https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

NA


ANAS MUSTAPHA


 


KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

BABI NA HUD’U


WASANNIN YARA MATA A K’ASAR FASKARI


4.0 Shimfid’a


A wannan babi na hud’u an tattaro yadda wad’ansu wasanni suke wad’anda yara mata ke gudanar da a lokutan wasansu da suke gudanarwa da yammaci ko da rana ko wani lokaci har da safe, wad’annan wasannin za a ga mafi yawancinsu suna tafiya da wak’a tare da rawa da ‘yan tsalle-tsalle na motsa jiki.

4.1Yadda Yara Mata ke Shirya Wasanninsu


‘Yan mata mashahurai ne wajen shirya wasanninsu. “Yan matan Faskari ma ba a barsu a baya ba wajen shirya wasanni dan kuwa ko basu k’ago sabbi ba suna yiwa na da k’ari ko kuma su sauya wani sabon salo a cikin wasannin don haka wannan ya nuna cewa ba a bar su a baya ba.

‘Yan matan Faskari sukan taru a dandali su rik’a shirya wasanni da wak’e-wak’e masu dad’i tare da armashi sannan ga jan hankali ga masu sauraro. Wad’annan ‘yan mata sukan tsara wak’ok’i wad’anda sune suke bi don su aiwatar da wasanninsu.

Haka kuma, ‘yan matan Faskari don bunk’asa harshe sukan aro wad’ansu wasanni na wasu al’ummar kuma su mayar da su na suduk domin su k’ara bunk’asa wasanninsu na yau da kullum. Wani lokaci sukan yi da’ira su rik’o hannuwa, sannan kowace daga cikinsu za ta raya wata irin rawa wadda za ta dace da wak’arsu.

Wani wasan kuma za a ga sun yi da’ira sama su rik’a shiga  tsakiya suna rawa ana wak’a da daidai (wasan ‘yar shigowa) wani lokaci kuma idan wak’an ta kwashi wasu abubuwa da ake son siffantawa sai ka ga wadda ke yin rawar tana siffanta abin tare da aikata abin da ake fad’i a wak’ar. A wani wasan kuma sukan yi da’ira sai a sami wata tana rawa tana rausayo da rangwada daidai da karin wak’ar da suke rerawa.

A duk wasannin ‘yan mata na rera wak’a a kan dubi yadda tafi iya wak’a a ce ta bayar da wak’a. Mafi yawancin lokuta har ma sukan k’irata da suna zabiya. Idan sun gaji sai kaji wata ta zani gida nan sai kowace ta ce nima gida zani, da zarar sun mik’e tsaye saii kowace ta bugi ‘yar uwarta dake kusa da ita, su rik’a cewa na ci ladar tafiya gida to daga nan sai kowa ya watse sai kuma wani lokaci sun k’ara had’uwa domin gudanar da wasanni.

 

4.2 Ire-Iren Wasannin Yara Mata a Faskari


Wasannin da ‘yan mata ke yi a garin Faskari suna da yawa don haka sai dai a kawo wasu daga cikinsu a yi bayaninsu. Su dai wad’annan wasanni sun kasu kashi biyu ne akwai wasanni na zaune da kuma na tsaye. Ga dai yadda ake aiwatar da wasu wasannin a yankin Faskari d’aya bayan d’aya.

4.2.1 Wasannin Zaune na Yara Mata


Wad’annan wasanni na zaune kamar yadda aka ambata wasanni ne da ake gudanarwa a dandali ko a k’ofar gida. Wad’annan wasanni ana gudanar da su a zaune a lokacin wasa.

4.2.2 Wasar ‘Yar K’wad’o


Wannan wasa ne da ‘yan mata ke zama su gudanar da shi a zaune a yankin Faskari. Yadda ake yin wasan shi ne ‘yan mata za su zauna su kalmashe k’afafunsu su gina rami mai d’an fad’i da kuma matsakaicin zurfi su sami duwatsu k’anana su rik’e a hannayensu, ta farko a cikinsu za ta zuba duwatsu a cikin ramin sai ta rik’e guda d’aya hannunta, idan ta jefa na hannunta sama sai ta d’auko guda d’aya a cikin ramin kafin wanda ta jefa ya fad’o k’asa sai ta ca’be shi , haka za ta yi har ta kwashe na cikin ramin da zaran ta kasa ca’be wanda ta  jefa sama ya fad’i k’asa to wadda ke gefenta za ta kar’ba ta ci gaba, haka za a yi har a gama wadda ta sami nasarar tsince duwatsu duka ba ta fad’i ba ita ce zakarar wannan wasan za ta yi ta jin dad’i tana murna.

Amfanin wannan wasan shi ne samun nishad’i da k’ara ba da himma yaro yasan idan ana abu ya na da kyau ya yi k’ok’ari kar a barshi a baya a mashi dariya.

4.2.3 Wasar K’asa


Yadda ake yi ‘yan mata sukan fita dandali ko k’ofar gida su sami wuri mai k’asa su zauna kowacce za ta samu wuri ta yi abin da ranta ke so wata za ka ga tana gina d’aki da ‘yan tukunya wata kuma ta yi tanda  tana zuba ruwa kamar tana soya waina (masa) ta had’a ‘yan kwanuka na laka tana zubawa wani lokaci, sukan sami ciyawa ko tsirai su yanka a cikin tukunyar da suke wasan abinci, idan suka gama sai kowace ta zo tana kallon abin da ‘yar uwarta ta yi, sai ka ga suna jin dad’i suna raha da annashuwa har ka ji suna tsokanar juna suna cewa nawa ya fi dad’i na nawa zan zuba miki.

Amfani wannan wasan shi ne ya na taimaka ma ‘yan mata su san cewa dafa abinci ya zama dole a kansu, yana koya musu yadda za su gyara abinci ya yi kyau tare da tsaftace wa.

4.2.4 Wasar Cin Dawo


A wannan nau’in wasan kuwa ‘yan mata kan had’u a dandali ko cikin gida su zauna su yi da’ira suna ‘yan wak’e-wak’e cikin nishad’i da walwala, kowace za ta mik’e k’afarta tana buga gwuiwar hannunta tana wak’a kamar haka:

Cin dawo cin dawo

D’an fafarin fafara

Uwar ladi tana daka

Na muk’a mata muciya

Ta ce menene haka

Na ce morewa na yi

Ana yayin wak’iya

Ana murza k’uli-k’uli

Da me za muci zogala

Da dinki da kwad’on rama

Da shi za muci zogala

Tsohuwa za ta mutu

Ba ta ce Allah ba

Ba ta ce Annabi ba

Sai ta ce

Ja da yalo

Yana maganin mutuwa

Sai ta je kasuwa

Sai ta fad’a ma gyad’a

Ke gyad’a bari magana

Kud’inki na aljihu

Na auduga ba su zo ba

Hikimar wannan wasan shi ne su sami nishad’i sannan wasan a cikin wak’ar akwai ake nuna cewa idan mutum zai mutu to ya ambaci Allah da manzonsa. Sannnan wak’a tana k’ara basira.

 

4.2.5 Wasar Tafa-Tafa


‘Yan mata kan taru a wurin da za su gudanar da wasa wani lokaci a k’ofar gida ko dandali kai har ma a tsakar gida, suna zaunawa cikin nishad’i da raha suna tafa hannuwansu suna wak’a kamar haka:

Muna tafa tafa

Akwai wanda nake so

Amma kunya na so

Ta wankeni da soso

In fad’a ku ji kar ku yi dariya

Fari ne siriri

Yana da tsawo ga gashi

Ya iya kwalliya kaman d’an sarki

Na mori saurayi mai kyawu

Allah yasa yana da halin kirki

Mu tafi mu ji dad’in zama

Mu yi wasa mu yi dariya

Muhimmancin wasan a wurinsu shi ne su sami nishad’i da d’ebe kewa, sannan zama wuri d’aya yana k’ara musu shak’uwa da son juna.

4.2.6 Wasar ‘Yar Tsana da Kayan D’aki


Yadda ake yi ‘yan mata kan had’u su sami su tsaftace shi su yi masa ado da mashimfid’i su mayar da wurin kamar d’aki babu mai taka musu ko wucewa dan kar a ‘bata musu sukan yi jere ne kayan d’aki su yi gadon kara ko katako su sami k’yalle su shimfid’a a kan gadon. Sukan yi amfani da ‘yar tsana ko roba ko su had’a wata ta kara su yi mata kitso a matsayin d’iya su yi mata ado da kwalliya su saka mata riga ta k’yalle ta yi kyau sosai har ma su yi mata kitso sannan in sun gama shirya ta sai su d’auko ‘yar d’iyar su d’ora ta a kan gadon, haka kowace za ta yi ma nata kowace za su zauna suna kallon d’iyan suna jin dad’i suna kula da ita a matsayin d’iya za su yi ta jin dad’i suna raha har sai sun gaji su tashi ko kuma lokacin tafiya makaranta ya yi.

Muhimmancin wannan wasan shi ne yana koya musu yanda za su kula da ‘ya’ya da kuma tsaftace wuri da gyaran d’aki sannan yana sa nishad’i a zuciya k’warai.

4.3 Wasar Tsaye na Yara Mata


Wad’annan wasanni yara mata kan gudanar a lokutan wasanninsu ko dai a dandali ko cikin gida ko k’ofar gida sannan mafi yawancin wasannin suna tafiya da rawa tare da wak’e-wak’e da kuma tsalle-tsalle.

4.3.1 Wasar ‘Yar Gala-Gala


‘Yan mata kan had’u su sami wuri mai fili musamman lokacin damina, su kan had’u a k’ofar gida su sami wuri mai k’asa su zana gidaje masu d’akuna shida shida mutum biyu biyu ake yin wannan wasan. Ta farko za ta sami d’an dutse ta rik’e ta tsaya a gaban gidajen da suka zana sai ta jefa a gida na farko, idan ta jefa sai ta yi tsalle da k’afa d’aya tana fad’awa cikin gidajen, idan ta zo kusa da na farko sai ta duk’a ta d’auki dutsen da ta jefa haka za ta rink’a yi har sai ta zagaya duka gidajen. Idan ta gama sai ta tsaya gaban gidajen ta juya baya ta jefa dutsen cikin gidajen. Duk gidan da dutsen ya fad’a to ya zama nata sai ta yi mashi zane. Haka za ta rink’a yi har sai ta fad’i abokiyarta ta amsa ta ci gaba da yi har sai sun zane gidajen duka sai a kirga kowace ta samu guda nawa ta cinye, wadda ta fi yawan gida ita ce zakarar wannan wasan sai ta yi ta jin dad’i.

Amfanin wannan wasan yana saka su cikin jin dad’i suna motsa jikinsu, motsa jikin kuwa yana taimakawa mutum jini ya samu hanya ya shiga ko ina a jikin mutum.

4.3.2 Wasar D’iyanmu-D’iyanmu


‘Yan mata kan had’u a wuri su tsaya wasu kuma su taho su same su cikin raha da wak’a kamar haka:

Assalalu alaikum a cikin wannan rana

Wa alaikumussalam a cikin wannan rana

Meye dalilin zuwan ku a cikin wannan rana

Akwai dalilin zuwanmu a cikin wannan rana

Sai ku fad’a mana dalili

D’iyarku ne muke so a cikin wannan rana

Sai ku fad’a mana sunanta

Sunanta Humaira

Sai ku d’auko mun baku

Kar ku barta da yunwa

Mu gidan mu ba yunwa

Mu gidan mu ba d’auda

A cikin wannan rana

Mungode mungode

Amfanin wannan wasan shi ne yana nuna idan ka d’auki mutum ka kula da shi ka kyautata masa ka tsare masa hak’k’i, sannan ga nishad’i da annashuwa.

4.3,3 Wasar D’an Maliyo-Maliyo


Yara mata sukan taru cikin nishad’i suna rera wak’a a lokacin da suke gudanar da wasan, za su yi da’ira d’aya ta shiga tsakiya tana fad’awa a jikin ‘yar uwarta wato sauran abokan wasan tare da rera baitoci cikin wak’e wasu na amsawa kamar haka:

D’an maliyo maliyo

Maliyo

D’an maliyo nawa

Maliyo

Yaje ina ne

Maliyo

Yajr Ilori

Maliyo

Ba zai dawo ba

Maliyo

Sai a watan gobe

Maliyo

Gobe da labari

Maliyo

Jibi da labarai

Maliyo

Tambotso mu gani rawar ki da kyau

Mai jego ta iyo Rumace da a daren jiya tai mana rumace

Maliyo

Hikimar wasan shi ne samun nishad’i a tattare da su sannan wak’a takan sa musu basira da iya haddace abu.

4.3.4 Wasar Madara ko Zuma


A wannan wasan ‘yan mata sukan taru a wurin wasanninsu na yau da kullum, sukan had’u suna tafi da hannayensu suna wak’e-wak’e kamar haka:

Ni madara

Ni zuma

Ni alkakin zuma

Haka za su yi har su gaji su tashi cikin nishad’i da walwala suna raha, wannan wasan yana nishad’antar da su matuk’a.

4.3.5 Wasar Ayye Rashidalle


Yadda ake yi a wannan wasan shi ma ‘yan mata yara kan had’u a dandali su yi da’ira cikin jin dad’i da kwanciyar hankali suna rawa tare da rera wak’e-wak’e, d’aya kan yi tsalle tana fad’owa a jikin ‘yar uwarta, ga dai baitocin wak’ar kamar haka:

Ayye Ra

Ayye Rashidalle

Rashida mai koko

Rashidalle

Wadda ba ta wanka

Rashidalle

Wadda ba ta wanki

Rashidalle

Sai ruwan sama ya zo

Rashidalle

Sai ka ganta a gona

Rashidalle
tana roro-roro

Rashidalle

Tana roron wak’e

Rashidalle

Ayye Ra Ayye Rashidalle

Hikimar wannan wasan shi ne yana nuna cewa yarinya ta tsaftace jikinta ba wai zuwa gona kad’ai ba.

4.4 Nad’ewa


Wannan babi na hud’u yana da taken: “Wasannin yara mata a k’asar Faskari.” Babin ya kawo bayani game da yadda yara mata ke shirya wasanninsu a k’asar faskari. Bayan nan kuma, babin ya kawo ire-iren wasannin yara mata wad’anda suka had’a da wasannin da ake aiwatarwa a tsaye da kuma wad’anda ake aiwatarwa a zaune. Babin ya kawo jerin wasannin yara mata daban-daban tare da bayaninsu. Daga k’arshe kuma an kammala babin da nad’ewa.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/