https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

NA


ADO MAGAJII MUSA


 


KUNDIN NEMA DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A K’ARK’ASHIN SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

BABI NA BIYAR


KAMMALAWA


5.1 Tak’aitawa


Hausawa kan ce “Komai nisan jifa k’asa zai fad’owa.” Wannan gaskiya ne. Wannnan shi ne k’arshen wannan bincike mai taken: Nazarin Littafin Dak’ik’a Talatin a bisa Ra’in Mazahabar Zahiranci.

An tak’aita wannan bincike ga rubutacccen adabi reshen wasan kwaikwayo kasancewar adabin Hausawa kandami ne wanda ya had’a abubuwa da yawa. Hakan ya sa aka tak’aita binciken a kan littafin “Dak’ik’a Talatin” na Ado Ahmed Gidan Dabino (MON).

An fara wannan aiki daa gabatarwa a inda aka kawo manufar bincike da mahallin bincike kana aka yi bayani kan bitar ayyuka, da suka gabata wad’anda suka shafi wannan aiki ta fannoni daban-daban. An duba hujjar ci gaba da bincike, an kuma tattauna a kan ra’in mazahabar zahiranci tare da manufofinta.

Sai a babi na biyu inda aka yi magana a kan tarihin Ado Ahmed Gidan Dabino da kuma bayanin irin gudunmawarsa a fagen adabin Hausa. Bugu da k’ari a babi na uku an ba da tak’aitaccen tarihin littafin Dak’ik’a Talatin da bayyana salon wannan littafi, kuma an yi bayanin jigon littafin na Dogaro-Da-Kai wanda ya had’a daa k’ananan jigogi na soyayya da kishi da kuma amana, tare da yin tsakure daga cikin littafin domin kafa hujja. Daga nan an yi magana a kan taurarin cikin wannan littafi wad’anda suka had’a da manyan taurari da k’anana tare da ambato fitacciyar tauraruwa da bayanin wad’ansu daga cikin taurarin.

Haka zalika a cikin babi na hud’u an yi bayani kan rayuwar zahiri a cikin littafin Dak’ik’a Talatin inda aka raba rayuwar zahiri ta cikin wannan littafi zuwa gida biyu:

  1. Masu faruwa na kyau

  2. Masu faruwa marasa kyau


Wad’anda suke faruwa masu kyau sun had’a da soyayya da amana da kuma tawakkali inda aka ba da ma’anar kowanne daga cikin wad’annan abubuwa ta yin bayani da tsakure da kuma k’arin sharhi a kai. Wad’anda suke faruwa marasa kyau kuma a wannan littafi sun had’a da:

  1. Kishi

  2. Hassada

  3. Gulma

  4. Zargi

  5. Ingiza-Mai-Kantu-Ruwa


Su ma wad’annan ba a yi k’asa a gwuiwa ba an ba da ma’anar kowannensu daga ciki kana an yi bayaninsu tare da yin tsakure da sharhi a kan kowanne d’aya daga cikinsu a littafin Dak’ik’a Talatin. A babi na k’arshe inda aka yi tak’aitawa da kuma zayyano manazarta.

 

 

Manazarta


 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/