Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’aziyyar Muhammadu Hambali Jinju Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com

  1. Bisimil ilaahi Ubangiji rok’ona,
Bayan salati ga Mustafa Manzona,

Babban muradi Rabbana kukana,

Ka san shi ba sai na yi rwa-rwa-rwa ba.

 

  1. Zancen hawaye ban hana zuba ba,


Rai yai bak’i fuska ba za ta fari ba,

Tausai ya dabirta ni ban ahumo ba,

Na zuban hawaye ba da shiryawa ba.

 

  1. Rabuwa da Hambali Jinju manyan fama,


Gogan da yas san hauni ya san dama,

Masani iyayen tsangayar alfarma,

Da baje karatu ba zaman tsince ba.

 

  1. Dogo tsayayye na kama da kwaranga,


Aukin jikinsa zubi irin na katanga,

Da ganin Muhammadu an ga manyan daga,

Ba ranke-ranke irin na renawa ba.

 

  1. Suturar jikinsa, gwanin k’awa k’i fansa,


Babban zubi riga asaken Hausa,

Kun san gudajin goro ya d’ara farsa,

Bai yarda boko ya yi mai cuta ba.

 

  1. Manyan mazajen Hausa tashin farko,


Suka assasa mata tubali mai k’arko,

In babu goshi dole kai shi yi sank’o,

Komai adon mai shi ba zai ma’ana ba.

 

 

 

  1. In ba uba a gida musiba ta yi,


Tamkar ya iccen an cire sauyoyi,

Mota idan ta kasance ba tayoyi,

Fasinja bai ga wurin shiga da fita ba.

 

  1. Kurin d’iya na ubansu ne ba su ba,


In ba uba doro ba zai taso ba,

Shege ba zai ga wuri na yin d’anga ba,

Domin sanin asalinsa ba na k’warai ba.

 

  1. Yaro ga manya zai la’be ya yi kuri,


Yau Hausa ta rasa ginshik’i mai kauri,

Ta d’auro himma an rage mata sauri,

Ta yada zango ba da shiryawa ba.

 

  1. Mun d’au hukunci Rabbana mai girma,


Taronmu yau rok’o muke alfarma,

Jink’ai kaza rahamarKa ya mai girma,

Su ishe Muhammadu Jinju ba da nawa ba.

 

  1. Allah Ka yafe kurakuransa gaba d’ai,


Ka yi mai gamo da katar ga al’amarinai,

A tsayin hisabi Rabbu sasauta mai,

Ya haye sirad’i ba da ya ahumo ba.

 

  1. Allah kushewatai ka yalwanta ta,


Fitinar cikin kabari ka sasanta ta,

Rok’onmu Ya Gaffaru kai masa gata,

Ka saba yi ko ba da rok’awa ba.

 

  1. Fatarmu ba sai an yi ja-in-ja ba,


Ba mu tsarkake bawanKa kan komai ba,

Ba ka saba k’yaccewa ga mai rok’o ba,

RahamarKa ba bawan da bai shaida ba.

 

  1. ‘Danjinju ya zama ginshik’in ‘yan Hausa,


Shi ne Magayak’in karatun Hausa,

Masanin da babu kamarsa fad’in Hausa,

Maganar ga ba washin kirari ce ba.

  1. Baharun muhiid’un ne fagen Larabci,


Injiniya ne can fagen Turanci,

A Faransi an ce ba kamar sa azanci,

Jamhuriyar Nijar ta ce ba mu ba.

 

  1. Babban fasiihi na fagen Rashanci,


Modibbo ne a cikin Lugar Girkanci,

Lahaja ta Sakkwato ga Kano Katsinanci,

Ba mu san gwanin da ya kai shi burgewa ba.

 

  1. Rasha ya kammala binciken kundinai,


Yaz zo a Ikko ya zazzage kayanai,

Birnin Kano ya zube dukan k’wazonai,

Zazzau da Sakkwato bai zaman wasa ba.

 

  1. Yau Jami’o’i ba guda tamkatai,


Gun shekaru an ce ina warinai?

Duk shehunan sunansu d’alibbai nai,

Ribar karatu ba ta jari ce ba.

 

  1. Mai tsara marsiya Alu sunanai,


‘Dan Bunza birnin Gagga kun ji garinai,

Inta da Lafau kun ji kakanninai,

Allah Ya gafarce su ba da gumi ba.

 

 

               

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments