Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangantakar Harshen Hausa Da Nufanci: Nazarin Tasirin Hausa A Kan Harshen Nufanci (1)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
KUDU MUHAMMAD SALIHU

Tabbatarwa

Na amince da cewa wannan kundi na Kudu Muhammad Salihu mai lamba 1210106003 ya cika dukkan k’a’idojin da aka gindaya domin samun digiri na farko a harshen Hausa (B.A Hausa) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO, Sakkwato.

 

…………………………….                                                   …………………………

Mai duba                                                                                             Kwanan Wata

Dr. A. A. Atuwo

 

 

 

 

 

…………………………….                                                   …………………………

Shugaban Sashe                                                                                  Kwanan Wata

Farfesa A.A Dunfawa

 

 

 

 

…………………………….                                                   …………………………

Mai Dubawa na Waje                                                             Kwanan Wata

 

 

Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan aiki nawa ga iyaye na Alhaji Salihu Suleiman Fogun (A.S.S.F) da Hajiya Fatima Asabe wanda cikin ikon Allah ne suka yi sanadiyar zuwa na wannan duniya, Allah ya jik’ansu tun suna raye, amin.

 

 

Godiya

Duka godiya da yabo ta tabbata ga Allah mad’aukakin Sarki mai kowa mai komai, mai wanda yaso, yayin da yaso, a inda yaso, ko ana so ko ba a so, lillahi Wahidul Al-K’aharu wanda ya rayar da ni a kan tafarkin addinin musulunci. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halitta cika makin Annabawa Annabi Muhammadu (S.A.W) da iyalansa da sahabbansa da duk wad’anda suka bi shi shiriyarsa har zuwa ranar k’iyama.

Godiya ta ga malamai na musamman babban jagora na Dr. A.A Atuwo wanda cikin ikon Allah ne ya tabbatar da cikakken kula tun farkon wannan aiki har zuwa k’arshensa, Allah ya saka masa da alkhairi, da kuma shugaban sashe Farfesa A.A Dunfawa da sauran malamai na sashe kamar su Malam Isma’il da Farfesa Amfani da Farfesa Birniwa da Farfesa Mukoshe da Farfesa A.B Yahaya da Farfesa Bunza da Farfesa Yakasai da Farfesa D’antumbishi da Dr. Birnin Tudu da Dr. B.B Usman da Dr. Gobir da Dr. Yahaya da Dr. S. Gulbi da Dr. Nasir da Dr. Umar Bunza da Malam Isah da Malam Mustapha da Malam Musa da Malam Dano Bunza da Malam Nazir da Malam Cika (Marigaye) dukkan su Allah ya saka musu da alkhairi.

Godiya ta musamman kuma zuwa ga iyaye na Alhaji Salihu Suleiman da Hajiya Fatima Asabe da iyalai na musamman uwar gida mai haskake zuciyata Malama Adama da amaryata abin k’aunata da Fatima da Khadijat (Kubura) da Hafsat da Aisha (Umaira) yara na kenan ‘ya’ya ye na musamman Hauwa’u da kuma k’annaina kamar Alfa da Fatima (Hajiya Wachika) da Fatima (Unako) da Jibril da Aisha (Kaka wan marigaye) da Muhammad Shafi’i (Marigaye) da sauran ‘yan uwa na wad’anda suka taimaka da dukiya da kuma addu’a da wad’anda basu yi ba, don ganin na kammala wannan karatu na, Allah ya saka wa kowa da alkhairi.

 

 

Gabatarwa

Masana da manazarta daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu a kan harshen Hausa da kuma harshen Nufanci, harsunan guda biyun su ne duk wanda yake d’an asalin harshen yake alfahari da shi kuma suna daga cikin harsunan nahiyar Afirka musamman Afirka ta yamma. Akwai amincewar masana ilimin kimiyyar harshe irin su Yakasai da Jinju a kan cewa, harshen Hausa yana cikin wani gundarin babbar rukuni na sauran harsunan duniya.

Haka zalika, harshen Nufanci, ya ke’banta da d’imbin tarihi a idon duniya wanda wannan fage ba zai damar zuwa da su ba sai dai d’an kad’an wanda a hak’ik’anin gaske, wasu dalilai ne suka haifar da rashin ci gaban harshen.

Bugu da k’ari, akwai dangantaka da ke tsakanin harsunan nan guda biyu musamman ma dangantaka ta huld’a da na kasuwanci da fatauci da auratayya da na aron kalmomi wanda a sanadiyar wad’annan dangantaka, ya kawo tasirin Hausa a kan Nufanci da dai makamantansu.

