Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’aziyyar Sarkin Bunza Alhaji Muhammadu Bande Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com


  1. Bismillahi Rabbana zan farawa


Ta’aziyyar da zan yi kan Alhaji Bande.

 

  1. Wanga rashi a Bunza ba k’arami ne ba,


Kan rabuwarmu mu da kai Alhaji Bande.

 

  1. Ba mu manta ba wanga ikon Allah ne,


Ba mai tunkud’e shi kan Alhaji Bande.

 

  1. Tilas hak’uri gare mu farilla ne,


Babban tasiri rashin Alhaji Bande.

 

  1. Sarki kamili tsayayye managarci,


Mai zatin sarakuna Alhaji Bande.

 

  1. Ga babban jiki da ruhin malammai,


Ga sanyin hali wurin Alhaji Bande.

 

  1. Ga kuma hank’uri garai ga k’yalewa,


Bai rigima da gardama Alhaji Bande,

 

  1. Shi yag gaji Abdu Baban Albora,


Wan su Haliru d’an’uwan Alhaji Bande.

 

  1. Abdu mazan kwaran ina muka manta ka,


Ka rik’i Bunza tun gaban Alhaji Bande.

 

  1. Sarkin Bunza Bande Rabbu ya saka ma,


Babu irinka Bunza yau Alhaji Bande.

 

  1. Jama’ar Bunza ‘yan gida duka har bak’i,


Sun yi bak’in cikin rashin Alhaji Bande.

 

 

 

 

Halayensa

  1. Alhaji Bande duk talakka yana son ka.


Domin ba ka tsangwama Alhaji Bande

 

  1. Ba ka kwad’en abin mutum ko shi waye


‘Kaiwa ba a kai gidan Alhaji Bande

 

  1. Bai  ta’ba gardamar turara husuma ba,


Ba a fad’a a fada don Alhaji Bande.

 

  1. Ba ya zolaya da muzanta talakka,


Ba ya cin ido dad’ai Alhaji Bande.

 

  1. Masu fad’in mutum shuru duka mugu ne,


Ni na k’aryata su kan Alhaji Bande.

 

  1. Tambayi dukkanin Babunje ya gaya ma


In ya kwan bak’in cikin Alhaji Bande.

 

  1. Ba d’aya wanda zai gaya ma ya cutai


Bai saba ba ko dad’ai Alhaji Bande.

 

  1. Tambayi hakiman garin Bunza dukansu,


Wa yak kwan cikin hushin Alhaji Bande?

 

  1. Masu jiran gadon garin Bunza dukansu,


Wat ta’ba sa-mu –sa da Sarki Haji Bande?

 

  1. Tajirran gari da naj ji bayaninsu,


Bai rok’o bale kwad’ai Alhaji Bande.

 

  1. Mallamai ka ce da shi Gabarabadau,


Bai rok’o bale kwad’ai Alhaji Bande.

 

  1. Bokaye matsafata kaico kanku,


Ga mak’iyyanku nan zuwa Alhaji Bande.

 

  1. To ‘yan jita-jita jifa bisa kanku,


Babu wurin zama gidan Alhaji Bande.

 

  1. Masu gamin fad’a wa juna ku tsaya can,


Babu wurin tsayi a fadar Haji Banza

 

  1. To ‘yan fankama, d’iyan mu ne manya,


Can ku ci kanku in ji Sarki Haji Bande.

 

  1. ‘Yan son handama ‘barayimmu na zaune,


Kunya za ku yi wurin Alhaji Bande.

 

  1. Masu ojoro danne hak’k’i na talakka,


Ga makashinku nan zuwa Alhaji Bande.

 

  1. Bai kar’ban shiri na ‘bata da cutarwa


Ko gun d’an cikinsa ne Alhaji Bande.

 

  1. Ko an so a sa shi Sarki bai yarda


Ni ne shahidi a kan Alhaji Bande.

 

  1. Ka yi kad’an ka tura Sarki shi yi ‘banna,


Mugan tanadinka bai cin Haji Bande.

