https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

Sauraro Da Rubutawa

Shu’aibu Murtala Abdullahi

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

 

 

Mu koma jawabin kud’i tara dangi

Akwai gargad’i masu neman kud’i,

 

Ina ‘yan uwanna ku zo ga jawabi,

Muna yin wa’azi ga neman kud’i.

 

A yau ba hari ba samame da yak’i,

A yau babu sauran batu sai kud’i.

 

Ku sa hank’uri ki kawai ku fahimta,

A yau zan gaya muku ranar kud’i.

 

Zama da duhun kai yana damuwarmu,

Mu bar yin sa yau gara neman kud’i.

 

Gama wajibi ne kud’i a bid’e su,

Musulmi da arne mu nemo kud’i.

 

Ku zo gargad’i zan yi duk mai fahimta,

Idan dai ya gane ya nemo kud’i.

 

Jama’a mu daure, mu cije, mu jure,

Mu tayar wa aiki da neman kud’i.

 

A je Ikko kar mu sake, don fatauci,

Mu je har Junaina mu nemo kud’i.

 

A dimanci jaki da jirgi da mota,

Kaza rak’umi mui ta neman kud’i.

 

Mu sa musu kaya mu hau su mu kora,

Mu keta dawa mui ta neman kud’i.

 

A jirgi mu sami abinci mu k’umshe,

Su ba mu ticket don su kar’be kud’i.

 

Mu zauna kujera mu kinkintsa kaya,

Mu dunga kula don ‘barayin kud’i.

 

Idan za mu sauka tasha sai mu shirya,

Mu d’aure tufafi da kayan kud’i.

 

Mu bar ribibin nan na jirgi ya fad’a,

Saboda da ‘barayi mayanka kud’i.

 

Ka lura da bai d’an dako sai ka bi shi,

Idan kai sake babu kayan kud’i.

 

Ka sauka ka nemi wuri mai mutunci,

Gama ba sakewa a neman kud’i.

 

Idan kai sake, sakiya sai ta hauka,

Su bar ka da kuwwa sun d’auke kud’i.

 

Idan kuwa a mota ka zauna a benci,

Da kayammu ba ya na neman kud’i.

 

Direba, “I” ja mu sannu don kar ta k’wace,

Mu tai tafiya mui ta neman kud’i.

 

Ku bar son a zauna a talbodi mota,

Gama lafiya ta fi taron kud’i.

 

Fatauci, giya, caca, neman kilaki,

A bar yinsu in dai ana son kud’i.

 

Idan ko akan rak’umi ne amale,

Ku gyara cukurfai na neman kud’i.

 

A kai rak’umi gun dawa ya yi kiwo,

A kamo shi kan za a neman kud’i.

 

A sa mai akala a ce, “Ish” ya duk’a,

A sa tarkace don fataucin kud’i.

 

A bar son a lauta amali ya kasa,

Ga babu kyawo manema kud’i.

 

Idan kau a jaki kake yin fatauci,

Ka sai aura ka jaba mai jud’i.

 

Ka sai mangala wanga aikata taiki,

Ka nemo tayakai na neman kud’i.

 

Ka sai akumari abin lauta taki,

A gyara shi don lauta kayan kud’i.

 

Ka nemo kwari da baka har da mashi,

Akwai ‘yam fashi masu k’wata kud’i.

 

A je nan kwana tashi a zarce,

Da d’ari da ra’ba a neman kud’i.

 

Ka je wani dajin ka kwan a ciyawa,

Ka kwan babu barci a neman kud’i.

 

Ka je gun tayi sai a zage ka malam,

Ba za kai fushi ba a neman kud’i.

 

Gama mai bid’a ba a son yai husuma,

Ida ya yi sai yai asarar kud’i.

 

Idan kai fad’a ba kud’i ka ci d’auri,

Kamar ya yi satar akwatin kud’i.

 

Ina mai fatauci da zamba da rinto,

A bar yin su in dai ana son kud’i.

