Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’aziyyar Malam Umaru Garba Bunza Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com

  1. Da sunan Allah ahadun wahidun Gwani,


Da yay yo sammai k’assai duk muna gani,

Ya yo mu mutane mala’iku da aljani,

Ya k’addaro mutuwa cikinmu babu magani,

Ko d’aya ba ta mantuwa.

 

  1. Dukan mai rai ta ishe shi ba ta mantuwa,


Mutane dabba na tudu ko cikin ruwa,

Su k’wari tsuntsu su tsiro ko itatuwa,

Da duk ajali yay yi Jalla ba shi mantuwa,

Ba wani k’ara shan ruwa.

 

  1. Wad’ansu akan bar su har su tsufa gwargwado,


Wad’ansu ga jinya taka riskansu kan gado

Wad’ansu suna lafiya ta je ta gargod’o,

Kamar wasa in ajali ne ya jewad’o

Sai ka ga babu rayuwa.

 

  1. Tunanin mutuwa shi ke katse hanzari,


Ha ba jama’a mi muka yanga da kumbari?

Da dogon buri ga mu muna ta tunzuri,

Ayyukkan banza d’ai muka k’ara k’ok’ari,

Don wauta da d’amuwa.

 

  1. Ina jin ta a nesa ga ta ta taho kusa


Mutum duka k’arshensa kwanciya cikin k’asa,

A sa shi a rame, a sa ice a sa k’asa,

Da an k’are sai matambaya su yo kusa,

Ranan ba ka mantuwa.

 

  1. Da duk nat tuna Sanda zuciya ta d’au rawa,


Idanu su cike da dinga d’uruwar ruwa,

Tunani shi tsananta duk na d’ora damuwa,

Hasara ce babba ta wuce misaltuwa,

Mun yi rashin na d’an uwa.

 

  1. ‘Dabi’un Ummar natsuwa babu magud’i,


Cikin k’annai koyaushe yana ta gargad’i,

Abokai koyaushe idan mun yi jewad’i,

A kan matsalar magani walau batun kud’i.

Ummaru ba shi damuwa.

 

  1. Dad’ai Ummar bai kula da ayyukan wani,


Bale hira a dandali ana ta gunguni,

Abokai mun shaida Sanda bai da tsegumi,

Yana tsoron kutsa kai cikin bak’in jini,

Ummaru bai da k’waruwa.

 

  1. Yana nisantar fad’a da ta da hargitsi,


Dad’ai Ummaru bai da aboki na yamutsi,

Kamar yada nas san Sanda irin sanin hatsi

Ruwan sanyi ne kashe bela da tartsatsi,

Kwas sha ba shi cutuwa.

 

  1. Umar ga fara’a ga wasa da dariya,


Da d’ai bai k’aunar wurin musu da tankiya,

Sana’a tai bai yin riya ba shi murd’iya,

Abokan huld’arsa sun yaba da godiya,

Don bai zamba bai ruwa.

 

  1. Umar bai sutura ta riya da tad da hankali,


Irin manyan rigunan ga masu k’yalk’yali,

Da ke sa kuri da fankama da d’an hali,

Umar bai tafiyar kuri ba shi tak’ama,

Ko ranar da yai k’awa.

 

 

 

 

 

  1. Ina ta’aziyya ga masu sai da magani,


Ku dubi halin Sanda da kyau kui ta tuntuni,

Idan kun koye shi hak’ik’an kuna gani,

Wajen jama’a koyaushe kuna farin jini,

Ku ke kar’be kasuwa.

 

  1. Ina ta’aziyya Altine Siddi ‘yan uwa,


Da Abdurrahman Usman Dangi d’an uwa,

Hak’ik’an Ali Kamfani kana da damuwa,

Rashin babban wa tamka tai rashin uwa,

Shi yi maka shi yi ma tsohuwa.

 

  1. Umar Usman Faruku mu d’auki hankuri,


Junaidu da Bande Dole mu d’auki tasari,

Zaman Ruwa Memba shi yan nuna k’ok’ari,

Muna wankan sanda shi ka ba mu hank’uri”,

Kuka ba shi dauruwa.

 

  1. Muna rok’on Rabbana abin kira d’aya,


Shi kunkare zunubanka Sanda duk gaba d’aya,

Shi kare maka dukkan fitinar matambaya,

Shi sa mutuwa ce k’arshen dukkanin wuya,

Gun ka da kai da ‘yan uwa.

 

  1. Gafurun mun rok’i gafararKa Kai k’ad’ai,


Rahimun rahamarKa howanenmu na kwad’ai,

Afuwwan afuwarka ce muke bid’a kad’ai,

Mujibud da’awati kar’bi addu’armu dai,

Sanda shi samu kar’buwa.

 

  1. Azizun kai Ka buwaya ba ka gasuwa,


Basirun ka san na tudu har cikin ruwa

Alimun iliminKa ya wuce misaltuwa,

Muna bisa rok’onKa gafara da affuwa,

Mun san ba ka mantuwa.-

 

 

 

 

  1. Muhid’un Kake komai ka kewaye sarai,


Abin da mukai fai da ‘boye ka sani sarai

Asirranmu na zuci Rabbu ka sani sarai,

Hakimun Sattaru lullu’be Umar k’warai,

Sa shi cikin gudunmuwa.

 

  1. Muna rok’o laifukansa kankare masa,


Zaman kai ke yi mu roho muke masa,

Hisabin da Kakai Rabbu Ka tausaya masa,

Sirad’i in zai hawa ka agaza masa

Ya gatan maras uwa.

 

  1. Litaffan aikinsa wanda Ka aje masa,


Hak’ik’an mun san ba k’arin da Kai masa,

Ayukkanai ne duniya babu fallasa,

Muna dai rok’o Rahimu Tausaya masa,

Mun san ba ka makkuwa.

 

  1. Halin mai rai ne kana shina da mantuwa,


Shina ga tafarkin k’warai shi fad’a d’emuwa,

Shina bisa hanyar k’warai shi sami rud’uwa,

Idan ba rahamar Allah gun mu ‘yan uwa,

Wa zai tsallake hawa?

 

  1. Dalilin haka ne muka rok’onKa wahidun,


Mu dage kuma ba mu bari ga mu juddadun,

Ka sa Ummaru gun ceton sidi ‘Dahirun,

Ya tsunduma aljanna cana gun ta halidun,

Tare da mu da ‘yan uwa.

 

 

 

 

 

  1. Hak’ik’an yau Sanda nau shina a lahira,


Ya bar mu cikin duniya muna ta dawara,

Muna yawo barkatai, kama da fakkara,

A ce mun manta da Sanda mun yi yaudara,

Wannan ba ta faruwa.

 

  1. Ganin gawar sanda kwance babu rayuwa,


Na so in arba da Sanda ba shi dubuwa

Jini ciki yak kwana Sanda babu ‘yan uwa,

Na ‘barke kuka kaico ni da ‘yan uwa.

Mai rai na da mantuwa.

 

  1. Ganin k’arshe ne da nai wa Sanda kasuwa,


Inai masa hud’uba yac ce ba shi mantuwa,

Idan tafiya ta ishe ka nemi ‘yan uwa,

Hadisi ne Sanda kar ka sami damuwa,

Hali ne na rayuwa.

 

  1. Ya ce min: “Madalla Ali ba ni mantuwa,


Akwai wani yaro Garba yana da natsuwa,

Amini ne adili da bai da cutuwa,

Da sassafen gobe sai Ilori Kasuwa,

Rabbu Shi sa da saduwa.

 

  1. Ashe k’arshen al’amari ya taho kusa,


Garin Makwa can Jalla Yan nufa shi zan k’asa,

Wuce Bakani can ajali ya ishe masa,

Cikin barci Garba yag ga shi ban k’asa,

Ummaru babu rayuwa.

 

  1. Haba mai rai mi kaka rigimar gada-gada?


Halan ka mance duniya na da gargada,

Bak’ar hanya ce kashe bak’o da d’an gida,

Takan d’auke maigida ta bar uwar gida

Ta mai she ta gwauruwa.

 

 

 

 

  1. Yawan samu shi ka sa wad’ansu fankama,


Wurin tafiya sai ka ga an sa da tak’ama,

Shi canza abokansa ko wajensu bai zama,

Shi kwazo wasu can na yaudara mahandama,

Wai shi ya ga k’aruwa.

 

  1. A yau Ummaru ya rasu ya bar uwar gida,


Dabaru duka ba su tun da babu maigida,

A dole ta kwashe nata ya hata tai gida,

Ki yafe laifinki kin jiya Uwar gida

Kin ga hali na rayuwa.

 

  1. Abokai muke amma dad’a mun fi damuwa,


A wayi gari babu Sanda mun fi tsalguwa,

Wurin yawo gun mu dole zai tak’aituwa,

Bale ni mai jewad’i tasha da kasuwa,

Yau dad’a ba wurin zuwa.

 

  1. Halin rai sabo kana shina da mautuwa,


Akwai wata Juma’a da naf fito a kasuwa,

Na rugo gun Sanda don shi ban abin hawa,

Da nat tuna ba Sanda sai jiki ya d’au rawa,

Rannan na ji damuwa.

 

  1. Irin kukan Ummaru Faruku nig gani,


Na so ni daure k’irji na ta gunguni,

A tilas nac ce: “Wayyo Allah, kaico ni!.

Umar ba shakka wallai mui bak’in gani,

Mun yi rashi na d’an uwa”.

 

 

  1. Ga siffar zati Ummaru ba shi d’ingishi,


Bak’i ne, dogo da wushirya ta murmushi,

Yana da jiki gwargwado irin na masu shi,

Yawan asawaki halinsa ne na armashi

Kaftani tufan k’awa.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments