Ta’aziyyar Mallam Ibrahim Awwal Albaani Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza


    1.       Shukura ga Allah guda masani halin kowa,
              Mai ƙaddarowa ta tabbata babu mai tsawa,
    Ya mai hukuncin da ba makara da gaggawa,
    Masanin da ilminSa ya wuce hankalin kowa,
              Subhaana lil laahi tsarki na ga Rabbani.

    2.       Na yo salati ga Manzo shugaban bayi,
    Ahalinsa dukkan sahabbai ƙoƙari sun yi,
    Na riƙo ga sunna ta sadu da mu ruwan sanyi,
    Mariƙa amana sahada kun riga kun yi,
              Matsayin shahidi ga nassi babu saɓani.

    3.       Mai rai a ce ya mace ba al’ajab ne ba,
    Mutuwar shahada buki ne ba na wasa ba,
    Ita ce manunin aƙida ba ta yi ƙura ba,
    Ita fassara ce mutum bai tabka shirme ba,
              Shaidarmu ke nan ga Awwalu namu Albaani.


    4.       Ba mu shaidi Awwal a kan ilminsa ya kai ba,
              Ba mu tsarkake ayyukansa hawa kurarra ba,
    Ba mu yanke ƙauna irinsa ba zai yi laifi ba,
    Katarin da Allahu yai masa ne abin duba,
              Kalimar shahada ta zan ƙarshe ga Albaani.

    5.       Ita ce alamar kusantar Rabbu mai girma,
    An zaɓi bawa cikin bayi na alfarma,
    Ya samu babban rabo na shiga sahun dama,
    Ladar karatunka ce Allah Ya saka ma,
              Zance ga nassi sahihi babu ƙaulaani.

    6.       Awwal haƙiƙan Tabaraka ya yi ma baiwa,
    Ya sa ka layi da muminnai suke kewa,
    Ka samu hasken da yaf fi gaban musun kowa,
    Haka Rabbu Yaƙ ƙaddaro tafiya ta gaggawa,
              Mutuwar shahada rabo ce babba Albaani.

     7.       Ƙarshen ƙwarai muminai abada ka alwashi,
    Rahama gado ce da babu kamar ta gun taushi,
    Ta zarce kaafur da almiski wajen ƙanshi,
    Shuhadaa’u Aljanna ke karɓa da lallashi,
              Fatarmu ke nan ga Awwalu namu Albaani.

    8.       Masani hadisi maƙoƙarci ga tsentseni,
    Fatawarka nassin hadisi babu saɓani,
    In ga sahihin hadishi ba shi sharani,
    Da gani da aiki zama ɗaya ne ga Albaani,
              Bai faɗa ɗirkaniyar rigima ta ƙaulaani.

    9.       Awwal a fannin hadisi ka yi tabarma,
    Fiƙihun hadisai na salla in gajerta ma,
    Matani da ilmul rijaalu maza na alfarma,
    Isnaadu bin taliyonsa hagunsa har dama,
              Sun zauni ƙirjinka Awwalu babu saɓani.

    10.     Fatawar Buhaari da Muslimu Tirmizi daidai,
    Kundin Nisa’i, Abu Dawuda zancenai,
    Haka Baihaƙi ko Muwatta mai karutu nai,
    Awwal idan ya hawo sharhinsu bakinai,
              Tamkar ka ce zamaninsu guda da Kirmaani.

    11.     Fatawarsa koyaushe dai a bi maluman farko,
    Masana hadisi ga sunna masu yin sabko,
    Su ne yake kwaikwayo fatawarsu yaɗ ɗauko,
    Sunansa Mamman Awal tun fil azal farko,
              Ƙaunar hadisi ya sa mu kira shi Albaani.

    12.     Bai yarda yin ƙungiyar raba kan Musulmi ba,
    Bai yarda Zazzau a wa bidi’a masauki ba,
    Bai kutsa kainai siyasar tara jalli ba,
    Bai yarda yin kore gwannati na biyanai ba,
              Roƙo da yin raraka faufau ga Albaani.

     13.     Ɗan kasuwa ne ga boko bai zama baya,
    Bai ɗau karatu asusu ba don hawan kaya,
    Komai tulin gingiraɓai ba shi yin zarya,
    Ba a game kai da shi a yi fassarar ƙarya,
              Filin wuri ne dabon Ɗankama Albaani.

    14.     Bai yarda bin Mazhaba a aje hadisai ba,
    Bai ɗauki ƙissa salo ga zubin karatu ba,
    Bai ɗauki wasa da kaulahasan karatu ba,
    Bin malami sau ƙafa bai ɗauki wannan ba,
              Sunna ake bi idan aka samu saɓani.

    15.     A bi taliki sai ka ce gunki yana kuri,
    A yi mai nasiha a kan nassi ya sha bauri,
    Harakar, karatu ta zan wasan kiɗin tauri,
    Kabbarbari had da kuwwa kanka na kauri,
              Alaramma na dama ga ɗan agaji hauni.

    16.     Ilmi a mai she shi hajar ɗaukakar suna,
    Ya zamo jidali da cin zarafi da ƙin juna,
    Haske ya koma duhu, inwa ta zan rana,
    Ustazu in za ka adalci ga zance na,
              Mabiya ga sunna a yau an sa su ruɗani.

    17.     An wa siyasa hadissai don biɗan romo,
    Wa’azi ya koma kamar wasan kiɗin komo,
    Mabiya da Malam kwaɗai kowa ya dai samo,
    Tsoro ya zauna zukata ce ka kai zomo,
              Taƙawa da bin gaskiya suka zan cikin rauni.

    18.     Samun irin Awwali ɗan Iro mai daga,
    Da irin su Jafar Kano bidi’a ta bar tunga,
    Sunna ta miƙe ƙafa mabiya suna farga,
    Yau jami’a ga hijabi har da sa raga,
              Ƙwazonku ne kai da Jafaru Shehu Albaani.

     19.     Kun taimaka raya sunna nan ƙasar Hausa,
    Aka ba matasa fahinta wadda ba nisa,
    Sunna ta tozarta ƙila-wa-ƙala ba fansa,
    Tafiyarku ta zan hasara gun mu kakkausa,
              Samun shahadarku shi yak kore ruɗani.

    20.     Makasanka Awwal hasara ta tuƙaƙe su,
    Ba mumini duniya da yake mutunta su,
    Ranar ƙiyama Tabaraka zai hukunta su,
    Nassi na aya ya ce wuta za a sakka su,
              Shi ne hukuncin kisan kai babu saɓani.

    21.     Mik kai matashi shiga fitinar kisan kanu?
              ‘Yan yara daidai karatu sun sake hannu,
    An birkice hankulansu a mai da su shanu,
    A saka su hanyar ta’addanci su sa hannu,
              An ɓata ƙarshen matasa dama har hauni.

    22.     Ƙarninmu yai arziki da irin su Albaani,
    Harakar ibadarmu ta huta da saɓani,
    Mun gane nassi sahihi mun ga mai rauni,
    Maganar da duk ba hadisi ba ta yin shuni,
              Nahawunta bai sa mu tabka musu da saɓani.

    23.     Babbar hasara gare mu rashinka Albaani,
    Babbar musiba ƙasarmu kashe su Albaani,
    Fitinar da ta’ kunno kai bayan su Albaani,
    Tsananin bala’insa ba magana ta saɓani,
              Yaƙi ake son ya tashi ƙasarmu mai gauni.

     24.     Sa hankali dubi Siriya yau ina saura?
    Bagadada birnin Iraqi ina batun gyara?
    Afgaani ta zan kamar akuya gaban kura,
    Islamabad mumbari aka kai harin sara,
              Nijeriya kan sahu take babu saɓani.
     
    25.     Modibbo Albaani sannu mazan sanin girma,
    Masani hukuncin zama da kiyaye alfarma,
    Samun ku ya tauye ‘yan bidi’a ganin dama,
    Miƙe ƙafafu da sokiburutsu ba dama,
              Fatawar da duk ba hadisi mun aje hauni.

    26.     Ita jarabawarka Malam ka riga ka ci,
    Kwanci kushewarka ba tsoro bale ƙunci,
    Samun shahadarka ya tayar da mu barci,
    Tilas faɗin gaskiya ko da akwai ɗaci,
              Babin gumuzu sahihi ne a Shaukaani.

    27.     Ba mu ɗebe ƙauna ba Malam ba mu manta ka,
    Ƙwazon karatunka dole ake mutunta ka,
    Nasarar shahadarka Awwal ta faranta ka,
    Ƙaunar hadisi gamo da katar ta sakka ka,
              Fatar mu Ya Rabbi gafarta wa Albaani.

    28.     Rigimar kisa ba ta sa sunna ta ja baya,
              Birnin Kano an yi je ka ga mib biyo baya,
    Makasa Umar yanzu Sakkwato dole sai ɓuya,
    Makasa ga Albaani ga su Abuja kan ƙwarya,
              Ƙarshen guluwi shiga babi na kaico ni!

    29.     Tammat bayani na tanzanko da juyayi,
    Babban abokinka Ali na Bunza ne yay yi,
    Na tababta Awwali dai lokaci ya yi,
    Zancen adashinmu masu zubinmu duk sun yi,
              Mu ke da kwasa na ƙarshe babu saɓani.

                                 
    Aliyu M. Bunza
                            Umaru Musa ‘Yar’Adua University,
    Katsina
    Jumu’a 7/03/2014
    Daga Katsina zuwa Sakkwato




    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.