 

Ka bar ‘bata kai don fura bando rinto,

Idan ka yi sai kai asarar kud’i.

 

Kud’i in da dad’i mutunci da dad’i,

A bar ‘bata ‘yanci manema kud’i.

 

Kd’i na sani ba a samun kamassu,

Samari mu daure mu nemo kud’i.

 

Gama lafiya dai da rai sun fi komai,

Akan ba da su don a samo kud’i.

 

Idan kai musu sai ka dubo ‘barawo,

Dare zai bi don ya sato kud’i.

 

Akan aje mashi dalilin ‘barawo,

Yakan je a soke shi domin kud’i.

 

Ilori su ce “Olie,” Hausa, “‘barawo,”

Fulani su ce, “Gujju” kayan kud’i.

 

K’asar Larabawa da “Sarrak’” na san shi,

Sukan yanke hannun ‘barawon kud’i.

 

Da ingalilo, gatari har da mashi,

Ana yin su domin ‘barawon kud’i.

 

Ana d’aure mugu da jifa da sowa,

A faffasa kayin ‘barawon kud’i.

 

Wad’ansu a harba su fad’a a rami,

Suna kan shiga don su sato kud’i.

 

Ku bar ma ta wannan ku zo ga misali,

Da zam ba ku domin sharar kud’i.

 

Ku dubo akan soja masu yak’i,

Suna sai da rayinsu domin kud’i.

 

Ana kashe wasssu, dubu su lahanta,

Ana kan shiga don a samo kud’i.

 

Ku sai ya da a daji jama’a,

Kud’i “cede belde” mu nemo kud’i.

 

Fulani mutan Yola – cede beld’e,

Jede hirma har sula neman kud’i.

 

Ku ji kuguna wuri dad’i jama’a,

Abin burge yaro da mata kud’i.

 

Maras lafiya na ta nishi a d’aki,

Da ka girgiza sai ya dubo kud’i.

 

Idan ban da rayi kud’i ya fi komai,

Abokin zaman lafiya rai kud’i.

 

Abincin da duk ka sani yau a duniya,

Kana so shi ka gan shi in kai kud’i.

 

Fatauci yakan karya k’arfin talauci,

A yau babu damar zama ba kud’i.

 

Akan bar iyaye, abokai da dangi,

A je wani lardi a nemo kud’i.

 

Akan bar iyali da mata da ‘ya’ya,

A watsar a ruga a nemo kud’i.

 

Wasu a neman su samo su dawo,

Wad’ansu su watse a neman kud’i.

 

Wad’ansu ko ba kud’i ba mutunci,

Da dama akan ‘badda su don kud’i.

 

A zo babu k’arfin jki ba mutunci,

A je babu ilmi, a zo ba kud’i.

 

A je babu tsuntsu, a zan babu tarko,

Ta’ala ka fisshe mu sharrin kud’i.

 

Kud’i za mu neme shi Allah ka ba mu,

Ka sa kar mu ta’be a neman kud’i.

 

Ku bar gajiya ga batu d’an k’alilan,

Ina son ishara a neman kud’i.

 

Kamar da ubanka ina yin sarauta,

Idan babu shi ba ka hanayr kud’i.

 

Kana duba bawanka ba ka ikon,

Ka ce masa k’ala idan ba kud’i.

 

Idan ba ka komai kan yi talauci,

Da kai gara bawan da ya san kud’i.

 

Idan shi ya samo kud’i shi fa bawan,

Ya ce d’an ya ji sai ya je don kud’i.

 

Ya aike shi tilas ya je ba shi ikon,

Ya ce ya k’i in dai yana son kud’i.

 

D’iya sai su bauta wa bawansu dole,

Idan sun ga bawansu ya san kud’i.

 

Idan kai kud’i babu sauran lalura,

Gama zamani ne na neman kud’i.

 

Idan kai kud’i mai k’asa sai I so ka,

Ka je shawara fada domin kud’i.

 

Ka je fada manyan gidan sai su tashi,

Ku gana da sarki a dad’in kud’i.

 

Abin da I dame ka duk sai ka bud’a,

Tsakaninku sai kai da shi don kud’i.

 

Ka shisshirya zancenka ko kwai da babu,

A kar’ba a zauna a kai don kud’i.

 

Idan ka yi zancenka sarki ya d’auka,

Bare di’o gwamna mutanen kud’i.

 

Idan mai kud’i yai fad’a babu shaida,

Da shedunsa ‘fefa’, takardar kud’i.

 

Shi k’umsa, shi kai fada in anka gane,

Ba a ta da tad’in ba domin kud’i.

 

Idan ba ka komai ina za ku gana,

Da sarki bare di’o mai son kud’i.

 

Da ka doshi k’ofar akwai masu gadi,

Bafade ya turo ka don ba kud’i.

 

Idan ka ga sarki akwai d’an  dalili,

Idan ba fad’a, ka yi satar kud’i.

 

Dalilinsa shi ne isa za ku gana,

Da sark’a a hannun ‘bayaryin kud’i.

 

Irin wagga ba ma buk’atar ganinsa,

Ta’ala ka fisshe mu satar kud’i.

 

Kud’i kan na ce zan fa d’ura in k’unsa,

Gari sai ya waye ga zancen kud’i.

 

Mu tashi mu bar gyangyad’i mui ta niyya,

Mu zage damtsu mu nemo kud’i.

 

Kud’i shi ya kan sa a saba da aren,

Musulmi akan k’i shi im ba kud’i.

 

Akan tashi malam a zaunad da arne,

Idan an ga arnen da halin kud’i.

 

Idan malami ya yi zance a murd’a,

A gaskata kasge a dad’in kud’i.

 

A bai jahili gun zama mai mutunci,

A zaunad da malam a k’ar don kud’i.

 

Kud’i shi ya kan hana ilmi hak’ik’an,

Mu zan Ingilshi na neman kud’i.

 

Kud’i shi ya kan sa zumunta ta watse,

Ana kashe juna a neman kud’i.

 

Kud’i shi yakan sa a watsad da dangi,

A kore d’iya masu ‘barnar kud’i.

 

Rashin mai yawa sai ya ‘bata ibada,

Yana tauye ilmi idan ba kud’i.

 

Tilawa izu arba’in sai ta rushe,

Ta dawo bakwai ko biyar don kud’i.

 

Idan kun ga gardi yana yin sikola,

Jimawa kad’an za shi neman kud’i.

 

Kud’i ya riga ya ciyo zuciyarmu,

Ana bin ta gangar jiki don kud’i.

 

A neme shi, amma idan anka samu,

A bar yin butulci manema kud’i.

 

Idan anka samu a bar ratse hanya,

Mu k’are da hairan idan mun kud’i.

 

Ashe shi kud’i ba shi gimsar jama’a,

Ka ce ya isan ba ka neman kud’i.

 

Ku dubo kud’in Larabawa jamu’a,

Ku dubo ga U.A.C. sun san kud’i.

 

Da mota da jirgi da bubur na aiki,

Da d’ayyar na jirgi na neman kud’i.

 

A kan ahu sisin kwabo in ka d’auka,

Sukan d’aure yaronsu domin kud’i.

 

Idan da kud’i na isan ‘yan jamu’a,

Kano Alhasan ba shi neman kud’i.

 

Na-Goda, Na-Malam a Jos sai su zauna,

Su ce ya isan, ba su neman kud’i.

 

Idan nai kure malamaina ku gyara,

Wa almaji Gamba mai son kud’i.

 

Da zai yi baiti d’ari shidda,

Da sittin da shidda na wak’ar kud’i.

 

Ku ji ni ku bar jin wuta jui kawaita,

Batun malamin masu neman kud’i.

 

Ku bar tsuguno, zaune za kui ku huta,

Da sauran kirari ga zancen kud’i.

 

Kud’i dai ana sonsa ba mu kad’ai ba,

Musulmi da arne ana son kud’i.

 

Kud’i ya fi kowa masoya a duniya,

Gama ga ishara masoya kud’i.

 

Kwara, Larabawa, Bature, Bahaushe,

A yau ko Majusu suna son kud’i.

 

Da mata, mazansu, da ‘ya’ya da bawa,

Tsaya ko na turu yana son kud’i.

 

Masuki, kaza kuturu duk da gurgu,

Makaho, laifi yana son kud’i.

 

Da malam da almajiri du da gardi,

Da kotso, da kuri suna son kud’i.

 

Mutum ya k’i salla da zakka da hajji,

Da tauhidi amma yana son kud’i.

 

Da arna da matansu sun huda le’be,

Mazan ga kororo suna son kud’i.

 

Da sarki kaza hakimai dagatansu,

Tsaya ko bafada ina son kud’i.

 

Sarauta da kanta idan babu samu,

Ina kwarjinin nata kan ba kud’i?

 

Abin tsere tsara a yau ba ya cede,

Ina wanda ba ya buk’atar kud’i?

 

Tsaya zan yi zance da Fulfulde malam,

Mu shaida wa ‘yan Ful’be ranar kud’i.

 

Da da liyari da cede,

Wuri da cambe sunansa babba kud’i.

 

Da sisi, sulalla, aninai da fefa,

Abin yai yawa na tak’aice: kud’i.

 

Kud’i kurd’abi na kud’i ‘boye muni,

Ka d’and’ana dad’insu zak’i kud’i.

 

Da dad’i da tabshi da k’amshi da zak’i,

Da haske da rayin da yas san kud’i.

 

Idan kai kamar alade don k’azamta,

Ba sa gane munin ba in kai kud’i.

 

Idan ka yi kaushi kamar na dabino,

Ba sa gane kircim ba in kai kud’i.

 

Miyangu idan yai kud’i sai a bi shi,

A ce masa malam na dad’in kud’i.

 

A ce masa gafarta malam ya amsa,

Ina d’an dalili? Dalili kud’i.

 

Ya dubo Musulmi ya ce masa arne,

A ce haka ne mai gida, don kud’i.

 

Idan kai kamar Larabawa a kyawo,

Ba sa gane kyawon ba in ba kud’i.

 

Ka zauna, su ce tashi, tilas ka tashi,

K’azami ya zuna a dad’in kud’i.

 

Idan ba su, komai farinka da kyawonka,

Da kai gara kunkuru mai kud’i.

 

Idan kai kud’i, dole kowa I so ka,

Ana bin ka in sun ga ka san kud’i.

 

Idan ko kud’i yai k’arancin gareka,

Su wa za su zo gunka in ba kud’i?

 

Ka bai wa d’iyarka miji sai ta k’i shi,

Ta ce ta k’i tad’inka im ba kud’i.

 

Idan ko ka dame ta zagi da duka,

Ta ce za ta karuwa neman kud’i.

 

Ta je can a rud’e ta ko babu ahu,

A d’ibganta ciyyo a domomin kud’i.

 

Idan d’anka ya girma ya kai misali,

Ya je can ya bauta wa wasu kud’i.

 

Ka kamo ka kawo, ya k’wace ya ruga,

Ina za ku zauna da shi ba kud’i.

 

Idan ko ka d’aure sarauta ta k’wace,

Su ce bar shi zai je I nemo kud’i.

 

Ka yayo d’iyan ‘yan uwa in ya data,

Su k’wace shi in sun gani ba kud’i.

 

Ka rok’e shi wai don shi huce shi ba ka,

Su ce za ka ‘bata shi don ba kud’i.

 

Da k’arni da d’aci da gautsi da zafi,

Da haushi ga rayin mutum ba kud’i.

 

Idan kai kud’i ko na bare ka kama,

Ina za a kar’be a gun mai kud’i.

 

Idan ba ka d’a sai su ce kar’bi karo,

Kana k’i suna ba ka domin kud’i.

 

A ce ga budurwa ka aura ka aihu,

Iyayenta sun hangi zaton kud’i.

 

Ka dubo mutum shekaru ba misali,

A kai mai budurwa a dad’in kud’i.

 

Ta zauna cikin ba ta ko k’ara yaji,

A kayi, a kayi, mijin ba kud’i.

 

Idan ka ji mata tana shirga yaji,

A kayi, a kayi, mijin ba kud’i.

 

Idan kai kud’i sai ka tattara shirgin,

Ka watsar su mai da a dad’in kud’i.

 

Iyayen d’iya sai su zo gunka biko,

Su sasanta zancenku domin kud’i.

 

Suna ba ka baki su komad da ‘yarsu,

Ka san ba abin so a yau sai kud’i.

 

Da girman gwani wanda ya yo Alhassan,

A birni, Na-Malam a Jos yai kud’i.

 

Ka sa in yi k’arshen irin na dabino,

Ba za sai na kifi ba, sai na kud’i.

 

A ce ga ka k’atonka kai saurayi ne,

Ina za ka san ‘ya idan ba kud’i.

 

Su ce ga budurwa ka nema mu ba ka,

Su cuce ka san nan su ba mai kud’i.

 

Idan ka yi wa mai kud’i d’an jawabi,

A doke ka nan yanzu gun mai kud’i.

 

A je nan da nan gun saraki a gana,

Ina za ka san gaskiya ba kud’i.

 

Ya ce za ya kotu ya rungumi lauya,

A mummurd’e zancenku domin kud’i.

 

A bar gaskiyar taka don ba ka afu,

A sa masu shaidar riya don kud’i.

 

A yau babu girma ina mai mutunci,

Idan ba sarauta ba sai mai kud’i.

 

Da matan k’warai har da doki da tufafi,

Ina za ka same su? Gun mai kud’i.

 

Hatsi maganin kwarjini har ibada,

Ina za a same su? Gun mai kud’i.

 

Da malam bafade ina za ka gan su,

Idan ba wuce fada, gun mai kud’i.

 

Mu tsoraci Allah, mu k’uanaci ilmi,

A bayan wad’annan mu nemo kud’i.

 

Kana zaune suddan a kai ka Madina,

Ka je kai ziyara a dad’in kud’i.

 

Wad’ansu idan sun kud’i su yi London,

Musulmi su je Makka domin kud’i.

 

A nemo kud’i jama’a kar ku zauna,

Ku bar ce bid’a ba ta kawo kud’i.

 

Abin dunya sai da nema ka samu,

Idan ka k’i ka shirga zambar kud’i.

 

Ka kamo dako yara k’atti su kama,

Su fizge su ture ka don ba kud’i.

 

Ku bar wasani babu shauran a huta,

Ina gun zama rai idan ba kud’i.

 

Idan ka yi gemunka ko yai na taure,

Da yara kake kokawa don kud’i.

 

Mutane su doke ka sarki ya d’aure,

Anai maka gorin ‘barawon kud’i.

 

Su dosa fad’in baba ka cika zanga,

Suna shafa gemunka don ba kud’i.

 

Idan ka ji kai baba mai saje ya kam

Ku tabbata sajensa babu kud’i.

 

Idan an jima ka ji tsohon tsiyan nan,

Ana tashi mai saje, to ba kud’i.

 

Kud’i in ka same shi, to ka zarce reni,

Idan ka rasa ka ji haushi kud’i.

 

Idan ba ka sisin kwabo ba ka ikon,

Fad’ar gaskiya tun da dai ba kud’i.

 

Musu d’anaka zai maka don ba ka ahu,

Ya gaskata k’arya a gun mai kud’i.

 

Idan kai dibararka kowa ya rena,

A ce bai yi daidai ba don ba kud’i.

 

Maras ahu kar kai batu ya yawaita,

Ka k’ask’anta kayinka don ba kud’i.

 

Ka bar cira kanka idan ba kud’i,

A yau ba mutunci idan ba kud’i.

 

Idan ba ka komai cikin masu komai,

Baka k’ulla komai ba im ba kud’i.

 

A cuce ka k’arfinka kai za ka gode,

Zatonka dalilinka kai za kai kud’i.

 

Ka shekara noma a kiyyo a daci,

Ka tara ka kawo wa masu kud’i.

 

Su fanshi arha su tara a d’aki,

A ce ba hatsi sai wajen mai kud’i.

 

A yau babu girma idan mai mtutunci,

Idan ba sarauta ba sai mai kud’i.

 

Ka bar son fad’ar gaskiya ba ka ahu,

Idan ka fad’a an k’i sai mai kud’i.

 

Maras ahu kar kai batu ya yawaita,

Ka k’ask’anta kayinka kan ba kud’i.

 

Ya ce ma ruwan shi ya ke fid da daud’a,

A a ce ka yi k’arya idan ba kud’i.

 

Ka ce rak’umi ya fi jaki jamu’a su ce,

Wane yamma za ai idan ba kud’i.

 

Ka ce na ga nono fari, sai su murd’a,

Su ce bak’i ne idan ba kud’i.

 

Idan ba kud’i babu sauran jawabi,

Zukata sukan damu im ba kud’i.

 

Idan kau kana da kud’i babu shakka,

Maza sa bi shayinka domin kud’i.

 

Karatunka bai kai izu ko guda ba,

Su ce maka malam na dad’in kud’i.

 

Kana baya can nesa ga Sabbi,

Ka dusa wa Ali na neman kud’i.

 

Akan je a tashishi ko wace sa’a,

Ana doka d’akin marasa kud’i.

 

A ce tashi ga mai gida na bid’arka,

Ka je yanzu tilas shi ce don kud’i.

 

Ka je da zuwarka ka duk’a gabansa,

A watsad da kai ai ta k’irgan kud’i.

 

A manta da kai kai zamar har ka k’osa,

Idan sun ga malam yana son kud’i.

 

Ya zauna awa uku san nan ya juya,

Ya ce wane, to ka ji ranar kud’i.

 

Ya ce d’azu wai na ji ka zo gare ni,

Yana hura hanci wai na dad’in kud’i.

 

Kana ladabi sai ka ce mai ibada,

Kana jin jawabin ogan kud’i.

 

Idan ya yi k’arya ka ce gaskiya ne,

Kana gyara tad’insa domin kud’i.

 

Idam ma kana so ka samu ka tashi,

Ka ce maigida ka fi kowa kud’i.

 

Mutane su ce haka ne wane,

To ba a minti guda sai ya mik’o kud’i.

 

Ina gargad’i kun k’i ji, to ku zuna,

A ranar biki a yi zambar kud’i.

 

A shekara arba anai maka gori,

Ina kwarjinin gun ‘barayin kud’i.

 

Ku farka ku bar gyangyad’i mui ta niya,

Idan kun k’i mu za mu neman kud’i.

 

Anai mana gori yana ‘bata rayi,

Ga mai zuciya sai ya nemo kud’i.

 

Maras ahu wai su ce mar kwatogo,

Su ce masa tika idan ba kud’i.

 

K’aho sai a busa, bid’a bashi aski,

Tike tuntu’be, tun’bare ba kud’i.

Fito, na fito, gatari tugga, waji,

Idan ka ji gyanderu rai ba kud’i.

 

Tsakin tsakuwa, tsagawaro, tsaga dutse,

Tsagera kirarin masara kud’i.

 

Maras ahu k’arfinsa ya zarce dutse,

Da k’unci ga rayin mutum ba kud’i.

 

Maras ahu ko shawara kar ku ba shi,

Ba zai gane komai ba don ba kud’i.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/