https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

 

 1. Da sunan Ilaahu gwani karatu ya fara,


Tsaya d’an’uwana ga salati mu k’ara,

Buk’ata mu samu tabarraki gun Tabara,

Zaman duniyarmu da lahira mun bid’e shi.

 

 1. Karatunmu yau ga zaman abota ya ra’ba,


Kiyaye zama bisa k’a’ida kar a sa’ba,

Da huld’a da zance kar a kwaso a kwa’ba,

A zan sese-sese zama wuya ke gare shi.

 

 1. Abota zaman yarda da k’auna aminci,


Ka cud’anni in cud’e ka ne ba butulci,

A baki da zuci a jittu shi ne zumunci,

A koyaushe d’aya k’aunar yakai d’aya ya gan shi,

 

 1. Mutuncinku bakin gwargwado kun fake shi,


‘Dabi’u na juna gwargwado an sane shi,

Wuraren da an ka yi canjaras ba a fashi,

Barafeshiya aka mak’ura kar ta tashi.

 

 1. A kan kowace matsala a zan sa fahinta,


Idan zuciya ta zaburo kar a bi ta,

A sa hankalin natsuwa a kore fushinta,

A bar bin halinta na son a yanka ta tashi.

 

 1. Abota ba za ta yi kyau ba in ba kusanta,


Tana wargajewa in ana sa husata,

Zama ba ya kyau in godiya ta k’aranta,

Zukata cikin gumuni gaba na ta nishi.

 

 

 

 1. Abota ta na fi gabanka ta zan adawa,


Zaman k’eta tarko ne mafarinsa rowa,

Zaman d’ari-d’ari aboki ya zan katawa,

Zaman tsegumi da rad’a hasumi ka tashi.

 

 1. Abokin aboki bai da babban muk’ami,


Abokin rashin samun abokin kalami,

Yawaitan abokai don bid’an kai ga tsomi,

Yana sa a gane halinka kowa ya k’i shi.

 

 1. Abotan bid’an a sani ka sa cin mutunci,


Abotan rashin ra’ayi ka kawo butulci,

Abotan maso wani ka ji raggon fatauci,

Kashe kanka za ka yi babu riba gare shi.

 

 1. Abota da manya tsegumi ke shigowa,


Abota da yara ga babba zargi ka zowa,

Abota da macce ka sa a hango kusurwa,

Idan babu daudanci k’azanta gare shi.

 

 1. Abokin buk’ata lokaci ke gare shi,


Idan ta biya a ware a ture batunshi,

Idan ta k’i jawo ruwa a nan za a k’i shi,

Abotan a so ka, a k’i ka, ciwo gare shi.

 

 1. Abokin zaman k’arya zaton za a samu,


Idan an ga ci sunansa Nasamu-namu,

Idan an ka tsinka wuya a ce: “wa ka kai mu?”

Da an hangi zai zauna wuri sai a tashi.

 

 1. Abokin k’abilanci bala’insa kissa,


Idan kar ta san kar, dole kowa ya k’osa,

Maci goro bai rik’a gandi in ya ga marsa

Zama kan k’abilanci bala’i gare shi

 

 1. Abokan munafucci da tsince da giba,


Zaman zurmugud’d’u da tsegumi bai da riba,

Zama juddadun a cikin zato yai musiba,

Zaman an yi an ce, wa ka k’aunar ya yi shi?

 

 1. Abokin da ke mazarin ya san tanadinka,


A koyaushe burinai ya rege cikinka,

Da duk za shi al’amarinsa bai son ganin ka,

Ka sa mai ido, ka bi taka hanya, ka bar shi.

 

 1. Abokin da harshenai yake zazzalowa,


Wajen ba da labarinka in ya ga sanwa,

Asirranka duk ya baza su gun ‘yan adawa,

Ka kauce, Tabaraka zai yi ma maganin shi

 

 1. Abokin adawa ba ya k’aunar a dace,


Ijabar da Jalla ya yo yake son ta noce,

Idan ya ga baiwa gun ka tamkar ya k’wace,

Hawaye kamar su zubo gaba na ta nishi.

 

 1. Aboki na tserereniya ba shi hanya,


Abin duk da kay yo, zan yi ya zan hamayya,

Ana tare an k’i rufe takaici a k’urya,

Zaman so ya hurhura har ya koma na kishi.

 

 1. Zaman yaudara cutar abokin amana,


Ana zaune tare cikin gaba na ta kuna,

Da duk yag ga mai ra’ayin ka zai zo shi zauna

Shi ‘bata ka dama da hanni, wai shi a so shi.

 1. Aboki ba zai k’i zama da kai shawari ba,


Ba zai k’ulla al’amarinsa bamban da kai ba,

Ba zai so ta’bin irlinka in ba ka nan ba,

Da an so a muzantaka kai ka ba da bashi

 

 1. Aboki na gaske ba zai yi zargin mutum ba,


Ba zai yarda gun ka a zo da mugun zato ba,

Magabcinka bai ga wurin la’bawa garai ba

Ina zai ganin sarari da fuska gare shi?

 

 1. Wurin kankajeli shirin abota ka ‘baci


Garin kakka’bi motar abota ka faci

Katsal na zube wa zaman abota mutunci

Kisisiniya na sa aboki a bar shi.

 

 1. Ka ce ba gawani a gare ka wa za ya so ka?


Rashin moriyarka na sa ana zulluminka,

A shaide ka ba ka da moriya ko ta tsoka?

Abota da kai k’arfin hali d’ai ka yo shi.

 

 1. Abota da Dad’in-kowa d’ai ad da ciwo,


Ya hau d’an rabonka da ci kamar zai yi zawo,

Idan ya farauto nasa ya kama yawo.

Shi ‘boye abinsa cikin akwatin gilashi.

 

 1. Abotar taho mu yi gardama kar ka yi ta,


Zaman tare ga a barambaram ba fahinta,

‘Dak’ok’i su tashi kamar a mik’e a kwafta,

Ji’bi na zuba kumfa ga baki na haushi,

 

 1. Abota da mai son kansa d’ai kar ka fara,


Bale zarumin rikici da dokin gadara,

Da wawa da shashasha ina mai dabara?

Bale sakarai asheraru k’arya gare shi.

 

 1. Da mai shishigi da yawan zak’ewa ga amri,\


Da mai faifaye abu dole sai ya ga sharri,

Da mai ba ka, in ka d’aga ya far ma da gori,

Da mai son a ce, ya fi ka kirki, ka bar shi.

 

 1. Butulci ka ‘bata zama ka zan mai fahimta,\


Ana taimakonka kana ta k’wazon ka cuta,

Tukuicinka cin zarafin abokin fahimta,

Zaman ba ni in cuce ka ciwo gare shi,

 

 1. Tunanin da nay yi a da fahimtar ak’ida,


Yana kankare gaba da mugun makida,

Wajen ‘yan abarba da masu lemo da gwadda,

Mad’i bai kirari ga zuma na ganin shi.

 

 1. Ashe hadda mallamai abin ya shige su,


Abota kaman dai ta fi muni cikinsu,,

Fad’in na fi wane sani ka watse zamansu,

Karatun kirari babu lada gare shi.

 

 1. Ana mazhaba d’aya d’an shirin sai shi ware,


‘Darikunsu sun yi dubu wane za ka kare,?

Ga ‘yan k’ungiya da kwad’ai da son rai ya cure,

Ana tare ci bamban takaici gare shi.

 

 1. A tarbe ka lablablab kaman babu kissa,


Idan an ka mik’e k’afa karatun darussa,

Ga filin Ta’ala za a soko dasisa,

Ta giba da ‘bata, fashin bak’i sai a bar shi.

 1. Idan an ga haske gun samari na sunna,


K’ira’a gwanin sha’awa da murya da gunna,

A fannin hadisi ya ci manyan rawunna,

Ana tare za ka ji gobe an sallame shi

 

 1. Abotar karatu yanzu ya zan na kishi,


Idan na karantarshe ka na ba ka bashi,

Abin duk da nac ce, so da k’i, za ka bi shi,

Kamar Rabbana kai ne ya aiko gare shi

 

 1. Wajen masu tink’ahon karatun shahada,


Abota a baki a zucci k’ullin makida,

Sanin yaz zamo tamkar karatun jarida,

Abotar kwad’ai makasarta shagon farashi.

 

 1. Wajen masu mulki dubi saddan Husaini,


Zamanai da Tarikh munzu dogon zamani

A k’arshenta yai sanadin kashewar Husaini,

Tukuicin ga mai muni ina isalin shi?

 

 1. Hukuncin ga an yi irinsa Borkino-fasso,


Tomas shugabansu da shi da Kampore fasso,

Abotansu tai tsanani a Barkino-fasso,

Ya harbe Thomas sai lahira babu fashi.

 

 1. A Nijar da Mainasara da Dauda k’asarsu,


Abokan k’uk’ut a firamare an ka san su,

Gari d’ai bukinsu guda ga sabgar garinsu,

Ashe can a k’irji ba ya k’aunar ganin shi.

 

 1. Ya sa bindiga ta fad’a da jirgin sama’u,


Ta watse shi d’aid’ai babu bakin buka’u,

Abota ta zan sababin bala’i fasadu,

Ashe duk zaman da ake da k’unshi cikin shi.

 

 1. Gawon yai irin ta ga Murtala kar ku manta,


Tsakanin Buhari da Iro in kun fahimta,

Zumuncin Abacha Husaini sun so kusanta,

A k’arshen abotar shan bala’in burushi.

 

 1. ‘Da Nzegu shi da Firimiya ba husuma,


Ya mai da shi tamkar d’a ga aikin hukuma,

Da yag girma al’amarin musiba ya koma,

Takaici dad’ad’d’e nan ya huce hushinshi.

 

 1. Rik’e wanga tarihi misali gare ka,


Aboki idan ya yi zamba yay yaudare ka,

Ka sa mai ido ka yi k’ok’arin yafe naka,

Tuwon yaudara tuk’insa tilas ya tashi.

 

 1. Ka yafe k’anana da manya-manyan jaza’i


Da mai yi duk’unce da wanda ke ta balli,

Ka saurari k’arshen masu tunk’a da k’ulli,

Da ‘yan sa’ido komai suke ba a fashi.

 

 1. Da Maula da Bn Ladan abin na da tsari,


Zama ne na Allah ba jiyewa da gori,

Zukatansu babu kwad’ai da gurin tujuri,

Hakuncinsu kowane ittifak’i gare shi.

 

 1. Suna nan a raye walau su kwanta shahada,


K’asa tasu ce komai tsanancin makida,

Irin shimfid’ar da sukai ta gyaran ak’ida

Jiragen Amerika babu mai kakka’bo shi.

 1. Alu hayya! Kak ka aboci k’aton bahili,


Ibadarku kowane lokaci kan k’ala’i,

Da mai tattalin Allah Ya koro bala’i,

Ganin bai aje ba, bak’in nuhinai shi bi shi

 

 1. Abota da malammai tana sa muruwwa,


Karatu a kwasai arha sai an yi kuwwa,

A k’auli guda an zargi laifinku rowa,

Muridanku sun ka fad’i ga hanya na ji shi.

 

 1. Abokanku ladannai da ke ta da murya,


Da uttazu masu rabon nasiha a hanya,

Suna k’orafin sadaka da zakka ta manya,

A d’an marmasa musu gwargwado don su san shi.

 

 1. Tsaya in tak’aita ma abokan amana,


Da mai son ka, mai sha’awar ka, kullum shi nuna,

Da mai son ganin ka a kulluyaumin ga sunna,

Da mai kau da kai ga kurenka in ya yi girshi.

 

 1. Da mai tattalin kullum ka dace ga harka,


Da mai taulahin auki wajen arzikinka,

Da mai son ganin ka, kana cikin hayyacinka,

Ka sa min da mai fatar ka samu ka ba shi.

 

 1. Idan kad’ d’aga kirkinka zai fassarawa,


Idan ka taho wa’azi yake nanatawa,

Da lurar da kai had’arin zama d’an adawa,

Da tausan gabanka da hank’uri don ka yo shi.

 

 1. Shina son ganin ka cikin mutane na kirki,


Ga jaruntaka bai son ka gwabce da raki,

Rigayanka kuka zai yi in ya ga miki,

Ya shafe jininka da kyau k’uda kar su bi shi.

 

 1. Ku duba ga Makau Bawa babban ‘barawo,


Da Gambo ya gan shi cikin jini babu kyawo,

Ya rugo da shi asibitti yak kama yawo,

Da rai ‘bace ceton ran abokin zaman shi.

 

 1. Ashe Bawa buk’u yo ya lafe abinsa,


Da yal lura an watse ya nik’e jikinsa,

Ya ce: “Mai tafashe jijjiga babu kissa,

Ka dahe su in ji suna ta gunza da nishi”.

 

 1. Abokin da duk bai kutso kai nai wurin ka,


Idan k’addara ta zo ya zo taimakonka,

Mutane su k’i ka ya murje fuska ya so ka,

Ya yo ma nasiha gwargwadon hankalinshi.

 

 1. Masoyinka ba ya gudunka komai musiba,


Tsayi zai yi sai an gane tsada da riba,

Abokanmu yanzu hak’ik’a in za ku duba,

Ana zaune fuska goma kowa da nashi.

 

 1. Kirana gare mu a dole gyaran halinmu,


Musibar ga ta yi yawa haba ‘yan’uwanmu!

Hak’ik’an idan Ustazu ya tsai da gemu,

Walankeluwa ga zama ya zan ya guje shi.

 

 1. A nan d’an Naturai zai rufe k’orafinsa,


Kwatancin Aliyu na Bunza in an ka bi sa,

Ana kai ga cin nasarar zama babu kissa,

Zaman nan na da, a fahinta, gyara gare shi.

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/