 

  1. Ko an k’i ka Bande tilas a yaba ma,


Ba don ka mace ba ne Alhaji Bande.

 

Fada da Mutanenta:

 

  1. Wasan dambe kokuwa bai dubawa,


K’atoo bai rawa gidan Alhaji Bande.

 

  1. Fadawan ga masu ‘banna da izawa.


Yau ba ko guda gidan Alhaji Bande.

 

 

  1. Masu zama a fada sauraren maula,


Ya watse mayaudara Alhaji Bande.

 

  1. Masu fad’an a ba mu sarki yas samu,


Duka ya sa su jan ido ido Alhaji Bande.

 

  1. Ba ya shiri da fasik’i ko d’an wane,


Kuma bai son mazambaci Alhaji Bande.

 

  1. Rabbu shi kankare zunubanka dukansu,


Yai maka gafara da mu duka Haji Bande.

 

  1. Saurare mu zo za mu yau ko gobe,


Za mu had’e da kai hak’ik’an Haji Bande.

 

  1. Matuk’ar ‘Dan’adam halinsa ka iske shi,


Kai Kan ka yi arziki Alhaji Bande.

 

  1. Ban ce bad’ini ba don shi gaibi ne,


Ba ka da gacce zahiri Alhaji Bande.

 

Masu Fata:

 

  1. Ma su jiran gado ku hank’ura tun yanzu


Ba mai hank’uri irin Alhaji Bande.

 

  1. Wa zai kau da kai idan ya ishe ‘baka?


Wa ka kwatanta gaskiya tamakar Bande?

 

  1. Wa zai hau ya daina d’anga ta sarakai?


Ya fito babu tak’ama tamkar Bande?

 

  1. Wa zai hau ya bar talakka ga walawa?


Ba shari’u na gonaki tamkar Bande?

  1. Yau kud’d’i na jangali wa ka barin su?


Bai yi na cefane ba, sai Alhaji Bande.

 

  1. Ban ce fankama da babban taggo ba


Don fad’in gaba a ce an wuce Bande.

 

Magabatan Alhaji Bande

 

  1. In dai hankali ake so tsurarsa,


Hatta Gagga bai wuce Sarki Bande,

 

  1. Mulkin hankali da ba fitina gunsa,


Mamman Yaud’i bai wuce Sarki Bande,

 

  1. Mulki ba ke-ce-na-ce babu fitinnu,


Hammada d’ai ake misali gun bande.

 

  1. Kau da ido ga duniya da gudanar ta,


Malam Siddi bai wuce Sarki Bande.

 

  1. Mulki mai tsawo da ba fitina Bunza,


Sarki Saini bai wuce Sarki Bande.

 

  1. Mamman d’an Husaini yai sarki Bunza,


Bai ruhi da hank’urin Sarki bande

 

  1. Malam Idda mun ji yai Sarkin Bunza


An shaidai da hankali bai wuce Bande

 

  1. Halirun Saini ya yi suna nan Dandi,


An ce bai da hank’urin Sarki Bande.

 

  1. Umaru d’ansa yai sarauta nan Bunza


Adalcinsa ko kad’an bai kai Bande.

 

  1. Sarki Abdu an na goma rik’on Bunza


Kyauta ag ga Abdu, sanyi sai Bande.

 

 

Salon Mulki

 

  1. An yi mulki a bar talakka da walawa,


Ko sarki Yahya bai furce Bande

 

  1. K’yale talaka ba a son komai gunsa,


Sarkin kalgo ak kinin Sarki Bande.

 

  1. Bunza mu d’auki hank’uri Allah na nan,


Mun yi rashin uban k’asa Alhaji Bande.

 

  1. Kowah hau gadon ga sai dai shi kwatanta,


Bai kai Abdu, bai wuce Alhaji Bande.

 

  1. Ban ga mutum da bai da mugun niyya ba,


Ko gun ‘yan’ubansa sai Alhaji Bande.

 

  1. Nan dai Buza hakimai babu irinsa,


Kai duk Gwandu hank’uri waw wuce Bande,

 

  1. Ba sarki kamarsa yau Gwandu dukanta,


Wanda ake hawa ya k’yale sai Bande.

