Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Abu A Yi Shi In Ana Son A San Shi Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com

  1. Mu gode Allah d’aya mai komai
Da yay yi komai a lokacinai,

Yay yi hukunci bisa yardaTai,

Ga lokaci wa ka karkare shi?.

 

  1. Bisa yardaTai ya k’ago bayi,


Ga k’assai ga sama’u Ya yi,

Da fasullan shekara da yay yi,

Na lokaci ba a gurgasa shi.

 

  1. Shi dai wak’aci a kiyaye shi,


In ya zo ba a tunkud’e shi,

Mai ik’irarin ya gurgusa shi,

Kar ku yi shakka ga k’aryata shi.

 

  1. Mai k’wazon kan ya zo ya lek’o,


Wai zai ruga ya sa ya shek’o,

Haba! Idan kai yana da sank’o,

Wa zai gashi ya sutarta shi?

 

  1. Gaggawa ba ta sa a girma,


Komi nakinka in gaya ma,

In wak’aci ya yi babu dama,

Komai shi za shi bayyana shi.

 

  1. Bari doro don kana da kud’d’i,


An shiga mulki ana ta fad’i,

In wak’aci ya yi babu dad’i,

Zama guda za shi toskana shi.

 

 

  1. Ilmi bai tsere lokaci ba,


In ka same shi zan ka tuba,

Daina kirari kana ta k’aba,

Ko an ce: “Wane ba awa shi”.

 

  1. Bil’ama ya so ya k’ure Musa,


Ganin karatunsa ya yi nisa,

Tabara yab bi shi har mak’osa,

Da lokaci an ka dambala shi

 

  1. Da lokaci yay yi an ka kammai


Mala’iku an ka sa su jimai,

Bugu guda an ka yo gaba nai,

Nahawunai an ka yamutse shi.

 

  1. Ga shi rugun zaune an ka nuno,


Sunanai an ka ce ya zano,

Yay yi ta wayon bid’an ya gano,

Amma yak kasa rubuta shi.

 

  1. Kun san K’aruna ya yi suna


Da lokaci yat taho na k’una,

Gaban mutane a tsakan rana,

K’asa ta kammai ta adana shi.

 

  1. In mai mulki bai manta ba,


Bai yi wa Fir’auna k’warjini ba,

Da lokaci yay yi bai kula ba,

Cikin ruwa an ka birkice shi.

 

  1. Duk mai cewa k’arfi ya zo,


Ya bar tsoro yana ta k’ozo

In wak’aci ya yi babu gwarzo,

Zama guda za a murk’ushe shi

 

  1. Ku dubi tsarin maza na farko


Da shirye-shiryen da sun ka d’auko,

Da lokaci yay yi sun ka sauko,

Kamin ya biya ya kakka’be shi.

 

  1. ‘Dan boko in ya sa agogo,


Kaman ya tusgo da shi ya rugo,

Kan ajima in ya je ya rego,

Nan wak’aci za shi ba shi haushi.

 

  1. A yau ina alfadar da jaki?


Kud’insu da sun wuce tumaki,

A yanzu sun zan adon musaki,

Wak’aci tilas a girmama shi

 

  1. Wak’aci kwas san irin halinai,


In ya ga ya fara isalinai,

Mik’a wuya zai yi kar ya farmai,

Ya sa shi mala ya mak’ure shi.

 

  1. In jiya ne kay yi naka loto,


To bari yau masu yi su k’oto,

In ka ce dole za ka gitto,

Wak’aci ko za shi ba ka kashi.

 

  1. Shi wak’aci bai jira ga kawo,


Kuma take ya gama da kawo,

Bai rigima bai fad’a da tsawa,

A hankali za shi hukunta shi.

  1. Ku dubi kyawon abu na sabo,


Kaman a lasa idan ka dubo,

In wak’aci yas shigo ya tarbo,

A kai shi Juji a jikkita shi.

 

  1. K’uruciya in tana da gauni,


Da shekaru za a  sa ta rauni,

A zo zama dole sai da, ‘wai ni’!

Tashi sai an kakkama shi.

 

  1. Mai karfin hankali fasihi,


Ka iske ya dambale wa kihi,

Shekaru sun shige da zurhi,

Wahmi ya fara sunsuna shi,

 

  1. Dubi irin zak’unon budurwa,


In wak’aci za shi ba ta kewa,

Haurun su zube ga gantsarwa,

Haibar fuska a tamuk’e shi.

 

  1. Lotto muddin yad darkako,


Kowat tarbe shi ba shi k’arko,

Zama guda zai mutuwar kasko,

A kai shi daji a turbud’e shi.

 

  1. Rana haskenta in ya ‘bullo,


Hantsi kowa yake ta kallo,

Kan agajenin karin kumallo,

Wak’aci shi za shi rarrabe shi.

 

  1. Mai cewa ya iya kwatse shi,


Mai doron sun k’ware ta’bo shi,

Mai cewa mu ka yi kiro shi,

Wak’aci muka sa shi hukunta shi.

 

  1. Tambayi mai kakka’bi da kaud’i,


Nuna zak’ewa gwanin zumud’i,

Le’bo kakan kwad’ai da laud’i,

Da mucciya an ka zungure shi.

 

  1. Mai cewa, yanzu ba kamata


Wak’aci ya mai da shi k’watata,

Har ya zan yanzu bai da gata,

Wak’aci ya ida kalmishe shi.

 

  1. Mai turo yara k’aryata mu,


Wurin karatu a kunyata mu,

Wak’aci yaz zo ya faranta mu,

Yau yaran su ka k’aryata shi.

 

  1. Tambayi ‘Dankama goga masu,


Uban samak’i mai ‘yan gasu,

Da lokaci za shi sud’ad’a su,

Zama guda an ka ba su kashi.

 

  1. Kai wak’aci ka yi ba ta kashi,


Masu gidajen k’arau gilashi,

Ga su k’uyaya su yanka kashi,

A sa k’asa ai ta rurrufe shi.

 

  1. Masu hawa rak’uma dawaki,


Da dubun kaji cikin akurki,

Yau abu ya zan kamar mafarki,

Duk wakaci ya kacaccala shi.

  1. Manyan girma ‘yan alfarma,


Jarummai masu ji da fama,

In wak’aci ya yi babu dama,

Da hawaye za su kammala shi.

 

  1. Maganar banza rashin azanci,


A ba ka girma ka sa bananci,

In wak’aci ya taho da k’unci,

Da mu da kai, wa ka tsallake shi?

 

  1. Da lokaci za a shirya komai,


Da shi ake kammalar da komai,

In ba shi ba shiri na komai,

Domin shi za shi barkata shi.

 

  1. Komai wak’aci garai sananne,


An ka gina kansa ayyananne,

Komai fitina ta tufananne,

K’yale wak’aci shi toskana shi.

 

  1. In ka ji an ce, mutum da kaifi,


Komai sai ya yi ci-da-k’arfi,

In wak’acinai ya zo da zafi

Zama guda za shi murk’ushe shi.

 

  1. In an ce, wane shi ka tashe,


Ya d’auko lokaci gasasshe,

Wak’aci zai sa shi dallasshe

Sai ka ji shu har an manta shi.

 

  1. Gwani ga k’ira da masu noma


Da ‘yan farauta da masu koma,

In wak’aci ya yi sai su koma

Kaman da d’ai ba su aikata shi.

 

  1. Wak’aci da rabo suna da sauri,


Komai k’wazon rabo da sauri,

Sai wak’aci ya yi zai yi kuri,

A bud’e hannu a rungume shi

 

  1. Ba a ta’ba yak’i da lokaci ba,


An ka yi nasarar kara da shi ba,

Bai ta’ba lattin zuwa wuri ba,

Bale a girsai a hukunta shi.

 

  1. Ka bar ganin wai kana da girma,


Don haka tilas ake raga ma,

Da lokaci ya yi in gaya ma

Girman duk zai warwatse shi.

 

  1. Ina Bika madugun azanci,


Da shi da Suda uwar habarci,

Da lokaci yat taho da k’unci,

Tsakan fak’o sun ka yanka kashi.

 

  1. Dubi ta’ba’b’ben ga ji’bananne,


Da shi da wawan ga toskanne,

An ce kawunsu tufanannen,

Yau wak’aci ya tozarta shi.

 

  1. Sukuntumau mai k’ullin k’arya


Da Kakka’bi mai bakin kurya,

Tuwonsu yau ya koma gaya,

Da lokaci yam muzanta shi.

  1. Komin nutse ruwa in ji Kabawa,


Tudu ake tarbon gaggawa,

In ya mace ciki ya zan gawa,

Ga tunku’ba aka dako nai shi.

 

  1. Mazambaci duk ku tabbatar mai,


Yana da wak’acin da za a kammai,

A karanto mai a fallasa mai,

Bayan kunya a hukunta shi.

 

  1. Mahassadi mantuwa ka kammai,


Rabon mutum wa ka tunkud’e mai?

Ubangijinai ya k’addaro mai,

Wak’aci ne, wa ka tunkud’e shi?

 

  1. Ka reni yaro ka suturta shi,


Da ya ga an fara girmama shi,

Kai zai duban ka mutunta shi,

Hadda fad’ar ba ka girmama shi.

 

  1. Ya za ni bari a cutata min,


A sa k’iyayya a k’untata min,

Don wak’aci ya d’an hasko min,

Ake bukatar a dak’ile shi.

 

  1. An hau karaga an yi ta sara,


A mumbari an hau ba gyara,

A dandali kullum barara,

Wai wak’acina a turmuje shi.

 

  1. Muk’addami da ka wannan sara


Yau wak’aci ya mai sai gara

‘Yan aikensa ka ci mai gyara,

Shi gilma rai su k’i gaskanta shi.

 

  1. A lokacinsu na ‘bannan suna,


Da shi da Bagudu d’an Maigona,

Da Bangaje mai k’aurin suna,

Da Ginshimi mai kan ramboshi.

 

  1. Ba sa tadar sunan kowa,


Magibaci wa zai yin kewa,

Mahassadi mai kushe gawa,

Ka’b’ba bakaniken gil’boshi.

 

  1. Mu tuba mu duka tun ba mu zo ba,


In jama’a ba su yafe ma ba,

Akwai tumulli ba k’arami ba,

A k’ulla dambe da mai tarkoshi.

 

  1. A lokacin da kake dai ka yi,


Da lokacin sakayya yay yi,

A d’ebe zancen samun sanyi,

Kamaa tad’inu a bar manta shi.

 

  1. Duk wani mai hankali shirarre,


Ya san zancen ga babu kore,

Kai ko mai hankali gajere,

Wak’aci bai fara makkasa shi.

 

  1. Allah rok’on na Bunza gata,


Wurinka ko na taho da rata,

Da lokaci yay yi min na k’eta,

Ka yi min ahuwa, a kunyata shi.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments