Ticker

6/recent/ticker-posts

Dusashewar Wasannin Gargajiya A Kasar Yabo (4)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Jahar Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
Sufiyanu Abubakar
Hassan Ladan
Hassana Mustapha Ibrahim

BABI NA UKU

Yadda Ake Aiwatar Da Wasanni A K’asar Yabo

3.0 Shimfid’a


Bakwanta, (2003) cewa ya yi: “Idan Bahaushe ya fad’i abin da ba gaskiya ba yakan ce wasa ne. haka kuma, duk wani motsa jiki da raye-raye ana kiransu wasa. Har yau Bahaushe yakan kira duk wani furuci da kan sa raha da annushuwa, da ba’a a matsayin wasa. Haka duk abin da yaron da bai mallaki hankalinsa ba zai yi (in ban da kuka) to ana kiransa wasa.

La’akari da wannan ma’ana. Za mu iya cewa, wasa na nufin wargi ko giri. Ma’ana duk wani abin da ba gaskiya ba. Yayin da aka fad’i wata magana domin wargi ko giri, to wannan magana akan kira ta wasa. Haka ma yayin da aka aikata wani aiki domin motsa jiki ko nishad’i, akan kira shi da wasa. Kowanne rukunin al’umma suna da nasu salon wasa. Wannan ya had’a har da tsofaffi da manya da matasa da kuma yara. Wato ko dai mutum bai yi wasa a aikace ba, to kuwa ya yi wasa ta magana. Wannan ne ma ya sanya ake da wasa ko barkwanci tsakanin jika da kaka.

3.1 Yadda ake Aiwatar da Wasanni a K’asar Yabo


        Kasancewar wasa abu ce da ta game duniya, don haka kowane gari da irin yadda suke gudanar da nasu wasanni. Akan sami wata wasu, yanayinsu guda, wurin aiwatar da su guda, amma ga suna sun bambanta. Don haka a k’asar Yabo ga yadda ake aiwatar da wasu daga cikin wad’anda na ambata a sama. Akwai:

3.1.1 Afajana


Wannan wata nau’in wasar gargajiya ce, wadda ake gudanarwa a k’asar Yabo kuma matasa ke aiwatar da ita bayan kalaci. Akan sami yara samari kimanin mutum goma (10) ko fiye. Daga cikin su kowane ya kasance yana da gwado (zane) sannan za a sami wani daga cikinsu ya kasance shugaba, watau shi ne sarki wanda zai fara shiga rawa. Sannan a sami wani ya zama mai rik’o (turke) ko kuma a sami falalen dutse ya zama turke.

Kowane daga cikin wad’anan mutane za shi ba da nasa gwadon, a tara wuri guda, sannan a d’auko gwado guda, turke ya rik’e gefe guda sarki ya rik’e gefe guda, daidai da inda aka tara wad’annan zannuwa, ta yadda ba za a iya d’aukar zane guda ba, face sarki ya rik’e ko ya ta’ba wanda ya d’auka. Bayan an shirya wannan, sarki zai ba da damar kowa ya d’uka. Ta haka za a d’auki hankalin sarki, domin a samu a d’auki zanen ba tare da ya ta’ba mutum ba.

Da zaran wani ya sami d’aukar zane, to zai gyara shi, ta yadda yake so ya rink’a ba sarki kashi, ta nan wasu za su sami damar d’auka. Da zaran sarki ya sami sa’a ya ta’ba wani, to wannan shi ne zai kasance a matsayin sarki, shiko ya koma a cikin masu wasar.

Idan kuwa bai samu sa’a ba, har kowa ya d’auka, to ya kama shan kashi ke nan sai ran da ya ta’bo wani, in ko ya ga abin ya wuce “zare tsawo”, to sai “ya ranta cikin na kare.” Su kuma saura su bi shi. Haka abin zai kasance sai in wani ya amsar masa, ko kuma an ga ya wahala sannan a k’yale shi, wani ya kar’ba.

Amma duk da kasancewar wahalar wannan wasa, sai ka ga wani daga ciki, in ya kasance sarki, sai ka ga ya yi kasada, ya ce kowa ya d’auka sadaka. Bayan kowa ya d’auka, an fara bugunsa sai ka ga nan take ya ta’ba wani, wanda zai kasance a matsayinsa. Haka ma wannan wasar za ta kasance, har a gaji ko a furfura wata ko kuma a watse.

3.1.2 Jini wa Jini


        Wannan wasa kuwa ana yin ta ne tare da a k’alla yara goma ko ma fiye. Akan za’bi jagora wanda ke jagorancin sauran yara, sannan kuma a shata wurin sha. Yara za su yi layi a tsaye wannan bayan wnnan, jagora ne ke gaba. A nan jagora zai rink’a fad’in sunayen abubuwan da ke da jini, sauran yara su amsa masa da “janja”. Idan jagora ya ambaci abin a bai da jini, sai su ce: “babu”. Duk wanda ya kuskure ya ce “janja” to sai bugu sai in ya shek’a zuwa wurin sha. Ko da hakan yara za su bi shi har ya isa can. Idan ya sami isa, sai su dawo, wani kuma ya amshi jagorancin. Wannan wasa ce mai matuk’ar amfani ga al’ada saboda tana d’auke da rumbun kalmomi na Hausa masu rai da marasa rai.

Ga yadda wak’ar take:

Jagora:        jini wa jini

Yara:           jan ja

 

Jagora:        kaza da jini

Yara:           janja

 

Jagora:        akuya da jini

Yara:           janja

 

Jagora:        rago da jini

Yara:           janja

 

Jagora:        dotse da jini

Yara:           babu

A nan duk wanda ya kuskra ya ce “janja” to sai a far masa da duka, sai shi kuwa ya tsere ya je ya ta’bo wurin da aka shata a matsayin wurin sha. Bayan ya sha sai a dawo a sake aza wata wasar har dai su gaji ko kuma su sake wata wasa ta daban. Wannan wasa ce da ake amfani da rumbun kalmomin Hausa.

 

3.1.3 Dundunge


Wannan wata wasa ce, wadda akan sami ak’alla mutum goma ko fiye. A cikin wad’annan ‘yan wasa za a d’auki mutum guda, sannan a rufe masa idanu da wani ragga (tsumma) a fuska, a kuma ba shi wani dogon kara ya rik’e. Bayan haka za a za’bi shugaba wanda zai tsaya a gaban wanda aka rufe wa ido (Dundunge) sauran yara kuwa na gewaye da su. Daga nan shugaba ya rik’a wa dundunge kare, ya rik’e gefe guda, shugaba kuwa ya rik’e gefe guda. Sannan shugaba da dundunge su ce:

Shugaba:     Dundunge

Dundunge:  Iyii

Shugaba:     Ke yi tuwo

Dundunge:  iyii

Shugaba:     Ke yi fura

Dundunge:   Iyii

Shugaba:     Ina nawa rabo

Dundunge:  Kare ya cinye

Shugaba: Ga d’iya na nan dubu-dubu kowa kis samu, har da ni babban su labta!

Sai ya saki kare ya shek’a, sauran yara kuwa su shek’a. Sai dundunge ta rink’a yawo tana bugun iska, da haka ne yakan sami wani ya buga. Su kuwa ‘yan wasa suna gudu suna gewayar dundunge, wasu har da zungurar ta suke yi suna cewa:

Kowa kis samu labta

Kowa kis samu labta

Za su ci gaba ta haka, har ta gaji ta kware fuskarta sannan a d’aura wa wani. Wannan wasa ta kasu gida biyu:

  1. Ta dandali, irin wadda aka yi bayani a sama,

  2. Ta tankar sabon d’aki. Wannan kuwa yara za su shiga a cikin tankar sabon d’aki, sannan a ba dundunge kara a ce duk wanda ta samu ta buga. Yara za su haye jikin tanka, dundunge kuwa ta yi ta bugu har wani ya wahala ya fito da gudu. A irin wannan wasa yara kan sha kashi sosai.


Ita dai wannan wasa ta mata ce.

3.1.4 ‘Yar Ato


‘Yar ato tana d’aya daga cikin nau’o’in wasannin da yara mata ke aiwatarwa a k’asar Yabo, ita wannan nau’in wasar ana yin ta ne mutum uku. Yarinya ta farko ta tsaya hannun dama, ta biyu ta tsaya hannun hagu kuma za su tsaya ne kusa da kusa. Ita kuma ta uku d’insu za ta tsaya a gabansu ne daidai tsakaninsu. Sai a fara wasar.

Wannan da ke tsaye gabansu za ta fad’o musu su ko su sa hannuwansu su rik’e ta ga damtse su rink’a jefa ta idan ta tafi kamar kimanin taku uku ko hud’u sai ta dawo, su ko su sake tura ta ta koma. Haka kuma za ta sake dawowa garesu. Duk lokacin da ta dawo a nan tsakiyarsu, ‘yan matan za su sake rik’e ta ga damtse su sake tura ta. Haka za a ci gaba, idan an wa wannan sai a yi wa waccar har a yi wa kowa sannan a watse ko kuma a canza wannan wasar.

Wannan nau’in wasar yara mata ke aiwatar da ita a dandali ko cikin gida a duk lokacin da suka had’u. Wannan wasar ana yin ta ne mutum uku ko fiye da uku. Suna yin wasar suna wak’ok’i kala-kala. Misali:

‘yar ato- ‘Yar ato

‘Yar ato d’iyar ato

Kama kunnen ato

Tafi ato na kiranki

3.1.5 ‘Yar Tsana


Wannan wata nau’in wasa ce da yara mata kan shirya ta hanyar amfani da toto na karen dawa, a yi d’iya a sanya mata tufafi da kayan k’awa (kwalliya). Sannan a yi gado da kayan d’aki a shirya biki na yi wa wannan d’iyar aure.

Ita wannan wasar da rana ake yin ta kuma a zaune sannan ko yara nawa za su iya yin wannan wasar. Yara na dad’ewa suna shirya gudanar da ita kamar yadda iyaye kan d’auki lokaci suna shirin wankin d’iyarsu (yi wa d’iya aure). Saboda sai an yi wa d’iyar tufafi sannan an gina gida (gidan kwali ko k’asa), kai wasu lokuta har da abinci ake dafawa ga gwango ko marfin k’wano na bikin auren d’iyar ‘yar tsana.

Idan an had’a bikin kamar yadda yara ke gudanar da shi wasu lokuta suna wak’e-wak’e kamar amaryar gaske. Misali:

Ke kika ce kina so,

Da ba ki ce kina so

Ba da ba a baki shi ba

 

3.1.6 Tafa-tafa


Ita wannan nau’in wasar wasa ce da ‘yan mata ke yi. Ana wannan wasar ne mutum biyu ko fiye. Za su yi tsaye suna kallon juna fuska da fuska, kusa da kusa. Sai su fara had’a hannuwansu daidai k’irjinsu suna tafawa da juna suna yin wak’a a lokacin da za a fara wasar za a fara ta ne sannu a hankali. Kafin ka ce kwabo, wasar ta fara sauri kuma  haka za a ci gaba da had’a hannuwa ta kowane gefe kuma da sauri.

Abin ban sha’awa za ka ga ta kowane gefe d’aya ta bugo hannuwanta za ta tarar da na d’ayan a wurin kamar yadda masak’i ke sak’a sak’arsa. Irin yadda tunaninsu zai zama d’aya a lokacin gudanar da wannan wasar gaskiya abin a kwai abin burgewa.

Sannan suna tafa-tafa suna wak’e-wak’e kamar yadda hannuwan suke tafiya tare haka bakunansu ke rera wak’ok’i tare. Kuma ita wannan wasar yara mata ke aiwatar da ita a duk lokacin da suka had’u domin gudanar da wasanninsu.

Tafa-tafa

Tafiyarnan da za mu tare

Da wa muka yin ta

Daga d’an Ali sai masoyi

Masoyi tsayamin in daka in kir’ba

 

3.1.7 Masu Aiwatar da Wasanni


Da yake mun san cewa, wasu tana koyar da tarbiyya don haka ta tanadi wani tsari na musamman a kan aiwatar da ita. Kamar yadda addinin Musulunci yake da nasa tsari na musamman, haka ma ita wasa take. Don haka masu aiwatar da wasa sun had’a da:

  1. Yara

  2. Samari

  3. ‘Yan mata

  4. Manya ko dattawa


Yara: Wasannin da yara k’anana ke aiwatarwa a k’asar Yabo sun had’a da:

  1. Bud’d’a

  2. Wasan teloli

  3. Wasan tsere

  4. Wasan alkwato da sauransu


Samari matasa: Wad’annan su ne masu aiwatar da wasanni irin su:

  1. Langa

  2. Jangiro-jangiro

  3. A fajana

  4. K’walo

  5. Dundunge da sauransu


‘Yam mata: Sukan aiwatar da wasu daga cikin wasannin yara, sannan kuma su k’ara da irin nasu na ‘yan mata. Wad’annan sun had’a da:

  1. Bud’d’a

  2. Wasar tsere

  3. ‘Yar ‘boyal

  4. ‘Yan kara (kid’in k’warya)

  5. Bowojo, wasannin amare, da sauransu


Manya ko dattawa: Wannan rukuni na masu aiwatar da wasa, sukan yi wasa ne a tsakaninsu da jikokinsu da kuma basantaka, don haka wasannin da suke aiwatarwa su ne:

  1. Wasan tobasantaka

  2. Wasa a tsakanin jika da kaka

  3. Dambe

  4. Kokawa


Dukan wad’annan wasanni akan aiwatar da su ne a wurare na musamman kamar:

Dandali ko kuma a gidajen amare, amma ita wasar manya takan faru ne a wurin da wad’annan mutane suka gamu ko dandali ko kasuwanni. Hasali ma ita wannan wasar ta tubasantaka tsakanin jika da kaka ko d’an mace da d’an namiji ba ta k’unshi wani dogon motsi ko tsalle-tsalle ko guje-guje ba illa dai wasanni ne na ba’a da ake yi tsakanin kaka da jika ko tsakanin taubashi da taubashi, ko neman kud’i ko suna.

3.8 Lokacin Aiwatar da Wasa


asa lokutan aiwatar da wasannin zuwa gida-gida kamar haka:

A kowace al’umma ta kowace nahiya sukan aiwatar da nasu wasannin gargajiya a lokuta daban-daban. A k’asar Yabo sun karkasa lokutan aiwatar da wasannin zuwa gida-gida kamar haka:

  1. Wasannin rana

  2. Wasannin dare



  1. Wasannin rana

  2. Wasannin dare


Wad’anda ‘yan mata ke aiwatarwa a wannan lokaci su ne:

  1. Tafa-tafa

  2. Fyad’e (bowojo/gad’a)

  3. ‘Yan kara (kid’in k’warya)

  4. Wak’e-wak’e da raye-raye


WASANNIN DARE: A wannan lokaci kowane rukuni daga cikin wad’annan rukunnan suna da irin wasannin da suke aiwatarwa a wannan lokacin. Misali ‘yan mata suna wasanni kamar:

  1. ‘Yar lunk’as

  2. Fyad’e (bowojo/gad’a/’yar ato)

  3. Wak’e-wak’e da raye-raye a dandali (fili)

  4. Tatsuniyoyi (gatana)


Wasannin Yara K’anana

  1. Langa

  2. ‘Yar lunk’as

  3. ‘Yar-dawaki

  4. Dundunge

  5. Tatsuniyoyi da sauransu


Wasannin Yara Samari

  1. Langa

  2. K’walo

  3. A farjana

  4. Jangiro-jangiro

  5. Dundunge

  6. Kacici-kacici da sauransu


Wasannin Manya ko Dattawa

Wad’annan wasanni, babu wani ke’bantaccen lokaci da ake aiwatar da wad’annan. Ke’bantaccen lokacin shi ne:

  1. Lokacin saduwa

  2. Lokacin ziyarar juna


 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Post a Comment

0 Comments