https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

NA

ANAS MUSTAPHA

 

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

BABI NA BIYU


TAK’AITACCEN TARIHIN FASKARI DA AL’ADUNSU


2.0 Shimfid’a


“Faskari ta d’an yabani ta Bawa mai shiga zuciya ka je da shirin yini ka kwana a can” wannan sanannen kirari da ake yi wa Faskari. Wanda aka kwatan ta da ta Bawa mai shiga zuciyar masoyinta, gwargwadon sunanta gwargwadon son ta. Haka ita ma Faskari gwargwadon yadda ka zauna gwargwadon yadda irin son ta kan shiga zuciyarka.

Saboda haka, wannan babi zai yi tsokaci a kan tak’aitaccen tarihin Faskari da kuma bibiyar yadda yanayin k’abilun k’asar Faskari suka kasance, sannan kuma da yadda mutanen k’asar ta Faskari ke gudanar da al’adunsu na yau da kullum.

2.1 Tak’aitaccen Tarihin K’asar Faskari


Duba tare da bibiyar ingantattun labarai da suka shafi k’asar Faskari, ya inganta cewa tarihin ya ne daga sannannun larabawan nan ‘yan gudun hijira wato gida da wari. Wad’anda suka fito daga alk’adewa ta k’asar Gobir zuwa Zariya, sai suka yada zango a wani gari da ake kira mafaskara (Ma’ana wajen da ake faskara itace) wad’anda a wannan lokacin duk maguzawa ne.

Garin Faskari ya faro ne tun shekarar 1778 ta ne a gurin da tunanin mutane sun fara wayewa ta hanyar wani magajin K’aura, Kuren Gamaru, a lokacin mulkin Muhammadu Bello na Katsina daga 1844 zuwa 1886.

Da farko dai sarautar ta fara ne daga gidan sarautar Faskari a lokacin mulkin Muhammadu Bello na Katsina amma daga baya sun mik’a mulkin zuwa gidan Kogawa, a sakamakon dangantakar auratayya a tsakanin Bani. Bani da kuma Gobirawa ne, bayan wad’annan tsane-tsane, Faskari ta zama Shedikwatar yankin Duba da tarihin Birnin Kogo an samo shi daga Wanke d’an Jatau a shekarar 1848 a lokacin sarautar Muhammadu Bello na Katsina a  cikin sansanin shugabannin Kogo, sun had’a da Kogo Muhammadu Kigo Ali, Kogo Ummaru, Kogo Musa, da kuma Kogo Abdu, kai har ma da Kogo Ibrahim (Abubakar, 2015).

Duba da hijirar Gobirawa zuwa Faskari wani muhimmin k’arni da ya wuce na Gobirawa tun wajen shekara d’ari a baya a lokacin da Gobirawa suka zo k’asar ta Faskari. Sai mazauna k’asar na asali ke cewa sunan garin shi ne Faskari, abin nufi shi ne ba a ta’ba cinsu da yak’i ba. Ma’ana dai shi ne sun Faskara. Wannan ne ya jawo ra’ayin Gobirawa da su zauna a wajen don kariya saboda tsari da had’in kan Gobirawa sai suka amshi mulkin yankin amma wannan bai sa sun canzawa garin suna ba. Mulkin Gobirawa a Faskari ya fara ne ‘yan shekaru kad’an bayan rasuwar a Gobir a shekarar 1804, a lokacin babban cibiyar sarautar Gobirawa da alk’alawa ta rushe wanda ya jaza tarwatsewar gidan sarautar zuwa sabon birnin Isa, Tsibiri, Ilorin, da kuma Faskari.

Wannan ya faru ne lokacin da Muhammadu Gido Magajin Bawa Jangwarzo da d’an yabani suka matsa zuwa yammacin yankin tsohuwar Faskari, a kan hanyarsu ta zuwa Zariya sai suka tsaya domin su huta sakamakon kumburin k’afar k’araminsu d’an yabayani.

A dai-dai wannan lokacin ne Magajin Dan-boka (Maguzawan kan dutse) wad’anda suka rok’e shi da ya zauna tare da su, ya kuma yarda wanda daga baya ya gane dad’in yankin a d’an zaman da ya yi ya yi addu’ar Allah ya ba da tabbacin zamansu domin gina kyakkyawan wurin zama mai tsaro da kuma tsari (Mufaskari a nan) wannan tabbas shi ne asalin sunan Faskari a don haka lokaci kad’an mutane suka fara zuwa daga sassa daban-daban suka fara tarewa suka ci gaba, suka ci gaba da yawaita a k’ark’ashin mulkin Muhammadu Gido, a cikin wannan ci gaban ne sai Muhammadu Gido ya yanke hukuncin ci gaba da k’udirinsa na zuwa Zazzau ya bar sauran jama’a a nan, daga abin da tarihi ya nuna an yi sarakuna masu yawa a k’asar  Faskari tun daga zamanin sarki Muhammadu Gido har zuwa yanzu lokacin sarkin yanzu wato Sarkin Yamman Katsina Hakimin Faskari Alhaji Tukur Sa’idu wato a zamaninsu ne sarautar Faskari: ke nan tarihi ya nuna an yi sarakuna goma sha takwas (18) daga kafuwar Faskari zuwa yau, ta kuma samu k’aramar hukuma a shekarar 1989, sannan ta na da k’auyuka da ke k’ark’ashinta guda goma sha bakwai (17). Ga sunayen sarakunan kamar haka:

Faskari Muhammadu Gidado             -        1811 – 1842

Faskari D’angabani                                     -        1842 – 1879

Faskari Ali                                         -        1879 – 1886

Faskari Yunusa                                  -        1886 – 1897

Faskari D’anbardo                             -        1897 – 1918

Faskari Abu                                       -        1931 – 1934

Faskari Abdu                                     -        1934 – 1935

Faskari D’an Ali                                -        1935 – 1936

Faskari Bawa                                     -        1936 – 1937

Faskari Madauci                                -        1937 – 1938

D’ankurciya                                       -        1938 – 1941

Faskari D’andaguma                          -        1941 – 1943

Faskari Ahmadu                                -        1943 – 1952

Faskari   Sani                                     -        1952 – 1957

Faskari Umaru Gajabu                       -        1957 – 1959

Faskari Umaru D’andago                   -        1959 – 1990

Faskari Ibrahim Sabongari                 -        1990 – 2000

Faskari Lawal Garba                          -        2000 – 2001

Alhaji Muhammadu Tukur Sa’idu      -        2001 – zuwa yau, (2017)

K’auyukan da ke kewaye da k’asar Faskari  wad’anda suke k’ark’ashinta sun had’a da Faskari, Mai Ruwa, Daudawa, Sheme, ‘Yankara, , Tafoki, Sarkin Fulani, Noma Dakamawa, Shawu, Tudun  Lakai, Unguwar Bakai, Birnin Kogo, Ruwan Godiya, Fankama, D’anbaduka.

2.2 K’abilun K’asar Faskari


Tarihi ya nuna cewa mafi yawan d’aukakar k’abilun k’asar Faskari su ne Kogawa, Lakabawa, da Gobirawa wad’anda su ne suka gudanar da sarauta a wannan yankin na Faskari.

Da farko sarautar ta fara ne daga gidan sarautar Faskari inda aka za’bi Faskari Abu da kuma Kogo Ummaru, a lokacin mulkin Muhammadu Bello na Katsina amma daga baya sun mik’a mulkin ga Kogawa a sakamakon auratayya tsakanin Bare-Bari da Gobirawa.

Hijirar Gobirawa daga Gobir zuwa Faskari wannan wani muhimmin k’arni ne na Gobirawa da ya wuce tun shekaru d’ari (100) a baya a lokacin da Gobirawa su ka zo sai mazauna yankin na asali (maguzawa) ke cewa sunan garin shi ne Faskari.

A dai-dai wannan lokaci ne Magajin D’anboka (Maguzawan kan dutse) wad’anda suka ziyarci garin daga Daura sai suka sami Muhammadu Gid’o suka taimaka masa ta hanyar ciyar dokinsa, sannan suka rok’e shi ya zauna tare da su, a d’an zaman da ya yi, ya yi addu’a da ba da tabbacin zamansu domin gina kyakkyawan wurin zama mai tsaro da tsari, a d’an lokaci kad’an mutane daga sassa daban-daban suka fara tarewa, suka ci gaba da yawaita a k’ark’ashin mulkin Muhammadu Gid’o.

Sannan k’abilun Bare-Bari wad’anda suka yi hijira daga bare-bari zuwa birnin Kogo babban ci gaban yankin Kogo ya fara ne daga Fasawa zuwa birnin Kogo akwai k’auyuka a gefen duwatsu da wadataccen ruwa da kyakkyawar k’asar noma da kuma wajen kiwo mai kyau.

Sannan a hankali Hausawa suka shigo kai tsaye har ma da Fulani a yadda tarihi ya nuna akwai kusan k’abilu bakwai da suka kafa k’asar Faskari sun had’a da Larabawa, Bare-Bari, Gobirawa, Kogawa, Kanuri, Hausawa, Fulani.

2.3 Al’adun K’asar Faskari


Mutane da ke zaune a k’asar Faskari mutane ne masu al’adu iri-iri na ‘bangarorin rayuwa kamar auratayya, zamantakewa, noma, bikin rad’in suna wasanni da dai makamantansu.

Ta ‘bangaren auratayya mutane masu k’ok’arin gaske wajen fito da al’adunsu idan ana bikin domin kuwa idan aka ce makon biki ya tsaya za su yi ta yin taruka na murna a gidansu amarya. ‘Yan mata kan samu d’akin da amarya ta ke su taru yau su yi kitso gobe k’unshi tare da jin kid’a na wak’ok’i daban-daban har ranar da aka d’aura aure. Sannan idan aka kai amarya d’aki to ba a wannan ranar ango zai shiga d’aki ba, sai dai amarya ta kwana da k’awayenta washegari da yamma su tafi sai ango ya shigo d’akinsa a wannan daren.

A ‘bangaren zamantakewa  a tsakaninsu kuwa akwai girmamawa da kyautatawa juna da ziyarar ‘yan uwa musamman a ranar juma’a bayan an sauk’a sallar juma’a sukan ziiyarci ‘yan uwa da abokan arzuka. Sannan idan wani ya faru sukan jajantawa ‘yan uwa idan kuma na murna ne sukan nuna farin ciki ga wanda abin ya sama.

Haka kuma sukan aiwatar da aikin gayya musamman a lokutan damina idan ruwa ya sauk’o hanyoyin ruwa sun cushe ko a samu hanyar wucewa ta ‘balle ko wani aiki na musamman sukan fito da yawa musamman iyaye masu k’arfi da kuma samarin gari domin su yi irin wad’annan ayyukan.

A ‘bangaren noma jama’ar k’asar Faskari suma ba a bar su a baya ba wajen noma hatsi da kayayyakin marmari daban-daban a lokutan damina da rani. A kan samu kowane mai gida yana da gona ta shi wadda a kowane lokacin noma musamman damina zai noma a k’alla abin da zai ishe shi ya ci har ma ya bayar ga ‘yan uwa na waje ko ya sayar da wani kashi a cikin abin da ya noma. Sukan rik’e noma da gaske  ba su wasa da shi idan lokacin ya zo.

A ‘bangaren haihuwa kuwa musamman wurin bikin rad’in suna ko kuma da zarar an yi haihuwa mata za su rik’a zuwa gidan mai jego domin ta ya ta murnar haihuwa da kuma yi mata ‘yan aikace-aikacen da ya dace, kamar d’ora ruwan wanka, dama kunu, da sauransu. Haka kuma sukan yi kwana bakwai suna wannan shige-shigen gidan mai jego  rana ta bakwai ne ake rad’a wa yaro ko yarinya da aka haifa suna. A wannan rana ne mai jego za ta fito ta yi kwalliya mata za su taru a tsakar gida, su yi ta kid’a suna rawa ana murna, mai jego za ta fito ana mata wak’a ta na rawa ana lik’a mata kud’i. Haka za su yi ta yin ire-iren wannan shagali har yamma ta yi kowa ya tafi gidansa. Sannan kusan kowace mata ta kan bawa mai jego kud’i ko sabulu ko riga domin a sakawa yaron da aka haifa. Haka za a rik’a yi wa kusan kowace mace idan ta haihu a wannan yankin.

A ‘bangaren wasanni mutanen  garin Faskari suma ba a bar su a baya wajen rik’o da wasanninsu na gargajiya domin kuwa yara sukan ware wani lokaci ko dai da rana kafin su tafi makaranta ko kuma da dare domin su had’u a wurin wasanni ko dai a dandali ko k’ofar gida wasu lokuta kuma sukan bar unguwarsu, sai kowa ya fito su had’u a unguwa d’aya duk domin su gudanar da wasansu cikin nishad’i da walwala. ‘Yan mata kan ware gurinsu da daban idan da daddare sun fi zama a k’ofar gida ko tsakar gida su kuma yara maza sukan za’bi inda za su had’u a mafi yawancin lokuta. Sukan had’u a filin k’wallo bayan sallar Mangariba a nan ne za su yi ta yin wasanni iri-iri na guje-guje da motsa jiki da kuma raha wani lokacin ana labarun ban dariya. Wannan ya sa kowane lokaci ake neman yaro an san inda za a same shi. Na sami wannan bayani ne daga bakin wani yaro da kuma wata yarinya wato Aliyu da Maryam. Wad’annan yara sun tabbatar min da cewa wad’ansu wasannin suna yin su a kusan kowane lokaci kuma kullum suna fitowa wasa idan lokutan wasan ya yi. Sun kuma fad’amin wasannin sun zama musu jiki domin in ka ga ranar da ba su fito ba to k’ila an yi rasuwa a gidan su d’aya daga cikin abokan wasan ko kuma rashin lafiya ta kama wata cikinsu. Sannan sun fad’i min cewa suna da ire-iren wasanni da suke yi da yawa wad’anda za su bani da yin aiki ingantacce.

2.4 Nad’ewa


Wannan babi na biyu yana da taken: “Tak’aitaccen tarihin Faskari da al’adunsu.” Babin ya kawo tak’aitaccen tarihin k’asar Faskari wanda ya k’unshi kafuwar garin. Sannan an kawo jerin sunayen sarakunan da suka mulki garin tun daga 1811 zuwa yau (2017). Bawan wannan, babin ya yi tsokaci game da k’abilun k’asar Faskari, da kuma al’adun k’asar Faskari. Daga k’arshe kuma sai aka kammala babin da nad’ewa.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/