Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakokin Hausawa Na Gargajiya (Traditional Music of the Hausa People) (2)

(An introductory study of the forms functions and the qualities of the traditional music of the Hausa people)

BABI NA BIYU: WAKOKIN WASANNI

2.0 Gabatarwa


A wannan ‘bangare, za a yi magana game da wak’ok’in wasannin yara ne. Akwai abubuwa daban-daban da za a iya la’akari da su wurin samar da rabe-raben wak’ok’in Hausawa. Sai dai a nan, za a dubi ire-iren wasannin gargajiya ne na yara ta fuskar jinsi da kuma yanayin gudanarwa. Wannan ne ya kai ga samar da rukunen wasannin yaran zuwa gida biyu kamar haka:

  1. Wasannin yara maza da wasannin yara mata

  2. Wasannin tashe da wasannin dandali


Lura da wannan, za a kawo misalan wak’ok’in da ake gabatarwa cikin wasu wasannin yara maza da na yara mata, da kuma wad’anda ake samu cikin wasannin tashe na yara maza da mata. Tun da buk’atar wannan darasi shi ne samar wa d’alibai bayanai game da wak’ok’in gargajiya na Hausawa, ya dace ne a je kai tsaye zuwa ga wak’ok’in da ke cikin wasanni, wato ba tare da bayanin wasannin kansu ba. Sai dai kuma wani abu shi ne, samar da bayanan wasannin zai taimaka wa d’alibai wurin samun hoton zuci na yadda tsarin falfasar wak’ok’in suke, musamman yayin da suka danganta su da salon gudanar da wasannin. Saboda haka, misalan wad’annan wak’ok’i za su taho tare da bayanin wasannin da a cikinsu ne ake samun wak’ok’in.

2.1 Yara Maza


Wad’annan su ne wasannin da yara maza ke gudanarwa a dandali. An fi gudanar da irin wad’annan wasanni da dare musamman lokacin farin wata. Za a kawo misalan wasanni biyu da ke d’auke da wak’ok’in gargajiya, sannan za a kawo sauran misalan wak’ok’i ba tare da bayanan wasannin da ke d’auke da wak’ok’in ba.

2.1.1 Jini Da Jini


Wannan wasa ce ta gargajiya. Misalin yara takwas ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa. Tana da sigar shugabanci na liman da ladan da kuma mamu.

2.1.1.1 Wuri Da Lokacin Wasa



  1. Jini da jini wasar maza ce ta dandali.

  2. An fi gudanar da wannan wasa ne da dare, musamman bayan an ci abincin dare.


2.1.1.2 Kayan Wasa



  1. Rigar da aka nannad’e wadda ake amfani da ita wajen dukan wanda ya ‘bata.

  2. Bishiya ko katanga ko wani wuri da za a nuna a matsayin sha.


2.1.1.3 Yadda Ake Wasa


Liman yakan tsaya a gaba. Ladan kuma tare da mamu za su yi sahu-sahu a bayan liman. Dukkanin ‘yan wasa za su nannad’e rigarsu, wadda da ita ne suke dukan duk wanda ya ‘bata. Daga nan liman zai bayar da sanarwa kamar haka:

“Za a fara, za a fara!”

Ladan zai maimaita wannan sanarwa. Daga nan kuma liman zai fara ambatan sunayen abubuwa d’aya bayan d’aya. Da zarar ya ambaci sunan abu, mamu za su amsa da danja idan har abin yana da jini a jikinsa. Idan kuwa ba shi da jini, to za su amsa da babu. Yayin da wani yaro ya kuskure, to ya fad’i. Don haka za a rufa shi da duka da rigunan da aka nannad’e a hannunsa. Ba za a bar shi ba har sai ya sha. Ladan ne yake da hurbin bayyana wanda ake duka ya sha ko bai sha ba. Da zarar ladan ya bayyana cewa an sha, to za a dena duka. Daga nan kuma wanda aka daka shi ne zai kasance liman a yayin ci gaba da wasa. Misali:

Liman: Jini da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Rago da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Akuya da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Kaza da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Zakara da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Mota da jini.

Mamu: Babu!

 

2.1.1.4 Sakamakon Wasa


Wanda ya ‘bata a wasar jini da jini yakan sha duka, har sai ya je ya sha. Akan doke shi ne da rigar da aka nannad’a.

2.1.1.5 Tsokaci


Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan tana koyar da harshe, musamman sanin sunayen abubuwa. Bayan haka, wannan wasa tana sanya nutsuwa ga yara, kamar yadda rashin nutsuwa kan kai ga yaro ya sha duka yayin da ya ‘bata wasa.

2.1.2 Belbela-belbela


Wannan ma wasa ce ta dandali da yara maza ke aiwatarwa yayin da akwai farin wata. Kimanin yara takwas zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wasar na tafiya da wak’a, sanna tana buk’atar kayan wasa yayin gudanar da ita.

2.1.2.1 Wuri Da Lokacin Wasa



  1. Wannan wasa ce ta dandali.

  2. An fi aiwatar da wannan wasa da dare, musamman lokacin farin wata.


2.1.2.2 Kayan Wasa



  1. Riga da aka nannad’e domin dukan wanda ya fad’i

  2. Wurin sha


2.1.2.3 Yadda Ake Wasa


Yara sukan tsaya ba bisa wani tsari ba, wato kara tsube. Daga nan kuma jagora zai shiga gaba. Jagora zai yi rik’a wak’a yayin da saura ke amsawa:

 

Jagora: Belbela-belbela,

‘Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Ina za ki je ki?

‘Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Gidan Audu rimi.

‘Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Da ced’iya da rimi,

‘Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Ala jik’an maza sun fad’i ragwas!

Da zaran an kai wannana gaci, kowa zai k’ame a yadda yake ba tare da motsi ba. Duk wanda ya motsa to ya fad’i, don haka za a hau shi da bugu har sai ya sha.

2.1.2.4 Tsokaci


Wannan wasa na koyar da yara abubuwa da dama ta taimakon wak’ar da ke cikinta. Da farko dai tana koyar da tsarin shugabanci sannan da bin doka da k’a’ida. D’an wasa bai isa ya yi magana ba ba tare da shugaba ya yi ba, ko kuma ba tare da lokacin da ya dace ya yi magana ya yi ba. Sannan wanda ya k’arya k’a’idar wannan wasa (k’amewa) zai fuskanci hukunci. Wak’ar wasar na d’auke da sunayin wasu bishiyoyi da ake samu a muhallin Bahaushe, wato ced’iya da kuma rimi.

 

 

 

K’arin Misalan Wak’ok’in Wasannin Yara Maza


2.1.3 Wak’ar Wasar Noti-Noti


Bayarwa: Noti-noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Mashin noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Mota noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Keke noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Inji noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Jirgi noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Akuya noti,

Amshi: Gulum babu!

2.2 Wasannin Yara Mata Na Dandali


Wad’annan wasanni ne da yara mata ke gudanarwa a dandali. An fi gudanar da wad’annan wasanni da dare, musamman lokacin farin wata. Su ake kira da wasannin gad’a. Mafi yawan wasannin gad’a suna tafiya da wak’ok’i. Wak’ok’in kan k’unshi bayyana muradin zuci (na masu wasa) da hannunka mai sanda ga iyaye da sauran jama’ar gari da makamantan wannan. Za a kawo bayanin biyu daga cikin wad’annan wasanni da ke tafiya da wak’a, sannan a biyo bayansu da wak’ok’in wasannin dandali na yara mata ba tare da bayanin wasannin da ke d’auke da wad’annan wak’ik’o ba.

2.2.1 Gamuna


Wannan wasar dandali ce ta mata. Ana buk’atar yara da dama domin gudanar da wannan wasa. Saboda haka, yawan masu gudanarwar na kasancewa ashirin zuwa sama a mafi yaran lokuta.

2.2.1.1 Wuri Da Lokacin Wasa



  1. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko gidan biki ko wani wuri da ake samun taron yara mata.

  2. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko kuma da dare, lokacin farin wata.


2.2.1.2 Yadda Ake Wasa


Masu wasa za su rabu zuwa gari biyu. Za a yi k’ok’arin daidaita yawan ‘yan garuruwan guda biyu. ‘Yan gari d’aya daga cikin garuruwan biyu za su tsuguna su dafa kafad’un juna. ‘Yan d’aya garin kuma za su koma can gefe, su ba su tazara. Daga nan za su tattauna tsakaninsu kan wadda za su d’auka daka garin wad’anda suka tsuguna. Da zarar sun k’are tattaunawa sai su dawo. Za su zo daf d’a wad’anda ke tsugune, yayin da suke dafe da kafad’un juna. Yayin da suka zo, za su fara wak’a wanda a wannan lokaci ne kuma garin da ke tsugune za su tashi su rik’a ba su amsa. Haka za su rik’a yi suna rangaji tare da ‘yan taku zuwa gaba da baya. Wak’ar ita ce kamar haka:

Masu D’auka: Ga mu nan muna zuwa,

Muna zuwa muna zuwa,

A cikin JSS Misau.

Masu Bayarwa: Meye dalilin zuwanku?

Zuwanku zuwanku,

A cikin JSS Misau?

 

Masu D’auka: Za mu d’auki d’ayarku,

D’ayarku d’ayarku,

A cikin JSS Misau.

Masu Bayarwa: Da sai ku fad’a mana sunanta,

Sunanta sunanta,

A cikin JSS Misau.

 

Masu D’auka: Da za mu d’auki A’isha[1],

A’isha A’isha,

A cikin JSS Misau.

A wannan ga’ba za su kama wadda suka ambaci sunanta sannan su dawo da ita cikinsu. Daga nan kuma za su fara tsalle tare da fad’in:

Mu gidanmu ba yunwa,

Sai biredi sai shayi,

Sai abincin Turwa,

Abin da muke ci ba kwa ci.

Daga nan za su koma can nesa kad’an su tsuguna. Garin da aka d’auke musu ‘yar wasa kuma za su tattauna game da wadda za su d’auko. Haka za a ci gaba da wasa har sai an gaji.

2.2.1.3 Tsokaci


Wannan wasa ce ta nishad’i tsakanin yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Wak’ar wasar na nuna hoton ziyara tare da neman buk’atar d’aukar d’iya daga wani gida. A kaikaice, falsafar wannan wak’a na nuni ga neman aure da bayarwa.

2.2.2 A Fiffigi Zogale


Wannan ma wasar dandali ce wadda ke da zubi da tsari irin na kwalba-kwalba dire. Mutane biyar ne ko sama da haka suke gudanar da ita.

2.2.2.1 Wuri Da Lokacin Wasa


Wasar ta gad’a ce da aka fi gudanarwa da dare, musamman lokacin farin wata.

2.2.2.2 Yadda Ake Wasa


Zubi da tsarin wannan wasa daidai yake da na kwalba-kwalba dire da kuma ruwan k’auye. Saboda haka za a yi amfani da sunan masu gudanarwa irin na ruwan k’auye domin tantance matsayin kowa a cikin wak’a. Ga wak’ar wannan wasa kamar haka:

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

Yarinya a fiffigi d’orawa,

Idan mamanki ta zo,

Yarinya yaya kike mata?

Mai Direwa: Hakannan nake mata,

Har ma in juyo ina haka.

Mai direwa za ta tsuguna ta nuna alamar ladabi na gaisuwa ga iyaye.

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

Yarinya a fiffigi d’orawa,

Idan babanki ya zo,

Yarinya yaya kike masa?

Mai Direwa: Hakannan nake masa,

Har ma in juyo ina haka.

Ladabin da mai direwa ke yi da salon da take yi daidai yake da na mahaifiya. Daga nan masu cafewa za su ci gaba da wak’a:

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

Yarinya a fiffigi d’orawa,

Idan uwar mijinki ta zo,

Yarinya yaya kike mata?

Mai Direwa: Hakannan nake mata,

Har ma in juyo ina haka.

A nan mai direwa ba za ta tsuguna k’asa ba. Sannan za ta rik’a gaisuwar tana gatsine da alamar reni.

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

Yarinya a fiffigi d’orawa,

Idan mijinki ya zo,

Yarinya yaya kike masa?

Mai Direwa: Hakannan nake masa,

Har ma in juyo ina haka.

A nan ma za ta duk’a cikin girmamawa da duna alamun yin maraba.

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

Yarinya a fiffigi d’orawa,

Idan kishiyarki ta zo,

Yarinya yaya kike mata?

Mai Direwa: Hakannan nake mata,

Har ma in juyo ina haka.

A nan kuma mai direwa za ta rik’a gatsine da kallon hadirin kaji tamkar dai wadda take da kishiyar gaske a gabanta. Da zarar an zo wannan ga’bar to mai direwa ta kammala yinta. Daga nan za ta koma cikin layi, wata kuma ta fito.

2.2.2.3 Tsokaci


Wannan wasa na samar da nishad’i da annashuwa ga masu yi da kuma masu kallo. Sannan hoto ne ko madubi da ke hasko wasu halayyar mata a gidan aure. Musamman da ‘bangaren yanayin huld’arsu da wasu mutane na musamman da suka had’a da iyaye da miji da kuma kishiya da makamantansu.

K’arin Misalan Wak’ok’in Wasannin Dandali Na Mata


2.2.3 Ruwan K’auye

Masu Cafewa: Ruwan k’auye,

Ruwan k’auye.

Mai Direwa: Jagwalgwale ne.

 

Masu Cafewa: A wanki kare a wanki doki,

Mai Direwa: A d’auko d’an mutum a jefa.

 

Masu Cafewa: Yarinya bak ki da yayu ne?

Mai Direwa: Yayuna sun fi d’ari goma.

 

Masu Cafewa: Iya lissafa mu ji labari,

A wannan ga’ba, mai direwa za ta fara lissafo sunayen yayunta d’aya bayan d’aya a sigar muryar wak’e. Saura kuwa za su ci gaba da amsawa. Misali:

Mai Direwa: Ramlatu,

Masu Cafewa: Ta iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Khalid,

Masu Cafewa: Ya iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Halima,

Masu Cafewa: Ta iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Abdul,

Masu Cafewa: Ya iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Ni ma na iya aikin bariki, bariki balle aikin Jos.

4.2.4 Ina Da Cikin D’an Fari


Bayarwa: Ina da cikin d’an fari,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata d’aya ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata biyu ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata uku ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata hud’u ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata biyar ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata shida ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata bakwai ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata takwas ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Sai a ran na goma na goma,

Amshi: To!

 

 

 

 

Bayarwa: Na haifi d’ana Mamma,[2]

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na je gidanmu da wanka,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na tarad da baba a zaure,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Yana cikin cinikinsa,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Yana cinikin goronsa,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya ce mu ga jikan namu,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Jikan namu har ya girma?

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya tsunkule yi a hanci,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na ce uhm! Ba komai,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya ce ku ji d’iya ba kunya?

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya ce ku ji d’iya ‘yar banza!

Amshi: To!

4.2.5 Ni Mota Nake So


Bayarwa: Ni mota nake so,

Amshi: Yayin mota ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni mashin nake so,

Amshi: Yayin mashin ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni keke nake so,

Amshi: Yayin keke ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni jirgi nake so,

Amshi: Yayin jirgi ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni allura nake so,

Amshi: Jeki gidan Malam Na gajere,

Ya iya allura talatin,

Wanda Bature bai iya ba,

Jish kankana jish kankana.

Jish kankana jish kankana.

4.2.6 Amali Kande


Bayarwa: Wayyo inna wayyo inna!

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai kunama,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai bala’i,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai jafa’i,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: To an kai d’an maciji gidansa,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Wayyo inna wayyo inna!

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

2.3 Wasannin Tashe Na Yara Maza


Tashe dai dad’ad’d’iyar al’ada ce a k’asar Hausa wadda ta samu tun lokacin da addinin Musulunci ya shigo k’asar Hausa. Za a iya hasashen lokacin da Bahaushe ya fara tashe ta la’akari da lokacin da ya fara azumi. Domin kuwa a cikin watan azumi ne ake gudanar da tashe. Akan gudanar da ita da dare (a mafiya yawan lokuta) bayan an sha ruwa da zummar a faranta wa wad’anda suka kai azumi rai tare da nishad’antar da su. A wannan ‘bangare na aikin, za a kawo bayanin yadda ake gudanar da wasu wasannin tashe a k’asar Hausa domin fito da wak’ok’in cikinsu fili. Daga k’arshe kuma za a kawo wasu wak’ok’in tashen ba tare da bayanin tashen da ke d’auke da wak’ok’in ba.

