Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakokin Hausawa Na Gargajiya (Traditional Music of the Hausa People) (3)


(An introductory study of the forms functions and the qualities of the traditional music of the Hausa people)

3.0 Gabatarwa


A rukunin da ya wuce, an yi bayani ne tare da ba da misalan wak’ok’in Hausawa na gargajiya da suka shafi wasannin yara maza da mata na dandali da kuma wasannin tashe na yara maza da mata. Wannan rukuni kuwa zai karkata ne zuwa ga misalan wak’ok’in gargajiya na Hausawa da suka shafi wasu ‘bangarori ko al’amuran rayuwar Bahaushe. Wannan ya k’unshi wak’ok’in da ake rerawa yayin gudanar ayyuka daban-daban da suka had’a da da’be da daka da nik’a da makamantansu. Sai dai za a kawo wak’ok’in ne kawai ba tare da nazartansu ba. Kenan akwai buk’atar nazarin wak’ok’in d’aya bayan d’aya domin fito da falsafar da kowace wak’a ta k’unsa.

3.1 Daka


Daka na nufin sanya tsabar hatsi ko wani abu makamancin wanann cikin turmi tare da amfani da ta’barya domin lallasa shi har sai ya koma gari. Bayan hatsi akwai abubuwan da ake dakawa da suka had’a da kayan miya irin su citta da kanamfari da masoro da barkono da da dai sauransu. Mace d’aya na iya yin daka, sai dai wani lokaci akan samu mata biyu ko ma sama da haka sun had’u a turmi guda domin daka. An fi samun irin wannan yanayi a gidajen bukukuwa kamar bukin aure ko na haihuwa da makamantansu.

Da yake daka aiki ne na wahala da ke buk’atar amfani da k’arfi domin gudanarwa, wak’a na kasancewa tamkar sinadarin k’ara k’aimi ga masu daka. Wannan ya sanya masu dakan ke rera wak’ok’i daban-daban domin d’ebe kewa da annashuwa da kuma k’arin kuzari da k’arfin guiwa dangane da aikin da suke gudanarwa. Irin wad’annan wak’ok’i na d’auke da zambo da habaici a mafi yawan lokuta.

A ‘bangare guda kuma, sukan gwama ta’baren da ke hannayensu cikin salon burgewa da sabo da k’warewa, wanda hakan ke samar da sautuka tamkar na kid’a. Akan kira wannan salo da suna lugude ko mama. Lugude kuwa tamkar gishiri ne ga wak’ar da masu daka ke rerawa. Gusau, (2008: 224) ya kawo misalin wak’ar daka kamar haka:

3.1.1 Ta Gidan Malam Audu


 

Ke ta gidan, ke tagidan,

Ke ta gidan Mallam Audu.

 

Uwar gidan Malam Audu,

Sha lelen Mallam Audu.

 

Ina yininki?

Binta ina yininki?

 

Gaisuwa da aminci,

Yarda ta fi aminci.

 

 

Hausa tana gaishe ki,

Kin kwana lafiya?

Kin tashi lafiya.

 

Wadda ake lugude da ita za ta ba da amsa kamar haka:

 

Ke ma kin tashi lafiya?

Ke ma ina gaishe ki,

Kin yini lafiya?

 

3.1.2 Ana Lugude Ana Mama


 

Ana lugude ana mama,

Cikin shigifa cikin soro.

 

Mama ba habaici ce ba,

Salon daka a hakan nan.

 

Ga maccen da ba a so ta haihu,

Ta haifi k’wandamin d’a namiji.

 

Shugaban daka shi ka daka,

‘Yan tanyo kissa sukai,

Sukus-sukus sai su aje.

 

Gidan Marafa kaji ka daka,

Tarmani na izo wuta.

 

Tarmani na izo wuta,

Angulu ka kir’ba dawo.

 

 

 

3.1.3 Ta Sa Ni A Dutse Ta Nik’a


 

Ta sa ni a dutse ta nik’a.

 

Ta sa ni a turmi ta daka!

 

Ni ma zan sa ta a turmi in daka!

 

Ni ma zan sa ta a dutse in nik’a!

 

Ta saci kud’in mallam.

 

Ta sayi nama ta yi ta ci.

 

3.2 Da’be


A al’adance, manyan mata ne suka fi gudanar da da’be. Da’be kuwa hanya ce ta gyara d’aki (musamman sabon d’akin amarya) da lailaye shi domin ya yi kyau. Bayan k’ara wa d’aki kyau, wani amfanin da’be shi ne rage tone-tone da ‘beraye (kusu) ko wasu k’wari za su iya yi a cikin dad’in. Da yake da’be aikin k’arfi ne, akwai wak’ok’i iri-iri da mata kan yi domin d’ebe kewa da samar da kuzari ga masu wannan aiki. Misalan wad’annan wak’ok’i sun had’a da:

 

 

3.2.1 Mu Je – Mu Je


 

Bayarwa: Mu je – mu je.

Amshi: In mun je ba dawowa.

 

Bayarwa: Za a da ni,

Amshi: Ba za a da ke ba,

Mai tsince,

 

Ba za a da ke ba,

Mai k’arya.

 

Ba za a da ke ba,

Mai zund’e.

 

Bayarwa: Mu je – mu je,

Amshi: Shan furanmu ikon Allah,

In mun je ba mu dawowa.

 

3.2.2 Bawan Allah


 

Bawan Allah,

Talakka bawan Allah.

 

Ba shi da baki,

Balle shi furta kalami.

 

Ba shi k’afafu,

Balle shi tashi shi tsere.

 

Bawan Allah,

Talaka bawan Allah.

 

3.2.3 Lumu Shege!


 

Ina Lumu shege,

Mai malmala ga munta.

 

Kare bak’in bahwade,

Ya hana mu walwala.

 

Mata ku yo aniya,

Bana Lumu k’wace yakai.

 

Ta masussuki yab biya,

Yat ta da gindi tsaye.

 

Wanga d’an bak’in mugu,

Ya hana mu walwala.

 

Kare bak’in bahwade,

Mai malmala ga munta,

Ba za ya gwaa hwashe ba.

3.3 Kad’i


Kad’i hanya ce ta yin amfani da mazari wajen sarrafa auduga domin samar da zaren da ake amfani da shi wurin yin tufafi ko gyara tufafin da aka riga aka yi. Manyan mata aka fi sani da sana’ar kad’i. A lokacin kad’i, mata kan yi wak’ok’i daban-daban. Misalai daga ciki sun had’a da:

 

 

3.3.1 Allah Ba Ni Kad’a


 

Bayarwa: Allah ba ni kad’a,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

 

Bayarwa: In yi zare na kaina,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: In yanke zugage,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

 

Bayarwa: Dela nan tara nan talatin,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Allah ba ni kad’a,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

 

Bayarwa: In wa masoyi riga,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: In wa masoyi wando,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

3.3.2 Amadu


 

Ayye yaraye zare nake yi,

Ayye yaraye nanaye.

 

Amadu kundu Amadu siliya,

Amadu kundu aska tara.

 

A kowas ya fad’a mini Amadu,

Na ce riga ni ka yo masa.

 

Mai aska tara, wando ni kai masa,

Hulla ni kai mai, mai aska tara.

 

Bana rawani ni kai masa,

Aljanna kusa fad’awa mu kai.


 

 

3.4 Kitso


Kitso hanya ce ta tsaftace gashi da gyara shi. Bayan an taje gashi, akan k’uk’k’ulla shi cikin salo ko tsari mai kyau. Akan d’auki tsawon lokaci kafin ga kammalawa mace guda kitso; wanda hakan ya danganta da salon kitson da ake yi. A maimakon zaman shiru, akwai wak’ok’i da akan rera yayin kitso da suka kasance d’ebe kewa da samar da nishad’i. Wannan zai sa a kammala kitso ba tare da k’osawa ba. Daga cikin wak’ok’in kitso akwai:

3.4.1 Mai Kitso


 

Mai kitso ‘yar salama.

 

Ka da mata ki taushe.

 

Ke ka da mata ki kalmoshe.

 

Ko da gidan mai gari ne.

 

Ko ko gidan talakawa ne.

 

Shige ki wa mata kitso.

 

Don kuma maigida yak kire ki.

 

Kuma mata sun kire ki.

 

Babu halin shari’a.

3.4.2 Ta Yi Kitsonta


 

Ta yi kitsonta,

Beru tai sak’arta.

 

Ta sai d’an zanen d’aurawa,

Ta fita.

 

Wagga Agola,

Ta zo ta d’auke shi.

 

Wagga Agola,

Ko kitso ba ta iyawa.

 

Wagga Agola,

Ai babu irinta,

 

Bak’ar Agola,

Ta hana mata sauran zanensu.

 

Ke dai Beru,

Zanka kitsonki.

 

3.5 Nik’a


Nik’a ma aiki ne da aka san manyan mata da shi. Hanya ce ta amfani da duwatsu na musamman domin sarrafa ko hatsi ko wani abin da ya shafi abinci zuwa gari ko dai mai laushi. Yayin da mata ke nik’a, sukan yi wak’ok’i iri-iri da suka had’a da:

3.5.1 Zakkar Gida


Hannunta ba shi tashi ga daka,

Ga cin tuwo yaka tashi.

 

Tasa uku hitarta fad’uwarta,

D’auki mai lak’ak’k’e-lak’ak’k’e.

 

Mai lak’ak’k’en hannu,

Da ba shi tashi ga daka,

Ga cin tuwo yaka tashi.

 

Malmala taka loma da ita,

Gidauniya kur’bi ukku takai mata.

 

Ban kula ba, ban sa kai ba,

Ban kula ba da marin k’ato,

Balle na d’an jariri.

 

D’auki-d’auki in tanye ki,

In ba ki so in d’ebo.

 

Zama daka tanyo ne,

Ido ka tsoron aiki,

Hannu na fad’in a kawo mu gani.

 

Maccen kurku maccen banza,

Maccen da ba ta wa namiji isa.

(Illo, 1980:11)

 

3.5.2 Wak’ar Kishiya


 

Ayye yaraye iye nanaye,

Ayye yaraye iye nanaye.

 

Ga wata kishiya ruwan sunni ce,

Wata ko na zafi ya fi ye mata.

 

Kishi da ‘yar malan nake gudu,

Ta yi maka magani ta saka a hanya.

 

Hanyar gidanku ta barbace maka,

Allah ba ni kishiya mai yaji.

Kamin ta dawo na ci duniya.

 

3.5.3 Nak’uda Ta Tashi


 

Wayyo nak’uda ta tashi,

Ciwon nak’uda ya tashi.

 

Kuma ciwon nak’uda ya motsa,

Yau kam babu zama zaure.

 

Wayyo Inna ki cece ni,

Ciwon nak’uda ya tashi.

 

 

Da kis sha dad’inki,

Ke tuna da Inna ta cece ki?

Ko ke tuna da baba ya cece ki?

Wayyo nak’uda ‘yar ziza!

 

Ciwon nak’uda bori ne,

Ko ko nak’uda hauka ce!

 

Wayyo nak’uda ta tashi,

Wayyo nak’uda ta motsa.

3.5.4 K’azama


Zanka wanka da wanki,

Ke yi mak’al-mak’al.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi dak’al-dak’al.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi k’azan-k’azan.

 

Zanka wanka da wnki,

Ke yi mujur-mujur.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi kuca-kuca.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi kurun-kurun.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi k’irin-k’irin.

 

Zanka wanka da wanki,

Ke yi bak’i k’irin.

 

A’a wanke zannanki sauna,

Sun yi tilin-tilin,

 

A’a zanka wanka da wanki,

Ko kya yi fari-fari. (Illo, 1980: 8)

3.6 Raino


Rainu na nufin rarrashi ko lalla’bin jariri yayin da yake kuwa domin ya yi shiru ko kuma domin kada ya yi koka ko ya k’osa da yanayin da yake ciki. Za kuma a iya kallon ma’anar rainu da “Kulawa da jariri na gaba d’aya.” Wato lura da al’amura da yanayi ko halin da jariri yake ciki, tare da samar masa da buk’atunsa. A lokutan reno, mai reno na rera wa jariri ko yaro wak’ok’i daban-daban tare da rausaya (yi masa rawa) shi. Daga cikin misalan wak’ok’in reno akwai:

Gusau, (2008: 225) ya kawo misalin wak’ar raino da aka samar a wajajen shekarar 1952 da ta kasance kamar haka:

3.6.1 Bari Kuka Sa’idu


 

Yi shiru bari kuka Sa’idu,

Me kake wa kuka Sai’du?

 

 

Mai kud’d’i Sa’idu,

Ku taho ku gane shi,

Ku yo ziyara.

 

D’an yaro ya buwaya,

D’an yaro sai dai a bi ka,

Amma ba ka bi su ba.

 

D’an Malammai Sa’idu,

D’an Alk’alai Sa’idu,

Gidanku an yi gadon karatu.

 

Ga kuma kud’d’i barkatai,

Kuma ga shi kun gadi hank’uri.

Kai yi shiru d’an yaro Sa’idu,

Yi shiru bari kuka Sa’idu.

3.6.2 Wane Ne?


 

Wane ne ya ta’ba mana Zainabunmu?[1]

 

Mu kama shi,

Mu kai shi caji’ofis a kulle shi.

 

Yaya ne ya ta’ba mana Zainabunmu.

 

Ku kama shi,

Ku kai shi caji’ofis a kulle d’an banza.

 

 

 

3.6.3 Tutu Kuletu


 

Tutu-tutu,

Tutu kuletu.

 

In uwar d’an nan ne?

Ta tafi rafi.

 

Kira ta ta dawo,

Ta ba shi mama.

 

Ya sha ya k’oshi,

Ya ba ni nawa.

 

Ya ba ni nawa,

Don ladan reno.

 

Takuletu,

Takuletu,

Takuletu!

 

3.6.4 Tashi In Raushe Ka


 

Tashi in raushe ka,

A daren jiya ko ka girma ne?

 

3.6.5 Tashi In Gan Ka


 

Tashi in gan ka,

Sabulun gale soson gale.

 

Tashi in gan ka,

D’an farin d’a kyakkyawa.

 

Tun da ake cikinka,

Ban ta’ba surfe ba.

 

Tun da ake cikinka,

Ban ta’ba yin tankad’e,

Abin ‘bata jiki ba.

 

3.6.6 D’an Yaro Fari Tas


 

D’an yaro fari tas,

Kamar daga Ingila ya taso.

 

D’an hanci surat rat,

Kamar daga maina ya karyo.

 

3.7 Tatsuniya


Tatsuniya k’agaggen labari ne mai tattare da hikima da fasaha da akan gina bisa wani jigo na musamman da ya danganci ilimantarewa ko fad’akarwa ko koyar da jarumta ko dabarun zaman duniya ko gargad’i da makamantansu. Akan samu wak’ok’i a cikin wasu daga cikin tatsuniyoyin Hausawa. Irin wad’annan wak’ok’i na cikin misalan wak’ok’in gargajiya na Hausawa. Duk da cewa mak’asudin wannan takarda shi ne fito da wak’ok’in gargajiya na Hausawa fili, za a kawo wasu daga cikin tatsuniyoyin kafin bayyana wak’ok’in da ke k’unshe cikinsu.

 

3.7.1 Tatsuniyar Icen K’osai


Ga ta nan ga ta nanku:

Akwai wata yarinya ne dai uwarta ta mutu. Ta kasance maraya a gaban kishiyar uwarta. Kullum kishir uwarta na gallaza mata idan ubanta ba ya nan. Ita ce take shara, take wanke-wanke da wanki da d’ebo ruwa a rafi da kuma kai dabbobi kiyo.

Ana nan ana nan sai kishiyar uwar ta k’udiri ta hallaka ta ta hanyar yunwa. Saboda haka ta k’uduri aniyar ba za ta sake ba ta abinci ba. Da gari ya waye ta ce mata: “D’auki goran ruwanki ki tafi kiyo.” Yarinyar ta ce: “Umma ban ci d’umame ba.” Kishiyar uwar tata ta daka mata tsawa: “Shashashar ‘ya, wuce ki ba ni wuri!”

Haka yarinyar nan ta nufi hanyar jeji tana tafe tana kuka. Tana cikin tafiya sai ta had’u da babanta zai dawo gida. Ya tambaye ta me ya faru? Sai kuwa ta sanar da shi cewa yunwa take ji. Uban nata ya d’auki sisin kwabo ya ce mata ta sayi k’owai. Yarinyar kuwa ta je wurin mai k’osai ta sayi ‘yan biyu sisi ta wuce da su jeji wurin kiwo.

Bayan ta isa jeji tumaki da awakin da take kiyo sun fara kiyo, sai ta zauna a gindin bishiya ta d’auko k’osanta guda biyu. Ta cinye guda d’aya. Ragowar d’ayan kuwa a maimakon ta ci, sai ta shuka shi a k’asa. Haka ma ruwan gorarta, ta sha rabi, rabin kuma ta yi wa k’osan da ta shuka bayi da shi.

Da ta dawo gida kishiyar uwarta ba ta ga ta galabaita sosai ba, sai ta ce a zuciyarta: “Ke jaruma ko? Bari mu gani zuwa gobe, yunwa sai ta kashe ki.” Haka kuwa aka yi, washegari ta kora ta kiyo ba tare da ta ba ta abinci ba. Yarinya ta kama hanya tana kuka har ta isa wurin kiyo. Tana zuwa ta tarar da k’osan da ta shuka ya tsiro ya yi nisa tsololo yadda ba za a iya ciran ‘ya’yan ba. Ko k’arshensa ma ba a hangowa tsabar tsawo. A nan yarinyar ta yi farin ciki. Sai kuma ta fara wak’a kamar haka:

K’asa-k’asa dai icen dabino,

Sauk’o icen k’osai,

Ba don rashin uwa ba,

Ba zan shuka ka ba.

Sai kuwa ta ga bishiyar ta fara saukowa a hankali a hankali. Har dai ta sauko daidai yadda yarinyar ke tsaye. Nan kuwa yarinyar ta kalli ‘ya’yan k’osai sun nuna sai maik’o suke yi suna k’amshi bus-bus. Ta cira ta yi ta, sai da ta k’oshi. Sai kuma ta sake wak’a kamar haka:

Sama-sama dai icen maraya,

Koma icen k’osai,

Ba don rashin uwa ba,

Ba zan shuka ka ba.

Sai kuwa ta ga bishiyar k’osai na komawa sama a hankali a hankali, har ya k’ule k’ololuwa. Lokacin da yarinyar nan ta dawo gida, kishiyar uwar ta yi mamaki. Ta daka mata tsawa: “Me kika je kika ci?” Yarinyar kuwa ta ce ai ba ta ci komai ba. Kishiyar uwar ta ce k’arya take yi. Amma yarinyar ta k’i fad’a mata.

Haka dai aka ci gaba da yi kullum kishiyar uwar yarinya na sa ido don ta ga yarinya ta mutu da yunwa. Amma sai ta ga a maimakon ta rame, sai k’iba da kyau take k’ara yi. Rannan sai kishiyar uwar ta yi shawarar za ta je ta ga me wannan yarinya ke ci a jeji. Ta bi ta a sand’a har suka isa wurin kiyo. Nan kuwa uwar kishiyar ta ga duk abin da ya faru.

Uwar kishiyar nan ba ta zarce ko ina ba sai gidan sarki. Da ma sarkin garin wani azzalumi ne. Duk wani mai arziki sai ya k’wace arzikin. Da isarta ta kwashe labari duk ta fad’a masa. Nan kuwa ya ce da fadawa maza a shirya masa sirdi a je wurin bishiyar nan. Da ma sarkin yana da wani d’a, saurayi kyakkyawa. Shi kuwa wannan d’a mai haknali ne da tausayin talakawa. Don haka ya ba da shawarar kada a ta’ba wa yarinyar nan bishiyarta. Amma sarki bai kula ba.

Haka aka d’unguma gaba d’aya aka nufi wurin bishiya. Ana zuwa aka ga bishiyar zosai tana ta k’amshi amma ba wanda zai iya kaiwa ga ‘ya’yanta. Uwar kishiyar nan ta zo wai za ta gwada wak’ar da yarinya ta yi. Ta fara wak’aar da gwardon muryarta kamar gogen raki:

K’ASA-K’ASA DAI ICEN DABINO,

SAUK’O ICEN K’OSAI,

BA DON RASHIN UWA BA,

BA ZAN SHUKA KA BA.

Ta yi ta wak’ar har sau uku amma babu abin da ya faru. Sai ta ba wa sarki shawara a je a kamo yarinyar ta zo ta yi wak’ar da kanta. Haka kuwa aka je aka jawo wannan yarinya tana ta kuka. Aka sa ta dole ta yi wak’ar ba tare da tana so ba. Sai kuwa ga bishiyar k’osai na saukowa a hankali, har ta zo k’asa-k’asa. Fadawan sarki suka tsinki ‘ya’yan suka mik’owa saiki. Da ya ci ya ji dad’in da bai ta’ba cin wani abinci irinsa ba. Nan da nan sarki da fadawa da sauran mutanen gari azzalumai suka fara rige-rigen hawa wannan bishiya. Suka d’ale gaba d’aya da yake bishiyar k’atuwa ce, kowa na ta faman ci. Wasu suna d’urawa a aljihunan manyan rigunansu.

D’an sarki da ke tsaye a gefe sai ya zo wurin yarinyar nan. Ya rad’a mata a kunne cewa, ta yi wak’ar da bishiyar za ta tashi sama. Nan kuwa ta yi wannan wak’a kamar yadda ya fad’a mata. Saiki da azzaluman gari da azzaluman fadawa sun shagala da cin k’osai mai d’an karen dad’i. Ba su ma ankara da bishiyar nan tana tashi har ta luluk’a da su cikin gajimare.

Wasiri da da kek’a ya dubi sauran fadawa ya ce: “Allah ya kawo mana k’arshen zalunci ta hanyar wannan marainiya. Yanzu ba abin da ya fi sai a nad’a wa yarima d’an sarki sarautar wannan gari.” Ba tare da musu ba dukkanin fadawa suka aminta. Da ma duk suna son yarima saboda hankalinsa da kuma adalci. Ba tare da ‘bata lokaci ba aka shirya gagarumin bikin nad’in sarauta. Ranar biki aka d’afa abinci iri-iri. Talakawa kowa ya ci sai da ya bari. Ga kayan sha kuwa sai an za’ba.

Bayan komai ya lafa, sai d’an sarkin da ya zama sarki ya aika a je a nema masa auren mareniyar nan. Aka je aka samu ubanta. Bai yi musu ba ko da na k’wayar zarra. Nan da nan aka had’a k’ayataccen bukin aure. Shagalin da aka yi har ya fi na nad’in sarautar. Kowa ya yi farin ciki da wannan biki.

A can kan bishiyar k’osai kuwa, sarki da kishiyar uwar marainiya da sauran azzaluman gari ba su ankara ba har sai da suka tsinci kansu a can cikin gajimare. A nan suka fara zare idanu. Suka duba suka ga ba sa ko hango doron k’asa. A nan idandunansu suka raina fata. Suka tsaya nan masu kuka na yi masu zawo na yi.

Tak’urun k’us.

Ba dan gizo ba da na yi k’arya …

 

 

 

K’arin Misalan Wak’ok’in Tatsuniya


3.7.2 Wak’ar Tatsuniyar Dogarido


Laba’adana da Baba Jikan Lado,

Yau na ga taken Dogarido,

Wa zai kira min Dogarido?

Kura tana mini ga juyi,

Kura tana mini ga juyi.

 

3.7.3 Wak’ar Tatuniyar K’wark’wata Ma Gadi


 

Kai! Kai! Kai! Kar ka ta’ba,

Gonan nan na mai gari ne,

Ka san maigari na da fad’a,

Cini carmana, cini carmana,

Cini carmana, cini carmana.

 

3.8 Kammalawa


Kamar yadda aka ambata a sama, wannan rukuni ya rattabo misalan wak’ok’in gargajiya na Hausawa ne, ba tare da fed’e su ba. Saboda haka, akwai buk’atar nazartar kowace daga cikin wak’ok’in domin fitar da jigo da salailai da kuma falsafofi da za a iya tararwa ciki. Da ma dai, wak’ok’in gargajiya na Hausa sun kasance tamkar makaranta da ke koyar da darrusa iri-iri da suka shafi fad’akarwa da nishad’antarwa da ilimantarwa da koyar da dabarun zaman duniya da makamantansu. Za a ci karo da wad’annan jigogi yayin da aka nazarci wak’ok’in d’aya bayan d’aya.

 

Manazarta


Dangambo, A. (2007). D’aurayar Gadon Fede Wak’a. Zaria: Amana publishers LTD

Gusau, S. M. (2003). Jagora Nazarin Wak’ar Baka. Kano: Benchmark.

Illo, S. S. (1980). “Wak’ok’in Nik’a.” Kundin NCE da aka gabatar a gwalejin ilimi ta Shehu Shagari College of Education, Sakkwato.

Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Wak’a. Kaduna: Fisbas Media Ser’bice.

 

Kafar Intanet


www.amsoshi.com

 

 

 

[1] A wannan wuri akan sa sunan yaro ko yarinyar da ake raino.

Post a Comment

0 Comments