https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
https://www.amsoshi.com/contact-us/
- Shukuran ga Allah wahidun mai agaji,
Da salati gun Manzo aminin shiriya.
- Na yo yabo matuqa dukan asahabihi,
Manyan gwaraje masu nakkasa qarya.
- Saqo garan ya xan’uwa ka tsaya ka ji,
Komi mukai mu bi gaskiya shiryayya.
- Ita ce amintatta a kowane zamani,
A sahu tana gaba ba a kai ta a baya.
- Launinta ba surki fari ne ko’ina,
Riga da taggo ba qananan kaya.
- Ta girmi kowa shekaru wane mutum!
In kai musun haka je ka tambayi qarya.
- Qarfinta ya fi na xan Adam da mutantani,
Doki da zaki ta aje musu kuyya.
- In ta tsaya gantsarwa doro babu shi,
Ziqau take tankar a soke tavarya.
- Muryarta daxi ke gare ta a ko’ina,
Ga shiga jiki ta zarce sautin kurya.
- Zance na kowa bai fice ba nata ba,
Ita qunshiyar zancenta bai da musanya.
- Zancen waninta ya bar xaga maka hankali,
Bari dai ta furta yanzu ka ji kumurya.
- Ba ta Karen miski da shadda don qawa,
Mai su idan ya rasa ta zai yi quyaya.
- Ba ‘yar sarauta ce ba, ba ‘yar fada ba,
Fadar da babu ta an baro ta a baya.
- Carbi, tulin rawani, gafakka, kandili,
In an rasa ta su zan tumullin kaya.
- Faxi gare ta qure ta wane xan Adam!
Wane gaban qato taya ta amarya?
- Ce babu shakka shi tsawo ko rijiya,
Qarya ka xan rame da babu mavoya.
- Iccenta shi ka fure da ‘ya’ya mai yawa,
Wane kaxanya xorawa da magarya.
- Ita ce nagartar jarumai a fagen faxa,
Ta tsere sanda wargajewar kwanya.
- Manyan mazanta a ko’ina su ke zara,
Maqiyansu dole su vuya tun day hanya.
- Dokinta dole fagen suka shi ke zagi,
Sauran a bayan nata sui ta tavarya.
- Mai son ta in ya guje ta kunyanai take,
Zangonsu bai nisa ta bar shi a hanya.
- Mai son ta, mai aurenta, ba ya da fargaba,
Shi ke zagin taro a kowace hanya.
- Komai ya lalace idan aka bincika,
Ita anka ba tsoro saboda hamayya.
- Ita xai ta kai maqiyinta ke kewan ta zo,
In an ka gurmatsai cikin gogaggya.
- Ita ce watan Salla saboda farin jini,
Ciyo ga reta ga masu wasan vuya.
- Akushin tuwo ce babba ta ishi unguwa,
Don ba ta varewa ya kumbun qwarya.
- Ita sanfara ce babba gagari muciya,
Tuqin tuwo in ga ta ba a tukunya.
- Allonta ba ya faso ku tambayi Gangaram,
Alaramma ba ya musanta iccen danya.
- Zaqinta ya zarce zuma saqa fari,
Balle maxi da ake da ‘ya’yan xinya.
- Ita tat tsayar da samai qasai ba ginshiqi,
Da wata da taurari irin su Surayya.
- Mai gaskiya bai waiwaya in ya wuce,
Bai dube-dube irin na xaukar kaya.
- Bai soke kai qasa juddadun ya qi tassuwa,
Fuskarsa ba ta baqi irin na tukunya.
- ‘Yar tsohuwa ke samun sa’ar zamani,
Tsufanki duk bai sa jikinki mijirya.
- Surukinki yai sa’ar xiyar babban gida,
Ko ba a so sunansa dai Rabakaya.
- Ba ta kira a qiya a tsira da arziki,
Magujinta sai ya gama da wasan vuya.
- Tsoron mijinki a dole ne don xaukaka,
Tun bai tsaya ba ake riqe masa kaya.
- Ki yi dariyarki da gaske ba mai ja da ke,
Hauru farare ba baqi da wushirya.
- An ce da ni ke yada zango Yawuri,
A cikin garin Ngaski in ji Baraya.
- Na gai da rini masu kere itatuwa,
Xan goriba tilas ya gai da giginya.
- Kushe ki yas sa duniya tay yamutse,
UN tana ta rabon faxa da tavarya.
- Nijeriya an bar Arewa cikin duhu,
Ta yi cefane amma tuwo ta ci gaya.
- Duk wanda yaq qi batunki zai da na sani,
Domin gudun ki ka sa a faxa haxaya.
- Muddin kina tsaye wa mutum ya yi kangara!
Wasan kixi da rawa a qaga mashaya.
- Fafau ba za ki faxa ba sai ke tabbata,
Zancen da duk ba ke ba shi ne qarya.
- Roqon da nay yi Aliyu Bunza ga Qadirun,
Koyaushe tare da ke muke baja kaya.
https://www.amsoshi.com/contact-us/
0 Comments
Rubuta tsokaci.