https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

NA


ANAS MUSTAPHA


 


KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

BABI NA BIYAR


KAMMALAWA


5.0 Kammalawa


Manufar wannan yanki shi ne ya tattaro muhimman abubuwan da aka ambata a babobin da suka gabata, domin mai karatu ko bincike ya sami damar ganin jimlar wannan bincike. Za a iya cewa daga farko dai, akwai ambaton tarihin k’asar Faskari tun daga likacin da aka kafa garin har zuwa bunk’asar da garin ya yi da yak’e-yak’en da aka yi da garin har zuwa yanzu. Wasu garuruwa da kuma bayanin irin muhimman sana’o’in da suka shahara, bayan haka akwai bayanin yadda Fulani suka kafa garin, bayan ya koma hannun ha’be.

Haka kuma na yi magnar yadda mazauna wannan garin suke da ire-iren al’adunsu a kan aure da haihuwa da mu’amula da irin tufafin da sukan sanya. Hak akwai yadda suke tafiyar da harkokinsu na wasanni da zamntakewa da juna. Saboda haka an kawo dun wad’annan abubuwan ne domin su kasance shimfid’a da fahimtar wasannin yara a k’aramar hukumar Faskari.

Domin duk wanda ya k’i bin wannan k’a’ida a hukunta shi ko kuma a hana shi yin wasa a wani lokaci, kuma bai isa ya k’i bin wannan doka ba da aka sanya masa. Haka kuma wasannin yara suna da amfani domin suna k’ara dank’on na tare a tsakanin yara, domin irin zumuncinsu, saboda haka wasannin yara suna da amfani ga yara.

Haka kuma su kansu wasannin yara suna da amfani wajen koya ma yara k’wazo, domin idan muka yi la’akari da yadda ake aiwatar da wasan langa, ta irin hanyar  da yara kan yi wazo domin ta’bo wurin da aka sanya a ta’bo. Saboda haka wasannin yara suna da amfani ga yara idan aka yi la’akari da irin k’wazo da wasu kan nuna a wurin wasa wanda irin wannan k’wazo yakan zauna har tsufansu.

Haka kuma binciken ya bayyana irin matsayi da muhimmancin wasannin yara, abun nufi a nan shi ne, tattaunawa kan irin amfani da ke tattare da wasannin ga rayuwar al’ummar Hausawa baki d’aya. Don haka a cikin wannan bincike ne na gano cewar wasannin yara suna taimakawa ga tarbiyar yara da tsara dokoki a cikin wasanni, wad’anda suke idan yaro ya karya akan hukunta shi domin kada ya k’ara maimaita wannan kuskure da ya aikata.

Haka kuma a cikin wannan bincike ne na gano irin wasannin da kan taimaka ga kiwon lafiyar yara wad’anda akasarinsu na guje-guje  ne da tsalle-tsalle. Irin wad’annan wasanni suna taimakawa ga motsa jinin yara su kasance masu lafiya da kuzari a ko da yaushe.

Ta hanyar bincike ne na gano cewar wasannin yara kamar kacici-kacici suna taimakawa ga koyar da harshe da tsarinsa na sanin d’imbin kalmomi da ke cikin harshen Hausa da d’imbin hikimomi da ke tattare da harshen. Saboda haka ne na fahimci dandalin wasa ya zama tamkar makaranta ga yara, saboda muhimmancinsa.

Haka kuma wasannin yara suna k’arfafa zaman tare tsakanin yara, har da tsakanin iyayen yara, saboda had’uwar da suke yi a gidajen juna kafin su tafi wurin dandalin wasa, irin wannan yakan sa a samu dank’on zumunci mai d’orewa har zuwa tsufansu. Haka wasannin yara sukan koya wasu jaruntaka da dabaru na kare kai da k’wazo da hak’uri da basira da wayo da k’ok’ari da kuma koyar da shugabanci, musamman a irin wasannin da akan yi a dandali.

Haka wannan nazari nawa ya bayyana rabe-raben wasannin yara a inda suka rabu zuwa wasannin yara maza da kuma wasannin yara mata, ko ‘yan mata. Wannan bincike ya kawo wasannin yara maza, wanda ake yi daga tsaye da wanda ake yi daga zaune. Daga nan na kawo wasanni guda biyar na yara na zaune da bayanin yadda ake aiwatar da su da lokacin da ake aiwatar da su da wurind a ake aiwatar da su. Haka zalika an kawo na tsaye su ma da yaran ke aiwatarwa.

Haka kuma su ma mata an yi bayanin wasu wasanninsu na tsaye da na zaune da suke gudanarwa a dandali ko a cikin gida ko k’ofar gida. Saboda haka adaga k’arshe wannan akundi na bincike akwai sunayen littattafan da aka lek’a da kundaye na neman digiri na farko da wasu d’alibai suka yi bincike a kansa domin gudanar da wannan bincike da na yi.

 

Manazarta