Ticker

6/recent/ticker-posts

Kashi Ya Game An Sake Rabawa



Waƙar mallama ce (ƙwar biyar). Babban amsa amonta “ba”. Yawan baitocinta saba’in da uku (73). An kammala ta ranar Jumu’a 19/05/2013 a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina. Saƙonta gargaɗi ne ga ma’abota riƙo da kira zuwa ga sunnar Manzo (SAW) da su gyara zama ciyawa ta ci doki. Abubuwan da aka kora a da, a yanzu ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Idan maƙoƙo ya fito a bakin zabiya zancen waƙa da zaƙin murya ya ƙare. Ina laifin wanda ya gaya maka bakinka na wari ka nemi ruwa da asawaki ka wanke ɗoyin ya kawa! Matuƙar imani na ƙaruwa da raguwa, to, namu ya ragu. Allah Ya cece mu.
--------------------------
----------------------------

1.               Ya maji kukan talikai idan sun ka kira,
Ya maceci ga waɗanda ke a tarkon mahara,
Babu tankar Ka samai ƙassai bale ai takwara,
Mai masu ga kaɗaitarKa zai yi ƙarshen masara,
          Tun da nassi ya ce, ba za a yahe masa ba.

2.               Na biyo da salati ga Ɗaha manzon ƙarshe,
Shugaban bayi ka wuce yabo da tafashe,
Mun ji Albuusiri da Zaazi sun yi hasashe,
Ɗanmuhibbu da Hassanu sun zuba shi a tarshe,
          Ko hakin susa ban aminta su bar muna ba.

3.               Gaskiyarka a fili ta zo ga bakin maƙiya,
Hanƙurinka da ƙwazonka mun ga nai gun mabiya,
Kai ka zo da shari’ar da dukiya ba ta saya,
Kai ka zo da tafarkin da wanda duk yaƙ ƙi biya,
          Ran hisabi ba za ya sha ruwan Kausara ba.

4.               Nai yabo ga sahabbanka ginshiƙan al’amari,
Masu ƙwazo masanan da ba su yin alfahari,
Babu tsoro ba fargaba mazajen katari,
Jarumai managartan da an ka ba Makka gari,
          Lata Uzza da Manata har Hubal ba a ga su ba.

5.               Tabi’ai yardaddun da ba su baddala saƙo,
Sun wuce fadanci na yada kai a yi roƙo,
Sun wuce zone, sa ido, a ce musu miƙo,
Ba a ruɗinsu da dukiya a ce musu: “Sheƙo”,
          Kan talauci ba su yarda shan wulaƙanci ba.

6.               Masu bin Sunna kun ji ‘yan’uwa magabata,
Masu ƙaunar Manzo mahimmata managarta,
Masu bin Sunna tantagarya tsabagenta,
Babu ja baya da zurfafa suna tsakiyarta,
          Ba su ɗa’a ga abin da bai zamo Sunna ba.

7.               Ba su leƙen sirrin waninsu ba sa tsince,
Ba su giba, da raɗa, da tsegumi, gun zance,
Ba su yin ƙiri-faɗi ko da ɗai sukan tantance,
Ba su yawo da batun da yaz zamo zaurance,
          Ba su muzanta mutum saboda bai gane ba.

8.               Ba su ƙaunar kunya ga kansu ko ga kininsu,
Babu cin fuska ko daɗai cikin tsarinsu,
Ba su fuska biyu ko’ina cikin hulɗarsu,
Ba su turke mutum ko ƙure shi don ilminsu,
          Kaffa-kaffa sukai kibriya’u bai kan musu ba.

9.               Shi fa ɗan Sunna ba shi hasadar samunka,
Ba shi kushe ka saboda ɗaukakar darajarka,
Ba shi ƙulla maka diddigi na gane cikinka,
In ya ja, kaj ja, zai sake ya ce maka jeka,
          Ban jidali da abin da bai zamo shari’a ba.

10. Ba ka tsintansa a dandali zaman kashe wando,
Bai zama kifin rijiya kwatancin gwando,
Ba su dogon hannu bale a ce musu maido,
Ba kasala, ga gatari, da kwasa, Kwando,
          Ka ji Sunnar ashaabu ba jiran sadaka ba.

11. Duk karatunsu nufinsu kai ga tsira gobe,
Ba su ba ka sani, sun ga ka ƙware, su yi zobe,
Ba su ɓoye sani ko hana ka kai ga gurabe,
Duk bayaninsu sukan tsaya su feɗe ababe,
          Yadda za a fahince shi ba da muzanta ba.

12. Gun amanar Ilmi ba za su ha'inci ba,
Ba su tura fahintarsu don ta zan hujja ba,
Ba su sakaɗa zancensu don ya zan nassi ba,
Ba su zance domin a gane sun burge ba,
Taka-tsantsan suka yi gudun siraɗi a gaba.

13. Manhajar Sunna ga ta ɗan'uwa ka kiyaye,
Alkitabu da Sunna ka zan riƙo kai waye,
Fassara magabata Salaf a bar wani tsaye,
Babu ɗa'a ga wanin Rasulu ko shi waye,
In bayanin bai hau ga mazhabin Sunna ba.

14. Malamin Sunna mazhabarsa nassin manzo,
Bai aƙida akasin Salaf mazajen ƙwazo,
Bai ƙawancen wata ƙungiya ta zan zo-zo-zo,
Ita da nassin wahayi ya bar hadisin manzo,
Me ya raunana ƙarfinmu yanzu in ba haka ba?

15. Malamin Sunna bai zama faɗa da Hadisai,
Bai barin magabata shi ƙirƙiro fassaratai,
Ba a ba shi hadisi ya kama yin surutai,
Babu shakka in an ka shaidi inganci nai,
Duk bayanin wani taliki ba za a riƙa ba.

16. Malamin Sunna dole zai mutunta sahabbai,
Jalla Ya yarda da su haƙiƙa nassi ya faɗai,
Kogunan Sunna ne maɓuɓɓuga ga hadissai,
Kway yi Sunna bai sa da su ba yai kaura da kai,
Ya zamo ɗan bidi' a na gaske bai gane ba.

17. Masu cewa duka mazhaba ɓata ce su kula,
Masu tilasta riƙo ga mazhaba a yi talla,
Babu shakka tsakiyarku gaskiya za ta ɓula,
Gaskiyar magana, sai akwai ruwa aka taula,
Don haruffa wasali ka jan su ba sauti ba. 

18.                    Shehu Ɗanfodiyo ya rigaya ya raba wannan,
Don Hidayatu Ɗullabi ta gama da batun nan,
Mun wuce wannan turnuƙu a daina haka nan,
Rarraba fitina ee, mu zo mu cuɗe haka nan,
Kan tafarkin manzonmu ba a kan son rai ba.

19.                    Ya kamata mu zauna mu sa ido mui nazari,
Malaman ga da ke jewaɗi da mu kan haɗari,
Sun ka kwance muna kai a kan da'ifin sharaɗi,
Sun ka tarwatsa kanunmu mun ka koma waɗari,
Don buƙatar son ransu ba da son Sunna ba.

20. Ba siyasar da a kai a bar su baya ku lura,
Kowace fada da su ake zaman shan ƙura,
Ba su ƙyama ga haramiya ƙazamar shara,
Kansu na haɗe koyaushe an ka murmure masara,
Mu su bar mu cikin hargitsi da gaba babba.

21. Ci da ceto suka yi da mu ku rinƙa kulawa,
Anniyarsu shiga dukiya suna holewa,
Ba su wa gwannati kayya! Ko tana cutarwa,
In tana ba su shiru sukai suna ƙyalewa,
An ci, an ba ka, batun muƙabula bai zaka ba.

22. Yau ku duba Sunnarmu ta bi ta rafashe,
Ba batun shara'a ko'ina ta'adi tarshe,
Ga yawan masalatai a ko'ina tuttushe,
Masu salla an tarwatsa su an tarsashe,
Malmnansu ka yin kwangilar ga ba Sunday ba.

23. Duk buƙatar fati wurinsu za a iza ta.
Su ka kawo nassin da za ya hau fasararta,
Sai a sa mu cikin ɗemuwa kamar mafarauta,
An biya su kuɗin ɗemuwarmu sun ƙauyanta,
Mun zamo tamanin cefanensu ban mu sani ba. 

24. Yau jihadi wa'azinsa an haranta muna shi,
Mai kira a ƙi Ɗagutu yanzu za a tsare shi,
Mai ganin laifin zamani ya kuka da kan shi,
Malamai ke fatawa zama guda a kashe shi,
Ce kakai in waƙatinsu yai ba za su zuwa ba. 

25. Dubi ɓarnar ga ta Foliyo da uttazu gaba,
An naɗe kai an bar gizon haɓa don zamba,
Yai adashi da mu ba kuɗinsa za shi zuba ba, 
Yanzu mallam kai za a turo ƙeyarka gaba,
Don a karkashe 'ya'yanmu ba a kan shara'a ba!

26. Duk buƙata ta Yahudu in ana son ta shiga,
Demokaraɗiyya za a kai ma wannan jinga,
Ita ka ɓaɓatun yekuwa ta sa mata riga,
Ita ka jawo ulama'u don ta sa su ga darga,
Mai kwaɗai bai ƙyama da ya ga masƙi babba. 

27. Ci da addini yai yawa ku duba sosai,
Shi ya sa jahillai shiga cikin malamai,
Wanda duk yag ga yana faɗa ana taɓa mai,
Ya zamo shehe babba can cikin limammai,
'Yan ta'addansa suna Imamu Shehe Babba.

28. Malamin Sunna bai zama da 'yan barara,
Bai shiga fada shi mamaye shina tsubarara,
Sai a mai da shi Khilaahumi cikin 'yan yara,
Mai faɗa a ji, shi zai faɗa a ce mishi gyara,
Ka fa san ba haka ƙa'idar ta Pati take ba.

29.             Dole tsuntsun da ya ja ruwa shi shirya jiƙewa,
Wanda duk yab bi ta duniya ya shirya ɓacewa,
Tun da mota ta kwaɗai idan ta doshi tsayawa,
Can tasha ta wulaƙanta 'yan Adam taka kai wa,
Dole sauka muzance ba cikin son rai ba. 

30. Ga ƙabilanci ya shigo mu kaico kaina!
Ga ƙiyayya a cikinmu ta taho ta zauna,
Ga rashin yarda ba tagomashi ko a in a,
Shi ya raurauna ƙarfinmu can ga bakin masana,
Yadda an ka fito da, haƙiƙa ba haka ake ba.

31. Ga bala'in rashawa ƙasarmu duk ta taɓare,
Yanzu cin hanci ya zamo taho mu ci tare,
Toshiyar baka in ka ƙi ci ka koma bare,
Yau muna kallo ga ƙasarmu za ta tarare,
Kuma da hannumu cikin abin ga ba da musu ba.

32. Wanda zai kwaso haramiya ya gina gidaje,
Su ake fatar ƙaruwarsu birni da waje,
Su ka gayyato wa'azi ana kiran su gwaraje, 
Masu saɓa wa Nabiyu an kira su mazaje,
Me ya kawo haka ba kwaɗai ga malumma ba? 

33.       Koni uttazu a daina mai da mu bobayi!
Wanda ke ba ka na ƙulƙule ya zamto masoyi,
Ran da yag gaji, ko yag gaza, ya zamto maƙiyi, 
Kungiya duk ka yabon ma'aikata ga ɓarayi,
Ba ta 'yan Sunna ce ba, miƙa kayanka gaba. 

34.             Yanzu mai albashin dubu ɗari a misalta,
Zai gidan miliyan goma gwargwado a ƙaranta, 
Kuma ana kallo ba wurin da za a hukunta,
Masu kurin Sunna sukai irin magabata,
Su ka doro da haramiya suna ta da gaba. 

35.             Ba sana' a kaka yi ba fil' azal ba ka da su,
To ina kas same su? Wa ya kawo maka su?
'Yar kujerar ga da an kwaɓe ta nan sai ka rasu, 
Malaman tsibbu da 'yan baranda ba a barin su,
Taka ta ƙare, sun cira ta, su sun yi gaba.

36.             Maguɗi da rashin gaskiya a same mu da su,
Keta haddi da taɓasgara a shede mu da su,
Babu tsentseni, Alƙana'u duk mu rasa su,
Mun zamo holoƙo mahassada sun gamsu,
Don kashi ya rikice mu sake gyara shi gaba.

37.             Masu auka wa kaba'ira suna annashawa,
Karuwanci ga maɗigo na rushe taƙawa,
Ga luwaɗi na tashe an kwatse mai da'awa,
Yanzu komai ya dulmuye sabili da hawaa,
Yanzu mai ƙyamar fasiƙi ba zai nasara ba.

38.             Sa ido, dubi arewa, har cikin tsakiyarta,
 Yanzu Borno gari an hana mu sada zumunta,
An kashe malammai mahardata managarta,
 Hakaza Yobe da Yola an guma musu cuta,
An ka sa Musulunci ya ƙaura ba da shiri ba.

39.             Ga Kano nan an gwamatso ta an sa ta gaba,
Ga Kaduna Musulminta hannuwa duk a gaba, 
Sakkwatawa an tunkuɗe su ba da shiri ba,
Tun da sun ga jini, tabbata ba a daina ba,
In mu miƙe tsaye, in a hau mu ba da shiri ba.

40.             Masu zancen Boko Haram su sake tunani,
Hare- haren da ake kai Arewa babu tunani,
Sun wuce 'yan Boko Haram ga nawa tunani,
Gaskiyar magana takkwali ka son kore gwani,
Ya ga in an yi mubaraza ba zai nasara ba.

41.             Wa ake kai wa hari ya kasa kare kansa?
Wa ake far ma gida a karkashe danginsa?
Wa ake wa kan mai uwa da wabi kansa?
In ya yunƙura yaf farga don ya kare kansa,
Sai a ce masa, Boko Haram da sunan zamba. 

42.             Wa ya haddasa fitinar ga, kai, gana ka tunane?
Shugaba Goodluck ya fahinci 'yan boko ne,
Gun riwaya ta Azazi masu PDP ne,
Mun ji gwannan Legas ya ce, "shirin manya ne",
An ka kushe aka koro 'yan Arewa gudane,
An ka sa su shahadar da ba ta addini ba. 

43.             Duk bala'in ga, ga nau gani, ga nawa kwatance, 
Maguɗi zalunci ya kai ƙasar ga a kwance,
Ga rashin aiki, tarbiyarmu ta lalace,
Ba mu kishi ga ƙasarmu ka ji babban zance,
Su ka sa tashintashina ba a daina ba.

44.             Na ji ciwo ainun ganin faɗan malammai,
Su da almajirinsu kana ga limammai,
An yi jan ayoyin shiri su fid da makamai,
Ga hadisan manzo su kau da kai su ƙiya mai,
Wa ka yin haka bai zan cikin hushin Allah ba? 

45.             Wanda yat take sani ina sani ka kiran sa?
Bai da hujja almajirai ku bar rakiyar sa,
Ba ya ƙaunar mu haɗe wuri guda ga darussa,
Bai da buri illa mu kama bin son ransa,
Har mu je barzahu ba a godaben Sunna ba.

46.             Yanzu halin da muke cikinsa mai ban tausai!
Za a neme mu, mu sake rarraba mu bi son rai?
Mai buƙatar mu da sake rarrabe mu ishe mai,
Bai buƙatar rahama gare mu balle jinƙai,
Ya zamo shaiɗan ba nufinsa bin Sunna ba.

47.             To ku tabbai can da,da mun ka zan warwatse,
Shin wane ci gaba na ta kai mu bayan tsintse?
An ka ragaice an taɓarɓare sai ratse,
Yanzu mun gane kurenmu ba mu sake kutse,
Danga-ɗangan bin ayarin da ba shari'a ba.

48.             Mun tsaya nan ga kitabu ba mu sake ɓarewa,
Mun bi Sunna bisa fassarar da ba rikitarwa,
Yaye-yayen kowa mu kau da kai ga biyawa,
Tun da shaiɗan ka shiga mu je mu ƙara ɓarewa,
Dan Aminatu bai ce, mu ƙirƙiro tawaga ba. 

49.             Ita lalura uzuri ka sa ana ɗaukar ta,
Ran da yak kawa tilas a sake tawilinta,
 In ana hangen maslaha akan gyara ta,
Maslahar da ka cutar da muminai illa ta,
Dole sake nazarinta ba biyar son rai ba. 

50.             In kashi ya rikice rabonsa sai adillai,
Dole manya ka shiga su dinga kawo dalillai,
In hukunci ya zo ga hannuwan alƙallai,
Masu ƙara su rage hasumiya da jidallai,
Gaskiya aka bi, ba batun muna da yawa ba.

51.             Dakatance ni aboki ban aron kunnenka,
Wanda ya tara kuɗi a dole zai biɗi jikka,
Dole falke ya yi tanadi na gyaran salka,
 Me ka sa doki taƙama shina sassaka?
Duk shirin sukuwa ne aboki ba kwanci ba.

52.             Masu ƙyamar mu haɗe mu manta bambancinmu,
Ga siyasar banza zama guda ta haɗe mu,
Don kwaɗan duniya mun ka ɓata addininmu,
Ga Musulmi ga ƙafiri muna harakarmu,
Sai ka ce Allah bai hana mu soyayya ba. 

53.             Yanzu Pidipi za ta ɓata imaninmu?
Yanzu Eenci ke ɓatar da hankullanmu?
Kan batun Enci mun ɓarar da rayukkanmu,
Kaico! Eenpipi ka ɓata addininmu,
Wai akida ba ta kai ga martabar Pati ba.

54.             Ga su ustazu cikinsu sui shiru ba su ɗumi,
Sai a fifita Bamaguje a ƙyale Musulmi,
An haɗe kai da Majusu an ka cuci Musulmi ,
Mai faɗan an yi kure a hau shi sai ya yi gumi,
Don mu kare ɗan ƙulƙulenmu ba Allah ba.

55.             Ka ji wawa wani sakarai magajin hauka,
Cefanen banza za ya ɓata addininka,
An ci an suɗe an ka bar ka zindiƙinka,
Ga tukuici nan yanzu ko'ina lardinka,
To ina wani mai agajinka ba Allah ba?

56.             Maganin mutuwa nab biɗa wajen bokaye,
Sun ka ban sauyoyin da zan jiƙa in shanye,
Nai wurin malammai da 'yan kuɗina na saye,
Sun ka ce ba su da maganin cikin kundaye,
Je ka hankura Ustazu ba da tawili ba. 

57.             Yanzu son rai ka hana mu sake gyara shirinmu?
Ga abokan gabanmu sun yi zoba kanmu,
Bindigogi da bamabamai ana ta kashinmu,
An ci alƙaryoyinmu an gama da yawanmu,
Don yawa bai ƙarfi idan ba za a haɗe ba.

58.             Me ya samu mazajenmu masu ji da Arewa?
Malamai mis same ku ba ku ko motsawa?
Ɗalibai me kuka dawara kuma kokawa?
Dole tsuntsun da ya ja ruwa ya shirya nutsewa,
Wanda duk yac ce, ya iya, a zan sa shi gaba.

59.             Ba jumudin riƙe mazhaba ka yin Sunna ba,
Ba riƙo ga ɗariƙa ake kira Sunna ba,
Ba zama shehen ƙungiya ya zan Sunna ba,
Ba zama dabbar ware ne riƙon Sunna ba,
Mai fahintar haka bai ɓace ga bin Sunna ba.

60.             Rabbu ya ce mu haɗe mu gyara tawilinmu,
Kar mu ƙirƙiro wata fassara ta zan jigonmu,
Kar mu sa son rai ko kaɗan ga addinimu,
In muna son nasara mu tsarkake niyarmu,
Kar mu ce, wani ba mu ba, bai shigo Sunna ba.

61.             Dakata bari rigima ka daina yin ɓaɓatu,
Wanga addini namu dole sai da karatu,
Ba a banga ciki, zage-zage ko sabbatu,
Ba yawan jama'a ne ba ko yawan masalatu,
          Mai sahihin nassi wurinmu shi ne babba.

62.             Mun ji kifi in ya buƙaci lalacewa,
Can ga kainai ne za ya bayyanar da ruɓewa,
Kana sannan gangar jiki ta fara sakewa,
To abin nan haka yat taho gare mu Arewa,
An rufe bakin jagabanmu an sa mu gaba.

63.             Ba rufewan takunkumi ba ne ka ji sosai,
Toshiyar baka, rashawa, gami da hanci da kwaɗai,
Babu bambancin jahilai kaza malammai,
Lura mamu haka yat tarar wajen limammai,
Ba a cin sa a suɗe shi ba da sun hallara ba.

64.             Ka ga dole kashi ya game ina za a tafi?
Masu wayo sun ce, aje wajen tsofaffi,
Su ka rarabe hanyar tudu.kaza da ta rafi,
Kan su ce, "uffan", anka fara ci musu zarafi,
An ka rafashe batunsu ba da sun furta ba.

65.             Ga nasiha gun shehunanmu manyan wa'azi,
Ɗinga yin sa da hikima a zan kiyaye lafazi,
Soke-soke da yin arashi da sunan wa'azi,
Cin mutunci da ƙarairayi da mugun lafazi,
Su ka kahaddasa fitina da rarraba a yi gaba. 

66.             Shawarata gun malamai a gyara a gaba,
Kar ka zan, faɗi a yi kabbara, ana tad da gaba,
Ko ka zan, mai wa'azin tuwo, a tara kwababba,
Samu hanyar neman na kanka ba da bara ba,
Ba karatu abadan ya zan da shi aka ci ba.

67.             Yin irin haka ka yawaita ƙungiyoyi na riya,
Malamai su zamo karnukan hayan masu saya,
Sai siyasa ta shigo ta tarwatsa musu mabiya,
Nan da nan gwannati sai ta ba mu sunan maƙiya,
Sai a far muna da kisa da rana ba da duhu ba. 

68.             Me ya sa duk fitina a kanmu za a azawa?
In wuta ta ci gidanmu sai mu kasa kashewa?
Sai a turo muna 'yan ta'adda masu hasawa,
Tsofafi, mata, 'yan ƙanana sui ta kashewa,
Borno ta koma Kandahar musiba babba.

69.             Ka da ku manta Afgaani an ka fara karewa,
An ka koma a Iraƙi an ka kama kashewa,
An ka watse Masar an ka sa Gadafi macewa,
Ga Somaliya Mali ana kashi da tsarewa,
Dubi Pakistan can cikin ƙasar Ƙurdawa,
An hana musu rawani lagen mayafi babba.

70.             Meya sa Nukiliya Iran ake ta matsawa?
Demokaraɗiyya Makka ɗai take kushewa?
Masu gemu da naɗi ake matsawa kulawa?
Yanzu hatta da Kaduna cibiyar Hausawa,
Mai kamannun Sunna ba zai sake ya baje ba.

71.             Na ji haushi sosai da nat tuna da yawanmu,
Hankalina ya tashi can ga malunmanmu,
Dole rai zai ci haki ganin halin manyanmu,
Dole zub da hawaye tuni da tarbiyarmu,
Ban ga mai kyau a cikin icen kushewa ne ba.

72.             Rabbu yafe zunubbanmu 'yan ƙanana da manya,
Taimake mu dabararmu ba ta kai mu ga hanya,
Babu aikin da muke tawussuli ka musanya,
Babu shakka mu mun ka sa abin da ya sanya,
An ka hau kaburan kakanninmu ban mu muɗa ba.

73.             Kun ji saƙo gun ɗalibinku Ali na Bunza,
Bunza alƙarya can gabas ga birnin Geza,
Unguwarmu tana tsalleka ga fadar Bunza,
Rijiyar Malam Ama in ka ɗan tutturza,
Unguwar Malammai tsakanta ba gehe ba.

Aliyu Muhammadu Bunza
Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua,
Katsina 19/05/2013


Post a Comment

0 Comments