Ticker

6/recent/ticker-posts

Tuna Baya: Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com

  1. Na kira Haliku mai jink’aina,
Sarkin nan da ka jin kukana,

Ban da waninKa dad’i Sarkina,

Don na dubi tulin kayana,

Karfin imu su bai kawo ba.

 

  1. Don haka nay yi yabon gaggawa,


Gun Manzonka maceci kowa,

‘Dan Abdalla sarakin baiwa,

Mai aiken ka mak’agi kowa,

Bai ta’ba kunyata mai tuba ba.

 

  1. Na yi yabo ga gwarajen fama,


Su Ashabu mazajen girma,

Duk wada kay yi suna mara ma,

Domin Rabbu yake shirya ma,

Ba ka fad’in abu ba daidai ba.

 

  1. Albishirinka abokin hira,


Sak’o za ni fad’i rarara,

In na rage ku cika min saura,

Rok’ona a dad’a min gyara,

‘Dan koyo nike ba goga ba.

 

  1. Ni mutuwa Ali na ban haushi,


Ba ta bugu ta tsaya lallashi,

Ga gawa aje ba numfashi,

Can kabari kuma ba d’an taushi,

Kwak kwanta ciki bai taso ba.

 

  1. Yau hikima aji zancen Hausa,


Bunza Kitari abin yai nisa,

Sun tafi babu mad’auki fansa,

Yau mu an ka bari 'yan kusa,

Masu fad’i a ji bai daidai ba.

 

 

  1. Farkon mai hikima Jank’osai,


Mai hikimar magana rwai-rwai-rwai,

In ya fara bugun turunai,

Bunza ciri taka yi garkanai,

Wa ka bari a yi bai zo nan ba?

  1. In dotti’be suna hiratai,


Yara ka d’ora fad’in: "Sai mun tai",

Wa ka bari a fad’a mai kwantai?

Kowa yaj ji batun Jank’osai,

Ya san bai ji batun banza ba.

 

  1. Dauri Dabera idan an hauro,


‘Dan su Talatu matashi K’aro,

Ya hana hira na koran sauro,

In ya taushe duma yak koro,

Sai namijin tsaye ba mata ba.

 

  1. In yat taushe duma kyankyandi,


Kuryar Dogo tana ringindi!

'Yan kar’bi su rik’e mai gindi,

"Gara da kaz zaka baban Idi,

Dajin namu da zabbi gumbi".

 

  1. Kun ji gwani masani kalmomi,


Masu fad’in magana zag galmi,

Ka ce nagge ka cin karmami,

In an fara kare dalmomi,

Mamman at tsaka ba k’ege ba.

 

 

 

 

 

  1. Mamman ku ka kid’in 'yan tauri,


Ga shi gajere fari zak kauri,

In yad dahe duma tai tsauri,

K’aro dole shi ke kakari,

Ba shi bari a yi bai je can ba.

 

  1. Mamrnan bai maganar k’arya ba,


Can ga batunsa da nay yo duba,

Ba zarbulle rage min k’aba,

"Ba wayo aka wa yuk’a ba,

Ba ta da ban magana sai tauri".

 

  1. Mamman kaico! A yau an haura,


Labbon Goggo Dawa ya k’aura,

Shi da su Amadu Mai'yarkura,

Manuga masu dawa ko saura,

Za mu ishe musu ba k’arya ba.

 

  1. Kaico na yi tunin ‘Dannani!


Ga Tsagwaro, Kwadaro, ‘Dansani,

Modu da Gago, Kada, har Mani,

Mai kifi kake baban Sani,

Kun ji mazan sababi ran gaba.

 

  1. Yau kuma babu tafashen noma,


Babu maza ma' abota homa,

Yanzu Ramaji kid’i ya suma,

Baba Naja’b’bi Mazajen fama,

Gero ya yi tumu sai girba.

 

  1. Ku ka ‘bari da tafashe gona,


Mai k’wazo ku d’aga mai suna,

Raggo bai aje geron tauna,

Ba shi miya da zawai sai tana,

Bai ta’ba d’ebe takaicinai ba.

 

 

 

 

  1. In sun fid da kidi har Gardi,


Bunza ta d’ungurna Gulbin Zandi,

Manun Tuu da lage har Gindi,

Baban Sarki ma ci kurmundi,

Wa ka shiga ruwa bai aiko ba?

 

  1. Yanzu mu dubi kalangu dambe,


Dogo ka rabka kid’in 'yan dambe,

Ga su Alun Tuni sarkin dambe,

Bunza da ku taka kurin dambe,

Gwalya'i yanzu idanu k’aba.

 

  1. Shi tittirga a yau dai ya kau,


Sarkin Fawa mazaje sun kau,

Wasan sa da k’aho in an hau,

Turun Dogo shina: "Kau-kau-kau!"

Sa ya kai k’asa bai taso ba.

 

  1. Sarkin Fawa mazajen daga,


K’igama ka wuce tsoron rugga,

In sa yak’ k’i zuwa yai tunga,

Yaggwai za ku saka sai zarga,

Kai tsaye, shi tsaye, bai taso ba.

 

  1. Haukan sa shi tsaya can garka,


In kun ce, shi tsaya yar rabka,

Wad’d’are yanzu a kawo yuk’a,

Shi ya kai adadi sai yanka,

Nagge ka d’aura fad’in: "Na tuba".

 

 

 

 

 

  1. Ga makasan magana na kawo,


Turkena na shiri nad dawo,

Ga kogin hikirna na shawo,

Kawu Balarabe in an jawo,

Gumbe su aka ji har Karnba.

 

  1. Dole Bala mu tsaya ma hira,


Ba mu barin haka ko ka k’aura,

Don mu mun ka ci 'ya 'yan taura,

Kan hikimarka Bala mun tsira,

Mun yi tuwo ciki ba k’arya ba.

 

  1. Gumbenai muka ce ma gata,


Domin ba shi kid’in 'yan mata,

Ba shi rawa Bala balle ritta,

Kan hikimar magana ko Shata,

Yaj ji Balarabe bai rammai ba.

 

  1. Dambenai da Gumel hiratai,


Yab buga kawu shina kallonai,

Ran da Balarabe yal luro mai,

Yas sa hauni guda tab bi sai,

An ka yi rinkiti’bis sai duba.

 

  1. ‘Dan Argungu zubewa yay yi,


Ga shi a ‘bingire suma yay yi,

An yi hana ka, kana sai ka yi,

Yau Digi ta ga iyakag Gayi,

Barzahu an ka yi ba a shiryo ba.

 

  1. In Bala yay yi shirin kalmomi,


Sauri-da-sauri shikan yo komi,

Tamkar yara suna lomomi,

Babu kure ciki balle tsami,

Mun duk’a maka ba wargi ba.

 

 

 

 

  1. Jink’an Jalla nake rok’a ma,


Dangana Rabbu shina kama ma,

Mun san Hausa a yau ta suma,

An rasa masu rik’a ma fama,

Ga mu zuwa Bala bai sauri ba.

 

  1. Kun ji mutum da tsayi dai-dai shi,


Ba gantsarwa bale tarkoshi,

Dole yabon Bala mai k’issoshi,

Dole kiranka mawak’in taushi,

Ba ka fad’in abu bai faro ba.

 

  1. Na tuna Walga mawak’in gad’a,


Mai tashe da kid’i rad’ad’a,

Dole ruwa su ji motsin mod’a,

Bunza Kitari uwaye had’ d’a,

Walga guda shike ba ‘boyo ba.

 

  1. Ga baki sake tamkar wawa,


Sai in ka ta’bi bakin garwa,

Za ka ji tasku cikin gaggawa,

Rannan kai ka zamowa wawa,

Ka hau maik’ari ba daidai ba.

 

  1. Yai wak’ar fadama mai dad’i,


Don in ta yi ruwa zad dad’i,

In kuma ta k’i ruwa sai laud’i,

Don halin fadama 'yar gard’i,

Ba dahir ga manoma can ba.

 

 

 

 

 

  1. Maisule shi ka rik’a mai kaya,


Ba su fad’i ka ji ta zan gaya,

Fafau ba su gaya ma k’arya,

Tun da Na' alla shina d’an kaya,

Ga ‘Dangwallo matashin duba.

 

  1. ‘Dangishiri ka bugun turunai,


Ko Gama ya yi tafashe daidai,

Maisule shi ka shiri in an tai,

Walga shi d’ora kiran sunanai,

Ba su shirin batu ba daidai ba.

 

  1. Tashe babu kamar ‘Dansani,


Ga hikimar batu ga tsentseni,

Ga magana sake tamkar rani,

'Yan kar’bi su rik’a zag gauni,

Ba su fad’i d’aya bai kawo ba.

 

  1. Borin goj e shikai hiratai,


Shi da wuta shika yin warginai,

'Yan gado ka tsayi hilinai,

Kowat taki wuta baminai,

Shi ka famn"Miyoni na tuba".

 

  1. Sai ‘Dankaka mazajen fama,


'Yan asali ga tama 'yan girma,

Bela dole take duk’a ma,

Gaushi ko shi suk’e sai suma,

Alk’awalinku shike sheda ma.

 

  1. Ga k’arfe da wuta an d’auko,


Yai jajir wa kwatancin kasko,

Sai ‘Dansani shi d’an tattako,

Kakale shi ka hayewan narko,

Bai ta’ba fargaba don zafi ba.

 

 

 

 

  1. Sai ‘Dansani shi d’au torok’o,


Ba hulla bisa kai sai sank’o,

Ya dahe katara ya shek’o,

'Yan kar’binsa su d’an dudduk’o,

Kakale bai yi kuren girma ba.

 

  1. Tammat kun ji irin hirata,


Waiwaya baya kawai manufata,

Manya sun tafi sun bar rata,

Mai nazarin adabi makaranta,

Ya san ban yi batun banza ba.

 

  1. Rok’on Jalla nikai Sarkina,


In na kai adadin kwanana,

Ban nasarar kalima bakina,

In yi gamo da katar k’arshena,

Wa zai min haka, ba Kai d’ai ba.

 

  1. Kun ji karinta arowa nay yi,


Wak’ar Audu da Sani yay yi,

Ga gindinta dad’awa nay yi,

"Gara da kaz zaka baban ldi,

Daji'n namu da zabbi gumbi”.

 

Post a Comment

0 Comments