Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Laifi Tudu Ne’ Ta Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

    www.amsoshi.com


  1. Allah na rok’i taimako ga rubutuna,


Na nemi dubun tsari ga dukkan lafazina,

Kar in cutar da masu son saurare na.

 

  1. Taso haba d’an'uwa ka zo in maka hira,


Na ji ana tsegumi shiru ba mai gyara,

Lungu-lungu ana k’idayan laifina.

 

  1. Laifin farko rashin zamana d’ibgagge,


In koma baya in kasance jibgagge,

In bi wanin Jalla kun ji farkon laifina.

 

  1. Ni da na yo sassabe da turbe nai maimai,


Ga taki ya yi kyau ga shuka ba k’amfai,

In tsiri yin k’wadago ga gonan mak’iyina.

 

  1. Wai don na gamsu gun rabon mahaliccina,


Na k’i aminta ga galihun mai tsince na,

Girman kai an ka fassara shi ga laifina.

 

  1. Laifin ga na ukku shi kad’ai ke ban haushi,


Gurgu ke arashi da zund’en tarkoshi,

Na ce a yi hattara a shashace batuna.

 

  1. An ce rowa gare ni wai ban sake hannu,


Ban kwaso kud’in haramiya in saye shanu,

In kai su kiyo gidan wad’anda ka zargina.

 

  1. In dai kauce wa d’an hali ne laifina,


In zama Nazak’i ko'ina a ji sunana,

Na yahe zama da ku abokan hirana.

 

  1. Laifi na biyar gare su wai na cika sabko,


Don me koyaushe ni ka kwashe kashin farko?

Kamin su iso su iske na kwashe rabona.

 

  1. Laifin ga na shidda wai Alu yai musu rata,


Don me koyaushe Rabbana nai mini gata,

Me zan cewa a nan, na kare laifina?

 

  1. Laifi na bakwai gare su na k’i zama wawa,


Na k’i aminta a sa zuma ga kunun kunwa,

In an ka ta’be ni take in hau bakina.

 

  1. Laifi na takwas da Audu yal labarta min,


Wai na cika hasadar su, nan sun ka diran min,

Me sun ka aje da babu ninkinsa gidansa?

 

  1. An so a had’a ni yin fad’a da abokaina,


An ka gaza an ka lalla’bo ga mak’wabtana,

Na'  ahumo nat tsaya da kyau da k’afafuna.

 

  1. Laifina k’in bari a ‘bata mini suna,


Bayan k’azafi da tsegumin cin zarafina,

Ya zama tilas a yanzu in hau bakina.

 

  1. An ce, wayo gare ni ba a yi min burtu,


Rami duk an ka yo ina mai sai guntu,

Take in tsallake hak’on ga k’afafuna.

 

 

 

  1. Laifina k’in bari a kad’a ni akulki,


Na k’i sako kai a dank’arai bahagon kulki,

Bayan na gangara a aure matana.

 

  1. An ce, rigima garan kaman mai kashe kura,


Don na hana doli-doli ‘bata muna shara,

Na kwakkwashe shi na zuba shi a kwandona.

 

  1. Laifina gyangyad’i idan na gaza kwana,


In ya fizge ni ba a j in hansarina,

‘Dan motsi d’an kad’an na bud’e idanuna.

 

  1. Na kai musu ko'ina saboda zuwa gona,


Hannu biyu kowane wata ga adashina,

Bakin k’arfin talakka na ima gidana.

  1. Mamakin duniya Alu na gaza barci,


‘Dan bokona ya tsunduma su cikin k’unci,

Hab bisa karaga ana ta kamun sunana.

 

  1. Na rantse har ga wanda yay yo ni Ta'ala,


Ban ta’ba jin kai ba ko kirarin sa mala,

An ka sawo an ka sakad’a bisa laifina.

 

  1. Laifina ba ni gaisuwa, ban kai kaiwa,


Na k’i tumulli da jewad’i garkar kowa,

In bi dare jijjihi ina kai kukana.

 

 

 

  1. An ce ni nah hana ma jam'iyya girma,


Don na k’i bari a mai da al'umma kurma,

Na ce a yi hattara da wasan Afajaana.

 

  1. Kwat tuba da yin kid’in duma ba ya na kurya,


‘Dan Babule ya tuba bai kama garaya,

Kun ji misalin da nay yi an ka ga laifina.

 

  1. Ban ta’ba jin kai ba ba ni k’aunar son girma,


Je tambayi 'yan ajimu had da abokai ma,

In ka yi musun su tambayo malammaina.

 

  1. Laifin Ali yai yawa rashin k’yale azazza,


In bar mak’iya su hau cikina su yi murza,

Har in yi kururuwa a ruga cetona.

 

  1. Laifina k’in hawa kujera mai laud’i,


In yi ta doro a kewaye ni ana kaud’i,

In ba da haramiya a k’ara mini suna.

 

  1. Ban ta’ba k’aryar had’in jini da sarakai ba,


Ban ta’ba cewa gidanmu an gaji kud’i ba,

Koyaushe fad’a ake had’a ni da Sardauna.

  1. Faufau ban gaji sank’iranci ga uwa ba,


Ban gaji zama a fada faufau ga uba ba,

Koyaushe a Kanwuri ake kai k’ara na.

 

  1. Don na k’i zama a fada tallan gil’boshi,


Kigama Malam Nak’ok’i mai 'yan k’issoshi,

Hannu ga gaba da ya ji an kiri sunana.

 

 

 

  1. Wai laifina da nag ga an matsa sara na,


Nag gangame nau-ya-nau na jaye jiragena,

Nak’ k’etara lafiya da ni da iyalaina.

 

  1. An ce sauri garan ga fid do ra'ayina,


Ga kuma tsaurin tsiya ga kare tunannina,

Na k’i zama rak’umi a ja da akalana.

 

  1. An ce suna Alu fad’a ne da hasumi,


Mis sa doki ka zabura in ya ji k’aimi?

Ai ta kilisa ana gumi ko ba rana?

 

  1. Kowa yas san halinmu mun fi zuma zak’i,


Wa za a haye da caccaka a ji mai sauk’i?

In wannan ne fad’a rina ne sunana.

 

  1. ‘Dan samuna da bai wuce d’ebi had’e ba,


Shi ne laifin Alu zaman ban ta’bare ba,

In zama kekenmak’a ga d’akin mak’iyana.

 

  1. Laifina babba sun ka ce neman kud’d’i,


K’aunarsu na zo wurinsu rance su ji dad’i,

In kasa biya a hau duron a ci sunana.

 

  1. Sun ce yawo garan kamar naira birni,


Take a gane ni na wuce ka ce zunni,

Na k’i zaman dandali na cin naman juna.

 

 

 

  1. To kai Mannanu mai d’uwawun kashe wundi,


Tun Ikko a k’unso tsegumi sai Mungadi,

Kai ka musu tsintar rubutunmu Kaduna?

 

  1. Laifin d’aya nai zaton kaman sun manta shi,


Nat tar da uban gidansu na nanata shi,

Wai na k’i shiri da masu ‘bata mini suna.

 

  1. Assha maganar ga ko kad’an ba ta taso ba,


Mai bin Sunna dad’ai shari’a yaka duba,

Don ita ke canjaras a gane kuren juna.

 

  1. Ban ta’ba jin muminin da an ka k’uk’unta ba,


An ka kwarare shi an ka so a sabatta ba,

Yak’ k’i ya ruga kwatankwacin k’yasta ashana.

 

  1. Ban ji sahabin da ya aminta a cuta ba,


Ban mu ga nassin da sun ka rungumi mak’iya ba,

Mai yawo ko’ina shi ‘bata musu suna.

 

  1. Ba mu da k’imar da taw wuce darajar suna,


Ba mu da girman da yaw wuce kyawon suna,

Mai cin zarafinsa ba shiri ku ji zancena.

 

  1. Kowane buzu da rak’uminai shika gata,


Malam bai d’aukaka idan ba makaranta,

Wa zai zama kamili idan ya rasa suna?

 

  1. In Dakka Na’umme na rawan gwalmo a gona,


Roggo da makunyaci da d’an gugar zana,

Ba ai musu take don gudun ‘banna suna.

 

 

 

  1. Zargi ya kasa cin Alu an bid’o yuk’a,


Had da itace da sanduna igiyar tunk’a,

Bayan an rataye a bizne kabarina.

 

  1. In nim mik’o wuya a damk’e sai yanka,


Barho na sha-da-yanzu mai mugun yanka,

Fatarsu guda shi samu kai ga mak’oshina.

 

  1. Babu faragar gudu zaman rami an nan,


Suna nai yunk’ura ka sake direwa nan,

Ga zarto an aje na yanke k’afafuna.

 

  1. Ko na yi gaba-gaba da taro wane ni!


Don na ga barandami da kaifi kaico ni!

Alk’awali sun ka yo na zazzage tumbina.

 

  1. Manta da batun zama bala’i yai nisa,


An sa ni cikin rutsin da ba d’aukar fansa,

An sa sark’a ga hannuwa da k’afafuna.

 

  1. ‘Dan dama na guda abin yai mini sauk’i,


Tuya an manta albasa ba ta mask’i,

An manta abin da za shi lik’e bakina.

 

  1. Laifina ba ni rena duk mai ra’ayina,


Zan sake fuska da murmushi gun bak’ina,

Ka ce mun shekare d’ari da sanin juna.

 

 

 

  1. Na k’i zama dabba’una mai fuskar shanu,


In sha toka da ‘bata rai in rik’e hannu,

Wai ni k’ato a daina wasa a wajena.

 

  1. Ban ce a k’i shugaba ba ban kuma zargai ba,


Shi ko shi sani fa ba kaman Annabi ne ba,

Bai kwaso ta’basgara ya ‘bata muna suna.

 

  1. Ni dai ban ce rabon kashin bai gamsan ba,


Ban ce a raba da ni a k’yale kowa ba,

Cewa a raba da kyau ya sa aka zargi na.

 

  1. Koyaushe uban kashi ya kwashe kashin farko!


In an luro shi ce gidanai aka aiko,

Wai ‘yammuna yay yi yaudara safe da rana.

 

  1. Laifina yin tsayin daka in bi abina,


Don na hana zurmugud’d’u faufau ga kasona,

An ka yi banga da ‘yan rawa a k’i takena.

 

  1. Ban ga dalili na mak’urar d’an aike ba,


Ga mai aiken ana gani ba a dokai ba,

K’arya filin wuri a sake mata suna.

 

  1. Babban nak’ali ka san halin masu kula ma,


Kai ko ka tsaya da kyau ka bar ba su makama,

An ce raggo ya sha hura ya sa’ba gona.

 

  1. Babban magana a kanka kowa ya gaya ma,


Kar ka yi aikin da za a rena maka girma,

In ta ru’ba Kamba sunsune ta a Banganna.

 

 

 

  1. Kyawon d’a har ya kwanta dama ga sarkinai,


Bai muzantar da malami magabacinai,

Balle a had’a da shi a ‘bata musu suna.

 

  1. In ga wayo da hankali da sanin girma,


‘Dan tsako zai gwada wa giwa ya girma,

Don ta kula mai ya je ya ‘bata mata suna.

 

  1. Wautan Jigji hawan kirari ga kura,


Ya ji awaki suna fad’in: “Ka wuce tsara”,

Wai don bokansa ya yi mai layar zana.

 

  1. In kag ga mutum shina kirarin ya girma


Tambas shi wurin da yas sayo shi, shi nuna ma,

Kowac ci tumu shi gai da mai shukan gona.

 

  1. Jin kai na mai da malami bawan gona,


Girman kai bai barin matashi ya yi suna,

Rowa na k’addaro wa d’a mugun suna.

 

  1. Son kai ka kashe mutum da sauran shed’anai,


Rena mutane ka sa mutum a k’i k’aunatai,

Cin fuska ke mayar da k’arshe mummuna.

 

  1. Mun dai san yau da gobe ba ta barin komi,


Shi ne hujjan hura da ta kwan ta yi tsami,

Komi k’arshe garai ka saurari batuna.

 

 

 

  1. Ba mamaki miloniya ya zama gyartai,


Mai mulkin duniya ya k’are d’an kwantai,

Malam ya yi sank’ira wurin taron suna.

 

  1. Kowa Allah Yana biya tai da halinai,


Bayinai kowanensu Ya san matsayinai,

Can ga hukunta su tabbata bai yin sauna.

 

  1. Komi muka yi mu san ana nanata shi,


Can ga hisabinmu Rabbu za Ya hukunta shi,

Ga zantukkanmu ga sikeli, kaicona!

 

  1. Ban dai ta’ba arashi ba ban san zambo ba,


Ba zan yi k’ire ba lura ba wak’a ce ba,

Tarihi ne nake zubawa a fagena.

 

  1. Komi nisan dare ana dakon rana,


Wane mutuwa ta d’auki mai sauran kwana,

Na shedi hakan ga tun ga Salihu kakana.

 

  1. Matarsa Gadaje san da taj ji kalamaina,


Tac ce: "Tafi sa ido ka kwanta ka yi kwana,

Sai ka ji karakkiyar damuttsansu da rana."

 

  1. Na yarda Waliyiya Waliyi taka aure


Ba su tunani a iske ya zamto gajere,

Ba su barin zuriya a ce ba ta da rana.

 

  1. Tammat na kammale muradin k’udurina,


Wak’ar da na hangi masu son su ga laifina,

Don d’ai hasada da kushe dukkan lamarina.

 

 

 

  1. Na rok’i rabo ga Rabbana mahaliccina,


Ranar da Ka k’addaro da k’arin kwanana,

In shiga ceton Nabiyu in tsallake k’una.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments