Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “wa” yawan baitocinta saba’in da ɗiya (71). An kammala ta ranar Larba 8/01/2014 a kan hanya tsakanin Katsina
zuwa Sakkwato. Burinta kakkaɓe ƙura ga ‘yan kurakuran da
suka gabata na rikicin ganin watan Ramala na shekarun 2012, 2013 da 2014. A
shari’armu, yaƙinin ganin wata ya kore kowane irin tawili. Ana dogara da yaƙinin gani a
kawar da maganar kowa, komai nauyinsa a sikelin zamaninsa. Idan ganin ido ƙuru-ƙuru ya tabbata
zancen kalanda da kwamfuta da hisabi ba su da gurbin zama in ji Manzon Allah
(SAW). Ƙaryata yaƙini domin sauraren umurnin wani ko wasu cin dugadugan Manzon Allah (SAW)
ne. Fatawa da tawili da ƙiyasi da duba zuwa ga al’adar ƙasa/jama’a na siyasar
shugabancinta duk ganin yaƙini ya haramtar da su. Dogara ga ganin ƙasa mai tsarki
ko kirdadon ibadojin da ake gudanarwa ciki na tsayuwar Arfa da yanka ba ya da
madogara ga littafin Allah da Hadisan ManzonSa (SAW). Kawar da kai ga yaƙinin ganin wata
a kan kowane irin dalili saki zari kama tozo ne. Annabi (SAW) bai ɓoye komai a saƙon manzancinsa ba. Da wane dalili za ka bar umurninsa ka
bi sabaninsa?
-------------------------------------
-------------------------------------
1. Na kiri
sarkin da shi kaɗai aka wa bauta,
Na yi
salati ya zamto tsanin adu’ata,
Duk
ahalil baiti ban rage ba ga tsarinta,
Na sa
ashabu ko guda kar ka musanta,
Haskensu ya barkace duhun da ka
cutarwa.
2. Allah Ya yo
samai ƙasai bisa tsarinSa,
Yai rana
Yai wata nujumu a gefensa,
Yaƙ ƙago gizagizai
suna shawaginsa,
Duk faɗin duniyarmu can ga hukuncinSa,
Ɗawafi taka yi da mu tutut babu tsayawa.
3. Aikin rana
ta rarrabe kwanukkanmu,
Don ga
ibada mu rarrabe lokuttanmu,
Taurari
an ka yo ƙawa ga sama’unmu,
Sannan
aka yo wata ya zan jagoranmu,
Kwanakkin shekaranmu nan muka ganewa.
4. Rana kwana
guda rawanta ka ƙarewa,
Taurari
ko cikin dare suka haskawa,
Hasken
rana gizagizai ke karyawa,
In sun
ishe jinjirin wata sai makewa,
Nan aka rigima ga lisafin tantancewa.
5. Sunan
farkon wata Hilalu ga littafai,
Wato ɗan jinjiri ga farkon dubi nai,
In ya yi
rabi ga kwanakinsa na ƙirganai,
Nan
sunanai Badar ga hasken zatinai,
Dan nan ya zamo Ƙamar Shahar gun ƙirgawa.
6. Kuwwar da
ake ga jinjiri don murnar sa,
Ga baki
hangahan ido na dubin sa,
Mata taɓi da yara na ta rawa gun sa,
Shi ne
aslain Hilalu can gun hilarsa,
An shiga sabon wata da fatar morewa.
7. Kwana
ashirin da goma su ne ƙolinsa,
In yai
ashirin da ukku sau ukku ƙidanSa,
Ya cika
sunna sahihiya ba a musunSa,
Nace
bisa lisafi ga farkon dubin sa,
Kowane adadi ka kai garai babu musawa.
8. In ka ga ya
hau ka sake duba hisabinka,
In ya
kasa ka ƙara bin lisafinka,
Gano
adadi ka bar kula da kalandarka,
Manta da
bugun ƙasa da ‘yar kwamfutarka,
Annabi (SAW) ne yai hani da furucin ƙyaccewa.
9. Nassi ya
ce, ganin ido shi ne zance,
Duk wani
ba shi ba anka hau an ragaice,
Kway yi
ibada da shi ku ce, ta lalace,
Ya shiga
saki zari dole ko zai dabirce,
Ya sake asali ya kama reshen rushewa.
10. In an ga
wata farin gani walkan ke nan,
Duk wasu
‘yan kame-kame an daina dan nan,
Ba
sauran jinkirin ibada das san nan,
Hujja ce
yanke dakata nan shi ke nan,
Duk wani uzuri gare ka nan za shi tuƙewa.
11. Shaida ga
tsayinsa adili ɗaya hujja ne,
Yardadde
kamili abin so ga mutane,
Mai
imani da gaskiya da aƙida ne,
In ya
ce, ya gani ga nassi hujja ne,
Sarki ya sanar da muminai ga hukuntarwa.
12. In su biyu
sun ka zo ga sarki shaidarwa,
Babu
sananne cikinsu kan tantancewa,
Ko
adalcinsu ya buwaya ga ganewa,
Nassi ya
ce Amiru na jinkintarwa,
Har wani shaidu ya samu don daidaitawa.
13. Tantance
adili yana can ga sarakai,
Haƙƙinsu su tanado
na sunna malammai,
Masu riƙon gaskiya na
Allah adillai,
Domin su
yi bincike na rarrabe adillai,
Kowace matsala ya zan suna gaba ga kulawa.
14. Ba a musun
adili ga shaidun shaidarwa,
Tabbata
zancensa wajibi ne kamawa,
Ba
hurumin dakata wa sarki ga sanarwa,
Ɗa’a sarki ka yi a nan ba ya musawa,
Shi zai jagora nan ga ɗauka da ajewa.
15. Ɗan bidi’a, fasiƙi da Kotiyo
shashasha,
Shaidunsu
ana gudun sa don aikin assha!
Don an ƙi batunsu don
suna aikata assha!
Ba su da
ikon su sha ruwa su yi mashasha,
Kamun bakinsu dole ne babu ragawa.
16. Wanda ya kai
kansa fada domin ya yi shaidu,
Ko aka
tura shi don ya je tabbata shaidu,
Sarki a
tufakkurinsa yas soke shaidu,
Ta
tabbata nana sai biɗan sabon shaidu,
Shaidan bai izgili ya sha ko farawa.
17. Wanda ya
shaide shi adili bisa ilminsa,
Yaj ji
bayaninsa fada gun iƙirarinsa,
Ɗaukar azumi yakai a nan ga hukuncinsa,
Ilmin
sarki daban saninsa daban gun sa,
Inkarin fada bai hana masa ɗaukawa.
18. Soke shaida
ga mai hukunci a kiyaye,
Rubba
yakan zo rashin sanin abu kai waye,
Ko ko siyasa
walau adawa ta iyaye,
Mai
dahuwa shi da masu banda da ‘yan soye,
Sirrin raɗaɗin wuta gashi suka iskewa.
19. Muddin ka
gan shi ka kiyaye da wata ne,
Ko kai ɗai kag gane shi taro na mutane,
Hujja ta
hau ka babu zancen kai wane?
Lura yaƙinin gani a komai
haujja ne,
Ba wata hujjar da ke gabansa ga shaidarwa.
20. Sai nassin Mustafiida
taro na mutane,
Masu
yawa ko’ina a birni zazzaune,
Sun ka
yi kuwwar hilalu hannu na nune,
Ko
labari a ko’ina yab bi birane,
Ba zancen bincike a nan sai ɗaukawa.
21. Ko da a
cikinsu adilai ga fasiƙƙai,
Ga
malammai ƙalilatan ga jahillai,
Ko
cunkoson da ba a rarrabe halinai,
Ba a buƙatar a kai su
zauren hakimmai,
Tanyonsu ciri a kai ga ɗauka da ajewa.
22. Zancen adadi
na Mustafida a kula shi,
In sun
kai ukku sun wadata a nassinshi,
Dan nan
kuma hat tawaatiri ga hukuncinshi,
Ba
hujjan shan ruwa da an ji jawabinshi,
An shiga Ramadhaana babu zancen kutsawa.
23. In gumma
alaikumu in irin haka ta auku,
Ƙauyenku gizagizai su mamaye sashenku,
Ba
sarari ko’ina sama’u a lungunku,
Nassi ya
ce ku ƙaddara ga ƙidayanku,
Don tabbata gaskiya ta ɗauka da ajewa.
24. Nassin ingumma
can wurin tawilinsa,
An yi
umurni da faƙdarun bisa nassinsa,
Nan
masana sun ka ce ana kirdadonsa,
In
babban girgije ya make gefensa,
Ƙaddartawa akai tsayinsa ga ƙirgawa.
25. Wansu mazaje
ganinsu ba haka nan ne ba,
Sun ce
masana fagen hisabi su yi kwamba,
Sai sun
rabe kainuwa da kifi bisa ɗamba,
Sun ce a
bi lisafinsu ba saɓo ne ba,
Muddin an kasa ittifaƙin ganowa.
26. Manyan mutaƙaddimina sun
soke batun nan,
An ga
hadisin hanin hisabi ga batun nan,
Zancen faƙdar lahu
ga kulkin nassin nan
Mujmal sunansa can Ussulu
a fannin nan,
Kurman nassi fashinsa nassi aka sa wa.
27. Manzo ya ce
ku ƙaddara ya yi talatin,
Wato ku
cike ƙida ku kuble shi talatin,
Shi ne
nassi mufassirun dakanta min,
Ya soke turaddudun
da ƙaulaani ɗaɗa min,
Babu khilaafun gare ta, ba ta da ruɗarwa.
28. Zancen a bi
shugaba ku gane bayaninsa,
Wato
babban Amiru koko waƙlinsa,
Alƙali ne gare ku
ko mufti kansa,
In an rikice
ga lisafi aka zo kansa,
Ƙaulin da ya tabbatas garai
aka komawa.
29. Hatta da
ganin mutum guda in ya yarda,
Ɗa’a aka yi garai a mai da ruwa randa,
Sunnarsa
ya ta da kat-ta-kwana da ‘yan sanda,
Ƙauye da birni a kai sanarwa da takarda,
Ta tabbata ba musu ga ɗauka da ajewa.
30. In sarki ɗai ya gan shi ba shaidu gunsa,
Kamun
bakinsa dole ne ga hukuncinsa,
Su ko
jama’ar gari su bar shi da aikinsa,
Ba ya da
nassin matsa wa ko da bawansa,
Nassi ne yanke Ummahaatu ka
nunawa.
31. Sarki ya
samu binciken shaidun baƙo,
Ko majahuli
da yat taho bayyana saƙo,
Koko Ibinis
sabili mai rataya ƙoƙo,
Tsoho
mai hurhurar gira zo dudduƙo,
Sarki na bincikarku don tantancewa.
32. Shaidu ba
rantsuwa yake ga bayani ba,
Ba zana
mai wata akai ya yi sharhi ba,
Ba
kwanakkin wata ake son ya faɗi ba,
Ba
mintocin ganin wata za ya faɗi ba,
Ba mu da nassin ƙididdigar ga ta ƙuƙewa.
33. Nassi bai ƙayyade wa
shaidu lotto ba,
Ko bayan
azzahar ya zo bai latti ba,
Kanun
baki akai da ranko Ɗanbaba,
Ga abu sahalan
a mai da shi babbar gaba,
An rarraba kawunanmu mun kasa haɗewa.
34. Ba wata
falala ga mai ganinsa a nassance,
Manzo
dai bai ganai ba mun gan shi rubuce,
Labari
an ka ba shi yak kuwa tantance,
Yay yi
umurni a kama baki a azunce,
Sunna sauƙi gare ta ba ta da kushewa.
35. Ku ‘yan sai
mun gani ku gyara fahintarku,
Hujjarku
guda ku ce kuna da ƙidayanku,
In
makuwa tas shigo shi wa zai fid da ku?
Wacce ko
an gani ku kama ƙidayanku?
Don Allah ‘yan’uwa mu zan sassautawa.
36. Kai ko mai
dargaza tsaya ji bayanina,
Uttazu
gaya wa ƙungiyarku ta bar ɓanna,
Soke
ganin adili gare mu bala’i na,
Kore
ganin mustafiida jawo fitina na,
An yi fito-na-fito da Manzon shiryawa.
37. Don sarki
bai gani ba ba a musun shaidu,
Ga Manzo
bai gani ba yaƙ ƙarfafa shaidu,
To wace
hujja gare ka kan ƙaryata shaidu?
Kun hana
sarki ya ji shi don ƙulla makidu,
Hurmin Ramadhaana kun ka kai mu ga ketawa.
38. Nassi bai
yarda an gani a ƙi ɗauka ba,
Bai ce
sarki ka ba da iznin ɗauka ba,
Bai ba
wata ƙungiya kafa ga hukunci ba,
Suumuu yac ce wa afɗiruu malam babba,
Muddin an gan shi an gama ba fasawa.
39. Ga wata
hikimar rashin sani can ga Nataro,
Wai mu
haɗe kanmu don mu ba maƙiya tsoro,
Ɗaukarmu a tare, gun ajewa mu bi taro,
Ba a ƙiyasi wurin da
nassi yai tooro,
Balle fatawa ta shisshigin ƙin ƙarawa.
40. Ban ga haɗin kai ga goge nassin sunna ba,
Ba wata
hikima na karkacewa shari’a ba,
Ban ga
karatu ga wanda yaƙ ƙi Hadisi ba,
Ni ban
ga barazana ga taron zunubi ba,
Son rai yat tarwatsa mu mun kasa kulawa.
41. Ɗan taron ƙungiyarmu ko na
ɗariƙarmu,
Bai ijma’in
da za shi kore farillarmu,
Mun
shaidi ganin wata da yara da manyanmu,
Sarkinmu
ya tabbatar ya yarda da ƙaulinmu,
Hujja ce babba shan ruwanmu da ɗaukawa.
42. Mai ce wa ba
a shan ruwa ba a ajewa,
Ba mu
hadisin da kag gani mai gansarwa,
Wanda ya
kore ganin yaƙini korewa,
Yac ce
Lamiɗo na da hujjar sokewa,
Ko da an gan shi ba a ɗauke da ajewa.
43. Mai fatawar ƙaryatar da taro
hanyanka,
Ɗan guntun bincikenka ne ke ruɗa ka,
Shaiɗan ya yaudare ka ya ci amanarka,
Ya kai
ka faɗa da gardama da Nabiyunka,
Ka bi hadisai kana ta faman sokewa.
44. Masu ganin
babu adili sai jama’arsu,
Sai wani
ɗan ƙungiyarsu ko na ɗariƙarsu,
Ko wani ɗan mazhabarsu mai bin son ransu,
Wanda ya
ce babu mumini sai danginsu,
Ya rufe ƙofar zama da shi tattaunawa.
45. An ga wata lokacin
Umar bisa mulkinai,
Bayan an
sha ruwa bayani yas mai,
An ka
gabatar da masu shaidu fadatai,
Bai ƙaryata kowane
ba can ga hukuncinai,
Ko mun fi Umar riƙo ga sunna da kulawa.
46. Baba Hadisin
Kuraibu babbar hujja ce,
Muddin
an gan shi lisafi ya lalace,
Shi aka
aiki da shi a bar sauran zance,
An kai ƙarshe, ganin yaƙini ne dace,
Modibbo da Maigari su huta da sanarwa.
47. Babbar hujja
ganin yaƙini na mutane,
Ko ƙittawan gira ya
ɓoye gun nune,
Muddin
an gan shi ba batun sake tunane,
Muminnan
ƙauye haa kazaa har na birane,
An hujjance su ba kalami na daɗawa.
48. In farali
yac cika walau ya zo ba ɗai,
Muddin
an gan shi lisafi ya zo bai ɗai,
Ya zama
raba gardama a miƙa wuya bai ɗai,
Wanda ya
ce ba a yi shi kawo hadisinai,
Wanda ya soke ganin yaƙini sokewa.
49. In an ga
wata ganin yaƙini na idanu,
Ya zama
hujja ga ‘yan Adam har aljannu,
Masu
walankeluwa da nassi ku bi sannu,
Ƙarya furta ta dole ne runtse idanu,
Bil’amu yau ko yana da rai wa ka kulawa?
50. Kore yaƙini ga malami
ya zan hauka,
Sake
karatun sani ka kyautata nahawunka,
Don ka
ga ana zuwa wurin tafsirinka,
‘Yan
banga na kururuwa ga bayaninka,
Sai ka ga ka furce malamai duka ganewa.
51. Don ka yi
zama Masar da Sudan ga karatu,
An kai
ka Madina don shahada ta rubutu,
Wai kai
a ganinka ka yi manyan makarantu,
Ko wai
zance ka ce ina yay yi karatu?
An koma cin ido da sunan koyarwa.
52. Mu a sama’un
garinmu Bunza Madinanmu,
Nan
Misirar Bunza ɗaukacin Sudaninmu,
Nan mun
ka ganai ƙuru-ƙuru a sama’unmu,
Mun ka
yi ɗa’a ga annabinmu abin son mu,
Mun ga yaƙini ƙiri-ƙiri ba mu sakewa.
53. In an ga
wata haƙiƙatan an shaida shi,
Duk wani
zance na Mazhaba sai a aje shi,
Babu ɗariƙar da za ta soke hukuncin shi,
Balle
wata ƙungiya ta ce ta kore shi,
In dai Allah ake nufi bisa shiryarwa.
54. A banzanta
ganin ido a bi shi a rafashe,
A ture
batun adilai a rungumi ‘yan tashe,
A
barkata nassi da falsafa ai ta hasashe,
A ɗau komfuta a bar hadisai tattarshe,
A ƙago kalandar ganin wata ai
ta bugawa.
55. A sa ƙattan kafirai
cikin addininmu,
Da ƙwarorin
jahilanmu don a ci irlinmu,
Da
malaman fada karnukan zamaninmu,
A ba su
na ƙosai su firgita mu su watse mu,
A ci muna fuska ƙiri-ƙiri babu ragawa.
56. Ganin Makka
daban ganin ƙasarmu daban ne shi,
Kaman
nisan Andolas Khurastani zubin shi,
Ga nassi
kowanmu zai tsaya ga ganin kanshi,
Bayanin
da Kuraibu yay yi in mun gane shi,
Ba za mu yi ɗa’a ga masu ƙaga kalanda ba.
57. Muna nan
rana kataa, a Makka ishaa’i ce,
Da
sallarmu da shan ruwanmu in ka tantance,
Akwai saɓani na lokaci a haƙiƙance,
A ce mu
haɗe duk mu zan guda an dabirce,
A mai da gabas yamma babu nassi na riƙawa.
58. Katafashen ɗalibi akwai shi da ban tausai,
Burakallin
malami takaici ka kashi nai,
Sakakken
mabiyi da hankali za a kira nai,
Zuma in
yai gardama wuta aka ruga mai,
Hayaƙi shi yi turnuƙu a huta da laɓewa.
59. Da kai nike
Rikitazu shugaban masu zaƙewa,
Na cin
irlin muminai da kai su ga kokawa,
Bala’in
ya kai ga limamai wa ka tsayawa?
A
tarwatsa mamu da ladanai babu kulawa,
A kan maagin cefane da naira ta
kashewa.
60. Bala’in ga
da kun ka ɓangalo rusheshe ne,
Jidalin
da ya takaro gudan tiƙeƙe ne,
Fasadin
da ya faru wa mutum! Jibgege ne,
Ta’adin
da ya yunƙuro gudan makeke ne,
Saboda tuwon alkama a kai mu ga
kokawa.
61. Da cin
zarafin muminai da ɓata aƙidarsu,
A
tozartasshe su haa ka zaa cin fuskarsu,
A ko
wofintar da su da cin zuƙuƙunsu,
Da safe
da maraice ƙunniya cin namansu,
Saboda yaƙinin ganin wata babu
musawa.
62. Idan sarki
bai ga ni ba bai ji bayani ba,
Da yai
cigiya har shigan dare ba a dace ba,
Ba zai
zama hujja ta ƙulle ƙofar shaida ba,
Haƙiƙan yanayin ƙasa guda ba ɗai ne ba,
Fa ba makawa dole jinkirin saurarawa.
63. Shaidu ko da
da rana yaz zo da bayani,
Sunna ta
ce a dole ne ba shi sukuni,
In an ka
ji gaskiya ana sake tunani,
Ba a
damo gungurum na manyan dodanni,
Ga addini ba a soka son rai da suƙewa.
64. A sa addini
zama siyasar saɓi-zarce,
Da
Pidipi ta shigo shi duk ya lalace,
Da
fadanci ya rufe shi duk an dabirce,
Da an
tsoma kwaɗai cikinsa duk an sagarce,
Ana haɗa mabiya faɗa buƙatar holewa.
65. Salon sa
sarki cikin batun ga akwai zamba,
Fa ba
don an so shi an ka sa shi ga aikin ba,
Ga
masalatai muna ta yi bai shaida ba,
Yau mun
ga wutar gashinmu tun ba mu shirya ba,
Mun dudduƙo mu samu hanyar tserewa!
66. Mu ka kiran
duniya ta kawo hujjarta,
Da
nassin aya walau hadisi a kwatanta,
Su koma
‘yan baya gaskiya sun ture ta,
Don kwaɗayin duniya su mara wa macuta,
Ana ta kashin ‘yan uwansu ba mai cetarwa.
67. Uttazu kiro
muƙaddami bari suka tai,
Haba ɗan gargajiya tsaya bari suruttai,
Da
Modibbo na unguwa a soro malammai,
Fa Shaiɗan ya ci mu ya kamata mu bore mai,
Dole haɗin kanmu lokaci na ta wucewa.
68. Masu ɗariƙa da ‘yan Izala hayyanku,
Ga maƙiya can suna
hararar lunguku,
Kun zama
kifi kuna ta cin kanku da kanku,
Kun zama
BOKO HARAM ga masu ƙiyayyarku,
Safe da maraice sai kashi sai ɗaurewa.
69. Wai kai
kurinka tun da ka bi ɗarikarka,
Kai ka
doronka ƙungiyarka ka ruɗa ka,
Ko tinƙaho da mazhaba
ga aƙidarka,
Ga maƙiya sun yi ƙungiya sun sha
toka,
Ku da ƙasashenku sai kisa sai korewa.
70. Hadda
siyasar ga makira an ɗebe ku,
Duk wani
aikin tsaron ƙasa an fid da ku,
Kun zama
almajirai ga baital malinku,
An
gayyato duniya a taru a watse ku,
Kun kasa tufakkarin dubaru na riƙawa.
71. Allah cece
mu kuk ka dubi dabararmu,
Mun san
in don halinmu sai mun ci bonenmu,
Ali
Muhamman na Bunza ne mai waƙarmu,
Jikan
Inta Imamu mai auren Danmu,
Dogo angon Gadaje manyan koyarwa.
Aliyu M. Bunza
Umaru Musa ‘Yar’Adua
University,
Katsina
8/01/2014 Larba
Daga Katsina zuwa Sakkwato
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.