https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

 1. Ni kiri Rabbana Jalla mai iko sarkin sarauta duka,


Sarkin nan da yay yo dare rana sammai da k’assai duka,

Wanda Ya k’addaro rayuwa mutuwa ikonSa ce Maiduka,

Ba makawa ga bayi kiranKa buwayayye gwanin d’aukaka,

Mai ilmin da ya kewaye komai da saninSa yat tabbata.

 

 1. Nasa sani gwani fil azal yake komai ba ya ‘boye Masa,


Babu kure bale mantuwa wane wahami ya riskan masa,

Shi yat tsara kaiNai da ilmiNai haka mun ka iske masa,

Ba ma shisshigin binciken ilminKa da istiwa’i bisa,

‘Dan ilminmu bai kai ba, in mun ce mu yi, nan yake barkata.

 

 1. Don haka mumini ba ya d’anga ba ya bugun gaban ya sani,


Taka sannu Modibbo, hayya da cewa: “wane mi yas sani”,

Allah Ya fad’a ba sani tari a cikinmu sai k’ank’ani,

Wanda ka tak’aman ya iya k’arshe sai ya yi da na sani,

Bil’amu yak karantar da mu masani duka bai wuce karkata.

 

 1. Don haka masu gori da imani sai su yi hattara sun jiya,


Shirya na ga Allah, ‘bata Shaid’an ka iza ka ko k’iya,

Nemi tsari wajen Rabbana manta da bugun gaban na iya,

Bawa bai da k’arfi wajen shiriyarsa a daina yin fariya,

Babu gwani ga Shaid’an dad’ai zuciya sha’awa yake sa mata.

 

 1. Mai neman sani don ya tara kud’i bai san da sirrinsa ba,


Mai neman sa domin ya burge bai amfana samun sa ba,

Mai neman sa domin ya kushe waninsa ba zai muruwasa ba,

Amfani da shi don a gyara miya a yi k’ulk’ule bai yi ba,

Ya zama ci-da-ceto da son girma tak’awa a cuta mata.

 

 1. Yin k’arya da shi don a san girman k’arshensa yin raraka,


K’in tashi bid’a don ganin ka tara sani ka cuta maka,

Amfani da shi don a kutsa fada a samu tsabar daka,

Sa rawanin sani don ka ja tawagar jama’a su mara maka,

Ba a ta’ba yi a more ba, tambola ce kar ka fad’a mata.

 1. Muddin zuciya na karanto ma ilminka ya gunguma,


Ka d’aure gafakka karatu ta ce, ka riga ka gama,

Ta jefa ka tarkon husuma ka zan mallamin gardama,

Kwa’ iya fassara duniya sai ka yo taka ‘yar tarjama,

Duk fatawar da ba taka ce ba, a dole ka ce a sa’ba mata.

 

 1. Kar ka hukunta wai d’alibinka ba zai taso ya furce ka ba,


Ko fanni kaza, wane ba ya fad’i ban goge k’aulinsa ba,

Ni da na yo karatu Masar lugga ba a kai ni gane ta,

Balle ni da nay yo Madina hadisai ban yi k’amfar su ba,

An koma kirari, shari’a tun tuni an ka sa’ba mata.

 

 1. Masu bid’an sani don a sa su sahun masana ka sheda masu,


Shi ke mai da Uttazu gojirgo goga kwamandan musu,

Sai raba kan musulmi su lalace mak’iya su, auka musu,

To don ka zamo mallami da wace sunna ka ceta musu,

Tauhidi ya koma sana’a, Tafsiri ya koma shata.

 

 1. Girman kai ka rushe sani Malam saurari d’an nan kira,


Mai jin kai karatunsa bai tasiri duniya lahira,

Mai kurin tsananta wa bayi Shaid’an na ganinai sara,

Malaman ga su ukku kowane na fama da ciwon mura,

K’irji ya rufe babu numfashi sun kasa gane mata.

 

 1. Malam mai farautar kurakurran takwara ya auka masa,


Duk ilmin ya koma na cin zarafi da tu’annuti fallasa,

K’arshen duniya ga sani tari amma ya zan nakkasa,

Ga ni’ima ta Allah tana sauka an kasa gode Masa,

In aka sallad’o ‘yar azaba sai a tarar da mun jikkita.

 

 

 

 1. Ban tausai ga Malam idan Shaid’an ya sa shi ‘boye sani,


Wai shi kar a gane karatu, kowa kar a ce, ya sani,

Kai ku ji d’anga-d’anga, a sa ka cikin haraka, ta zan d’an zani,

Hasken Rabbana ne, ka dubi fitan rana ga tsarin yini,

Wa ka hana ta lek’o gidan wani, in haskenta ya karkata?

 

 1. Cewa na fi kowa sanin abu, kun ji musabbabin hasada,


Ran da waninka yay yo fice k’irjinka ya kwana k’ugin cid’a,

Babu zama, tsayi, ka ji an ce, Malam wane ne kan gada,

Wai kai ba ka yarda a san wani, don kai an ka shaida a da,

Ilmi bai da Malam da zai cewa, a wurinsa zai tabbata.

 

 1. Ilmin rena ilmi musiba ne abu sai ya koma fad’a,


Don an fi ka aiki da sunna kullun tsegumi sai rad’a,

Ka ga ana fahimtar samarin ilmi, sai ka kushe dad’a,

Ga nassi a kulkin hadisi kai ko sai ka sa tambad’a,

Wai kai dole sai an ishe ka gida fatawa take tabbata.

 

 1. Mai da fagen karatu sarauta shi ke kawo ka-ce-na-ce,


Sannu abin ya koma na fadanci sunna ya zan ta ‘bace,

Sai hasken karatu ya lalace a wurin bid’an zak’k’ace,

Yarjejeniyar kai ga samu nan tak’awarmu duk ta’b ‘bace,

In da kwad’ai ya zauna zukata, sunna dole kauce mata.

 

 1. Alfaharin yawan d’alibai da magoya baya ya zan ba’a,


Ko wata k’ungiya ko d’arik’a, yau mun furce wannan sa’a,

Duk mu had’e a sunna wuri d’aya shi ya fi kyau mu zan addu’a,

Watsewarmu d’aid’ai hak’ik’a alama ce ta k’arshen sa’a,

Ka da mu bari k’iyama ta cin muna rarrabe ce kakai kwarkwarta.

 

 1. Ce-mini-ce-minin malami, ke sa mabiya su watse masa,


K’orafe-k’orafen d’alibai ke sa malam a rena masa,

K’yashi ke kashe malami d’alibbainai su watse masa,

Mai da wurin karatu dabar tsince abu ya zamo kwarkwasa,

Sai tak’awa ta k’are ga baki ga’b’bai sun k’arba mata.

 

 

 1. Malam mai kwatancin karatunai da ma’ilmatan duniya,


Mai sukan Salaf don ganin mabiyanai na fad’an ya iya,

In ga hankali, wanda anka yi yau, bai rena aikin jiya,

Albarka ga k’arnin gabaci, nassi yaf fad’ai, mun jiya,

Duk rigima ta sukan gabaci, sharri ce a kauce mata.

 

 1. Ilmi ba azanci ba ne, makarinsa a je a bauta masa,


Wayo bai karatu a je makaranta can a iske masa,

Babu salo wajen gane nassi sai an hau shi an imasa,

Wanda ya san sahihin karatu burga ba ta rud’i nasa,

Duk nahawun da’ifin bayani bai rud’a shi bai firgita.

 

 1. Ilmi bai buk’atar shahadar kwali tambayo maluma,


Don tak’awa da ilmi gidansu guda ba sa zaman gardama,

Amfanin karatu khushu’i tsoron Rabbana mai sama,

Dole a yarda sunna ta zan jagora idan ana tarjama,

Duk hidimar ibadar da taw wuce sunna ta zamo barkata.

 

 1. Ba a kiran ‘batacce da tsauri ko ya kangare ya k’i ji,


Sa hikima a kai, ba shi girma, Mallam ko a ce Alhaji,

Lallashi a kai har ya ankara don ya tsaya cikin masu ji,

In aka tsaurara mai ya kafurce, an sa shi mugun aji,

Laifi na ga Uttazu shi da ya darkako shi yaf firgita.

 

 1. Yaushe sani ya koma asusun yin giba da yin takara,


‘Dalibban sani ba had’in kai, an shiga ukku an takura,

Wanga ya warware, wanga na tunk’a, mabiya tara in tara,

Ko Shaid’an idan zai yi adalci ya san akwai yaudara,

Mai da’awa ya dabirta masu biyansa su zan cikin k’untata.

 

 

 1. Yaushe sani ya koma dabarar ba mu kud’i mu gyara maka?


Masu kaba’ira su da d’aguttai sun ba ka, ka sa baka,

Kullum ba a nan, ba a can, baki sake dole kad’a maka,

Fassik’k’ai suna isgili, “Uttazawa mazan raraka”,

K’asumbar bara ba ta sunna ce ba, ku je ku yo binkita.

 

 1. Malammai na sunna k’azanta ba su bari ta riskar musu,


Ba a kwaso k’armamuwa a ishe su gida a mik’a musu,

Kutsawa cikin ‘yan kashe-mu-raba na sa a rena musu,

Yau su fad’a a ce, ba a yi, fatawarsu gabansu za ai musu,

K’arshen lokaci al’amurra ne sun soma yin jirkita.

 

 1. Cewa mallami bai shiga wuta, zance ne a kan kuskure,


Me ka hanawa mallam shiga Lazza in ya k’i gyaran kure?

Ilmi ba ya ceto ga mai gangancin isgilin kuskure,

Dole hawan sirad’i ayukkan kowa Rabbana zai k’ure,

Wanda ya je da shirka Jahannama za a kira a mik’a mata.

 

 1. Rena sani da kushe ma’ilmanta ba a saba more shi ba,


Yin k’azafi, jafa’i ga mallammai a yi hattara ‘yan daba!

Muzantar da ilmi da muminnai ba a saba k’yale shi ba,

K’arshen isgili nakkasa da bala’i babu kyaun ak’iba,

Nuhu da an ka wa shi ruwa aka sa suka mai da arna gata.

 

 1. Mai da sani makami na cin zarafin wasu ba dabara ba ce,


Mai da fashin bak’i zage-zage hak’ik’an hankali ya ‘bace,

Sa mabiya k’iyayya da yak’i ba shiriya ta sunna ba ce,

Shi ke sa matasa ta’addanci don hankali ya ‘bace,

An ka mayar da su cefanen shehunnai ka ji babbar ‘bata.

 

 1. Kaicon malamai masu raya ta’addanci cikin al’umma,


A yi hud’uba muridai su gigice su husata sai d’unguma,

Kan k’aramar fahinta maras tushe k’ura ta musk’e sama,

A yi gayyar muridai a ba su makamai don kashe maluma,

An yi Kano da Zazzau da Sakkwato ba a gudu a tsere mata.

 

 

 1. In Ustazu yag gane cin banza tak’awa ka kubce masa,


Ba ya mutunta sunna wajen d’agutu idan ana ‘yanmasa,

Shi ake tuntu’ba don a bud’e wuta ga wad’anda ke ja masa,

Ai ta kashe musulmi da hannunai Uttazu an nakkasa,

K’arshen k’aik’ayi masu shik’a za ya lak’e kamar kwarkwata.

 

 1. Son a sani ka sa mallami limancin masu cuta muna,


Kun raba kanmu kun sa ido sojoji na ta cuta muna,

Kun koma gidajenku in an kanmuna ba ku ceta muna,

Yanzu k’iri-k’iri za a bin mu ana yanka kamar raguna,

Masu kashinmu sun ba ku jinga kun maishe mu motar shata.

 

 1. Mugun mallami bai da kunya bai tausai wajen danfara,


Bai shakka wajen cin amana bai k’yama ga yin yaudara,

Muddin ya fasa ya ga mask’i ko Shaid’an yana gagara,

Sun yi yawa k’asashenmu shi yas sa shari’armu tag faskara,

Ga su cikinmu kullum dasisa al’amarinmu na karkata.

 

 1. Shehu Mujaddadi ya kira su uban falale cikin k’orama,


Ka ga k’adangare in ya hau tulu kama shi sai an k’wama,

In an d’auko sanda, a ce a buge, biyu babu ce an gama,

In an bar shi, su ko ruwan tulu sun ‘baci, ba gardama,

Kun ji bak’ar musibar zama da miyagun malamai kwarkwata.

 

 1. Yaya za a gane su? Farko sun fi kare kwad’ai awwalan,


Rowa ko Juhaa, ka ji babbar siffa nan rik’e saniyan,

Son banza, afafa, kamar a yi sata, da’iman salisan,

Son dad’i a hole ana ta bushaha khaliyan rabi’un,

Muddin sun ga samu aje sunna suka yi su sa’ba mata.

 

 

 

 

 1. Komi an ka shirya da su, in dai ba su d’au rabo babba ba,


Saurara da kyau, ba a k’arewa ba su fara sukar sa ba,

Muddin kag ga sun kame baki to ba su gane sirrinsa ba,

Ba shi had’e kwad’ai, ba shi jin kunya, in bai ga k’unshinsa ba,

Bai k’oshi wajen ka da girma sai mabiyansa ke kunyata.

 

 1. Yau haka zamani yak kasance ga gaba baya ta nakkasa,


Masu kira a so Rabbana su za su taho su sa’ba masa,

Su ke taimakon fajiri mai imani su cuta masa,

Ba su shiri da mai gargad’ar d’agutu ya sa a sa’ba masa,

Sun fi da son walankeluwa maganar sunna a sa’ba mata.

 

 1. Wai yau malamai had da ‘yan banga harakar ga ta hurhura,


A yi kuwwa ana kabbarori kan mallam yana kumbura,

Sai ai mai kirari ya hau karagar wa’azi yana bank’ara,

Ga d’an agaji baya ga alaramma a hau ana tunzura,

Ba zancen tawali’u, ko tak’awa an fara kauce mata.

 

 1. Bar-ni-da-mugu in yai ruwa aka matse ‘bata fuska yaki,


Maruru ga dattijo ba ya fad’in gehen da shegen yake,

Ita k’azuwa bala’in ta k’aik’ai susa har cikin mummuk’e,

Kun ji rutsin da Nijeriya taj jefa Arewa duk mun suk’e,

Barno, Kano, k’asar Yobe, Bauchi, Abuja yanzu sun jirkita.

 

 1. Malamman da ke agajin mak’iya ba za mu k’yale su ba,


Cin zarafi k’azuffa da ‘bannan suna ban mu yafe su ba,

Bambancin fahimta ba zai zama hujja keta haddinmu ba,

Yanzu a ce musulmi k’asarsa ba zai kare ak’idarsa ba,

Dole aje ak’ida nagartatta ‘banna a auka mata.

 

 1. Ga mu muna tumulli da jahilci malam ya k’ara muna,


Babu k’awa ta gemu na sunna yau rawani kamar an hana,

An hana tsangaya ba karatun zaure ba batun alluna,

An harbe matasanmu an bar tsofaffi cikin d’akuna,

Ba mai ta da murya a ba maganarsa gari a duba mata.

 

 

 1. Mun san lokaci ya taho k’arshe wada anka sheda muna,


Komi’b ‘baci gyaransa na da wuya haka anka nuna muna,

Domin masu gyaran da su aka ‘bata abin da yan munana,

Tun da haki ya cinye awaki yuk’a tah had’e raguna,

Jahillai su ja jahilai shara’a tilas a cuta mata.

 

 1. Rok’ona Ta’ala Ya gafarce ni da ni da ku maluma,


Ba shakka musibun ga yau kowa ya shaidi sun gunguma,

Ni dai shawata mu tuba gaba d’ai ba batun gardama,

Ali na Bunza na Sallama Mallam Uttazu sai an jima,

Rabbu Ya ba mu Ikon rik’on sunna bidi’a mu kauce mata.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/