Bayan haka, na karkasa wannan aiki zuwa babuka guda biyar domin samun damar bayyanar da kai da kuma samun nasarar kammalawar aikin.

A babi na farko, wato gabatarwa an yi bayanin abubuwa inda aka fara da shimfid’a da manufar bincike da farfajiyarsa da muhimmancinsa da dalilansa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da kuma nad’ewa.

A babi na biyu, an yi bayanin  tarihin huld’ar al’ummun inda aka kawo tak’aitaccen tarihin Hausawa da na Nufawa da huld’arsu da mazaunin Nufawa da kuma nad’ewa.

A babi na uku kuwa, an yi bayanin dangantakarsu a fuskoki daban-daban da suka had’a da ma’anar dangantaka da dangantaka ta addini da fatauci da zuwan Turawa da wasu kayan k’walamar Hausawa da d’inki da noma da kamun kifi da sabulun salo da daddawa da k’ira da kuma dangantakar auratayya sannan nad’ewa.

A babi na hud’u kuma, an yi bayanin tasirin harsunan nan guda biyu a kan juna inda aka gabatar da shimfid’a da ma’anar tasiri da yanayi da tsarin tasirin aron kalma da dabarun aiwatar da aron kalma da kashe-kashen aro da dalilan aro da matsalolin aro da kuma tasirin ararrun kalmomin Hausa daga Nufanci sannan nad’ewa.

A babi na biyar kuma, an fara gabatar da shimfid’a da sakamakon bincike da kammalawa da kuma shawarwari sannan kuma nad’ewa.

 

 

K’UMSHIYA

Tabbatarwa

Sadaukarwa

Godiya

Gabatarwa

K’umshiya

BABI NA D’AYA

GABATARWA

1.0 Shimfid’a

1.1 Manufar Bincike

1.2 Farfajiyar Bincike

1.3 Muhimmancin Bincike

1.4 Dalilan Bincike

1.5 Bitar Ayyukan da Suka Gabata

1.6 Hujjar ci Gaba da Bincike

1.7 Nad’ewa

 

BABI NA BIYU

TAK’AITACCEN TARIHIN HULD’AR NUFAWA DA AL’UMMAR HAUSAWA

2.0 Shimfid’a

2.1 Tak’aitaccen Tarihin Hausawa

2.2 Tak’aitaccen Tarihin Nufawa

2.3 Tarihin Huld’ar Hausawa da Nufawa

2.4 Mazaunin Al’ummar Nufawa

2.5 Nad’ewa

BABI NA UKU

3.0 Shimfid’a

3.1 Dangantakar Nufawa da Hausawa

3.2 Ma’anar Dangantaka

3.3.1 Dangantaka ta Fuskar Addini

  1. Almajirci/Neman Ilimi

  2. Malanta


iii. Jihadi (Sarautar Tutar Shehu)

3.3.2 Dangantaka ta Fuskar Fatauci

3.3.3 Dangantaka ta Tarihin Zuwan Turawa

  1. Yak’in Turawa


3.4 Dangantaka ta Fuskar Wasu Al’adu

3.4.1 Sana’ar Kayan K’walamar Bahaushe na Gargajiya

  1. Tuyar K’osai

  2. Guguru


iii. Dakkuwa

i’b. Gyad’a

3.4.2 Sana’ar D’inki

3.4.3 Sana’ar Noma

3.4.4 Sana’ar Su (Kamun Kifi)

3.4.5 Sana’ar Sabulun Salo

3.4.6 Sana’ar Daddawa

3.4.7 Sana’ar K’ira

  1. K’iran Bak’in K’arfe

  2. K’iran Farin K’arfe


iii. K’arau (Glass Work)

3.5 Dangantaka ta Fuskar Auratayya

3.5.1 Bikin Aure

3.5.2 Bikin Haihuwa

3.6 Nad’ewa

BABI NA HUD’U

TASIRIN HARSHEN HAUSA A KAN HARSHEN NUFANCI

4.0 Shimfid’a

4.1 Ma’anar Tasiri

4.2 Yanayi da Tsarin Aro a Tsakanin Hausa da Nufe

4.3 Dabarun Aiwatar da Aron Nufe daga Hausa

4.4 Kashe-Kashen Aron Nufe Daga Hausa

4.5 Dalilan Aro Daga Hausa Zuwa Nufe

4.6 Matsalolin Aro a Harshen Hausa Zuwa Nufanci

4.7 Tasirin Ararrun Kalmomin Hausa a Kan Harshen Nufe

4.8 Nad’ewa

BABI NA BIYAR

5.0 Shimfid’a’

5.1 Sakamakon Bincike

5.2 Kammalawa

5.3 Shawarwari

Manazarta

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments