Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasannin Yara A Yankin Faskari Ta Jahar Katsina Jiya Da Yau (4)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com


NA

ANAS MUSTAPHA

BABI NA UKU


WASAN YARA MAZA A YANKIN FASKARI


3.0 Shimfid’a


Wannan babi zai yi bayani ne dangane da yadda yara ke shirya wasunsu da tsara sannan kuma su gudanar da wasanninsu da kuma kawo ire-iren wasanni da suke gudanarwa a wannan yankin na Faskari tare da fayyace amfani ko muhimmancin da ke tattare da wasannin.

3.1 Yadda Yara Maza ke Shirya Wasanninsu


Faskari gari ne kamar sauran garuruwan k’asar Hausa. Kamar yadda aka sani yara kan taru a kowane gari domin su gudanar da wasanninsu iri-iri na motsa jiki, haka ma a Faskari yara kan had’u a dandali da sauran wuraren wasanni domin su shek’e ayarsu.

Wasannin dai na yara maza za a iya kallonsu a matsayin gadaddun wasanni na motsa jiki, sai sai a kan samu d’an banbanci a kowane lokaci ko kuma zamani dangane da jama’ar zamanin da kuma halayensu, sannan kuma idan muka shiga cikin wasan gadangadan za mu ga cewa wasu amfaninsu motsa jiki wasu kuma koyar da dabarun rayuwa, nishad’i da kuma bin dokoki.

 

3.2 Ire-Iren Wasannin Yara Maza A Faskari


Idan aka ce ire-iren wasannin yara maza to ba za a iya kawo su duka ba, sai dai mai magana a kansu ya d’ebo fitattu daga cikinsu ya yi magana akai saboda wasu canje-canje da ake samu a cikin wad’ansu wasannin.

Su dai wasannin yara maza sun kasu kashi biyu ne wato akwai wasanni na tsaye da kuma wasanni na zaune don haka za a yi k’ok’arin kawo bayani a kan wad’annan wasannin.

3.2.1 Wasannin Yara Maza na Zaune


Wad’annan wasu wasanni ne da yara maza ke gudanarwa a zaune.

3.2.2 Wasar Efa-Efa


Yadda ake yi yara maza kan samu wuri su zauna su kalmashe k’afafuwansu su yi sikel kowa zai fad’i yawan yatsun da za a buga a k’asa idan aka buga yatsun aka k’irga wanda ya yi nasara aka k’irga daidai yawan wad’anda ya fad’a to zai koma gefe d’aya ma’ana ya ci wasan. Haka za a yi har sai kowa ya fita an bar mutum d’aya a k’arshe dukkan yaran da suka yi nasara za su motsa wanda aka bari a k’arshe zai had’e hannuwansa biyu kowa ya zo yai masa mari biyar a bayan hannu.

Fa’idar wannan wasan shi ne yaro ya san cewa komai zai yi ya rink’a k’ok’ari kar a bar shi a baya ma’ana barin mutum a k’arshe ba abu ne da ake so ba.

3.2.3 Wasar Zan-Zaniye


A wannan wasan kuma yara kan zauna su jera layi su mik’e k’afufuwansu a sami yaro d’aya ya rink’a ta’bo gwuiwoyinsu yana wak’a duk wanda wak’ar ta k’are a kan gwuiwarsa to ya ci wasan sai ya koma gefe haka za a yi har a gama na k’arshe kuma a yi masa dariya ana tsarguwar shi. Ga wak’ar wasan kamar haka:

Zani-zaniye

Zani kadisau

Kadisan doki

Dokin kara

Kara na albasa

Albashi kwaddi

Zuciyar damo

Na fad’a kudu

Na kuma na fad’a kudu

Hikimar yin wannan wasan aa gurinsu shi ne samun nishad’i da kuma walwala a tare da su. Sannan zaman da suke yi yana k’ara musu shak’uwa a cikin zukatansu.

3.2.4 Wasar Kod’i


Yadda ake yi yara kan taru a wurin da yake akwai k’asa su zauna. Sukan sami mufin biro da kuma murfin batiri su had’a kod’i domin su yi wasan da ita. D’aya daga cikin yaran zai rik’e kod’i ya murza sai ya sake ta a k’asa tai ta yawo tana juyawa sai ya sa d’an yatsa ya sak’alo idan ya ci sa’a ta kife a kan murfin batiri tsinin biron ya kalli sama to ya ci wasan kenan. Abokin wasan zan aje bayan hannunsa a k’asa, shi kuma ya d’auki kod’i ya k’wala masa a bayan hannu, yana k’ara sak’alota da yatsa idan ta k’ara kifa a kan murfin batiri zai k’ara buga masa haka za a yi har sai ta kifa ba daidai ba, sa’annan shi ma amsa ya murza idan ya sak’alota daidai to shi ma haka za a juya masa bayan hannu ya k’wala yadda akai masa haka za su yi har su gaji su tashi.

Amfanin wasan shi ne bin doka domin kuwa an saka cewa idan mutum bai fad’i ba to zai ta k’walawa d’an uwansa. Idan muka lura dokoki a wasannin yara suna da muhimmancin domin sukan sa musu d’a’a su basu himmar yin abu kar a bar su a baya.

3.2.5 Wasar Jar d’illa


Yadda ake yi yara kan samu wuri mai k’asa su k’wak’ula rami mai d’an matsakaicin zurfi kowa ya ja layi taki d’aya a gabansa sai a samu k’wallon zaitun kowa ya rik’a dillawa da d’an yatsansa d’aya, na farko zai fara d’illawa idan ya samu sa’a ya fad’i a ramin to zai k’ara jan layi tak’i d’aya a gabansa. Idan kuma ya fad’i ma’ana bai sami sa’a ta fad’a cikin ramin ba to wani zai amsa ya ci gaba, haka za a yi har mutum ya yi k’ok’ari ya had’a allo a gabansa.

Hikimar wannan wasan shi ne yaro ya kan koyi dabarar yin abu da sauri domin kada a bar shi a baya ya kasa had’a abin da d’an uwansa ya yi na ban sha’awa.

3.2.6 Wasar K’wak’ulowa


Yadda ake yi a kan yi da’ira a zauna mutum biyar ko sama da haka, kowanne zai yi k’ok’ari ya gina rami a gabansa za a tafi bayan kowa ya gina ramin sai a samu mutum d’aya wanda babu raminsa a ciki ma’ana ba ya da rami sai ya samu k’wallon dabino, dutse, zaitun, k’arfe da dai nau’in wani abu ya zo ya saka abu d’aya d’aya a kowane rami sai ya rufe ramin da k’asa bayan ya saka, sannan sai ya k’ira su kowa ya zo ya fad’i abin da ke cikin raminsa idan mutum ya fad’a sai a ce ya tonen ramin idan ya tone aka ga abin da ya fad’a daidai to ya sami nasara haka za a yi ma kowa wanda suka canki daidai to sai su yi ta jin dad’i.

Hikimar wannan wasan shi ne su sami nishad’i a zuciyarsu domin za su ji dad’i su da suka ci nasara, wad’anda kuma suka fad’i za a yi musu dariya, wannan dariyar za ta sa gobe su yi k’ok’ari kar a barsu a baya.

3.2.7 Wasannin Yara Maza na Tsaye


Wad’annan wasannin yara maza ne da suke aiwatarwa a tsaye lokacin da suke wasan.

3.2.7.1 Wasar Jirgi


Yadda ake yi yara had’u su fita su sami fili ko filin k’wallo musamman don su yi wasan. Galibi wannan wasan jirgin yara kan aiwatar da shi lokacin da suka lura akwai ban iska a gari ma’ana iska tana kad’awa, sai su sami tsinkaye guda uku, da leda da kuma zane mai d’an tsawo sai su aje leda da kuma zane mai d’an tsawo sai a aje ledan nan a k’asa su gitto tsinken a kan ledar su k’ulla k’yalle a kusurwar, kowane tsinke sai su sami zare su k’ulla jirgin. Wannan ledar da suka had’a, idan kowa ya had’a nasa to sai a rik’e a jera wuri d’aya a tsaya sai kowa ya saki na shi iska ta yi sama da shi duk wanda nasa ya yi nisa sosai a sama sai ya yi ta jin dad’i yana murna ya had’a jirgi ya tashi sama ya wuce na wani wanda nashi yak’i tashi sama sai a yi masa dariya.

Amfanin wannan wasan shi ne samun nishad’i a tatttare da su da kuma had’uwa wuri d’aya, yana kuma hana musu yawon banza.

3.2.7.2 Wasar Kyauro


Yadda ake yi yara kan sami kyauro su tafi su sami wuri me siminti su tsaye a tsaye su ja layi na farko zai harba nasa duk wanda ya yi nasara kyauronsa ta hau kan kyauron da aka jefa har aka samu kofa to komai yawan kyauron da aka jefa sun zama nasa zai kwashe su duka ya bar guda d’aya a k’asa. Sannan na kusa da shi ci gaba haka za a yi ta jefawa har sai an jefa kan wata, wanda aka yi ta jefawa baya ci nasa suka k’are to zai koma gefe d’aya an cinye shi haka za a yi har na kowa ya k’are su zamana a hannun mutum d’aya ya tafi yana murna, idan kuma ya rage mutum biyu sun kasa cinye d’aya cikinsu kuma sun gaji, sukan yi ma kansu sulhu kowa ya d’auki ta hannunsa a tashi hakanan saboda sun gaji ko lokacin wasan ya wuce za su makaranta ko gida wurin aike. Shi ma wannan wasan a kan sami nishad’i da walwala a tattare da su, kuma had’uwarsu a wurin wasan yana k’arfin zumunci.

3.2.7.3 Wasar Rafi


Yadda ake yi yara kan had’u a bakin rafi musamman da yamma ko da safe idan ba a makaranta. Galibi sun fi zuwa rafin lokacin damina domin mafi yawancin wasannin a cikin ruwa suke aiwatar da su. Sukan taru a bakin rafi kowa ya nuna bajintarsa wani lokaci zaka ga suna tsalle suna juyi su fad’a cikin ruwan su nitse suna tafiya ba tare da sun fito da kansu waje ba. Sannan suna yin nitso cikin ruwa su sami wani ya tsaya waje ya kalla musu wanda zai saurun fitowa wani lokaci kuma sukan nitse a cikin ruwa suna yawa a samu mutum d’aya ya rink’a yawo yana nemansu. Haka za su yi ta wasa iri-iri a cikin ruwan kowa yana nuna bajintarsa a cikin rafin,

Amfanin wannan wasan shi ne samun dabarun iya shiga ruwa ko da ka samu kanka a hanyar da teku ya ke ko wani ya fad’a ya kasa fitowa mutum yana iya taimakonsa, sannan yana tattare da motsa jiki yana taimakawa wajen yawaitar jini a kowane sashe na jikin mutum.

 

3.2.7.4 Wasar Jini da Jini


Yadda ake yi yara kan had’u a dandali ko wani guri na musamman domin gudanar da wasan. Suna had’uwa wuri d’aya su yi kusurwa su tsaya a tsaye mutum d’aya yana bayar da lafuza cikin salon wak’a kamar haka. Da ya fad’i suma su fad’i:

Bayarwa: Jini da Jini

‘Yan wasa: Danja

Bayarwa: Akuya da jini

‘Yan wasa: Danja

Bayarwa: Dutse da jini

‘Yan wasa: Babu

Bayarwa: Yaro da jini

‘Yan wasa: Danja

Bayarwa: Dutse da jini

‘Yan wasa: Babu

Bayarwa: Kaza da jini

‘Yan wasa: Danja

Haka za su yi ta lissafa abubuwa masu jini ana cewa danja wad’anda basu da jini ana cewa babu. Duk wanda ya yi kuskure aka fad’i abin da ke da jini ya ce babu to zai sha duka ‘yan wasa duka za su yi ta bugunsa, haka in aka fad’i abu mara jini wani ya ce danja to za a had’u a yi ta bugunsa.

Hikimar wannan wasan shi ne yaro zai san abu mai rai da kuma marar rai ma’ana zai rik’e abu mai rai yana da jini marar rai kuma ba shi da shi, sannan ya kan taimaka musu wurin rik’e yaya abu yake wane iri ne.

3.2.7.5 Wasar Wane Tsallaka Wane


Yara sukan had’u su biyar ko fiye da haka a samu d’aya ya zauna ya mik’e k’afafunsa sai mutum d’aya ya rufe masa ido sauran za su rink’a tsallaka k’afarsa duk wanda ya tsallaka k’afarsa aka tambaye shi wa ya tsallaka ka? Idan ya fad’i daidai to zai tashi wannan ya zauna shi ma ya mik’e k’afa a rufe masa ido a tsallaka shi, ana tambayarsa wa ya tsallaka ka? Idan ya fad’i daidai shi ma ya tashi idan bai fad’i ba haka za a yi ta tsallaka shi, haka za su yi har su gaji su tashi.

Amfanin wannan wasan shi ne suna samun nishad’i da walwala sannan ga motsa jiki.

Wad’annan wasannin na yara maza na yara a garin Faskari da aka kawo suna da amfani ga yara k’warai da gaske domin kuwa dukkan wasannin suna da amfani kamar haka:

Motsa jiki; wasannin yara suna da amfani ta hanyar motsa jiki domin motsa jiki hanya ce da ake samun sa a wasannin yara ta hanyar tsallake-tsallake ko guje-guje wannan yana taimakawa wajen yawaitar jini a kowane sashe na jikin mutum.

Haka yana da amfani ta hanyar koyar da harshe, misali, irin Hausar da akan gudanar a wurin wasanni da irin wasa k’wak’walwa da yaya kan gudanar misali kaman wasan jini da jini irin wannan wasan ya kan k’ara ma yaro kaifin basira da sanin harshensu.

Sannan wasannin suna taimakawa wajen koyawa musu bin dokoki da kuma d’a’a, domin idan muka lura da irin wad’annan dokoki da ake sanyawa a wurin wasanni, misali idan aka ce kada a yi abu to zaka yara a wurin wasan sun kiyaye.

Haka kuma yana taimakawa wajen had’a kan yara su zamo tsintsiya mad’auri d’aya, ga nishad’i da kuma hana yara yawon banza.

3.3 Nad’ewa


Wannan babi na uku yana da taken: “Wasanni yara maza a yankin Faskari.” Babin ya fara kawo bayani game da yadda yara maza ke shirya wasanninsu. Daga nan kuma sai babin ya kawo ire-iren wasannin yara maza wad’anda suka had’a da na zaune da kuma na tsaye. Babin ya kawo wasannin daban-daban na maza tare da bayanin yadda ake aiwatar da kowanne. Daga k’arshe kuma an kammala babin da nad’ewa.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments