Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’aziyyar Mallam Jafar Mahmuda Adamu Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com


  1.      Da sunan Allahu Alhayyu rayayye kake,

Mai rayarwa a hannunKa numfashi yake,

Kowa Ka kira a tilas abin haka nan yake,

Ko so ko k’i hukuncinKa duk daidai shike,

Yau bisa ikonKa Kab bar mu Kak kiri Jafaru.

 

  1.      Na yi salati ga d’an Abdu Manzo Annabi,


Na sa ashabu har tabi’ai duka bi-da-bi,

Na sa duka tabi’ut tabi’ina da masu bi,

Fatata yau ma’aunin ga nawa da nai zubi,

Rabbu Shi yahe wa Shehunmu malam Jafaru.

 

  1.      Dole da k’in gaskiya anka ce sai bin ‘bata,


Kwab bi ‘bata babu shakka ku san ya karkata,

Ranar had’uwa gidan gaskiya zai k’untata,

Azzalummai a rannan wuta suka tabbata,

Masu masaukisu su ne Nakiri da Munkaru.

 

  1.      Tabbas mutuwar shahada akwai ta da d’aukaka,


Kowas same ta ya zan aminin Maiduka,

Alk’awalin Jalla na wa ka fara musun haka,

Lallai shuhada’u aljanna sun ka yi su duka,

Firdausi muke buk’atar a kai muna Jafaru.

 

  1.  Ranar Jumu’a shahadarsa ta d’au jiniya,


Daidai Asuba hukuncin a nan ne yat saya,

Bayan raka’a ta farko ya d’auko anniya,

Ya yo sujada ta k’arshe zamansa a duniya,

Sauran ta biyun a aljanna za ka yi Jafaru.

 

  1.      Kai ne na biyun shahidin da anka kashe haka,


Don ‘Danhad’d’abi shi yar riga ka zuwa haka,

Tarihi ne ya maimaita kansa na d’aukaka,

Su ko makasanka mu za mu kai maka su duka,

Sai an je can ka ja naka hak’k’i Jafaru.

 

 

  1.      Shi d’an bidi’a tunaninsa ba dogo ba ne,


Shi wai ga zatonsa in yai irin haka ya gwane,

Ya cika burinsa kan wanga aiki k’ank’ane,

Ranar da k’ilui ta jawo balau zai sha bone,

Don ga dubbai matasa magadan Jafaru.

 

  1.      Kukan da nikai mazajen k’ira’a sun wuce,


Duniya ta san tilawarka babu ka-ce-na-ce,

Nassi ya zauni k’irjinka Jafaru ka fice,

Gun tajwidinka duk duniya haka nan ta ce,

Kai ne zakaran matasa na Sunna Jafaru.

 

  1.      Masu hadisi sukan ce da mu nan kak’ k’ware,


Gun isnadi fahintarka ba ta da fand’are,

A wajen matani k’warewarka Jafaru ta zure,

Ilmi na Rijaalu an ce a nan ka kare kare,

Fassara ma’ana a yau babu tamkar Jafaru.

 

  1. Kan zancen Mazhaba ba kamar sa ga fassara,


Komai tsaurin kilafa yakan yi da hattara,

Bai zagi ba ya neman yabo bai takara,

Bai kuri ba ya d’aukar gaba bai kumbura,

Bai kushe mutum bale cin mutunci Jafaru.

 

  1. Kan Arbiya a tilas ake ta’ba masa,


Domin nahawun balagarsa an ka yaba masa,

Tasrifi, Mand’iki ko Masar a bar masa,

Gogan Adabi, Aruli a yanzu ana k’asa,

Allah Shi yi ma ijaba da Kausara Jafaru.

 

 

 

 

 

  1. Kan tafsiri k’asar Hausa mun ce an gama,


Bayan rasuwarka Malam ina mai azzama,

Mai yi wa nassi fashin albasa ba gardama,

Gogaggen hazik’i gangaram kan tarjama,

Hatta mak’iyanka sun girgiza maka Jafaru.

 

  1. Kyawon ilmi ga bawa ya zan mai kama kai,


Ba fahari babu izza bale kibiri ga kai,

Babu kwad’ai babu rok’o bale k’ask’anta kai,

Ba fadanci wajen masu mulki barkatai,

Don haka ‘Dagutu ke d’ari-d’ari da Jafaru.

 

  1. An sha jawo shi shrimen siyasa ya k’iya,


Har yam mutu bai da katin zama d’an jam’iya,

Balle rigimar siyasa ta kai shi cikin k’aya,

To kun ji abin da yas sa adawar duniya,

Malamman fada suka tattara kan Jafaru.

 

  1. Ya k’i aminta shiga k’ungiyoyin fariya,


Masu gwadogo da nassi a ba su abin miya,

Don su suka ka da girmanmu nan Nijeriya,

Yau mun rasa malami d’ai da zai yi gwagwarmaya,

Korar ‘Dagutu bayan wucewar Jafaru .

 

  1. Duk k’aryar rijiya dai ruwa kogi suke,


K’arya zafi ga rana wuta dahir yake,

Lantarki bai yi hasken wata ba da tsallake,

Lallai da fad’a da aiki a nan sunna take,

Kun ji dalilin matasa na k’aunar Jafaru.

 

  1. Yai ilmin zamani ya karanci Filosafa,


Ya tsani yin ci-da-ceto bale kamun k’afa,

Cuta ko tsito yag gan ta ba shi rufa-rufa,

Ai don haka malaman nan da ke buga dundufa,

Ke kakkausan bayani da sukar Jafaru.

 

 

 

 

  1. Ya wa bidi’a kushewa Kano sun san haka,


Ya wa shirka kisan gilla dar rana tsaka,

Hasken sunna a birni da k’auye ya haskaka,

Tilas bidi’a da ‘ya’yanta dole su harzuk’a,

Babu wajen shanya gari Kano ga Jafaru.

 

  1. Zance uku malamai sun ka ce gadonsu ne,


Sun ce farko kashewa matas sunnarsu ne,

Koko a tsare ga ‘Dagutu duk aikinsu ne,

Sannan hijira fad’in malamai ta ukunsu ne,

Shahiddai an na farko kana cikin Jafaru.

 

  1. Mansur ne malamina na yo mishi tambaya,


Kan juyayin shahidi uban gwaggwarmaya,

Na ga idanunsa jijir ya barkonon miya,

Yac ce, da Aliyu dad’in da naj ji a duniya,

Samun shaida a kan yin shahadar Jafaru.

 

  1. Malam Masa’udu baban Muhibbu da yaj jiya,


Shehena na a rannan ya ratsi Gadon k’aya,

Ya ce, ya kwan da mikin rashinsa a duniya,

Amma daga baya ya d’au tunani ya tsaya,

Wa ke k’yamar shahada kama da ta Jafaru.

 

  1. Laifinka guda wajen ja’irai kashe fariya,


Rok’on Umura kujerar zuwa Haji ka k’iya,

Rok’on mota bid’ar kwangila a yi jar miya,

Ka nisance su domin gudunka ga duniya,

Mai son wa’azi a amsa shi kwaikwayi Jafaru?

 

 

 

 

 

  1. Girman Malam tsarewar hukuncin Maiduka,


Bai shawagi a Ofis a ba shi abin daka,

Tsentseninai ka sa martabarsa ta d’aukaka,

‘Yan bangan malamai masu yawon raraka,

Su sunka yi k’ulle-k’ullen kashe muna Jafaru.

 

  1. Ramin k’arya dad’ai bai tsawo fad’i yakai,


K’arya kuwa ba ta ‘ya’ya fure d’ai ne takai,

Kashin ‘bera dad’ai ba shi taki ko tak’ai,

Kwaf fara hari ya san martani na nan a kai,

Wannan ita ce fahintarmu kan kashe Jafaru.

 

  1. An k’i fitowa a fili a ja mu a kan diga,


Wai sari-ka-nok’e ne an ka d’au ‘yan bindiga,

Ko kun manta ruwan rakke su ke yin suga,

Bambanta zuma da zak’in mad’i sai an d’iga,

Dad’in mutuwar shahada irin ta su Jafaru.

 

  1. Kwaf fara rutsi dad’ai bai da tausai mun sani,


In an masa martini ba a nuna idon sani,

Duk wada ta’b ‘baci tilas ya yo da-na-sani,

Ranar artabu duk ‘yan jihadi sun sani,

Fatar kowa shahada irin ta su Jafaru.

 

  1. Duk d’an Sunna macewa mazark’olarsa ce,


Kwanta kushewar shahada daren sallarsa ce,

K’undunbala a rutsa da shi nasararsa ce,

Yai ciniki an biya ransa to me za ka ce,

Fatarsa guda ya bud’e ido ga Jafaru.

 

  1. Fatar da nikai matasa ku kar’ba min kira,


Huce zukatanku na lalla’be ku ku hank’ura,

Kak ku yi rigima, da kowa, ku dai bi da hattara,

Ku bi tsarin nan na sunnan na rushe yaudara,

Tamkar yadda shahidin namu yai mata Jafaru.

