- Allah na kiraye ka,
Salati nikai wa manzonKa,
Ga Sayyidina ma’aikinKa,
Muhammadu mai gari Makka,
Aminu mazan nagarta.
- Bayani nai nufin sak’a,
Cikin lafazi na mai wak’a,
Saboda kuranye gaggak’a,
Wuyanmu da an ka sa sark’a,
A kan tsananin mugunta.
- A yau mu d’ai ake dako,
Da mui zance a sa tarko,
A hau bisa kanmu ba tsaiko,
A sa muna tarnak’in iko,
Gabanmu da baya cuta.
- Musiba babba nah hanga,
Aboki tsaya ka d’an waiga,
K’asarmu tana cikin sabga,
Na rud’ani da damaga,
Da babu irinsa wauta.
- Ga tarihi na tarayya,
Zama aka yi na soyayya,
Idan aka fara jayayya,
Gabaci za a ba hanya,
A tabbata an tuk’e ta.
- A bar fitina ta gawurta,
Ana kallo ta k’asaita,
A jefa k’asa ga ragaita,
‘Diyanta a sa su tozarta,
Saboda d’iyan mak’wabta.
- A kan tsabar munafucci,
Da makircin k’abilanci,
A ware k’asa da ‘bangarci,
A sa mu cikin agolanci,
Da yin hijirar barin ta.
- Muna kallo a k’ware mu,
A yo gayya a yak’e mu,
Ana ta kashe matasanmu,
A watse dukan biranenmu,
A sa mu cikin asuta.
- Musiba duk a ce mu ne,
Idan aka hango mun gane,
A gayyato masu jan kunne,
A ce musu ga su can su ne,
Su bud’e wuta da hauka.
- K’asa duka an ka wa miki,
Mutan ciki na da jan aiki,
A tilasta su yin raki,
A kwana a tashi ba girki,
K’asa tilas barin ta.
- Buk’atar masu yak’anmu,
Gaban a raba su k’ware mu,
A karkashe masu k’azonmu,
A tarwatsa arziki namu,
Su tura d’iyanmu bauta.
- Takaici na gidan soja,
Mazajen rungumar danja,
Muk’ami sai d’iyan Neja,
‘Diyanmu a ba su masinja,
Wad’ansu su zan kurata.
- Tsaro da shirin k’asa tamu,
Suna hannun magabtanmu,
Muna kallo a k’ware mu,
Mu kasa tsayi da k’arfinmu,
Mu tabbata an kwatanta.
- Ina aka kai mu ‘yan boko,
Sarakai masu jin iko,
Da ‘yan d’amarar dakon ciko,
Birai su mayar da mu soko,
K’ashi ya kashe mahauta.
- A bi mu ana ta mammara,
Mu fad’i ana ta shusshura,
Mu kama shi’ba da bankaura,
A d’auko Igwa mu d’au gora,
A kanmu ake daka ta.
- Irin rigimar da ke Delta,
Ta k’are babu algaita,
A ba su kud’i su sai mota,
Tukuici han na ragaita,
Su zub da jinin mak’wabta.
- A ce musu ‘yan bid’an ‘yanci,
A ba su dukan muhimmanci,
Da albashi na sagarci
Su k’asura sui ta shashanci,
Batunsu ake mutunta.
- Arewa batunmu k’arya ne,
Da mui magana a ce mu ne,
Jininmu zubansa daidai ne,
Batun diyyarmu shirme ne,
Wa ka biyan k’azanta?
- Mafarin yin fa’addanci,
K’asa ta halasta zalunci,
A dinga mutunta cin hanci,
A ja d’amarar k’abilanci,
Bala’i ya rufe ta.
- Idan aka fara ha’inci,
Hana wa d’iyan k’asa ‘yanci,
Da ‘bangarci da bambanci,
Da gardancin ak’idanci,
K’asa tuni an kashe ta.
- Matasa an ka wa fanho,
Su zabura ce kakai shaho,
Suna kuwa suna eho!
Su jikkita babu mai hoho,
Kisan kai an halasta.
- Abinda ka ba ni mamaki,
A ofis can wajen aiki,
Kujera ta zamo gunki,
A kan ta a d’ora yin raki,
Na kare martaabarta.
- Saboda a nan ake sata,
A tara kud’i a k’asaita,
A jefa k’asa ga ragaita,
Talauci duk shi dame ta,
Ta nakkasa gun mak’wabta.
- A sa marashi da mai samu,
Suna kwana cikin gammu,
Matasa har da mai gemu,
Su takura ba wurin kamu,
K’asa duka an fusata.
- Matasa an ka cuce su,
Ga ilmi an ka k’ware su,
Ga aiki babu mai ba su,
Siyasa taf farauto su,
A dole su je kiran ta.
