https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
https://www.amsoshi.com/contact-us/
- Na kiri Allah ahadun jigona,
Shi wuturin nan xaya mai ikona,
Sarkin jinqai ga dukan talikkai.
- Na yi salati ga ma’aikin qarshe,
Alayenai da Sahabbai tarshe,
Tabi’ainai a saka duk bai xai.
- Yau kuma babbar magana tas saman,
Dole amayo ta zama ta daman,
Zo kusa in xan gutsura ma daidai.
- Ni dai halin mutuwa nad duba,
Ba ta da yaro haka balle babba,
Ba ta kure kan wa’adi ko tausai.
- Ta ishe mai naquda ta hau kanta,
Ba a ga xa babu uwar ta kwanta,
Shi xan yaye da gudu tar rittai.
- Mai wayo ta qi bari nai wasa,
Shi babane ta rufe labarinsa,
Barde a tsakan waqaci tag girsai.
- Ta tuqe Nomau kakar aikinai,
Mai mulki na tsakiyar ikonai,
Tai masa yanka ciki shi xai rainai.
- Je ga fatake su gaya ma zance,
Kamin zango wani yal lalace,
Ga kaya tarshe ga raqummanai.
- ‘Yan wasa sun tafi dubo Shago,
Dubo Xankurja giye gojirgo,
Xanwasa Garba ga labarinai.
- Tajirrai sun ka zamo goronta,
Dubi su Qaruna zuwa Xantata,
Sai labarinsu ga bakin dubbai.
- Don ilmi Bil’amu bai tsere ba,
Yau Salafus Saalihu ba su ne ba,
Ga mu gurabunsu muna gardanmai.
- Sha’irran gaske su Hassanunmu,
Alfaa Zaazii madahan jigonmu,
Sai dai adu’ar rahama don jinqai.
- In ta zo ba makawa sai kwance,
Ga mai rai ya yi zugum lalace,
Wa ka kiranai ya ji ya amsa mai?
- Al’amarin mautu akwai ban tsoro,
Tamkar zaki ya dakako taro,
Wa ka tsayawa ya ga mai kamamai?
- Duk fitina ta ishe al’ummarmu,
Take mu yi zoru ga malummanmu,
Don su kuranye muna alhininai.
- In ta zo su muka ba aikinta,
Su ke wanka su yi likkafanta,
Su ke salla, adu’a don jinqai.
- Yau ta zo babu sani ba sabo,
Ta hana kowanmu tsayawa tarbo,
Domin ta faxa gidan limammai.
- Wanga rashi namu zama nai babba,
Ba mu da jigon da ya furce baba,
Liman Usman jama’a sun shaidai.
- Babu kasala da nawa ba wasa,
Mamu sun shaidi irin halinsa,
Bai makara wa ka tsayi dakonai?
- Bai da mazauni bayan zaurensa,
Sai masalaci na tsare jam’insa,
Ham mutuwa taz zaka ta iske mai.
- Manu daxai bai da mazaunin tsince,
Zaurenai za ka ga kainai noce,
Gun Qur’aninsa shina bitanai.
- Bai da abokin rigima ko gaba,
Bai tava sa kai fitanar dangi ba,
Ko a gidanai take bai bobotai.
- Mai iya kainai yake mai kamewa,
Mai haqurin gaske mazan jurewa,
Babu kwaxai wa ka tavin irlinai?
- Annashawatai ta kiran salla ta,
In mukhtarinta ya xan tsatsanta,
Zai ciri sandarsa zuwa aikinai.
- Mai ladabi ne da kulawa sosai,
Mai fikira ne ga sanin xalibbai,
Kowa sunansa yake xoramai.
- Ba ya da jin kai da cikawar baki,
Bai da xabi’ar da ka sa ai tsaki,
Zaven Allah mutuwar ban tausai.
- Shakundun ne ga kiyaye doka,
Ba ku gamamma ka ga ya sha toka,
Shi ke gaisheka ga al’adatai.
- Ba ku gamamma ya qi tunkararka,
Ba ka hasara ya qi jajantarka,
Mai kirki ne a fagen jin tausai.
- Manu ruwa masu kwarare sannu,
Tun yaranta da halin yag ginu,
Har mutuwa taz zaka tax xau rainai.
- Ba don mutuwa hutawa ce ba,
Ba don ita ce qarshen mai rai ba,
Da mun zarge ta da cin haqqinai.
- Dubi irin qarshen zamaninmu,
Duk da irin munin halayyarmu,
Liman girmansa yana nan kainai.
- Bai yi takaici na hawan qarhe ba,
Bai tava shawar shi shigo mota ba,
Bai aje ko keke ba domin kainai.
- Bai da gida ban da gidan gadonai,
Aunaka tai daidai jallinai,
Haw wa’adi yay yi shi nan kainai.
- Bai tava sha’awar rigimar xinki ba,
Don haka bai yarda shiga Fati ba,
Ba shi jawabi a ci zuququnai.
- Ba ya da buri na zama hababba,
Ko haasave, a yi ba su gane ba,
Sin’ara hauru sake sai suruttai.
- Mai imani kake duk mun shaida,
Taka-tsantsan da kake mun yarda,
Ka tafi ka bar mu da tarihinai.
- Mai son Allah shi tsare haqqinSa,
Mai son Manzo (SAW) ya fake sunnarsa,
Nassi ne tabbace gun Maisammai.
- Liman Usmanu mazan gyarawa,
Babu jiyewa da yawan kushewa,
Bai da zurewa gaba an shaida mai.
- Baban Ummar bawan Allah ne,
Bai da masoka ga mutum ko wane,
Mai halayen manyan shehunnai.
- Wafatinai wata ilhaama ce,
Ta haxa kanunmu shuru ba zance,
An sallace shi gaba xai, bai xai.
- Wagga ishara magana ce tarshe,
Shi na qwarai ko ya mullo kirshe,
Mai imani bai tsamar bi nai.
- Mugu ko ya naxe maqoqonai,
Ko da giginya yaka tasbihinai,
Wa ka kula mai, ya yi alhininai?
- Don haka mai rai ya kiyaye sosai,
Kar ya yi wasar riqe imaninai,
Shaidun jama’a Allah bai qi nai.
- Don haka kurin ni mai ilmi ne,
Ko ce wa ni babban shehe ne,
Ba shi da rana a yi aikin daidai.
- Ga liman bai yi zama shehe ba,
Bai da xariqa bai shiga hizbi ba,
Amma ya samu cikawa daidai.
- Kowa ya yarda da addininai,
Mu duka mun yarda da imaninai,
Ba mu da suka ga irin sabgatai.
- Roqon da mukai a wajen mai jinqai,
Wannan da ya yo sama, yay yo qassai,
Yai maka rahama a cikin taskaTai.
- Allah kukanmu ga limaminmu,
Yadda yabonai ya bi alqaryarmu,
Can ga hisabi ka cike mudunai.
- Babbar qaunarmu ga aljannarKa,
Har can Firdausi Ka sa bawanKa,
Tare da maban ga da ke roqamai.
- In ka ce: “Kun”, “Fayakun” tilas ne,
Muddin Ka yarda abin diimun ne,
Mun ce: “Amin!” Ya Sarkin sammai.
- Dakanta mai neman ganewa,
Liman Usman a wajen nunawa,
Ba dogo ne ba ga talittatai.
- Shi matsakaicin mutume ne daidai,
Tamkar Saninsa zubin qiratai,
Amadu shi ko ga fari yas satai.
- Malami shi yay yi aron fuskarsa,
Ali ka tangam ga irin zatinsa,
Xan’auta Bello baqi yac cutai.
- Can ga xuminai Sa’a ta gane shi,
Ummaru aka ba natsuwar halinshi,
Ba rigima babu yawan suruttai.
- Liman Usman suturatai riga,
Sai rawaninai malagi gefen ga,
Kaftani ba shi cikin tsarinai.
- Takalminai faxe ne ko yaushe,
Bai xangarfa rigimar ‘yan tashe,
Ba shi da kuri ga irin tsarinai.
- Haurunai sun cika baki daidai,
Baki daidai da tsawon fuskatai,
Gemu daidai ga zubin kuncenai.
- Gun tafiya bai cika yin miqo ba,
Bai yin sauri kuma bai toge ba,
Sannu yake yi tafiyar malammai.
- Kambilinai daidai zatinai,
Bai da tsawo ba ya da gwaffa kainai,
Xan siriri ga zubin siffatai.
- Na’ibbainai ta’aziyya gun ku,
Ladannai sai ku tsare aikinku,
Nai muku tanzanko da fatar jinqai.
- Tammat Allah ka ji kukan Ali,
Share hawayensa ka sa mai kwalli,
Kai shi a Firdausi cikin limammai.
https://www.amsoshi.com/contact-us/
0 Comments
Rubuta tsokaci.