
Sufiyanu Abubakar
Hassan Ladan
Hassana Mustapha Ibrahim
BABI NA BIYAR
Kammalawa
Babi na biyu na wannan aiki an masa taken ‘tak’aitaccen tarihi da asalin garin Yabo.’ Yayin kawo wannan tarihi, an kawo tarihin wasu muhimman mutane da su ne suka samar da garin na Yabo. Daga cikinsu akwai Malam Muhammadu Moyijo, wanda shi ne sarkin Kabi na farko. An kawo tarihin rayuwansa da kuma wuraren da ya zauna a lokacin rayuwarsa. Sannan wannan babi ya kawo tarihin yadda aka samu lalacewar dangantaka tsakanin Moyijo da hukumomin daular Kabi. Sannan an tattauna mubayi’arsa ga Shehu Usmanu Danfodiyo. Daga nan kuma aikin ya kawo ire-iren wasannan gargajiya, musamman wad’anda ake samu a garin Yabo. Sannan aikin ya kawo amfanin wasannin gargajiya, wad’anda sun had’a da tarbiyyar yara da motsa jiki da makamantansu.
Babi na uku ya kawo bayani game da yadda ake aiwatar da wasanni a k’asar Yabo. Wasannin da aka yi sharhinsu sun had’a da afajana da jini wa jini da ‘yar ato da ‘yar tsana da makamantansu. Babin ya kawo yadda ake gudanar da wad’annan wasanni da kuma irin wak’ok’in da ake rerawa yayin aiwatar da wasu daga cikinsu. Sannan aikin ya kawo rukunnen jama’ar da ke gudanar da wasanni. Wannan rukunne sun had’a da na yara da samari da ‘yan mata da kuma manya ko dattawa. Baya ga wannan, aikin ya kawo bayani game da lokutan wasanni. Lokutan sun had’a da wasannin rana da kuma wasannin dare.
Babi na hud’u ya yi duba ne zuwa ga tasirin zamani a kan wasannin gargajiya na Hausawa musamman a k’asar Yabo. Babin ya kawo dalilan da suka kawo dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo. Wad’annan dalilai sun had’a da samuwar ilimin addini da ilimin boko, da kuma samuwar hanyoyin sadarwa na yanar gizo. Wasu k’arin dalilan susashewar wasannin gargajiya a k’asar Hausa wanda babin ya kawo sun had’a da halin ko-oho da shuwagabanni suka yi ga wasannin da kuma samuwar finafinai a k’asar Hausa.
Sakamakon Bincike
Wannan bincike ya kai ga fahimtar ko gano wasu abubuwa da dama. Daga cikinsu akwai:
- Wasannin gargajiya suna da matuk’ar amfani musamman ta ‘bangaren motsa jiki da k’arfafa dank’on zumunci da samar da tarbiya da makamantansu.
- Wasannin gargajiya a k’asar Yabo suna fuskantar barazanar ‘bacewa kwata-kwata, wanda idan ba a d’auki wasu matakai ba, za a iya neman su a rasa nan ba da jimawa ba.
- Akwai dalilan da suka samar da wannan dusashewa na wasannin gargajiya, sun had’a da tasirin zaman da rashin kulawar hukuma da makamantansu.
Shawarwari
Ta la’akari da sakamakon bincike da aka zayyana a sama, wannan aiki ya tanadar da shawarwari kamar haka:
- Ya kamata a rik’a tuna d’inbin amfanin wasannin gargajiya, hakan zai sanya a ga dacewar hu’b’basa domin tabbatar da farfad’o da su.
- Ya kamata a yi hu’b’basa daga ‘bangarori daban-daban, wato tun daga ‘bangaren hukumomi da kuma al’umma karan kansu, domin tabbatar da farfad’o da wasannin gargajiya tare da ingantasu, musamman a k’asar Yabo.
- Ya kamata a yi karatun ta nitsu a dalilan da suka kawo dusashewar wasannin gargajiya, domin magance su.
https://www.amsoshi.com/game-da-mu/
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.