 

2.3.1 Ba Mu Kud’inmu


Wannan wasa ce ta tashe wadda yara maza ke gudanarwa. Kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da ita. Sannan akan yi amfani da kayan wasa yayin gudanar da wannan wasa. Kasancewarta wasar tashe, an fi yin ta da dare, bayan an sha ruwa.

2.3.1.1 Kayan Wasa



  1. Filo/matashin kai

  2. Sanduna marasa nawi sosai ko tsumagu


2.3.1.2 Yadda Ake Wasa


Yara za su goya wa d’aya daga cikinsu filo guda d’aya ko biyu. Wannan ya danganta da girman filon. Domin buk’ata shi ne, yayin da aka doki wannnan yaro, kada ya ji zafin dukan. Kowanne daga cikin sauran yara kuwa zai nemi k’atuwar tsumagiya, ko ma sanda marar nauyi ya rik’e.

Yayin da ake wurin wasa, wad’annan yara za su hau dukan wannan da suka goya wa filo. Shi kuwa zai rik’a sanya wak’a, saura na amsawa. Ga yadda wak’ar take:

Bayarwa: Wayyo Allah!

Amshi: Ba mu kud’inmu.

 

Bayarwa: Wanne kud’inku?

Amshi: Kud’inmu na bashi.

 

Bayarwa: Bashin mene?

Amshi: Bashin doya?

 

Bayarwa: Na doyar yaushe?

Amshi: Na doyar bara.

 

Bayarwa: Ta nawa kuka ba ni?

Amshi: Ta dala muka ba ka.

 

Bayarwa: A ina kuka ba ni?

Amshi: D’akin baba.

 

Bayarwa: Ina shaidarku?

Amshi: Mu je gun inna.

Wannan d’a na k’arshe akan fad’e shi ne idan a cikin gida ake wasan. Idan kuwa a dandali ne, wurin maza, yaran kan ce:

Bayarwa: A ina kuka ba ni?

Amshi: D’akin inna.

 

Bayarwa: Ina shaidarku,

Amshi: Mu je gun baba.

Hikimar hakan shi ne, yayin da aka ce a je wurin inna a cikin gida, za a je wurin da mata ko matan gidan suke tsaye ko zaune ne. A dandali kuwa, idan aka ce mu je gun baba, to za a matsa ne kusa da wurin wanda ake wa tashe. Daga nan kuma sai su ci gaba da wak’ar:

Bayarwa: Wayyo Allah!

Amshi: Ba mu kud’inmu.

 

Bayarwa: Ku tsaya in ba ku,

Amshi: Sai ka ba mu.

 

Bayarwa: Ni fa d’an gata ne,

Amshi: Ina gatarka?

Bayarwa: Ga shi ubana?

Amshi: To ya ba ka ka ba mu.

 

Bayarwa: Baba ba ni in ba su,

Amshi: Da dai ya fi.

 

Bayarwa: Baba za su kashe ni,

Amshi: Sosai-sosai.

 

Bayarwa: Baba ba na fa jigata,

Amshi: Sosai-sosai.

 

Bayarwa: Baba har da gumi fa,

Amshi: Sosai-sosai.

2.3.1.3 Tsokaci


Wak’ar wannan wasa na samar da nishad’i musamman ga masu kallo. Sannan tana nuni ga munin wani d’abi’a ko hali, wato cin bashi. Wanda wannan hali na kai mutum ga wulak’anta kamar dai yadda mai cin bashin doyan nan ya wulak’anta. Baya ga haka, wak’ar wasar na tabbatar da kasancewar iyaye gata ga ‘ya’yansu.

2.3.2 Zule-Zuleyya


Wannan ma wasar tashe ce ta yara maza. Tana tafiya da wak’a, sannan akan buk’aci kayan wasa yayin gudanar da ita. Kimanin yara biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. Kamar sauran mafi yawan wasannin tashe, an fi gudanar da ita da dare.

 

 

2.3.2.1 Kayan Wasa



  1. Sakaina

  2. Wuk’a ko wani abu mai kaifi



  • Igiya



  1. Kayan fenti iri-iri

  2. Sandu biyu gajeru


2.3.2.2 Yadda Ake Wasa


Yara za su nemi sakaina sannan su yi amfani da wuk’a ko wnai abu mai kaifi su gyara ta daidai fad’in fuskar mutum. Sai kuma su yi huji jikinta daidai wurin da hanci da idanu da baki za su fito. Daga nan za su bi jikin sakainar su yi mata fenti iri-iri. Sukan yi amfani da abubuwa kamar bula da bayan tukuncya da farar k’asa da makamantansu. Bayan an kammala tsaf, za a d’aura igiya ko lilo ko wani zare mai kaure a gefe da gefen wannan sakaina, sannan a d’aura a fuskar d’aya daga cikin ‘yan wasa. Wanda aka d’aura wa sakainar shi ake kira Zule. Sannan zai nemi sanduna guda biyu gajeru.

Masu wasa za su d’unguma zuwa wurin tashe. Yayin da suke iso wurin da za su gudanar da wannan tashe, Zule zai sunkaya ya rik’a dogara sandunansa a k’asa. Zai kasance tamkar wata dabba ce mai k’afa hud’u. Ga kuma fuskar da aka amsa da sakaina. D’aya daga cikin yara zai sa wak’a, saura kuwa za su rik’a amsawa. Ga yadda wak’ar take:

Bayarwa: Iya ku ‘boye ‘ya’yanku ga abin mafarki,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Zule-zuleyya mai idon sakaina,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

 

Bayarwa: Kura ta lek’a ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Damusa ta lek’a ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: ‘Bauna ta lek’a ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Gwanki ya lek’a ya ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Zaki ya lek’a ya ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Giwa ta lek’a ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

Yayin da ake wannan wak’a, Zule zai ci gaba da dogara sandanunasa yana tafiya a sunkuye, tamkar dai dabbar da ake zancenta cikin wannan wak’a. Yara da dama sukan tsorata idan suka gani. Wasu har sai an ‘boye su.

2.3.2.3 Tsokaci


Duk da k’ananan yara na tsorata yayin da suka ga Zule, wasar ta kasance nishad’antarwa ga masu kallo (manya). Sannan wak’ar wasar na d’auke da sunayen dabbobin dawa kamar yadda Hausawa ke kiransu. Wannan kamar ilmantarwa ne tare da kundance sunayen. Bayan haka, wasar na nuna gaba mma da gabanta ko a cikin dabbobi.

K’arin Misalan Wak’ok’in Tashen Maza


2.3.3 Danda Dokin Kara


Bayarwa: Assalamu alaikum kun yi bak’o,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Masu gidan nan kun yi bak’o,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Sai ku ban kaji bakwai dak’wale,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Da tuwon shinkafa da miya ja,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Sai ku ban soyen nama na rago,

Amshi: Ga danda dokin kara.

2.3.4 Tashi Wali


Wali: Wali zai tashi,

Amshi: Kar ka tashi wali.

 

Wali: Zan tashi,

Amshi: Kar ka tashi Wali.

 

Wali: Zan lula,

Amshi: Kar ka tashi wali.

 

Wali: Zan cilla,

Amshi: Kar ka tashi Wali.

 

 

2.3.5 Ka Yi Rawa


Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ban yi ba.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da gemuna?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da carbi na?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da rawanina?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da allona?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: A ina wai?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: K’arya ne.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ban yi ba.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ku ji sharri.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: To bari in ta’ba

 

 

2.4 Wasannin Tashe Na Yara Mata


Kamar yadda aka ba da tak’aitaccen bayani game da tashe a sama, wannan ‘bangare na d’auke da misalan wak’ok’in tashe na yara mata. An kawo bayanin wasu daga cikin wasannin tashen, ta fuskar yadda ake gudanar da su. Daga nan kuma sai aka ba da misalan wasu wak’ok’in wasannin tashen ba tare da mai da hankali zuwa ga yadda ake gudanar da wasannin tashen ba.

2.4.1 Kallo Da Ido


Wannan wasar tashe ne da yara mata ke yin ta. Tana da sigar wasar tashe ta maza mai suna Jatau Mai Magani. Wasar sananniya ce, don haka wak’ar da ake gudanarwa ciki, da kuma shirin wasar ya bambanta daga wuri zuwa wuri. Sannan masu wasa sukan sauya wasu daga cikin kalaman wak’ar, kasancewar tana da tsawo. Kimanin mutane bakwai zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

2.4.1.1 Kayan Wasa


Garin sabara ko lalle ko kuka ko dai gari makamancin wannan

  1. Ledoji

  2. Kwanuka ko k’ore



2.4.1.2 Yadda Ake Wasa


D’aya daga cikin ‘yan wasa za ta kasance mai maganin gargajiya. Wannan yarinya ita ce shugabar wasa. Za ta sanya layu a hannunta, ko dai ta d’ora su a cikin tarkacen kayan maganinta. Kayan maganin kuwa bai wuce garin sabara ko da lalle ko kuka, ko dai makamancin wannan. Wani lokaci akan k’uk’k’ulla wannan garin magani cikin ledoji, sannan a bar wani gari cikin k’warya k’arama ko wani kwano.

Yayin da aka shiga gida domin tashe, jagora za ta baje kayan maganinta. Daga nan kuma za ta fara wak’a sauran kuma suna amsawa. Wani lokaci za ta rik’a ba wa abokan wasan nata garin magani a hannu, tamkar mai ba da maganin gaskiya. Wak’ar kuwa ita ce:

Bayarwa: Kallo na ido,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Mata ga garin magani,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Mata ku fito ga magani,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Duk ku fito ga maga ni,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: A yau ni zan ba ku shi,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: In har ba ku san ni ba,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Ni ce mai magani,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: A nan kin ga na kishiya,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Idan kika kar’bi na kishiya,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Bad’i ya war haka,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Kin kore kiyoshi d’ari,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Nan kin ga na mai gida,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Idan na ba ki na mai gida,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Kullum ba ya k’i ta taki ba,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Nan kin ga na arziki,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Domin ki kore tsiya.

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: A nan kin ga na haihuwa,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Idan kin kar’bi na haihuwa,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Ya war haka in mun je bad’i,

Amshi: D’an gajere.

 

Bayarwa: Kin haife ‘ya’ya d’ari.

Amshi: D’an gajere.

Za ta rik’a wannan wak’a tana k’ok’arin bayar da maganin, kamar dai da gaske abin da take fad’i duka gaskiya ne. Haka za su ci gaba da yi har sai an sallame su.

2.4.1.3 Tsokaci


Wannan wasa tana nuni ga wata al’adar Bahaushe, musamman kafin ya kar’bi addinin Musulunci. Wato al’adar kar’bar magani domin samun biyan wata buk’ata. Wannan ya had’a da mallake miji da kuma korar kishiya.

K’arin Misalan Wak’ok’in Wasannin Tashe Na Yara Mata


2.4.2 Ga Kud’in Toshinki Na Bara


Bayarwa: Malama ga kud’in toshinki,

Malama: Bankad’a lefena ku zuba mini,

Ba na barin salla ta wuce ni.

 

Bayarwa: Malama me kike ta fad’i ne?

Malama: So nake na yi tarin salla,

Don bana kun ga ko ba a wuce ni.

 

Bayarwa: Malama ya batun tashen ne?

Malama: Tashen bana ya fi na bara samu,

Dole ne yanzu nai farawa.

 

Bayarwa: Malama me kike ta fad’i ne?

Malama: Ca nake ku taho mu yi taku,

Mui haka mui haka mui juyawa.

 

Bayarwa: Malama kin yi sallar safe?

Malama: Ban yi ba in kun yo taku,

Anjima ni zan yo tawa.

 

 

Bayarwa: Malama ashe halinki yana nan?

Malama: Kai ku k’yale ni tashen za a yi,

Koko tambaya kuke so kui min?

 

Bayarwa: Malama ai dukka muna so,

Malama: To ku bari sai gari ya waye,

Tambayarku dole in amsawa …

2.4.3 Wak’ar Wasar Tashen Ke Kika Je Ki Gidansu Direba


 

Yara: Ke kika je ki gidansu direba,

Mai Ciki: Da ban je ba ina zan samu?

Kullum biredi kullum shayi,

Kullum tsire yanka goma,

Na je likita ya auna ni,

Ya ce cikin direbobi ne,

Wayyo direba ka cuce ni,

Wayyo direba ka ji amana!

2.5 Kammalwa


Wannan babi ya bi da mu cikin wasu daga cikin misalan wak’ok’in gargajiya da suka shafi wasanni. An misalai daga wasannin dandali na yara maza da mata, da kuma wasannin tashe na yara maza da mata. Yana da kyau a fito da wad’annan wak’ok’i fili sannan a daddage su filla-filla domin bankad’o falsafar da kowanne ya k’unsa.

 

 

 

 

 

Manazarta


Abdullahi, S. M. (2017). “Kud’i A Idan Mawak’an Hausa Na Baka Da Rubutattu, Wak’ar Kud’i Ta Alhaji Audu Wazirin D’anduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja” Kundin digiri na farko da aka gabatar a Sashen Harunan Nijeriya, Jami’ar Usamnu ‘Danfodiyo Sakkwato

Bello, S. A. (2017). “Tasirin Wak’a A Cikin Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Wak’ok’k’in Aminu Ladan Abubakar.” Takardar da aka gabatar a taron masoya Aminu Ladan Alan Wak’a, a makarnatar Ado Gwaram, Kano

Birnin-Tudu, S. Y. (2002). “Jigo da Salon Rubutattun Wak’ok’in Fura’u na K’arni na Ashirin.” Kundin babban digiri na uku (Ph. D.) wanda aka gabatar a Sashen Harrunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (1988). “Nason Kirari Cikin Rubutattun Wak’ok’in Hausa na K’arni na 20.” Mak’alar da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Dangambo, A. (2007). D’aurayar Gadon Fede Wak’a. Zaria: Amana publishers LTD

Gusau, S. M. (2003). Jagora Nazarin Wak’ar Baka. Kano: Benchmark.

Habibu, L. (2001). “Bunk’asar Rubutattun Wak’ok’in Hausa a K’arni na Ashirin (20).” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.

K’aura, H. I. (1994). “K’awancen Salo a Tsakanin Rubutattun Wak’ok’in Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa.” Kundin kammala digiri na biyu (M.A.) wanda a aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

D’angambo, A. (1980). “Hausa Wa’azi ‘Berse Fron CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style. A Ph. D. thesis submitted to the Uni’bersity of SOAS, London.

Yahya, A. B. (1987). “The ‘Berse Category of Madahu With Special Reference to Theme, Style and the Background of Islamic Soures and Beliefs.” A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu ‘Danfodiyo Uni’bersity, Sokoto.

Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Wak’a. Kaduna: Fisbas Media Ser’bice.

‘Yar’aduwa, T. M. (2010). Jagoran Nazain Rubutaccen Adabin Hausa. Ibadan: HEBN publishers PLC.

Zurmi, A. D. (2006). “Tsoratarwa a Cikin Wak’ok’in Wa’azi na Nana Asma’u.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.

 

Kafar Intanet


www.amsoshi.com

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

[1] A nan za su fad’i sunan wacce suke son d’auka daga cikinsu.

[2] Mamman na d’aya daga sunayen da Bahaushe ya samu bayan cud’anyarsa da Laraba, musamman bayan ya kar’bi addinin Musulunci. Mamman na nufin Muhammadu. Sannan Bahaushe na da al’adar sanya wa d’an fari suna Muhammadu, wanda zai iya kasancewa Mamman ko Mammalo. Mai bi masa kuwa akan sa masa Abubakar. Haka abin zai tafi har sai an sanya sunayen manyan kalifofin manzo (SAW) guda hud’u.

[3] A mafi yawan lokuta ana had’a irin wad’annan layun ne da takarda. Wato za a ned’e takarda a mata siffar laya.

Post a Comment

0 Comments