- Da nan aka sa su ‘yab banga,
A ba su giya su sha daga,
Su gigice da damaga,
Fasadi ga shi an shirga,
K’asa sama har k’asanta.
- Ganin an rena k’urarmu,
A banzantar da wayonmu,
A ta da fad’a k’asashenmu,
Saboda a karya k’arfinmu,
Da ganganci da cuta.
- A ofis an ci k’arfinmu,
Siyasa an galale mu,
Yawan jama’a a cuce mu,
Muk’amai an ka kore mum,
Kujerin an ka k’wata.
- Muna kallo mu zan le’bo,
Tufanmu kad’ai ka yin ra’bo,
A kwashe zuma mu d’au so’bo,
Da an gamu sai a ce, Ja’b’bo,
Ina Mudi da Auta?
- A nai muna izgilin raini,
Ganin an samu zamani,
Siyasa mai bak’in muni,
Da mai gemu da mai huni,
A tabbata an talauta.
- A yau mabiya ga alk’ibla,
Musulmi masu yin salla,
Ake ta yi wa kisan gilla,
Saboda muna fad’in Allah,
Ka tsari mai nagarta.
- Siyasa ce gidan tasku,
Zaman ciki babu dottaku,
Da mai rawani da mai diku,
Kwad’ai ya rufe k’wak’walwarku,
Ku zan manyan macuta.
- Ku jefa k’asa a Basasa,
Tsaro ya zamo barafasa,
Ta’addanci ya bunk’asa,
Dukan tsarinta an rusa,
Musiba ta rufe ta.
- Haba jama’a mu hankalta,
K’asa ta k’are muzanta,
Zaman tuni an ga wallenta,
Mutane sun galabaita,
Suna ta shirin barin ta.
- Ku dubi irin halin maiki,
Da yag gamu shi da gauraki,
Wurin tad’i da hankaki,
Gaban jimina yana raki,
Sanin ya ‘barka cuta.
- Biri in yai kuren reshe,
Dabaru nasa sun rushe,
Irin tsololuwar baushe,
Da ya fad’o yana mushe,
Su angulu za su zabta.
- Musulmi wanda yad dace,
Shahada langa’bunai ce,
Ya sha romo ya d’au kwalce,
Da likkafaninsa zai zarce,
Cikin murnan zuwan ta.
- Kisa bai k’are Imani,
Zaman rai na da zamani,
Akwai shi a kowane k’arni,
Da shi aka maganin raini,
Shiga Aljanna kyauta.
- Ganin mu za a rinjaya,
Ake yin martanin gayya,
Na k’one yara har manya,
Da rodubulo a kan hanya,
A firgita masu bin ta.
- A turbud’e bom k’asashenmu,
Ya karkashe ‘yan uwan namu,
A bi mu ana ta kamo mum,
Da hujjoji na zarginmu,
Da an ka shira na cuta.
- Mutum da gidansa an bi shi,
Ya yunk’urto a harbe shi,
Ya mik’a wuya a d’aure shi,
A runtuma gun iyalanshi,
Da yin fyad’e da ‘bata.
- Gabanka a harbe tsohonka,
Walau a kashe iyalanka,
A sa ‘ya’yanka yin shirka,
A sa ka rutsi na cin fuska,
Da tun tuni an hukunta.
- Muna ji Borno ta watse,
Gaba d’aya Yobe ta motse,
Na Bauchi gabansu ya katse,
K’asar Adamawa ta gintse,
Filato an kashe ta.
- Kano ta sha harin girshi,
Kaduna karen ka wa habshi,
Jahar Nasarawa sai nishi,
Abuja kwatsam yake tashi,
A kama gudu a kwalta.
- Gusau a wajen manomanta,
Kaza sashen makyayanta,
Bala’in ya malale ta,
Rahotannin musibunta,
Abin sai an tak’aita.
- K’asar Katsinanmu an yi hari,
Da gawakki gudan tari,
Abin ya kasance labari,
Hukuma ba ta inkari,
Da tunkarar macuta.
- A Sakkwato an yi mai muni,
Awon ya furce mizani,
Zuma sun harbi mai gani,
Kare ya shuri k’ur’ani,
Ruwa su kashe masunta.
- Ina kuka zacci zai tsere?
K’asa can da tana kore,
Hamada ta bi ta share,
Ina wani wanda zai more,
Zama ya ci gajiyarta?
- Mak’ark’ashiya shirin manyan,
A tunkud’a yara jayayya,
Da son a ga masu rinjaya,
A ba kowa makamayya,
Su karkashe kai da wauta.
- Tammat kun ji k’arshen ta,
Mak’ark’ashiya ga sunanta,
Alu d’an Bunza yay yi ta,
Masar aka nome k’wazonta,
Kano aka kai tuk’inta.
https://www.amsoshi.com/contact-us/
0 Comments
Post your comment or ask a question.