 

Shaidun Jama’a

 

  1. “Bai ta’ba tak’amar gwajin sarki ne ba”,


Halirun Inta kun ji shaidunsa ga Bande.

 

  1. “Sarki ba ruwansa don bai cutarwa”


Dangishirin kid’i ka sharhi kan Bande.

 

  1. “Ko yaron gidansa bai ta’ba duka ba”,


Alhaji Sambo shi ya shaidai haka Bande.

 

  1. “Gwarzon hank’uri rashinka hasara ne”


Zancen Tanko ne mak’wabcin Haji Bande.

 

  1. “Ba ka zamba, babu wanda ka tura ka”


Sharhin Ali ne ga juyayin Bande

 

  1. “Ma’u ruwa da hankali kuka aikinku”


Haka dotti’be ke ta juyayin Bande.

 

  1. “Manyan sa ido gwani gun yafewa”


Haka dotti’be ke ta juyayin Bande.

 

  1. “Bai ta’ba hargitsi saboda sarauta ba”


Haka duka ‘yan’uba ka juyayin Bande.

 

  1. “Bai ta’ba k’untata macce da daginta”


In ji Sa’adatunmu mata tai Bande.

 

  1. “Mu yi rashin uban k’asa nan k’arninmu”


‘Yan bokonmu ke fad’an haka kan Bande.

 

  1. “Bai da abin da za mu suka datsammu”,


‘Yan shagon kara wajen iccen Monde.

 

  1. “Anya! Bunza yau akwai tamkar Bande?”


In ji Najabbi sahibin Sarki Bande.

 

  1. Ba mu barin gidansa sai dai mutuwarmu,


Haka ‘Dangwaggo ke ta juyayin Bande.

 

  1. ‘Dandare-Bankada ya ce, sai dai tamka,


Namijin hank’uri irin Alhaji Bande.

 

  1. Na ji k’anensa ‘Dantalata yana zance,


“Dattijon gayinga babu kamar Bande”.

 

 

 

 

Jana’iza:

  1. Alhaji Bawa d’a ga Abdallah mazaje,


Mun had’u gun jana’izar Alhaji Bande.

 

  1. Bello Aliyu Bunza yak kwana a rannan,


Juyayin ubansu Sarki Haji Bande.

 

  1. Na ga bak’in gani ina tsaye da idona,


San da ake ginan kushewar Haji Bande.

 

  1. Liman Hali na gina ga mu a tarshe,


Ga gawar uban k’asa Alhaji Bande.

 

  1. An d’auko shi za a sa shi ga raminsa,


Nan naj juya baya don tausan Bande.

 

  1. Ga jama’a turu-turu babu kuzari,


Kuka dai akai rashin Alhaji Bande.

 

  1. In waiga a baya ga d’ansa a zaune,


Ya rikice rashin uba Alhaji Bande.

 

  1. Ga sauran d’iya da jikoki tarshe,


Fuskoki suna ji’bi na rashin Bande.

 

  1. Ran Lahadin da ransa yai halin bak’i,


Ba mai k’yarga d’an mutum kofar Bande.

 

Ta’aziya:

  1. Ta’aziya maza da mata ka tahowa,


Safe da rana har dare k’ofar Bande.

 

  1. Manyan malamai sarakai tajirrai,


Sun fi dubu zuwa ga juyayin Bande.

  1. Duk ‘yan kasuwa samari da matasa,


Sun yi sahu sahu ga juyayin Bande.

 

  1. Ban ji talakka wanda yac ce uffan ba,


Ko kalma guda a kan sukan Bande.

 

  1. Sarkin Fawa Sani Rabbi shi gafarta,


Ka yi rashin uban k’asa Alhaji Bande.

 

  1. Altine Mairuwa ka kar’bi nasihata,


Ban da sake da addu’a domin Bande.

 

  1. Sarkin Daji kar ka yarda ka manta shi,


Rok’i Tabara gafara gun Haji Bande.

 

  1. To Sarkin Mak’era yau ta hau kanka,


Rok’on gafara wajen Alhaji Bande.

 

  1. Noma ina taya ka babban juyayi,


Na hasarar uban k’asa Alhaji Bande.

 

  1. To, Sarkin Tasha, Tabara Ya gafarta,


Duk laifin da aw wajen Alhaji Bande.

 

  1. Malamman gari salamu alaikunku,


Juyayi nike rashin Alhaji Bande.

 

Gudummuwar Marigayi Alhaji Bande:

 

  1. Dubi garimmu yau ka lura da tsarinsa,


Ci gaba bai k’id’ayuwa mulkin Bande.

 

  1. Hanyoyin cikin gari an gyara su,


Hak kwalta a zamanin Sarki Bande.

 

  1. Makarantun firamare an gyara su,


Sun zama ukku zamanin Sarki Bande.

 

 

  1. Da asibitti ‘yar guda ce duka Bunza,


Sun zama ukku zamanin Sarki Bande.

 

  1. Bunza tasharmu da cikin d’an zaure ce,


Yau mota dubu su zo ba mu da sanke.

 

  1. Tanko tasha da kansa zai zamto shaidu,


Bunk’asar tasharmu zamanin Bande.

 

  1. Nura da kasuwarmu yau babu irinta,


Duk a cikin rik’onsa ne Alhaji Bande.

 

  1. Ga manyan ma’aikatu ga aiki nan,


Babu zaman kashin tufa yau Harande.

 

  1. Mun amfana mun wadata a mulkinsa,


Da kud’i had da dukiya mulkin Bande.

 

  1. Ga attajirai matasa sun k’aru,


Alhazzai da dukiya mulkin Bande.

 

  1. Kowace unguwa da ginan Turawa,


Na siminti da zamani mulkin Bande.

  1. Da boko a Bunza ‘yan tsito ka yin sa,


Yau digiri a bargaja mulkin Bande.

 

  1. Hatta kotu da guda d’ai ce Bunza,


Suka zama ukku zamanin mulkin Bande.

 

  1. Can ga miyammu dauri kifi ne d’anye,


Yau nama muke miya mulkin bande.

 

 

 

Gyaran Tarbiya da ‘Dabi’un Jama’a

 

  1. Can da ai zaman kid’in Tauri bori,


Wasan dambe babu shi mulkin Bande.

 

  1. ‘Yan boko ana ta haukan mashalo,


Duk an tuba zamanin Alhaji Bande.

 

  1. Yau dad’a ga mahardata ga makaranta,


Bid’i'a ta ji gwangwaza mulkin Bande.

 

  1. Mun manta a yau da kurbin girbani,


Ko cin maganin duhu mulkin Bande.

 

  1. Wa ka tuwo da k’asari yau ko dussa,


Ko shan dummakata mulkin Haji Bande?

 

  1. Ko wahalan sayen ‘bula don kalaci,


Sai dai yamadilla mulkin Haji Bande.

 

  1. Ba wahala ta gala yau ba ‘yan matse,


Altine mai ruwammu ya san haka Ande.

 

  1. Mun manta da babbake balle d’auke


Yunwa ta yi kwaid’i mulki Haji Bande.

 

  1. Ba d’ancaca mai bajan kai nai Bunza


‘Dantaro na Tak’iji can nesa ga Bande

 

  1. Ba wani d’an fashi bale gumbi Bunza


Ango Buzumbuzun shina nesa ga Bande

 

  1. Yau ‘yan Bunza ba fitaccen d’an k’waya,


Ja’b’bi mala’ikansu na tsoron Bande.

 

  1. Duka fad’in garinmu yau ba mai goge,


Sai bak’in biyo wuce mulki Bande.

 

 

  1. Ba dan dambe yau gudun fad’in Bunza,


Sun huta da shan bugu mulkin Bande.

 

  1. Sarkin Dambe Ali dogo d’an kaza,


Yau kamisho ya kai cikin mulkin Bunza

 

  1. Gero bak’i a yanzu an d’ebe rero,


Ga sunnah cikin gidan Bawa Nakande.

 

  1. Yau duka Bunza babu dillalin k’waya,


‘Daya ya tuba hag gidan Alhaji Bande.

 

  1. Ba mugu irin iyalan ga na Gambo,


Duka sun tuba zamanin mulkin Bande.

 

  1. Ya hana masu cije kan biro cuta,


‘Yan bocar gada-gada nesa ga Bande.

 

Kamun kai da Gudun duniya

  1. Bai ta’ba shisshigi shiga mulki yara,


Na siyasa da handama sarki Bande.

 

  1. Ko Naira ka jan k’asa bai rok’awa,


Bai ta’ba kwangila ba Sarki haji Bande.

 

  1. Bai ba duniya amana na kwabo ba,


Bai da asusu don aje kud’d’i Bande.

 

  1. Bai da gida guda da yag gina Bunza,


Ko k’auyenta bai da ko bukka Bande.

 

  1. Bai yi rak’e-rak’en shiga marsandi ba,


Ko dokin hawa guda babu ga Bande.

 

  1. Bai yi gada-gadan jidalin kiyo ba,


Ba turke guda da suna nai Bande.

 

  1. Bai iya fankama na haukan d’inki ba,


Tad da gaba cikin nad’i bai yi Bande.

 

Sarakunan da Suka Kama a Surar Jiki:

 

  1. Siffa tai guda da mai Gwandu ku lura,


Baba Haruna shugaban Sarki Bande.

 

  1. Ahmadu Bello ke da siffatai sosai,


Tun ga jikinsu har nad’i Sarki Bande.

 

  1. Ado mai Kano ga zati suka daidai,


Can ga nad’insa anka sha bamban Bande.

 

  1. Ga jiki ce kakai Bashar ne mai Daura,


Ko Cikasoro Bubakar ga kama Bande.

 

  1. Ya yi kama da Mera Sarkin Kabi Babba,


Kundukukinsa ne ya sa’ba wa na Bande.

 

  1. Sarkin yamma Gwandu k’irarsu iri dai,


Fuskatai, jiki nad’i tamkar Bande.

 

 

Rayuwarsa Gabanin Sarautarsa:

 

  1. Kar fa ku shafa Bande yai aiki sosai,


Tun kafin ya hau gadon mulki Bande.

 

  1. Yarancinsa yai karatunsa na allo,


Gun Malam Tafa uban Alhaji Bande.

 

  1. Modi’bere yai karatu gun Siddi,


Kakan mai rubuta wak’ar ga ta Bande.

 

 

  1. Liman Inta ya karantassai sosai,


Gado ta ce, a nan ta san Alhaji Bande.

 

  1. Malam Bande yai karantarwa sosai,


Tun kamin hawa gadon mulki Bande.

 

  1. Ya zama malami na yak’ar jahillai,


Shi yaw waye kan mutanen Raha Bande.

 

  1. Bande ya je a Gardi can yaw waye su,


Ya yi zama a Tilli koyarwa Bande.

 

  1. Nan Gwade kulluhinsu shi yaw waye su,


‘Yan Zogirma sun ji dad’i nai Bande

 

  1. ‘Yan Giro na fad’in maraba da ‘Danbunza,


Mai nak’alin sabatta jahilci Bande,

 

  1. Kai a tak’aice Bande ya sami yabawa,


Ogunezan fad’a da jahilci Bande

 

  1. Sai da ya k’are zagaye har ya zauna,


Rabbu ya k’addarai da yin Sarki Bande.

 

Nad’i da Sarauta

  1. Watau shekarar ’76 ke nan,


An ka nad’a shi hakimi Sarki Bande.

 

  1. Sai da ya shekaru yana hakimtarmu,


Kuma yaz zan Uban k’asa Sarki Bande.

 

  1. Sarkin Yamma Bubakar ne yag gada,


Sai da ya kwanta dama anka nad’o Bande

  1. Zamaninsa ne sarautu suka k’aru,


Bunza gabas da yamma don Sarki Bande.

 

  1. Bunza gabas ta ‘Dangaladima ke nan,


Yamma akwai Mafara hakimman Bande.

 

  1. Ku bi babbanku Bande shi Rabbu ya za’ba,


Kun zama k’ark’ashin rik’on Alhaji Bande.

 

Wasu Sarakai da Suka zo Ta’aziyya:

  1. Nai muku gaisuwa mutanenmu na Bunza,


Na hasarar uban k’asa Alhaji Bande.

 

  1. Mai Raha shi da kansa yaz zo a uzurce,


Ran da ya sami ‘bir’bishin rasuwar Bande.

 

  1. Sarkin Yak’i bai tsaya ba da jama’arsa,


Daga Zogirma don fa tanzzankon Bande.

 

  1. Mai Digi ya taho da kai nai har Bunza,


Shi da Amiru don fa tanzankon Bande.

 

  1. Wa zai k’arga d’an mutum ko shi waye?


Ta’aziyyar rashin da mun ka yi kan Bande.

 

  1. Yau dad’a fada al’amurra sui tinjim,


Wa ka fad’i a ce na’am bayan Bande?

 

Shawara ga Duk wanda Zai Hau Gadon:

  1. Yau dai Bunza in sarauta mota ce,


Mai tuk’inta Gagga tayoyi Bande.

 

  1. Tayoyi ka tuk’a mota a gudane,


Mudin tar  rasa su ko ta zam keke.

 

  1. Mu dai shawararmu gun wanda ka zo wa,


Sai ya kula gidan akwai kabarin Bande.

 

  1. Kar ya bi shawarar miyagun malammai,                                                      a                   Har ya yi shisshigin ta’bin Bande.


 

 

Wallahi Ba Ma so:

 

  1. Mai burin ya k’untata masa ko waye,


Kada Allah Ya ba shi gado nai Bande.

 

  1. Mai k’udurin zubar da datti a kabarin nan,


Ka da Allah Ya ba shi gado nai Bande.

 

  1. Mai niyyar ya walwale duka tsarinsa,


Ba ma son sa mu talakkawan Bande.

 

  1. Mai k’udurin fashe fushi mai ga mutane,


Sai shi mace karaje bai gadon Bande.

 

  1. Mai niyar hawa ya cuta wa talaka,


Faufau bai hawa gadon gadon Bande.

 

  1. Mai niyar had’a mu yak’i da Fulani,


Allah kak Ka k’addarai gadon Bande.

 

  1. Duk mai son ya sa k’abilanci Bunza,


Kada Allah Ya k’addarai gadon Bande.

 

  1. Mai son kai da nuna bambancin wofi,


Bai gadon uban k’asa Sarki Bande.

 

  1. Yanzu talakka Bunza sun zama wayayyi,


Sun san hak’k’unansu tun mulkin Bande.
 

  1. Ba a matsar da su bale a ci irlinsu,


Don ba su san da shi ba can mulkin Bande.

 

  1. Don haka wanda za ya hau duk ya kiyaye,


Sese-da-sese dai irin mulkin Bande.

 

Allah ka Nad’i Mutum duk bai Wuce Lokacinsa:

  1. Mai gadon gidan ga Allah ka nad’a shi,


Tamkar yadda yad nad’o Sarki Bande.

 

  1. Ba wani wanda zai fad’a ko shi wane,


Allah dai Ya san magaji nai Bande.

 

  1. Kowa Jalla za ya ba tuni mun yarda,


Domin shi ya kar’bi ran Sarki Bande.

 

  1. Kowa zai hawa ya lura da d’ani ne,


Don da dawwama akai an bar Bande.

 

  1. Da dai dawwama a kai kan karagar ga,


Da mun ce a bar shi har Madi Bande.

 

Misalin Wasu Sarakuna da Mazaje:

  1. Da tsare gaskiya yana sa da doge wa,


Da Sarki Yahayya ya iske Bande.

 

  1. Da tsanani ka sa sarauta dogewa,


Mairigaggo bai wuce wa Harande.

 

  1. Da suna ka sa sarauta dogewa,


Da har gobe Garba ke Dikkon Gande.

 

  1. Da kyauta ka sa sarauta dogewa,


Sarki Abdu, bai wuce wa a yi Bande.

 

  1. Ai mutuwar sarakuna ma aya ce,


Dubi Firimiya bale Alhaji Bande.

 

  1. Da kud’d’i ka kare rai ba ya macewa,


Monde Waliyyi na ishe Sarki Bande.

 

  1. Alti Magaji ya yi kud’d’i tirk’ashi!


Ga Maitangaraho duk sun bar Bande.

 

  1. Da sihiri ka kare rai ba shi macewa,


Ibrahimu Gardi ba shi rigon Bande.

 

  1. Da mutuwa tana da tausai ga karatu,


Da Mamman Kwadarko ta bar shi da Bande.

 

  1. Da ta gadi k’yale manyan limammai,


Liman Yalli bai rigon sarki Bande.

 

  1. Da mutuwa tana da tausan malammai,


Salihu Inta bai rigon Sarki Bande.

 

  1. Mun ji halinta d’auke manyan ladanai,


Ladan Juga ya riga Sarki Bande.

 

  1. Ba tsufa ka sa ta je ta yi aiki ba,


Don ga ‘Binga zaune ta d’auke Bande.

 

  1. Ba kunyanta masu ilmin boko ba,


Daudun Manu ya wuce yab bar Bande.

 

  1. In ta fara kakka’ba ba ta tausai,


Sai mu yi hank’uri talakkawan Bande.

 

  1. Dubi gida guda takan d’auke taro,


Sa natsuwa da kyau ka dubi gidan Bande.

 

  1. Ali Babunje an misali nan babba,


Tad dawo ga ‘Dangaliman Bande.

 

  1. Maliki tak kira shi ko Shamaki na can,


Sannan ta yi yi d’ungurungum kan Bande.

 

  1. Wanga kawai abin kula da misali ne,


Da gidan Abdu hag gidan Sarki Bande.

 

‘Yangalimomi a Tuna da Zumunta:

 

  1. Babu wurin shiga ga bare shi yi ‘banna,


Sarki Abdu kansa kan Sarki Bande.

 

  1. Mai son ta da hargitsi ga sarautar ga,


Bai son Abdu kana bai k’aunar Bande.

 

  1. Shin ku ‘yan d’iya da ke rigimar wauta,


Wat ta’ba tuntu’ben fad’an Audu da Bande?

 

  1. Ko sarayya za a yi birnin Bunza,


Sarki Abdu bai ta’bin Sarki Bande.

 

  1. Mai son ta da hargitsi ba mu yafe ba,


A gidan Abdu ko gidan Mamman Bande.

 

Kira ga Sha’irai:

  1. Yanzu kira nikai ga dukkan sha’irrai,


Wak’ek’eniyar rashin Sarki Bande.

 

  1. Kaftin Suru sai ka zamo bayaninka,


Ta’aziyyar uban k’asa Sarki Bande.

 

  1. Monde Abubakar na Birnin Kabi taso,


Kawo gudummuwar rashin Sarki Bande.

 

  1. ‘Danmasani na Jega taso aikinka,


Marsiyya a kan rashin Sarki Bande.

 

  1. Baba Waziri Gwandu ba sai na ce ba,


Ta’aziyya a wak’e nas so don Bande.

 

  1. Sambo Wali a gwamatso ga aiki nan,


Wak’a don tuni da mai girma Bande.

 

  1. Garba na Gwandu ba fa rok’o nika yi ba,


Baitoci nake buk’ata kan Bande.

 

Nad’ewa:

  1. ‘Yan Gamzaki k’ungiyarmu ta ‘yan Bunza,


Kun ji ganin Alu a kan Sarki Bande.

 

  1. Jama’ar Bunza ‘yan gida duka har bak’i,


Ta’aziyya nike rashin Sarki Bande.

 

  1. Ali na Bunza ya yi don ta’aziyya ne,


Ba shi bid’an yabo ga duk dangin Bande.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments