko matsayin kowa. Haka wannan rayuwa take  ga wasu mutane da yawa. Kud’i kan sauya tunaninsu, su manta komai, su kuma aikata komai ido rufe komai muninsa.

Shi ma littafin Tsumangiyar Kan Hanya marubucinsa ya kawo yadda kud’i ke sauya tunanin wasu mutane. Wani mutum ne mai suna Malam Sambo wanda daga farko shi talaka ne k’warai. Ana nan ya sami hanyar samun kud’i abin da ya sauya tunaninsa ya fara neman mata. Da kud’in suka k’aru sai ya sake sauya tunaninsa gaba d’aya. Ga yadda aka kawo sauyin tunanin nasa:

‘Ganin kud’i na shiga na fita a hannun Sambo sai ya sake wani sabon salo na neman mata, ya kuma yi mirsisi da magan-ganun jama’a, suna da d’aurin aure, da jana’iza duk ya k’aurace musu. Kyauta ga karuwai, da ‘yan daudu ya k’aru, yaran ‘yan daudu kuma suka sami dokinsu mai dad’in hawa, da zaran sun hango shi tafe kafin ya k’araso gidan matan sai sukan yi rige-rigen bud’e masa motar da gaisuwa don neman shiga domin sukan washe, sukan kuma ci kaji da k’wai da soyayyar doya da ‘yan daudu ke yi a k’ofar gida. ...Sambo bai tsaya kurum ga bai wa karuwai kud’i ba har kayan d’aki yakan yi musu, ya kuma biya musu kud’in haya, ya d’auki d’awainiyar su, san nan ya kawo na taba da giya ya ba su..’ (shafi na 40).

Idan aka yi nazarin wannan wuri za a ga cewa, lallai kud’i suka sauya tunanin Malam Sambo. Da can shi talaka ne wanda sai da k’yar yake samun abinci. Wannan yanayin rayuwa ya sa bai damu da kowace mace ba sai matarsa d’aya. Da ya fara samun kud’i, sai ya shiga neman mata. Da kud’in suka k’aru, sai ya manta da al’amurran abokan zamansa, ya tsira inganta rayuwar karuwai da ‘yan daudu. Wannan sauyin tunani na Sambo ya wakana ne saboda tasirin kud’i a kansa. Haka ake samun irin wannan sauyin tunani a rayuwar wasu mutane da yawa.

A littafin Ado Ahmad Gidan Dabino na In Da So Da K’auna an kawo wata tsohuwa wadda kud’i suka sauya mata tunani. Ita wannan tsohuwa an nuna ba ta san komai a sha’aninta ba sai kud’i, kuma don kud’i tana bin kowace irin hanya. Ga yadda aka nuna halayenta game da kud’i:

‘Da Abdulk’adir ya ga Sumayya ba ta ba shi had’in kai ba, sai ya nemi a rake shi gidan kakannin Sumayya. Haka aka yi, Aminu da Abdulk’adir suka je gidan kakannin Sumayya. Wata tsohuwa ta fito. Ita wannan tsohuwa kowa ya san ta wajen son kud’i, in dai ba aka da kud’i, to ba ka da mutunci a wurinta. Sannan ba ta sa Allah a cikin al’amuranta sai dai kud’i. In dai ta san za ta bi hanya ta samu kud’i, ko da wannan hanya ta sa’bawa shari’a ce za ta bi... Bayan sun gama gaisawa, Aminu ya gaya mata abin da ke tafe da su. Yayin da kakar Sumayya ta ji haka, sai ta ce, ‘Ai wannan abu ne mai sauk’i. Ba mu muka haifi iyayenta ba, ta isa ta k’i bin umurninmu? Iyayenta ma mun juya su ballantana ita.... Abdulk’adir da Aminu suka ji dad’in wannan bayani da ta yi musu, nan take Abdulk’adir ya ciro naira dari biyar ya bai wa kakar Sumayya. Nan da nan ta kar’ba tana tsima.’ (36).

 

Wannan tsohuwa da aka kawo bayaninta a sama ta d’auki kud’i da k’ima sosai. Kud’i sun sauya tunaninta ta yadda ba wani abu da take kallo idan dai ba kud’i ba. Ba wani abu da take ba muhimmanci komai dacewarsa idan ba da kud’i a ciki ba. Wannan ya sa Abdulk’adir ya yi nasara kanta ga lamarin soyayyarsa da jikanyarta Sumayya. Ita Sumayya ba Abdulk’adir take so ba, wani mai suna Ahmed take so, amma shi Ahmed ba ya da kud’i. Wannan yanayi ya sa kakar ta goya wa Abdulk’adir baya, ta tursasa mahaifan Sumayya kan aurar da ita ga Abdulk’adir.

Littafin Kitse Rogo ya k’unso wani bayani da yake nuna tasirin kud’i wajen sauya tunanin mutane a yau. A cikin littafin an kawo yadda wani d’an sanda kud’i suka hana shi kama mai laifi. Ga yadda ya kawo batun.

‘...In ka fahimci zancena, yalla’bai wallahi ba shi da nakasa,                                                illa gaskiya, a bisa kanta, mai d’acin taunawa. Ado yana                                                maganar yana saka hannayensa a aljihu. Ko ba ka ji abin da                                            Shata ya ce bane? Ya sasanta ya sami abin sayen dussa..’                                      (shafi na 11)

‘Ai wannan ba sasantawa ba ce. Laifin ‘Dan kunama ya cika                                               muni, Kofur d’in ya fad’a da murya mai saukowa.’

..To, na ji maganarku. Ni dama ba wai an bi rahoto ba ne. Na                                              d’auke ku kamar k’annena saboda haka dole in kwa’be ku, in                                              gargad’e ku..’

Kofur Tanko ya zazzare musu idanu ya ce, ‘Na gaya muku                                      ku bar wurin nan, in wani ya kama ku ba ruwana.’ Ya juya                                                ya kad’a k’afa ya fita.’ (shafi na 11-12).

 

Musa ya yi kisan kai ne. Ana nemansa don gurfanar da shi gaban Alk’ali abin da ya sa har aka buga hotonsa a jarida. Tsawon lokaci ba a sami wani jami’in tsaro da ya gan shi ba. A wannan wuri ne kofur Tanko ya gan shi, kuma ya cancanta ya kama shi don a caje shi. Sanin yadda kud’i ke sauya tunanin ‘yan sanda su k’i yin abin da ya dace, ya sa Ado abokin Musa ya sa hannunsa aljihu. Ko da yake ba a nuna k’arara kud’i ya ba da ba, amma sanin kowa ne idan aka sa hannu aljihu kud’i ake fitarwa yawanci. Aljihu ma’ajiyar kud’i ne a jikin mutum. Kud’in sun sauya tunanin kofur Tanko har suka sa ya sauke muryarsa k’asa. Batun kama Musa d’an kunama Tanko ya bar shi. A maimakon haka sai ya gargad’e su su bar nan wurin. Wannan ya nuna yadda kud’i ke sauya tunanin mutanen da aikin tsaron k’asa.

Shi ma tauraron littafin Za’bi Naka mai suna Kyauta samun kud’i ya sauya tunaninsa inda yake ganin ya fi k’arfin zuwa daji. Ga yadda aka kawo labarin:

‘Maigidana dai bai yi hak’uri ba sai da ya ga ya saman mani aiki na                                           wani d’an lokaci a wata ma’aikatar ruwa, ana biyana Naira sittin a                                          wata. Ganin na kama aiki, sai kankanba. Ga ma’aikacin Gwamnati.                                             Ran nan sai damana ta fad’i. Dama Mallam Tausayi rik’ak’k’e                                                      manomi ne, saboda haka, ranan ya yo shirin gona sai ya ce mani in                                                ta so mu tafi in d’an taimaka masa aiki. Sai na ji kamar ya zage ni                                                 saboda ni ina ganin na fi k’arfin noma tunda na kama aiki. To, don                         kada in tozarta shi sai na ce masa ya ci gaba ina nan zuwa.’ (shafi na24)

Kyauta da aka kawo labarin yadda kud’i suka sauya tunaninsa, maraye ne shi. Wannan mutum malam Tausayi shi ne ya d’auke shi ya rik’a. Shi ya yi masa komai har da lalurorin karatunsa. Ya nema masa aikin da yake samun albashi. Albashin na naira sittin a wata ya sauya tunaninsa har ya yi wa wannan mutum butulci. Kafin wannan albashi, Kyauta ba ya tsallake maganar malam Tausayi domin ba ya da kowa sai shi. Samun kud’in sai ya kangare masa ya bar taya shi noma k’arshe ma ya bar gidansa. Irin wannan na cikin sauyin tunani da kud’i ke haddasawa a rayuwar mutane da yawa.

Shi ma Musa da ke cikin littafin Tuwon K’aya kud’i sun sauya tunaninsa. Musa na cikin matsin talauci ta kowane hali. Ana haka sai matarsan Hassana ta sami kyautar naira miliyan d’aya daga yayanta Mustafa. Samun wannan kud’i sai Musa ya yi tunanin tsayawa takarar kansila a unguwarsu. Ga yadda aka kawo shi:

‘Bayan samuwar wannan kud’i da wata Musa ya k’i sanya hannu a                                    kan duk wata shawara ta yadda za’a yi da wannan kud’i da Hassana                         ke kawowa, sai wata rana ne ya zo ya shaida mata shawarar da ya                                   yanke na tsayawa d’an takarar kansila a unguwarsu. Inda ya nemi                                   alfarmar rance wannan kud’in don yak’in neman za’be. da fari dai                          Hassanan ta tirjewa wannan d’umbin kud’i mai tsautsayi ba, kuma                          ba wai don nata ba ne a’a’ ta ce ko na Musa ne ma ba za ta bari ya                                 yi wannan kasada ba. (shafi na 30)

 

Idan aka yi nazarin wannan labari za a ga cewa, Musa bai nuna sha’awarsa ba ga tsayawa takarar kujerar siyasa ba sai da ya ga wad’annan kud’ad’en. Da can Musa abin da zai ci ne yake fafutukar bid’a domin bai ga alamun kud’i ba. Wannan ya nuna tasirin kud’in ne ya sauya tunaninsa daga yadda yake a can farko na mai neman yadda zai ci abinci zuwa d’an takarar kujerar kansila.

A littafin Kowa Ya bar Gida an nuna yadda kud’i suka yi tasiri wajen sauya tunanin wasu iyaye suka yarje wa wani tsoho auren d’iyarsu tare da ba ta son sa, tana da saurayi daidai ita da take so. Ga yadda aka kawo wannan batu:

‘...A yadda ta ce mini, wai ita Bakanuwa ce kuma wannan Alhajin ya tura wa        iyayenta kud’i masu yawan gaske domin ya aure ta, amma ita ba ta son shi.         Saboda haka sai iyayenta suka rik’a hana ta fita wajen wani saurayin da take   mutuwar so, suka kuma ce masa kada ya sake taka musu k’ofar gida da sunan             ya zo wurin ‘yarsu. Suka kuma ce tilas Alhajin za ta aura domin gidansa gidan      hutawa ne. Shi kuma wancan saurayin nata da ya ga haka sai ya hak’ura, daga baya kuma sai ta sami labarin cewa ya yi aurensa..’ (shafi na 39).

 

Wannan bayani ya nuna tasirin kud’i ta yadda suka sauya tunanin iyayen Zinaru. Suna sane da akwai wanda d’iyarsu ke so, amma da yake Alhaji ya ba su kud’insa, sai tunaninsu ya sauya zuwa gare shi.

Bisa ga wad’annan misalai da suka gabata ana iya tabbatar da cewa, kud’i na taka rawa k’warai wajen sauya tunanin mutane su aikata abin da ba shi ya cancanta su aikata ba.

5.1       KAMMALAWA


Kud’i a rayuwar mutum abu ne mai muhimmancin gaske. Kowane mutum yana son ya sami kud’i. Son samun kud’i abu ne wajibi saboda kasancewar kud’i komai da ruwanka. Ba wani abu a duniyar nan da ke tafiya daidai ba tare da kud’i. Abinci, lafiya, kariyar mutunci da sauransu duk masu kud’i suka fi samun su a yau. Irin wannan yanayi ya sa kud’i suke sauya tunanin mutane.

Wani abin lura shi ne, a duk lokacin da kud’i suka sauya tunanin mutum ya aikata wani abu, k’arshe sakamako zai zama akasin abin da ake so. Da yawa daga cikin misalan da aka gabatar, mutanen da kud’i suka sauya tunaninsu, k’arshe sun ci karo da abin da ba su so. Da mutane za su lura su zan masu tsayayyen ra’ayi, su hana kud’i gur’bata tunaninsu da lamurransu za su tafi daidai, k’arshe kuma ya yi kyau.

Daga k’arshe dai muna iya cewa, ba shakka rayuwar yau ba ta yi sai da kud’i, kuma da kud’i ake sauya tunanin mutane ko dai saboda matsin talauci da ke tare da su ko kuma saboda k’arancin wadatar zucci. Da mutane za su nemi kud’i su kashe su inda ya dace da lamurran duniya sun tafi daidai. Shi kuma tunani da ra’ayi su tsaya inda suke, su kasance suna juya mutane, abin da ya kamata a yi shi, wanda bai kamata ba a bar shi. Yin haka zai gyara tsare-tsaren rayuwar mutane, duniya ta zauna lafiya.

6.1       MANAZARTA


 

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Post a Comment

0 Comments