Ticker

6/recent/ticker-posts

"Mutuwa" Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

www.amsoshi.com


Rok’o nika yi ga Wahidun mai gyarawa,

Sarkin da ya zarce masu ilmi ganewa,

Kai kay yi sama’u kay yi k’assan zaunawa,

Kay yo Aljanna kai wuta mai k’onarwa,

Kay yo duniya da rayuwa don zaunawa,

Kak’ k’addaro lahira ga k’arshen komawa,

Kowace rai la muhala k’arshenta macewa,

Tilas in ya mace k’asa zai komawa,

Tsoron mutuwa ga masu rai bai k’arewa,

Domin ba ta kure da ta zaka kamawa,

‘Bera bai ce wa mage sannu da hutawa,

In sun gamu hanya wa mutum sai rugawa,

Don me akuya ka ba da bai babu tsayawa?

In kura ta yi mui guda ba ta tsayawa.

Don me zaki ka watse taron Gardawa?

K’ato ko sun yi su dubu ba su tsayawa?

Don me zakara idan yana son carawa,

Yaj ji muzuru yana wurin bai motsawa?

Me ke sa d’an Adam gudun ba waigawa,

Kayansa su fad’i bai tsayawa d’aukawa?

In ka ga ango gudane ba sassautawa,

Ya wuce matarsa ba kula ba waigawa.

Ta lek’o ya gane ta ne yaka zuk’ewa.

Wai d’ammaninsa ko yana iya tserewa.

In ka ji ana ku gurgusa an k’i d’agawa,

In ta zo kan ka ce kwabo sai darewa,

Ba a kirari ta ba da fili na sakewa,

Shago da uban kid’insa yau ko motsawa

Da tauri na hana ta kamu da bugewa,

‘Dankurja da Dak’k’wahe suna iya tserewa.

Ba ta tayawa da ta taho ba fasawa

Muddin ta sauka an gama sai shurewa.

Ba ta kure gun da tan nufa sai dacewa,

In ta damk’a aradu ba a ku’bucewa.

Mai jinya kwance ko ruwa ba ya had’awa,

Ta d’auke majinyacinsa mai iya rugawa,

Wa ka iyawa? Ina maza masu gwadawa?

Mata sun hau dugadugai babu tsayawa,

In ka ishe ‘yan rawa kid’i na cashewa,

Dad’i aka ji ganin kamar ba a macewa,

In ta dako rida mai kid’in taka dahewa,

Masu rawa sai batun gudu babu tsayawa.

Tsuntsu a sama’u ta buga sai fad’owa,

Kifi a cikin tsakar ruwa sai tasowa,

Ke mai sa tagumi zugum babu mud’awa,

Mai sa murya ta kumbure sai shek’ewa.

Ba ki bugawa a mirmije don tserawa,

Kun fa yakuninki babu mai iya jurewa,

Mai sababin balbalin bala’in rud’arwa,

Mai tashin tashinan da zai hana cashewa.

Ya ke makasan maza da ke saba kashewa!

Ke ka kashi d’an Adam ruwanai yaka sawa.

Ya mai izo k’addara idan za ta isowa

Sai ta yi barazana ki kwakkwahe shed’awa.

Ya takwarar duniya ga d’auka da ajewa.

Sai ta d’auka ki mak’ure sai shurewa.

Yayin da ta yunk’ura da niya na ajewa.

Sai ki yi tarbon da ba maraba da kushewa.

Mai sa mutukabbari da d’anga rikicewa,

Mai ladabi babu rangwame babu ragawa.

Muminnai malamai sarakai fadawa,

Rumbace ne zama guda sai rugewa.

Masu fad’ar sun buwaya su taka murjewa

In ta buga rida ko guda bai tserewa.

Ta iske k’addara ta ce: “Ga mu tahowa”.

Sai ke kutsa mu samu daman lek’owa.

Ta ce: “Yar tsohuwa halinki da rud’arwa,

Ke ka ta’adinki la’bo ni aka shafawa”.

Ciwo yac ce wa k’addara. “Me kika cewa?

Ku ka ta’adi musabbabi ni aka cewa”.

An ka kira lafiya wurin sasantawa,

Tak kiri mutuwa da k’addara tattaunawa.

Laifinku guda gare ni shi za ni tunawa,

Shuka nika yi ku k’wazzabe ta ga tonewa.

Malam Boka da Likkitoci ka tahowa,

Don tanyo na zama ku ce ba su tsayawa.

Kun saba tarar da ni rik’is ba shiryawa,

Kamin in farga kun gama sai biznewa.

Ciwo ya ce wa lafiya: “Wa ka iyawa?

Mu da ka yin shekaru ana fafatawa.

In adadi zai wakana mu za a rutsewa,

Rai ya ji tsoro ya sud’ad’a sai tserewa”.

K’arshen taron baran-baran ba kintsawa,

An kasa hukunta inda laifi ka fitowa,

Laifin mutuwa bak’in jini aka farawa,

Ga mugun rai da k’eta ba sassastawa,

Ke ko laifinki k’addara son kutsawa,

Girshi ki fad’o wa rayuwa ba kintsawa.

Ciwo laifinka magani ba shi iyawa,

Ba ka da ranar shiga da loto na ficewa.

Ai zargin lafiya da tsoro da la’bewa.

Ciwo k’arami ta gangara tai ta cirawa.

Ke ko mutuwa zamanki k’arshen k’arewa.

Ba wani mai rai da ke bid’an ki ga ganawa.

Yara da manya maza da mata kokawa.

Mai ta’aziyya da masu tanzonko haba wa!

Mai marsiyya da alk’alam shika zanawa.

Ga ta muna yi ga Rabbana muka rok’awa,

Rok’onai gafara da jink’ai k’arawa,

Tammat Ali Bunza ne na birnin Kyangawa,

Babbar fadama da k’aramomin hutawa.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments