Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangantakar Harshen Hausa Da Nufanci: Nazarin Tasirin Hausa A Kan Harshen Nufanci (2)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
KUDU MUHAMMAD SALIHU 

BABI NA D’AYA


GABATARWA


1.0 Shimfid’a


A wannan babi na d’aya, zan yi amfani da shimfid’a a matsayin ginshik’i ko mabud’i na wannan bincike sannan kuma zan yi waiwaye a kan manufar gudanar da bincike da farfajiyar binciken da muhimmancin binciken da dalilin binciken da kuma ayyukan dam asana suka yi gabannin wannan bincike da hujjar ci gaba da bincike duk zan yi bayaninsu filla-filla a k’arshe kuma nad’e shi da bayanin abubuwan da babi ya k’unsa.

Haka kuma zan wanzar da aikin ne bisa ga hanyoyin da masana suka bi wajen gudanar da ayyukansu. Da farko dai zan yi amfani da wallafaffen littattafai na masana da manazartan harshen  Hausa da harshen  Nufe da wasu harsuna da za su taimaka wajen gudanar da wannan aiki. A k’arshe kuma zan tuntu’be wasu mutane da suka yi rayuwa mai tsawo cikin harsunan kuma suka san tarihin harsunan.

1.1 Manufar Bincike


Abin da ya ba ni dama a a kan manufar wannan bincike nawa shi ne, ganin cewa Nufawa k’abilu ne da suke da nasu harshe na asali kuma da shi ne suke dogara wajen gudanar da mu’amala na yau da kullum tsakaninsu da Hausawa majiya harshen ta fuskoki daban-daban kamar addini da fatauci da neman ilimi da malanta da dai sauran abubuwa da suka shafi rayuwa.

Da haka ne ya dace a fito da dangantaka ko alak’a ta fuskar aron kalmomi da ake iya samu a tsakanin harsunan wato na Nufanci da Hausa, ta yadda mai sauraro ko karatu zai iya gano ararrun kalmomi da harshen Nufanci ya ara daga harshen Hausa da kuma wanda Hausawa suka ara daga harshen Nufanci ta haka ne d’iyan wad’annan k’abilu za su gano tarihin alak’ar dake tsakaninsu ne a nan gaba.

1.2 Farfajiyar Bincike


Wannan bincike ya k’unshi dangantakar harshen Nufanci da harshen Hausa a kan abin da ya shafi tasirinsu cikin ararrun kalmomi da harsunan kan yi tsakaninsu da juna da yadda suke fasalta su domin ya dace da harshen aro na daga cikin kalmomi da babu su a cikin harshen. Yin hakan na iya zama wata dabara ta nazari ga ‘yan k’abilun musamman Nufawa na abin da ya shafi harshensu, ta dalilin kallon da ake wa harshen da cewa ya na daga cikin tsirarrun harsunan Nijeriya. Don haka, wannan binciken zai k’ara fito da harshen fili, ya kuma kau da irin kallon da ake yi wa harshen.

1.3 Muhimmancin Bincike


Akwai buk’atar nuna muhimmancin abu a idon mutane muddin ana neman aikin ya samu kar’buwa. Wannan bincike ya na da matuk’ar muhimmanci don kuwa zai taimaka wajen fito da azuzuwan kalmomi na cikin harshen Hausa da harshen Nufanci ya ara daga cikin harshenta da kuma irin kwaskwariman da aka yi na kalmomin har ta zama banufiyar kalma da kuma yadda za a iya fasalta su cikin jumloli.

Bugu da k’ari binciken zai taimaka mana wajen yin nazari game da abubuwan da ke faruwa cikin harshen Nufanci da kuma harshen Hausa na abin da ya had’a da zamantakewa irin na addini da fatauci da ilimi da dai sauran mu’amalolin yau da kullum. A k’arshe, binciken zai k’ara taimaka wa al’ummar Hausawa wajen gano gaskiyar al’amuran da magabata suka yi a game da harshen don fitar da shakku cikin zukatansu.

1.4 Dalilan Bincike


Komai da mutum ya sa gaba tana da dalili. Bisa ga wannan an k’udiri ne na zayyano wad’annan dalilan na gudanar da wannan aiki:

  1. Domin tabbatar da cikawar k’a’idoji da jami’a ta rataya a kan duk d’alibin da ya kai k’arshen kammala karatunsa ya ba da gudunmawa a gefen karatunsa.

  2. Domin bunk’asa da kuma ciyar da harsunan Hausa da na Nufanci gaba ta fuskar nazari.

  3. Domin nuna alak’a da dangantakar da ke tsakanin harsunan Hausa da na Nufanci ta fuskar aron kalmomi.

  4. Nuna dangantaka da tasirin harsunan a tsakaninsu ta fuskoki daban-daban.

  5. Nuna tarihin harsunan domin tabbatar da asalin kowannen su ne da irin rawar da suke taka a idon duniya. Wad’annan sune dalilan gudanar da wannan bincike.


 


  1. 5 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata




Akwai muhimman hanyoyi da za a yi amfani da su wajen gudanar da bita game da ayyukan magabata da suka shafi k’undayen digirori da littattafan da aka buga da samu k’ok’arin haske daga wasu mutane na musamman da malamai da manazarta cikin harshe Hausa da harshen Nufe domin samun nasarar kammala wannan binciken.

Muhammad (2016) a kan kundinsa na neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato sashen koyar da harsunan Nijeriya mai taken “Auren Zumunta Jiya da Yau a Garin Sakkwato”. Manazarcin ya yi k’ok’arin fito da ma’anar aure da matsayinsa a musulunci da hanyoyin gudanar da shi a al’adar Bahaushe. Haka kuma ya kawo asalin zumunta da rabe-rabenta da nau’o’inta da tasirinta da kuma illolinta, a hak’ik’anin gaskiya, wannan aiki bai shafi wannan bincike nawa ba, amma akwai fa’ida wajen duba dangantakar Nufawa da Haausawa ta fuskar auratayya.

Mungadi (2016) a kan k’undinsa na neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato sashen koyar da harsunan Nijeriya mai taken “Al’adun Kamun Kifi a K’asar Mungadi” inda ya fito da dabarun kamun kifi da ire-irenta da nau’o inta da kuma sunayensu daban-daban. Kamar dai yadda taken binciken nawa ya nuna, wannan aiki na Mungadi bai shafi wannan bincike ba, amma kuma ya na iya taimakawa wajen fito da dangantakar Hausawa da Nufawa ta fuskar sana’o in gargajiya musamman abin da ya shafi al’adarsu wato kamun kifi a al’ummar Nufawa.

Tureta (2011) a kan k’undinta na neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato sashen koyar da harsunan Nijeriya mai take “Al’adun Hausawa a Goyon Ciki a Sakkwato”. Manazarciyar ta bayyanar da ma’anar goyon ciki da amfaninsa da al’adunsa da tanadin kayan haihuwa na gargajiya da na zamani da halartar ungozama har ma daa illolin goyon ciki. Amma kuma babu nasabar wannan aiki da bincike na sai dai wajen yin duba kan dangantakar tasirin Hausawa da Nufawa ta fuskar haihuwa.

Auwal (2003) a littafinsa mai suna “Diginities of the Nupe Race Yesterday and Today” inda ya yi tsokaci a kan abubuwa guda biyar wad’anda suka had’a da asalin Nufawa da yad’a addinin musulunci da malaman Nufawa suke yi da had’in kai tsakanin al’ummar Nufawa da yanayin gudanar da mulki gabanin sarakunan Fulani wanda ya samu nasaba da lokacin jihadin Shehu Usmanu ‘DANFODIYO.

Marubucin ya bayyana cewa, ya samu hasken wallafa littafinsa ne da wasu aikace-aikacen masana kamar Sheik Adamu Abdullahi Al-Ilory da Sheik Muhammadu Bello a littafinsa (Infak’al Al-Maisur) da kuma S.F Nadel a littafinsa “A Black Byzantium and Nupe Religion”.

Abdullahi (2008) “Nupe the Origin” a wannan littafin marubucin ya lak’abce shi da cewa Nigeria’s number 1 most contro’bersial Book! Nigeria’s Number 1 most Closely Book! Africa’s number 1 most hea’bily Documented Book! Idan dai muka fahimci abin da ke faruwa a wannan littafi, sai mu yi mata lak’abi da abin da Hausawa ke k’ira Bakandamiya. Dalili kuwa shi ne, ya fito da abubuwa na ban al’ajabi inda ya ke cewa, duk harsunan Afirika sun samu asali ne daga harshen Nufe musamman inda muka harsunan da muke da su a cikin gida (wato Nijeriya), an sami harsuna kamar Yoruba inda harsashe cewa Oduduwa Banufe ne. Haka kuma harshen Hausa ya sami asali ne daga harshen Nufe har ma ya kawo misali cewa “Banza Bakwai” da Hausawa ke danganta Nufawa a kai, asalin kalmar shi ne kamar haka ‘BASSA BAKWA’ wanda kalmar a harshen asali wato Nufe shi ne “BAK’O KO BAKARO”.

D’an Arewa (1996) “Afirka tun daga farkon tarihi ya zuwan Turawa Littafi na D’aya” marubucin ya yi k’ok’arin kawo ko jawo hankalinmu a kan huld’ar farko tsakanin Turawa da al’ummar Nijeriya. A bayaninsa cewa Turawan da suka fara shigowa Nijeriya sune Turawan Portugal a shekara (1470) a ga’bar tekun Ikko shekarar (1805) wanda ake wa lak’abi da mabud’in kwara saboda ta kogin.

Bayan abubuwan da suka wakana tsakaninsu da Turawan Ingila na ta’asan da suka tafka, sai suka tura wani d’an lek’en asirinsu zuwa Had’ejia daga Katagum mai suna Captain Philips wanda mutanen Had’ejia suka rad’a masa suna ‘MAI TUMBI’. Wannan Bature ya je Had’ejia ne da sunan shi d’an kasuwa ne, kuma Balarabe ne shi wai. Amma abin da ya kai shi, shi ne gano asirin Had’ejia. Saboda an ce da su Turawan Ingila shi sarkin Had’ejia d’an tak’adari ne. don haka ne, suka tura masa d’an lek’en asiri, wato Sarkin Had’ejia Muhammadu Mai Shahada.

Mahdi (1978) “The Hausa factor in West Africa History” marubucin wannan littafi ya yi k’ok’ari ainun domin ya fito da bayanai da suka shafi tarihin Hausawa da K’asar Hausa da addininsu da tattalin arzik’insu da k’aurace-k’auracensu da dangantakarsu da wasu k’abilu musamman k’abilun Nufe da irin rawar da Nufawa suka taka wajen tasiri irin su fatauci da yak’e-yak’e wanda kuma wannan bincike ya k’unshi danngantakar da ke tsakanin Hausawa da Nufawa ta fuskoki daban-daban wanda a hak’ik’anin gaskiyar al’amarin.

Bugu da k’ari, littafin ya nuna dangantakar da ke tsakanin Hausawa da Nufawa kan abin da ya shafi jaddada addini a zamani Shehu Usmanu ‘DANFODIYO da kuma dangantaka a tarihin zuwan Turawa da makamantansu.

Mani (1966) “Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa”. Marubucin wannan littafi ya yi k’ok’arin fito da zuwan Turawa inda yake cewa, wannan batu, ya fito ne daga bakin Mujaddadi Shehu Usmanu ‘DANFODIYO, da yadda Turawa suka yi da Arewacin Nijeriya da gwagwarmaya da suka sha a wasu sassa na Arewa musamman Kontagora da Bida a zamanin Sarki Abubakar Nasaba da kuma Sarki Umaru Nagwamatse.

1.6 Hujjar Ci Gaba Da Bincike


Ko shakka babu hujjar ci gaba da bincike domin kuwa, duk wani aikin da mutum ya sa gaba da yinsa, ya na tare da dalilai ko hujjojin gabatar da shi don haka, hujjar ci gaba da wannan bincike shi ne, tabbatar da cewa ba a ta’ba gudanar da irin wannan aiki ba kuma na samo tabbacin ne daga k’undaye da littafai da suke shud’e inda hakan ya bani dama ko k’arfafa min gwuiwa na ci gaba da binciken. A hak’ik’anin gaskiya, akwai wasu aikace-aikace da yawa wad’anda mutane daban-daban suka gabatar wad’anda za su iya yin kama da wannan daga wasu harsuna daban-daban amma kuma ba a ci karo da wani aiki ko bincike da ya yi dai-dai da wannan ba.

Bugu da k’ari, aikin ya tsayu ne wajen kallon irin dangantakar da ke tsakanin harsunan nan guda biyu wato harshen Hausa da harshen Nufanci ta fuskar tasirin da wani ke da shi a kan wani.

1.7 Nad’ewa


Dangane da wannan babi kuwa, an yi k’ok’arin nuna yadda wannan aikin bincike zai kasance ta hanyar nuna manufar bincike da farfajiyar bincike da muhimmancinnsa da dalilansa da bitar ayyukan da suka gabata har ma da hujjar ci gaba da wannan bincike, inda kuma a k’arshe aka nad’e wannan babi.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

Post a Comment

0 Comments