 

 

 

 

  1. Kar ku sake gun karatu na sunna sarmadam,


Don ilmi shi ka fansan mutuncin d’an Adam,

Kamin mutuwa ta riske mu ko ta zo kwatsam!

Sai da karatu ake yin gumuzu ko rugum!

Ilmi shi ne dalilin kashe muna Jafaru.

 

  1. Ilmi ya fitar da shi an ka san shi a duniya,


Ya rik’a yad’a shi har d’alibainai sun iya,

Sun dahe Kano kwatancin Kaduna da Zariya,

Sun wa bidi’a kashin mummuk’e bisa anniya,

Raddin ‘ya’yanta shi ne shahadar Jafaru.

 

  1. Wauta ce babu shakka kashe muna maluma,


Don ko sun k’aura dukkan karatu sun gama,

Sun yaye dubai kwatancinsu sun zama maluma,

Yanzu jidalin ga ku kun ka sa yag gunguma,

Ba makawa dole ne nemo hak’k’in Jafaru.

 

  1. Kokenmu ga Shekarau kamo ‘yan jingar kisa,


Tilas a yi bincike ko ana tashi bisa,

Komai darajarsu komai kud’insu a fallasa,

Matuk’ar aka dak’ile to jidali na k’asa,

Don ba mu shiru da baki a kan kashe Jafaru.

 

  1. Ya zama tilas musulmi ya yarda da k’addara,


Amma ya yi hattara kar ya yarda da yaudara,

Sunna a wajen jihadi a murk’ushe kangara,

Shirmen bidi’a, da shirka, da ‘yan wasan dara,

Wuk’ar yankansu na can ga hannun Jafaru.

 

 

 

 

 

  1. Shirka har gobe sunanta shirka za a ce,


Ita ko bidi’a k’azamar aba nassi ya ce,

Komai kyawonsu dai babu lada an ka ce,

Wannan shi ne dalili na kawo ka-ce-na-ce,

Shi ne sanadi ga samun shahadar Jafaru.

 

  1. Masu ganin an gama yanzu ne aiki yake,


Mai yin noman ruwa dole ne ya yi tsallake,

In zabo yay yi k’afa da babban fiffike,

In shaho ya taho gun sa kaji kan fake,

‘Dan sak’o ne zuwa gun Khalifan Jafaru.

 

  1. Ba ma ja baya komai ake a yi mun k’iya,


Me za a yi wanda yak kai abin da a kai jiya?

Kwak kwashi adashi ranar zubi aka tambaya,

Ba wani uzuri garai sai zubi shi ne biya,

‘Dan sak’o ne ga ‘yan bindigan kashe Jafaru.

 

  1. Masu fad’ar ba a komai su saurara muna,


Wai su sun tara Naira da manyan kamfuna,

Komai na nan zuwa kar ku gaggauta muna,

Matuk’ar aka zo da ku duniya duka tas shina,

Rannan muka yin walimar shahadar Jafaru.

 

  1. Komai aka yi Talala Yana kule Ya sani,


Ranar gamuwa da shi ne nake muku tuntuni,

Zunubin hak’k’in kisan kai yakan zama d’an zani,

Don ba a haye sirad’i jahannama ke hani,

Sai hargowa da kuwwa a kai su ga Jafaru.

 

  1. Kowane mai rai hak’ik’an macewa za ya yi,


Kuma ba shakka da mun tai hisabi za a yi,

Komai ‘bannarka rannan bayani za a yi,

Ba uzuri ko guda gaskiya ce za a yi,

Rannan muka murmushin jawo hak’k’in Jafaru.

 

 

 

 

  1. Kaiconmu zumai mazajen Badar sun tsar muna,


Sun ka bi Allah da Manzo saboda tsare muna,

Addinin gaskiya kar ya zan ya raunana,

Sun zama dagatai na firdausi dogon zamuna,

Babban bak’on talakkansu shi ne Jafaru.

 

  1. Lallai a Uhud sahahadar sahabbai tai yawa,


Rannan ‘Dagutu sun kwan jahannama day yawa,

Manyan shuhada’u sai kabbara suka tassuwa,

Sun tafi da jini na artabu don shaidassuwa,

Haka an ka rufe muridinsu Malam Jafaru.

 

  1. Ko kura ta mace ba a sa ta a mangala,


Ta fi gaban bunsuru wa kare ya yi takala,

Jafaru gawarka kallonta na sa hamdala,

Ka hana shirka da ‘ya’yanta ta da mujadala,

‘Dan bidi’a ba ya wasan kiran ka muk’abala,

Ka wuce a yi ma dabara da Lugga Jafaru.

 

  1. In dai an jawo aya ina aka inma ka,


In an ka fito Hadisi ka datse mutum tsaka,

In an shiga Mazhaba nan kake yin sussuka,

Tauhidi ka yi suna wurin ga fatattaka,

Sunanka makamashin k’ona shirka Jafaru.

 

  1. Wani gomozo da kay yo a Borno da nij jiya,


Ka wa bidi’a kashin dankali na mazan jiya,

Shehenta zama guda kay yi mai d’iban k’aya,

Ka sa shi shiru da baki kamar bai duniya,

Ko ka mutu bai da sauran ta cewa Jafaru.

 

 

 

 

  1. Masu adawa Kano mun ji an ce sun taya,


Bayan ka sallama sun ka kasa kud’in biya,

Kunya ta rutsa da su sun ka tada hasumiya,

An ka yi gayyan muriddai da ‘yan bangan haya,

An ka yi jinga da su sun ka har’be Jafaru.

 

  1. Mai gina ramin mugunta nasiha zan maka,


Gina gajere da bai gagararka ga tsallaka,

K’arshen k’aik’ai mashek’a yake bi har d’aka,

In kun yi musun batuna ku tambi Amerika,

Yau ga Bagadaza nan ta zamo musu Satiru.

 

  1. Ba a kashe Malami d’alibansa su zan kurum,


Ba makawa dole ne za su kwana shirin kwaram,

Don mun ga Irak’i tun ran da an ka kashe Sadam,

Babu zaman lafiya kodayaushe cikin rugum!

Yau ba damar kirairn kashewar Antaru.

 

  1. Kwantar ka da lafiya jarumi namijin jiya,


Gogaggen malami ko’ina sha tambaya,

Ka hana bidi’a da ‘ya’yanta yin sharholiya,

Shirka da cikinta yad’ d’au ruwa sai bahaya,

Ta zama mushe gabanin shahadar Jafaru.

 

  1. Giwa ko an yi tarko ina yaka kam miki?


Ke furce kaho farautan kare bai kam miki,

Mai bindiga ya gaza mai baka kwanta haki,

Karnukkan fada tilas su kwan da bak’in ciki,

Ka tattake su sun ka sa motsi Jafaru.

 

  1. Kai ne manzon sahabbai wajen gwaggoriya,


Nan Hausa gare mu ka zan kamar ‘Danfodiyo,

Ka rarake Ghana, Nijar, Benin, har Saliyo,

Ka zama Abdalla Maigwandu goyon Fodiyo,

‘Daukaka sunna a k’arnin ga babu ya Jafaru?

 

 

 

 

  1. Ka hana k’arya da ilmi bale na walittaka,


Balle a la’be ga addini don a yi raraka,

Ba ka da d’an agaji odale mun san haka,

Yin tsentseninka shi ne ya ja maka d’aukaka,

Tamkar ba malami duk Kano sai Jafaru.

 

  1. Muddin salla cikin ginsik’ai ita ce a kai,


Ma’anar sujada wajen Jalla k’ask’antar da kai,

Jumu’a ce babba duk ranakunmu guda bakwai,

Sallar asuba kiyaye ta sai mai kama kai,

Na bar muku fassara kan shahadar Jafaru.

 

  1. Tsarin sha’aninka sunna ka sa gaba Juddadun,


Tafiya ba tak’ama ba a yin ta buzun-buzun,

Dukkan suturarka bakinsu k’wauro sarmadan,

Sunnar Manzo mijin Ai’isha kakan Hassan,

Ba ka yarda da katse gemu ba Malam Jafaru.

 

  1. Samun aljanna sai wanda yay yi muwafak’a,


Sai wanda ya kama sunan da k’arfi yar rik’a,

Yat tsarkake kansa gemunsa yab bar sassak’a,

Can ga ak’idarsa Tauhidu babu rak’a-rak’a,

Shi zai katarin shahada irin ta su Jafaru.

 

  1. Nai ta’aziyya ga du’atu dukkan duniya,


Nai ta’aziyya ga ‘yan raya sunnan duniya,

Nai ta’aziyya Kanawa da Bornu mazan jiya,

‘Yan salafiyya mu d’au hank’uri na gwagwarmaya,

Babbar nasaramu samun shahadar Jafaru.

 

 

 

 

 

  1. Kwantan da lafiya Hafizi da arangama,


Sannu da d’aukar burusai gwanin yin tarjama,

Barkanka da watse arna fitaccen alarama,

Koway yi fashin bak’i gun ka sai ya gunguma,

Tilas bidi’a da ‘ya’yanta ke k’in Jafaru.

