Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Littafin Dakika Talatin A Bisa Ra’in Mazahabar Zahiranci (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

ADO MAGAJII MUSA

BABI NA HUDU

RAYUWAR ZAHIRI A CIKIN LITTAFIN “DAK’IK’A TALATIN”

4.0 Shimfid’a


Wannan babi ya yi magana ne a kan rayuwar zahiri a cikin littafin Dak’ik’a Talatin: Rayuwa ta zahiri ta kasu zuwa gida biyu: akwai masu faruwa na kyau kamar amana, tawakkali da kuma soyayya. Akwai kuma rayuwar zahiri masu faruwa marasa kyau, wad’anda suka had’a da kishi da hassada da kinibibi da zargi da ingiza-mai-kantu-ruwa da kuma tuhuma tare da ba da ma’anarsu. Daga k’arshe an yi nad’ewa.

4.1 Rayuwar Zahiri Masu Faruwa Na Kyau


Mazahabar zahiranci na kula da yadda abubuwa suke faruwa na rayuwar zahiri masu kyau domin samun kyakkyawan koyi na rayuwa ga sauran al’umma daban-daban. Don haka ne ma marubucin wannan littafi na Dak’ik’a Talatin ya yi k’ok’arin fito da abubuwan zahiri masu kyau da suka faru a cikin wannan littafi. Za a yi bayaninsu d’aya bayan d’aya a wannan babi. Wad’annan halayya masu kyau sun had’a da:

 

  1. Amana

  2. Soyayya  • Tawakkali


4.1.1 Amana

Ma’anar amana (K’amusun Hausa 2006:15) ya bayyana amana da cewa “Ba mutum ajiyar kaya ko wani abu yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya salwanta ba, ko wani abu ya ci ba; misali, ya ba abokinsa – dukiyarsa (yarda)”.

Saboda haka akwai jigon amana a wannan littafi na “Dak’ik’a Talatin”, kuma suna cikin abubuwa masu kyau na rayuwar zahiri da ke faruwa a wannan wasa. A cikin wannan wasa an ga yadda Aminu yake tarairayar Zannira saboda halin nuna amana ga abokinsa Yassar.

A shafi na 87 an ga inda Aminu ke nuna halin rik’e amana ga matar abokinsa Zannira. Ga misali:

Aminu: “To ba haka ne ba. Kin fi kowa sanin halin da Zannira ta shiga saboda rasuwar aminina Yassar, in ba a kula da ita ana kwantar mata da hankali ba a san wane hali za ta shiga ba”.

To a nan an ga yadda Aminu aminin marigayi Yassar ke k’ok’arin kwantar da hankalin Zannira saboda ka da ta shiga cikin damuwa na rashin Yassar. Wannan abu ne mai kyau yana faruwa a rayuwar zahiri.

Haka zalika a shafi na 53 Aminu yake tuntu’bar Zannira a kan karatu:

Aminu: “Kuma yaya maganar ci gaba da karantunki, yaushe ne?”

Zannira: “Ba rana balle wata”.

Aminu: “Ni kuwa ina ganin ya kamata a sa rana domin ya fi zama haka”.

Aminu a nan yake k’ok’arin inganta rayuwar Zannira matar Yassar, domin ta koma makaranta. Wannan abu ne mai kyau da amana ke sa a yi, kuma haka na faruwa a rayuwar zahiri a cikin wannan littafi na “Dak’ik’a Talatin”.

4.1.2 Tawakkali

K’amusun Hausa 2006, an nuna ma’anar tawakkali da “Dogara al’amari ga Allah”. A cikin wannan littafi akwai tawakkali. Zannira ta nuna halin tawakkali a inda Samira ta kad’eta da motar Sadiya domin ta hallaka ta, amma da saurayinta Yassar zai bincika don gano wadda ta kad’e ta, sai Zannira ta ce a k’yale ta tun da Allah ya tsare abin ya zo da sauk’i, sannan kuma a bar ta da Allah don kanta. Ga yadda Zannira take fad’a a shafi na (8):

Zannira: “Kawai ka rabu da ita tun da dai ban yi wani rauni da yawa ba, kuma ban mutu ba, ai shi ke nan, in kuma da ganganci ta yi, to ta Allah ba ta ta ba. kada ka tsaya ‘bata lokacin nemanta”.

Zannira buduwar Yassar ce wadda yake son aura, kuma ta nuna halin tawakkali a cikin wannan wasa, inda ta ce kar Yassar ya wahalar da kansa wajen neman wadda ta kad’e ta a mota, tun da Allah ya kiyaye. A nan Zannira ta nuna halin dogara ga Allah (tawakkali). A shafi na 9 Zannina ta k’ara fad’a

Zannira: “Ba komai, ka sani ko tsorata ta yi, ai ka san mu mata tsoro gare mu, k’ila shi ya sa ta gudu”.

To a nan an nuna halin tawakkali wanda a rayuwar zahiri yana faruwa kuma abu ne mai kyau, wanda ya kamata mutane su d’auka domin kawo zaman lafiya da junansu da kawar da zargi da mai da al’amurra ga Sarki mai duka (Allah).

4.1.3 Soyayya

Sa’id (1981) ya bayyana soyayya da cewa “So na nufin tsananin k’auna da kusanta ga mutum ko wani abu daban. Shi kuma so wata iska ce mai kad’awa wadda babu wani d’an Adam da bai shak’e ta ba. Tilas ne kowane mahaluk’i ya zama yana da d’abi’ar son wani abu a ransa, wanda galibi son nan yakan tsananta har ya kai in ba a sami abin nan ba zai iya fad’awa wani hali, ko kuma ya kasance ya sami abin, amma a hana shi saboda wasu dalilai.”

A wannan littafi akwai jigon soyayya. Soyayya na faruwa a rayuwa ta zahiri. Idan aka yi duba da zahirin gaskiya, za a ga yadda Yassar ke nuna wa budurwarsa so da k’auna na gaskiya, kuma a magana ta gaskiya irin wannan soyayyar ta zama kamar ruwan dare.  Duk inda aka zagaya a cikin al’ummar Hausawa za a samu irin wannan soyayyar. Dubi yadda Yassar yake fad’a wa abokinsa Habu a kan Zannira, a shafi na (2):

Yassar: “ Duk na san da su, amma babu wadda ta kwanta min a rai kamar ta, kuma ita nake so ba gudu ba ja da baya…”

A nan Yassar shi ne saurayin Zannira wanda yake nuna mata gaskiyar so da k’auna. Abokinsa Habu yake ganin bai dace ya so ko ya k’aunaci Zannira ba saboda kawai ita gurguwa ce, amma Yassar ya k’i ya domin son Zannira ya kama shi sosai tun da har karin magana yake saki “Abin son rai ne k’awa da makauniya.” Haka ma a shafi na (4) akwai inda Yassar yake zantawa da Samira a kan aurensa da Zannira. Ya ce:

Yassar: “Ba ta fi ki ba, amma kin san an ce abin a zuciya ne, zomo ya auri giwa”.

To a nan ma wannan gajeren bayani yana nuna yadda Yassar yake son Zannira  yadda abin ya kai cikin mutane har ta kai tsohuwar buduwarsa Samira take tuhumarsa a kan neman Zannira har ta kai tana gaya masa an yi fad’urwar tasa a rai-rai, amma hakan bai sa Yassar yin nadama ba a kan so da k’aunar da yake nuna wa Zannira.

4.2 Rayuwar Zahiri da ke Faruwa Marasa Kyau


Akwai abubuwa marasa kyau wad’anda ake son al’umma su nisanta saboda illar su, su wad’annan halayen kuma sukan faru a rayuwa ta yau da kullum. A nan an yi magana ne a kan kishi da hassada, da kinibibi da kuma ingiza-mai-kantu-ruwa da makamantansu. Wad’annan halayya marasa kyau sun had’a da:

  1. Kishi

  2. Hassada  • Kinibibi  1. Zargi

  2. Ingiza-mai-kantu-ruwa


4.2.1 Kishi

D’akin-Gari (2011) ya  bayyana kishi da cewa: “Shi ne irin k’iyayyar da ake samu a tsakanin mutane, musamman mata masu miji d’aya.”

K’amusun Hausa (2006) an kawo cewa: “ Rashin jituwa da nuna k’yashi irin wanda matan da ke auren mutum d’aya ke yi wa juna”.

Hausawa na cewa kishi kumallon mata. Kishi na daga cikin abin da yake na rayuwar zahiri da ya fito a cikin littafin “Dak’ik’a Talatin” Samira ta sami labarin saurayin da take so, zai auri Zannira, a inda ta kasa hak’uri sai da ta je wajen Yassar da kanta domin ta ji shin zai auri Zannira: Ga abin da Samira ke cewa a shafi na 3:

Samira: “(Ranta a ‘bace) k’warai ni ce da kaina ba sak’o ba. Na ji wani labari ne, shi ne na zo da kaina don in tabbatar da shi”.

A nan Samira ta fito ne a matsayin budurwar Yassar wadda take son sa da aure, amma sai ta ji shi kuma yana son Zannira. Hakan ya sa take yi wa saurayinta magana gatse-gatse domin nuna tsananin kishinta. A wani wuri Samira ta k’ara cewa:

Samira: “(Cikin nuna alamun tsiwa a fuskarta) amma kuwa an ji jiki, kuma an yi k’arkon kifi Wallahi. Ba ka kyautawa kanka ba”.

A wannan kalaman da Samira ta furta, tana nuna kishi a zahiri na auren da Yassar zai yi wa Zannira wanda take ganin bai dace ba, a matsayinsa na mai k’afa ya auri gurguwa, alhalin ga masu k’afa suna son sa, ba su samu ba. A zahiri wannan kishi ne da ya faru a cikin wannan wasan na Dak’ik’a Talatin, kuma yana faruwa a rayuwar zahiri.

4.2.2 Hassada

K’amusun Hausa (2006) an nuna hassada na nufin nuna damuwa ko bak’in ciki a kan wani abu wato ni’ima da Allah ya yi wa wani. Cikin irin abubuwan da wannan littafi na “Dak’ik’a Talatin” ya k’unsa ya had’a da hassada kuma ita ma tana faruwa a rayuwar zahiri kamar yadda ta faru a wannan littafi. Samira take wa Zannira hassadar auren da za ta yi da Yassar inda take ganin Zannira ba ta dace da auren Yassar ba. Hakan ya sa ta yi yunk’urin kashe ta, amma ina? Zakaran da Allah ya nufa da cara sai ya yi. Ga kalaman nuna hassada da Samira take fad’a a shafi na goma sha biyu (12):

Samira: “Don Allah rabu da ita in da za ta mutu ma ai haka nafi so, kin ga sai in samu ranata yadda nake so in yi shanya”.

To in ko haka ne, to a wannan littafi akwai hassada a cikinsa, kuma tana faruwa kai tsaye a cikin rayuwa ta zahiri kuma kishi shi ne silartasa ba abin da ba zai haddasawa da mai yin sa alheri ba.

4.2.3 Gulma

Gulma a cewar K’amusun Hausa (2006): “Maganganu da za su iya kawo rashin jituwa tsakanin wani da wani (kutunguila ko kutunka)”. Gulma. Shigi-da-fice, kitinka”.

A wannan littafin akwai inda ake yin gulma wanda a zahiri yana faruwa, kuma abu ne wanda yake kawo fad’a da tashin hankali, ba kuma abu ne mai kyau ba. Mutum a wurin yin gulma yakan fad’i har ma abin da ba a yi ba, domin labari ya yi dad’in fad’a. Da yawa abin da mutum yake yin gulma a kansa bai shafe shi ba, illa kawai yana son had’a husuma ce kawai. To a cikin wannan littafi Samira ta yi k’ok’arin had’a Aminu da budurwarsa Amina fad’a, inda suke yin maganar Zannira ta yi cikin shege ta lak’a wa Yassar a maimakon Aminu da yake tare da ita kodayaushe. Ga yadda suke fad’a a shafi na (76-77).

Samira: “Ashe kuma haka abu ya faru Zannira ta yi ciki?”

Samira: “Wane marigayin?”

Samira: “(Ta rik’e baki) ashe kema an yi kwana da ke, an ‘batar da ke?”

Amina: “Ban gane ba, an yi kwana an ‘batar da ni ba.”

Samira: “Wane ne ya fi kowa kusa da Zannira bayan rasuwar Yassar?”

To a nan idan mai karatu ya duba da kyau zai ga ana hira ne tsakanin Amina budurwar Aminu da kuma Samira wadda take son Yassar saurayin Zannira. A nan Samira na ta k’ok’arin gulma tsakaninsu domin ta yi wa Aminu k’azafi, kan cikin da Zannira take da shi, ita Samira tana zargin Aminu ne ya yiwa Zannira ciki ba Yassar ba.

4.2.4 Zargi

Zargi shi ne: “tuhumar mutum da wani laifi”.

Wannan littafi na Ado Ahmed Gidan Dabino akwai lamarin zargi a cikinsa tun daga lokacin da likita ya bayyana cewa Zannira tana da ciki na wata uku. To daga nan aka fara zargin Aminu abokinYassar da shi ne ya yi wa Zannira ciki ba mijinta ba wato Yassar. Samira na daga cikin wad’anda suka fi zargi da kuma Kawu Namata, wai saboda irin kusancin Aminu da Zannira, kuma zargi abu ne mara kyau, wanda yawanci al’umma na gudanar da shi, musamman idan mutum ya zo da wata sabuwar d’abi’a ko al’ada wadda ta sa’ba wa al’ummarsa. Ga abin da suke cewa a shafi na 78 da 81 da 90:

Samira: “An ke kin yarda da namiji ke nan? Lallai ganin kallon ruwa kwad’o zai yi miki k’afa”.

Amina: “Oh abu kamar wasa k’aramar magana ta zama babba. Ashe dai Samira ta fi ni gaskiya. Wannan sakewa ta yi…, kai amma Aminu ya ci amana har da ya aikata haka….

Kawu Namata: “(cikin ‘bacin rai) kai Aminu mai ya kai ka aikata wannan aika-aika? Maimakon kawai ku samu ku yi aure sai kawai ku ‘bige da aikata mugun abu? To yanzu mene ne amfanin hakan?”.

Zargi ya zama ruwan dare a al’umma, musamman in sun ga wani abu da ya sa’ba wa addininsu da kuma al’adunsu na yau da kullum. Zargi a zahiri abu ne maras kyau wanda ba ya barin wanda yake yin sa ya zauna lafiya a duk lokacin da ya ga wani abu sabo. Wannan shi ne abin da ya faru a kan Samira da Aminu da kuma Kawu Namata har ma suke zargin Aminu da shi ya yi wa Zannira ciki saboda irin ma’amala da ake gani a tsakaninsu.

4.2.5 Ingiza-Mai-Kantu-Ruwa

Ingiza-Mai-Kantu-Ruwa: Shi ne ziga wani da turashi ya aikata wani abu da zai yi da-na-sani a gaba. A littafin nan akwai ingiza-mai-kantu-ruwa (wato zuga) mutum, idan wani abu ya faru a maimakon a ba shi hak’uri a nuna k’addara ce. Wannan irin zuga tana faruwa ne a zahiri, kuma aba ce maras kyau. An fi yi wa mutane wawaye irin wannan ingiza-mai-kantu-ruwa: A wannan littafi an ga yadda Alawiyya ta yi k’ok’arin zuga Samira har ma take niyyar kashe Zannira kan sun had’a saurayi kawai. Haka kuma ita ma Samira ke k’ok’arin zuga Aminu har suna neman ‘batawa da Aminu da Zannira.   Ga abin da suke cewa a cikin shafi na (55-78)

Alawiyya: “E, amma lokacin da aka zalunce ka, an ce idan ba za ka iya hak’uri ba ka rama dai-dai yadda aka yi maka”.

To ka ga a nan maimakon Alawiyya ta ba Samira hak’uri a kan abin da ya faru ta d’auke shi a matsayin k’addara, sai k’ok’ari kawai take yi ta yi mata ingiza-mai-kantu-ruwa ta d’auki wani mummunan mataki kan Zannira. Hakan ya sa Samira ta kusa hallaka Zannira da motar k’awarta Sadiya.

Samira: “…kuma kin san gurgu yanzu k’wacen maza suke yi, tun da kin gani ta faru gare ki”.

Samira: “Af, gara da Allah ya nuna miki da idonki, yanzu sai ki san ta yi”.

Samira: “ In ma yak’in duniya na tara za a yi sai dai a yi. Ni lokacin da nake nawa yak’in ba cewa ku ke na k’i hak’uri ba? Kai har mahaukaciya ma kun ce min, don ana so a yi min k’wace na ce ban yarda ba. Da ma an ce yau…”.

Wannan shi ne irin ingiza-mai-kantu-ruwa da yake faruwa a cikin wannan littafi, kuma wannan abin yana faruwa a zahiri. Shi irin wannan ba abu ne na gaskiya ba. Kamata ya yi duk wanda mutum zai ba shawara to ya ba shi ta k’warai, ba hura wutar fitina ba.

4.3 Nad’ewa


A cikin wannan babi an tattauna a kan rayuwar zahiri a cikin littafin Dak’ik’a Talatin na Ado Ahmed Gidan Dabino, an kuma raba rayuwr zahiri zuwa gida biyu: rayuwar zahiri mai kyau da kuma rayuwar zahiri maras kyau.

Rayuwar zahiri mai kyau an yi magana ne a kan amana, tawakkali da kuma soyayya tare da kawo misalai daga cikin littafin don kafa hujjar abin da aka ambata.

Haka abin yake a rayuwar zahiri maras kyau, ita kuma an yi bayani a kan kishi da hassada da gulma da zargi da kuma ingiza-mai-kantu-ruwa. Duk wad’annan abubuwa ne marasa kyau wad’anda suka faru a cikin littafin “Dak’ik’a Talatin”, kuma suna faruwa a mu’amalar al’umma ta yau da kullum.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments