https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

NA


ANAS MUSTAPHA


 


KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

BABI NA ‘DAYA


                                       GABATARWA


1.0 Shimfid’a


Wannan bincike mai take “Wasannin Yara a Yankin Faskari Jiya da Yau” ya mayar da hankali ne a kan fito da wasanni da yara ke gudanarwa a yankin faskari.

A kowace al’umma ta duniya yara nada wasu halaye wad’anda suke gudanarwa a cikin al’ummar nan da suka tashi a ciki. Hakan na iya faruwa ne tun farkon rayuwarsu. D’an adam tun yana k’arami ya kan yi amfani da ga’b’ban jikinsa ya aiwatar da wasu halaye na rayuwa.

Wasanni na d’aya daga cikin abin da d’an adam kan fara aikatawa ta yin amfani da ga’b’ban jikinsa. Don haka ake ganin cewa ba a kula da wasannin yara da ake yi ba a nan yankin Faskari. Shi ya sa na yi tunani a raina na cewa ya kamata in rubuta wani abu akan wasan yara da ake gudanarwa a garin Faskari.

Na kasa wannan aiki har zuwa gida biyar kamar haka: a babi na farko zan yi Magana akan gabatarwa, babi na biyu zan yi Magana a kan tarihin wurin bincike, a babi na uku kuwa za a yi bayani a kan ire-iren wasannin yara maza, a babi na hud’u za a yi bayani a kan yadda yara mata ke shirya wasanninsu tare da kawo ire-iren wasannin, babi na biyar shi ne zai zo k’arshen wannan aikin gaba d’aya wato kammalawa da kuma manazarta.

1.2 Manufar Bincike


Kasancewar kowane irin lamari yana da irin tasa manufar da yake son ya cimma, haka ma wannan binciken, manufarsa shi ne fito da wasannin yara a cikin al’ummar yankin Faskari tare da nunawa ‘yan kallo ko bak’in haure irin rawar da yaran wannan yanki ke takawa ta fuskar wasanni da motsa jiki da suke gudanarwa yau da kullum.

Bugu da k’ari wannan binciken za a yi k’ok’arin nuna yadda yara ke shirya wasanninsu da kuma ire-iren wasannin da kuma yadda wasannin suka kasu zuwa na jinsi biyu wato maza da mata.

1.3 Dalilin Bincike


Babu shakka “Kowace k’warya da abokiyarta” don haka, wannan binciken yana tattare da dalilai k’warara da suka bani zummar gudanar da shi. Na farko akwai k’arancin bincike dangane da wannan binciken na wasan yara a yankin Faskari. Na biyu kuwa shi ne domin kar a bar baya da k’ura domin mafi yawancin wasu wasannin sun fara ‘bacewa a wasu layuka na yankin Faskari. Na uku kuwa domin fitowa da yadda ake gudanar da wasannin tare da ware na maza da na mata yadda za a fahimci yadda suke ko da kuwa an yi watsi dasu nan gaba.

Wannan dalilan suna d’aya daga cikin dalilan wannan aiki nawa. Amma akwai wasu dalilan da za a cimmawa idan an karanta wanna k’undin.

1.4 Farfajiyar Bincike


Wannan bincike ya tak’aita ne a kan wasannin yara a yankin Faskari. Ma’ana yadda yara ke taruwa su shirya su kuma gudanar da wasanninsu.

Wannan bincike zai yi k’ok’arin bin lungu da sak’o na wannan yanki da wannan binciken ya ta’allak’a a kan sa, domin zak’ulo da wasannin yara maza da na mata da ake gudanarwa a wannan yanki na k’asar Faskari.

1.5 Bitar Ayyukan da suka Gabata


Ya zama wajibi ga kowane irin bincike a dubi nazarce-nazarcen da a ka yi a fagen bincike domin ganin abin da aka yi ko dai a d’ora a kai ko kuma a dubi wani ‘bangare ko kuma kafi hujja da rashin samuwar wannan ‘bangare don samar da mafita a wannan binciken.

Saboda haka, wannan nazarin shi ma ba zai kaucewa wad’annan k’a’ida ba, saboda haka a nan za a mayar da hankali ga duba ayyukan da suka gabata a irin wannan aikin da kuma wad’anda suke da dangantaka da wannan aikin. Daga cikin ayyukan dana nazarta akwai wad’anda suka shafi wasannin yara a garuruwa daban-daban cikin k’asar Hausa da kuma wad’anda suka shafi wasannin manya maza da wasannin manya mata da kuma wad’anda suka shafi wasannin gargajiya da aka gudanar.

Akwai kuma wad’anda ake cin karo da su a kan wasantakai da wasan kalankuwa da wasan maguzawa a k’asar Katsina da kuma wasannin yara a k’aramar hukumar matazu. Dan haka za a mayar da k’arfi ga duban ayyukan da suka gabaci wannan aiki.

Yalwa (1977) ya rubuta k’undinsa mai taken wasannin yara don neman digirinsa na farko a Jami’ar Bayero ta Kano. Wannan k’undi ya mayar da hankali ne a kan wasannin yara gaba d’aya ba tare da rarrabesu ba.

Sama’ila (1982) ya rubuta k’undinsa na neman Digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato wanda ya yi ma lak’abi da “Wak’ok’i da Wasannin Yara a Sakkwato ya yi bayani kan ire-iren wasan yara da lokutan yin su da amfaninsu.

Ya’u (1984) Shi kuma wannan ya rubuta k’undinsa na neman digirin farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato a kan wasan tashe a cikin Azare.

Shi kuma Yusuf (1988) ya rubuta k’undinsa na farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato a kan wasannin Maguzawa a k’asar Katsina. Shi ma wannan mai binciken, ya yi bincikensa ne kawai a kan wasannin da Maguzawa ke yi.

Bunza Koko (1988) Wad’annan manzarta sun rubuta k’undinsu mai taken Wasannin Yara a K’asar Gwandu a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato, su wad’annan manazarta sun kawo yadda wasannin yara maza da kuma mata (Garin Gwandu).

Abdulk’adir (1989) ya rubuta k’undin digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya mai taken wasannin yara na wasan kwaikwayo. Shi wannan k’undi ya rubuta shi a kan wasan da yara kan yi a gurin tashe wanda a kan yi idan azimi ya kai goma.

Mustafa (1998) ya rubuta k’undin neman digirinsa na farko a kan wasan kalankuwar zamani a k’asar Safana ta jahar Katsina. Shi wannan mai binciken ya rubuta wannan k’undi nasa ne domin neman digirin farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato ya rubuta wannan k’undin ne a kan yadda wasa yake da kuma yadda ake gudanar da wasan kalankuwa a yankin Safana.

Umar (2002) ya rubuta k’undinsa mai taken wasannin gargajiya na yara a da a Sakkwato don neman kundin digiri na farko a Jami’ar Usman ‘DANFODIYO Sakkwato, wannan k’undin ya mayar da hankali ne a kan tsoffin wasannin yara, domin bai kawo wasu sabbin wasanni ba, domin a wurin ba su ne ya mayar da hankali ba.

Shi ma Umaru (2004) ya rubuta k’undinsa na neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato inda shi ma ya yi wa k’undinsa lak’abi da “ Wasannin Yara a K’aramar Hukumar Matazu”. A cikin k’undin nasa ya kawo wasanni a k’asar Hausa da rabe-raben wasanni da ire-iren wasannin yara tare da muhimmancinsu, amfaninsu da lokutan yin su.

M.U Balarabe (2009) Ya rubuta littafi a kan wasannin Tashe. A northern Nigeria Publishing Company Limited. Gaskiya Building P.O Bod’ 412 Zariya. Ya yi bayani a kan wasannin Tashe da ake yi.

Gusau S.M (2013) ya rubuta littafi mai taken wasanni don yara, a century research and publishing company Kano. Ya yi bayani a kan wasannin yara da rabe-rabensu da ma’ana da kuma wurin yinsu.

1.6 Hanyoyin Gudanar da Binccike


Hanyoyin da za su taimaka wajen gudanar da bincike na su na da d’an yawa. Saboda haka don cimma nasarar samun bayanai da suka taimaka na samun nasara wajibi a bi wad’annan hanyoyi domin tattaro bayanai.

Nemo wasu littafai da kuma kundayen da ake rubutawa a kan wasannin yara ko wad’anda suka yi bayani a kan wasannin gargajiya.

Dangane da wurare da ake samun wad’annan littattafai kuwa su ne d’akunan ajiye littattafai da kuma shagunan sayar da littattafai.

Wannan bincike zai yi amfani da k’undayen da aka rubuta wad’anda suka shafi wasan yara saboda haka za a nemo su duk inda aka ji wani ya rubuta k’undi a kan wasannin yara.

Bugu da k’ari, na tafi na yi tattaki har dandali domin yin hira da yara a wuraren da suke aiwatar da wad’annan wasanni, kuma na tafi wurin ‘yan mata domin yin hira da su a kan yadda suke aiwatar da nasu wasan.

Haka za a yi tattaki domin tafiya wurin Hakimin Faskari domin yin hira das hi dangane da tarihin garin Faskari da al’adunsu. Haka za a ziyarci wad’ansu k’auyuka da lunguna na k’asar Faskari kamar Sabon Layi, Magora, ‘Yar Malamai da kumaa k’auyen Mai Ruwa domin samun yadda suke aiwatar da wasanninsu.

1.7 Nad’ewa


Wannan babi na farko mai taken “Gabatarwa” ya kasance shimfid’a ne ga wannan aiki. Babin ya kawo manufar bincike wanda ya had’a da fito da wasannin yara fili, tare da ware na maza daban haka ma na mata daban. Bayan haka, babin ya kawo dalilin bincike, wanda d’aya daga cikin dalilen shi ne kasancewar ba a gudanar da wani bincike ba dangane da wasannin yara a yankin Faskari. Sannan aikin ya kawo farfajiyar bincike, wadda ta kasance yankin k’asar Faskari. Bayan haka, babin da farko ya zo da bitar ayyukan da suka gabata, inda aka yi bitar ayyukan masana da manazarta masu dangantaka da wannan bincike. Sannan aikin ya kawo hanyoyin gudanar da bincike, wato hanyoyin da za a bi domin tattaro bayanai masu inganci. Daga k’arshe sai aka kammala babin da nad’ewa.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/