 

  1. Sunnu da kwancin kushewa mazan jaruntaka,


Sannu da famar shahada cikin yarantaka,

Barka da hawa mataki na k’arin d’aukaka,

La shakka hak’ik’a mun shaida an cuta maka,

Amma a wajenka ta zan shahada Jafaru.

 

  1. Duk mai wa’azin da yas sam irin haka duniya,


To bai da bak’in ciki tun da yai gwaggwarmaya,

K’arshenai ya yi kyau ya yi sa’a duniya,

Barka! Madalla Malam da samun tazkiya,

Ingantaccen sahihin hadisi Jafaru.

 

  1. Rok’on da nikai Ta’ala ka kar’ba min kira,


Duk mai hannu cikin wanga aikin yaudara,

Rabbu azabtar da shi k’untata shi da takura,

Ranar tsayuwar hisabi hana mishi Kausara,

Sa shi a wailun ka gammai da kulkin Munkaru.

 

  1. Nan duniya Rabbana kar ka yalwanta musu,


Sa su a k’unci zaman lafiya ka hana musu,

Sa su yi kunya gidan duniyar ga a kan musu,

Aika hasara gida har dawa ta isam musu,

Kar ka ji tausan su ya Wahidun ya K’ahiru.

 

  1. Allah narkon azaba ka gaggauta musu,


Ta’bewar lahira shi muke rok’a musu,

Kask’ancin duniya mun ka so Ka saka musu,

Ranar tsayuwar hisabi hushinKa ya far musu,

K’arshensu ya zo da muni su tabbata fajiru.

 

 

 

 

  1. Mulkinsu ya zan hasara gare su da fallasa,


Kud’d’insu ya zan na K’aruna duk su nutse k’asa,

Ilminsu ya zan tukuicin shiga wuta can k’asa,

Su har zuri’arsu Allah Ka k’addaro nakkasasa,

Ta rufe su gaba da bayansu ba su da Nasiru.

 

  1. K’arshen zana muke son Ka sa su yi Ka iya,


K’arshen kifi muke addu’ar su yi duniya,

K’arshen fara garin Garki Halik’u Ka jiya,

K’arshen Fir’auna shi mun ka so su yi duniya,

Su zamo aya a kan awwalinsu da akhiru.

 

  1. Duk rahama gun Ka Allah su d’ebe an gama,


Duk wani sauk’i a gefenKa ya Kai mai sama,

Kar ya kusance su tun dak’ k’asansu zuwa sama,

Kawo fitinar da taf furce ridda su d’unguma,

Shaid’an ya saka su gaba da Annabi ‘Dahiru.

 

  1. ‘Ya’yansu su zan musiba gare su ta dawwama,


Matansu su zan dalilin shigar su Jahannama,

Dangi su zamo azaba gare su da tsangwama,

Birni har k’auye Allah raba su da lalama,

Jingarsu da sun ka kar’ba ta zam musu khasiru.

 

  1. Allah Ka zubo musiba gare su ta rarraba,


Bayan sun barkace sakad’a musu jarraba,

Sa musu cuta ta k’in ‘yan’uwa da ta haddaba,

Sa musu kircin zukuta ya iccen goruba,

Koyaushe suna cikin zalluminmu da Jafaru.

 

 

 

 

 

  1. Allah Ka hana su jink’an Ka kowace nahiya,


Sa su cikin damuwa ko’ina suke duniya,

Sa musu uzurin zurewa ga tarkon duniya,

‘Bad da dabara ta tuba gare su da anniya,

Har su yi da-na-sani can gamonsu da Munkaru.

 

  1. Sa musu jarabar tsiya kodayaushe cikin rashi,


Jingarsu da sun ka kar’ba gama su da ‘yan fashi,

Sa musu ciwon da tilas a hank’ura sai kashi,

K’arshensu ya zo da muni irin na su ‘yan fashi,

Ba wanka babu salla da tausan Ja’iru.

 

  1. Tammat nai hamdala kan kirarin Jafaru,


Jigon wak’armu tanzonku domin Jafaru,

In kun ji kure ku gaggauta gyara Ummaru,

Rok’on da nikai ga wak’ar ga in zama Nasiru,

In samu shiga cikin arzikin ga na Jafaru.

 

  1. Sunan mai tsara bege Aliyu Muhammadu,


Mai son rayar da Sunnar Nabiyu Muhammadu,

Mai k’aunar masu kishi ga sunna ba gudu,

Fatar da nikai ga ceton Nabiyu Muhammadu,

In samu shiga cikinai da Malam Jafaru.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments