Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai

Amsoshi

NA


SHEHU HIRABRI


08143533314KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘Danfodiyo, SAKKWATO


https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-5/

 BABI NA BIYU


TAK’AITACCEN TARIHIN RAYUWAR ALHAJI MUSA ‘DANBA’U GIDAN BUWAI2.0 Shimfid’a


        A babin da ya gaba an yi bitar ayyukan da suka gabata tare da bayyana k’udurin bincike. Shi kuma wannan babin za a yi bayanin tarihin rayuwar Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai. Tarihin zai k’unshi haihuwarsa da iliminsa da matansa da ‘ya’yansa da fara wak’arsa da makad’ansa da marok’ansa da nau’in waok’ok’insa da nasarorin da ya samu a cikin wak’a da yawace-yawacensa har zuwa rasuwarsa. Haka kuma za a bayyana dangantakarsa da sauran mawak’a da kuma sauran al’umma baki d’aya.

2.1 Tak’aitaccen Tarihin Alhaji Musa ‘Danba’ub Gidan Buwai


2.1.1 Haihuwarsa


        An haifi Alhaji Musa ‘Danba’u a shekarar 1958 a shekarar da aka yi wata yunwa a k’asar Hausa wadda ake kira mud’a. An haife shi ne a garin Gidan Buwai da ke cikin k’aramar hukumar Mulkin Rabah ta jahar Sakkwato. Duk da yake wasu manazarta da suka yi rubutu a kan Alhaji Musa ‘Danba’u sun sha bamban dangane da shekarar da aka haife shi, Bala da wasu (1993) sun bayyana cewa, an haife shi a shekarar 1955. Shi kuma Shagari, (2011) ya bayyana an haifi ‘Danba’u a shekarar 1962.

Ganin irin wannan bambanci ya sa na zage dantse domin samun tabbacin shekara da aka haife shi inda na yi tafiya har zuwa garin Illela inda wazirinsa mai suna Shehu waziri wanda a yanzu shi ne halifan ‘Danba’u domin shi ke wak’a tare da duk makad’a da marok’a da kuma kayan kid’an da Alhaji Musa ya bari inda ni yi hira da shi da kuma wani makad’in ‘Danba’u Adamu Tozai inda suka bayyana mini wannan shekara. Mun tattauna da su ne a ranar Lahadi 19-03-2017 a garin Illela inda ranar 20-03-2017 na ga littafin Sa’idu Muhammad Gusau mai suna Makad’a da Mawak’an Hausa na Biyu wanda aka buga a shekarar 2016 a d’akin karatu na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo inda a shafi na goma sha d’aya (11) ya tabbatar da an haifi Alhaji Musa ‘Danba’u a shekarar 1958, wanda wannan hujja ta tabbatar mana cewa an haifi Alhaji Musa ‘Danba’u a shekarar 1958.

2.1.2 Iliminsa


        A wajen ilimi, Alhaji Musa ‘Danba’u ya yi karatunsa na addini tun yana k’aramin yaro a wajen kakansa, inda ya sauke Alk’ur’ani mai girma kuma ya karanci littafai da dama kamar Ahalari da Ishmawi da Iziyya da Risala da Hadisai haka kuma kamar yadda Waziri Shehu da Adamu Tozai suka fad’a mini cewa ya hardace ishiriniya gaba d’aya.

A ilimin zamani kuwa, Alhaji Musa ‘Danba’u bai yi zurfi ba domin mahaifinsa ya sa shi firamare yana aji uku kakansa ya fitar da shi domin ya yi zurfi ga iliminsa na addini domin kakansa liman ne da ma ba su cika son boko ba.

2.1.3 Iyayensa


        Sunan mahaifin Musa ‘Danba’u Abdullahi Maid’anjaki, wasu kuma na kiran sa Audu jikan Liman. Asalin kakan ‘Danba’u daga wani gari ne mai suna Kurgaba a k’aramar hukumar Mulki ta Wurno ya taso ya komo Gidan Buwai.

Abdullahi makad’in goge ne amma haye ya yi domin bai gaji kid’a daga iyayensa ba. Hasali ma, mahaifin Abdullahi, Liman Muhammadu, malami ne wanda ya kafa makarantar ilimi sannan ga shi liman. Shi kansa Abdullahi mahaifin Musa malami ne har kuma ya fara limanci sai ya daina ya ci gaba da kid’an goge.

Sunan mahaifiyarsa Aminatu (Amo ko Umma). Ita ma haifaffiyar Gidan Buwai ce, ita ma mahaifinta malam Musa malami ne. ‘Danba’u ya yi karatu wurinsa a nan ya hardace ishiriniya kamar yadda wazirinsa Shehu da makad’insa Adamu Tozai suka sheda mini.

2.1.4 Matansa


        Alhaji Musa ‘Danba’u ya yi aure a ranar 11 ga watan 10 na shekarar 1979 yana da mata uku kafin rasuwarsa wad’anda suka had’a da:

 1. Hajiya Asabe

 2. Hajiya Sadiya

 3. Hajiya Aminatu


Bayan wad’annan matan uku, ya auri wasu uku amma sun rabu kafin rasuwarsa. Daga cikinsu akwai:

 1. Jumma

 2. Ta’Allah

 3. Asabe k’arama


Jumma ita ce matarsa ta farko wadda ita ce mahaifiyar babbar d’iyarsa Hauwa’u (Kulu).

Ta’Allah ita ce matarsa ta biyu. Ita ma sun haihu sun samu d’a mai suna Zayyanu.

2.1.5 Yaransa


Wazirin Alhaji Musa ‘Danba’u ya sheda min cewa, Alhaji Musa na da ‘ya’ya goma sha tara (19) da jikoki bakwai (7). Daga cikinsu akwai maza da mata.

Jumma Gidan Buwai

 1. Hauwa’u Kulu


Ta’Allah Gwaddodi

 1. Zayyanu


Hajiya Asabe Illela

 1. Ubaida

 2. Abdullahi

 3. Bashari

 4. Aminu

 5. Mas’udu

 6. Mustapha


Hajiya Sadiya Wurno

 1. Zara’u

 2. Amina (Uwani)

 3. Mas’uda

 4. A’isha

 5. Aliyu

 6. Abubakar

 7. Nana Firdausi

 8. Maryam


Hajiya Aminatu K’auran Namoda

 1. Hadizatu

 2. Kabiru


Asabe K’arama Illela

 1. Murjanatu


https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-2/

2.1.6 Fara Wak’arsa


Wazirin Alhaji Musa ‘Danba’u Shehu Waziri ya sheda min cewa, ‘Danba’u ya fara wak’a shekara bakwai kafin kafuwar jam’iyoyin NPN da GNPP da UPN da kuma NPP. An kafa wad’annan jam’iyyun ne a shekarar 1978 (Birniwa, 1987) da Funtua (2003: 37). Kenan ya fara wak’a ne a shekarar 1972. Kuma ya fara ne da wak’ok’in kokawa. Daga ciki akwai wak’ar Isiya Zakinsu ‘Danba’u ga yadda wak’ar take:

Amshi: Isiya zakinsu ‘Danba’u

Kowaj ja da kai bai ji dad’i ba,

 

Jagora: Wahabu Allah ka kiyaye bayinka,

Yara: Wahabu Allah gyara gyararre

Isya zakinsu ‘Danba’u

Kowaj ja da kai bai ji dad’i ba.

(Shagari, 2011; Gusau, 2014).

Haka kuma akwai wata wak’ar kokawa wadda wazirin ‘Danba’u ya rera min ya ce tana daga cikin wak’arsa ta farko wak’ar ita ce:

Ya ci maza giyen ‘Danba’u,

Kadi maza suna saunatai.

 

Wannan d’an bara ya kaka,

Ya ci tsakin miya yai k’arhi.

 

To irin yanda ya taho maka Buba,

Buba ka fad’i rwahin gulbi,

Ga ‘yan yara na dwaga tai.

 

Daga wak’ar kokawa wazirinsa ya ce ya fara had’awa da wak’ar noma. Inda ya yi wata wak’a ta Abba na D’anladi. Ga yadda wak’ar take:

Kana da noma,

D’an Aba na D’anladi.

Na d’anguje,

Na D’anladi,

Na Akki mai aiki,

In dai ina da raina,

Sai kowa ya ji sunanmu.

Haka ko ya tabbata domin dun inda ake jin harshen Hausa an san ‘Danba’u daga nan ya ci gaba da wak’ok’insa har zuwa shekara ta 1978 lokacin da siyasar jamhuriya ta biyu, inda aka samu jam’iyyun NPN da GNPP da UPN da kuma NPP inda wasu ‘yan jam’iyyar NPN suka buk’aci ya yi musu wak’ar jam’iyyarsu ta NPN sai ya fara tunanin, shi da ke wak’ar kokawa yaya zai yi wak’ar siyasa? Daga k’arshe ya yanke shawarar ya wak’e jam’iyyar. Daga cikin mutanen da suka buk’aci ya yi wa NPN wak’a sun had’a da:

 1. Umaru Jikan Macca

 2. Arzika Maikujera Ciyan Party

 3. Wakili Buhari


Ga yadda wak’ar take:

Amshi: Aminci ya fi kud’i,

Mu yarda da NPN

 

Jagora: in kag ga mutum kajin-kajin

Kag ga mutum mak’al-mak’al,

Ba rigar dala garai,

Yara:    Alhaji haske ne,

Alhaji mai zamani,

Allah magaba,

Allah raba mu da d’an kwakwa.

Amshi:  Aminci ya fi kud’i,

Mu yarda da NPN.

 

Wannan wak’a da ya yi ta burge jama’a k’wari da gaske. Daga nan sai ya kama harkar wak’ar siyasa gadan-gadan har zuwa k’arshen rayuwarsa.

2.1.7 Yaransa Makad’a da Marok’a


        Lokacin da na yi hira da wazirin ‘Danba’u ya tabbatar min da cewa yana da yara goma sha d’aya da marok’a hud’u. Su goma sha biyar (15) kenan. Amma Mande direba ya riga shi rasuwa.

Yaransa

 1. Shehu Waziri Gidan Buwai

 2. Garba K’yamashi Gidan Buwai

 3. Muhammadu Bello Gidan Buwai

 4. Adamu Tozai Illela

 5. Muhammadu D’anmafara Gidan Buwai

 6. Muhammadu Nasiru Acida

 7. Baba Garba Tsaumawa/Jangebe

 8. Abdu Bagobir, Kadagiwa/Wurno

 9. Muhammadu Wandon K’arfe Gidan Buwai

 10. Mande Direba Acida

 11. D’anladi Dogo Illela


Marok’ansa

 1. Abdu Wakili Huci/Gwadabawa

 2. Muhammad D’anmaraya Kalmalo/Illela

 3. Zakari Ya’u Darma/Illela

 4. Muhammadu Nakogo Gidan Buwai


Wad’annan mutanen Wazirin ‘Danba’u da Adamu Tozai su sheda min cewa duk inda ‘Danba’u yake yana tare da su. Kuma shi ne cinsu da shansu, da suturarsu da su da iyalansu gaba d’aya. Kuma daga cikinsu akwai masu mata biyu akwai masu mata uku. Kuma shi ke yi musu kowace lalura.

Yanzu haka Wazirin ‘Danba’u ne halifan wak’a kuma duk yaransa da marok’ansa da kayan kid’ansa duk da su yake amfani wurin gudanar da wak’ok’insa kamar yadda maigidansu ke yi. Yanzu haka suna nan suna wak’ok’insu daga cikin wak’ok’in da waziri ya yi akwai wak’ar Aminu Waziri Gwamnan Jihar Sakkwato da Wak’ar Madawakin Daura Sanata Mustapha.

Wak’ar Aminu Waziri

Amshi: Rik’a k’warai ka hi su sa’a,

Sabon gwabna d’an waziri,

Aminu mai halin bajinta.

 

Jagora: Yara ku shirya za mu Sakkwato,

Yara: Don in iske Aminu gwamna.

Jagora: Yara ku kimtsa za mu Sakwkato,

Yar:   Don in iske Aminu gwamna.

 

Amshi: Rik’a k’warai ka hi su sa’a,

Sabon gwabna d’an Waziri,

Aminu mai halin bajinta.

 

Jagora: Mun san Allah ad da mulki,

Sannan shi ke ba da mulki,

Inda ya so zai ba da mulki,

Yau kai ne matawalle Sakkwato,

Kai ne gwamnan Sakkwato

D’auki halin da Aliyu ya yi.

Yara: Rik’e talakawanka da kyawo,

Ka rik’e amana d’an waziri.

 

A cikin wani d’an wak’ar yake cewa:

 

Jagora: Ga gwamna da mataimaki nai,

Ga Ahmad Ali ga Aminu,

Akwai wani d’an sak’o gare ni,

Kun san ‘Danba’u ya hurce,

To ku rik’e mu amana Allah,

In kun rik’e mu kun yi daidai,

In kun aje mu babu komai

Yara: Mu mun tsaya ga sarki Allah,

Mun san Allah shi ka baiwa.

 

 

Wak’ar Madawakin Daura Sanata Mustapha


Amshi: Maganin maza,

Yaro ba ya hwad’a ka wargi,

D’an Abubakar,

Sanata Mustafa madawaki.

 

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Ka ga halinta duniya,

Wata rana a sha zuma,

Wata rana a sha mad’aci,

In yau anai da kai,

Wata ran ba a yi da kai.

Yara: Ai ta bi d’a mutum,

Ba a ganai ba.

 

Amshi: Maganin maza,

Yaro ba ya hwad’a ka wargi,

D’an Abubakar,

Sanata Mustafa Madawaki

 

Jagora: ‘Danba’u ya wuce,

Ga yaran da ya bari,

Baba rik’e mu amana.

Yara: Sanata Mustafa Maigidana.

 

Jagora: D’an Audu rik’e mu da k’ima,

Yara: Sanata Mustafa maigidana

 

Jagora: D’an Garba rik’e mu amana,

Yara: Sanata Mustafa maigidana.

 

Haka wazirin ‘Danba’u yake gudanar da wak’ok’insa yana biyar zubi da tsarin wak’ok’in ‘Danba’u da kuma amfani da irin salailansa.

2.1.8 Nau’in Wak’ok’insa


        Alhaji Musa ‘Danba’u ya shahara a fagen wak’a saboda haka ya zama hantsi lek’a gidan kowa. Don haka yana da wak’ok’i iri-iri kamar haka:

 1. Wak’ok’in kokawa

 2. Wak’ok’in noma

 3. Wak’ok’in siyasa

 4. Wak’ok’in sarauta

 5. Wak’ok’in masu mulki

 6. Wak’ok’in sauran jama’a

 7. Wak’ok’in yekuwa/fad’akarwa/gargad’i


Haka kuma duk wata wak’a da aka buk’ata a yi, ‘Danba’u na yin ta.

2.1.9 Yawace-yawacensa


Shagari (2011) cewa ya yi, ya yi hira da ‘Danba’u inda yake cewa: “mawak’in ya tabbatamin cewa ba ya iyakance wurare da ya tafi amma nan gida Nijeriya babu jihar da bai tafi ba. Haka kuma Nijar ma ya shige ta kamar Nijeriya. Wato babu jihar da bai shiga ba a cikin jamhuriyar Nijar. Sana’arsa ta wak’a da kid’a ita ce ta kai shi jamhuriyar Nijar. Sannan kuma ya je Makka wajen aikinhajji da Umra ba sau d’aya ba.

Ni kuma hira da na yi da wazirin ‘Danba’u ya sheda min cewa, a Nijeriya jihar Barno (Maiduguri) can ne kad’ai ba su je ba. Domin sukan je cin rani a shekara k’asashen kudu kamar Anaca da Benin da Okene da Wari da Legas da sauransu. A Nijar sun zagayi ciki da wajenta sunje Difa da Agadas da Zandar da Marad’i da Tawa da Doso da Birni Bayero da Niamey da Tiliberi da sauransu.

 

2.1.10 Nasarorin da Ya Samu a Cikin Wak’a


        Waziri ‘Danba’u a hira da muka yi da shi ya sheda mini cewa duk wata nasara da ake samu a rayuwa D’ana’u ya samu a cikin wak’a domin a cikinta yake ci, cikinta yake sha, a cikinta yake sutura, iyalansa da makad’ansa da marok’ansa da duk wani wanda ke ci k’ark’ashinsa duk wak’a ce. Haka kuma a cikin wak’a ya yi gida, ya yi wa yarana, motoci da kujerun Makka duk a dalilin wak’a ne.

Wazirin ‘Danba’u Shehu da Adamu Tozai sun sheda min cewa, ko ‘Danba’u bai iya bayyana adadin motar da suka samu a dalilin wak’a wanda ya fara ba shi mota shi ne Abu Zahara k’aura lokacin jam’iyar NPN a shekara ta 1978. Sannan sanata Ila Gada ya ba su Bus mai rubutun NPN, kuma ya samu mota ta k’arshe bayan an bayyana sakamakon za’ben gwamna na 2015 inda aka bayyana Aminu Waziri ya lashe za’be, sai gwamnan ya ba shi mota k’irar honda mai suna Anaconda.

Wanda ya fara ba shi kujerar Makka shi ne sanata D’anmalam Ila a Legas. Amma asalinsa d’an jihar Kebbi ne. Haka kuma waziri Shehu ya fad’a min cewa ya samu lambar girmamawa a wurare kamar haka:

 1. Rima Rediyo Sakkwato

 2. K’ungiyar ‘Yanjarida ta Jihar Sakkwato

 3. Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato


Haka kuma shis ne Ambasadon mawak’an Hausa na Nijeriya da Nijar.

2.1.11 Sha’awarsa


        Alhaji Musa ‘Danba’u mutum ne mai sha’awar wasanni. Hasali ma sha’awar wasanni shi ya sa ya fara wak’ar kokawa kuma yana sha’awar wasar k’wallon k’afa kusan duk wanda ya san ‘Danba’u a Illela ya san yana sha’awar k’wallon k’afa musamman ta k’asashen Turawa domin yana cikin rik’ak’k’un masu goyon bayan k’ungiyar Barcelona ta k’asar Spain. Haka kuma yana sha’awar tafiye-tafiye. Ta ‘bangaren abinci kuma ‘Danba’u bai da kamar tuwon dawa da hurar gero.

2.1.12 Rasuwarsa


Kullu nafsin za’ik’atil mauti, duk mai rai mai d’and’ana mutuwa ne. Allah ya yi wa Alhaji Musa ‘Danba’u rasuwa ranar talata 7-4-2015, jim kad’an bayan bayyana sakamakon za’ben 2015.

Babangida Kaka Dawa a cikin wak’arsa yana cewa:

Mutuwa mai yanke k’auna,

Da duk kake son mutum,

Bai tsayawa in ta zaka.

 

Mutuwa mai d’auke shed’a,

Da duk kake k’in mutum,

Ya mutu sai kai ka mutu.

 

 

Gindi: Murna mukai,

Ka yi sarkin Musulmi,

Muhammad Sa’adu,

Ya gadi halifan Bubakar.

 

Allah ya jik’an Alhaji Musa ‘Danba’u amin.

https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-3/

 

2.2 Dangantakarsa Da Sauran Mawak’a


Alhaji Musa ‘Danba’u kamar yadda na tattauna da mutane sun sheda min da cewa yana da kyakkyawar huld’a tsakaninsa da sauran mawak’a domin mutum ne da bai da hasada kuma duk inda hak’en mawak’i ya kai zai bi don amsar masa hak’insa. Haka kuma idan wani mutum ya yi wa wani mawak’i alk’awali bai cika ba, ‘Danba’u yakan bi wannan mutumin har sai ya kar’bo wa mawak’in alk’awalin. Shi ya sa mawak’a ke kiran sa Ambasadan mawak’an Hausa Nijeriya da Nijar. Haka kuma sun fad’a min cewa, yana kyautata wa mawak’a har ta kai karnan makad’an Nijeriya da Nijar da sauran mawak’a ke zuwa har gidan ‘Danba’u suna yi masa wak’a. Daga cikin mawak’an akwai:

 1. Sani karen makad’a Gwadabawa

 2. Shehu karen makad’a kurya

 3. Makad’a Dauro da dai sauransu.


Akwai lokacin da mawak’a suke k’orafi cewa idan aka je taro da an gabatar da ‘Danba’u to ba za a sake gabatar da wani mawak’i ba, ko kuma duk wanda aka gabatar hikimar ‘Danba’u za ta dushe tashi ba a ganin k’ok’arinsa. Da ‘Danba’u ya ji haka duk inda aka je taro yakan ce a bar shi k’arshe.

Game da kyautata wa mawak’a ni kaina na sheda a lokacin da aka yi taron siyasa lokacin da shugban k’asa Obasanjo ya zo Sakkwato a filin sukuwa, da idona na ga ‘Danba’u yana wa Gambo mai wak’ar ‘barayi karin kud’i naira d’ari-d’ari.

2.3 Dangantakarsa da Sauran Jama’a


        Dole makad’i ya yi huld’a da mutane musamman wad’anda yake shirya wa wak’a da kuma masoya masu ra’ayin wak’ok’insa. Kuma yana wak’ok’in siyasa yana zuwa kamfe kuma yana huld’a da saurakuna da masu mulki da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da sauran jama’a daban-daban.

Wannan ya ba ni damar tattaunawa da wasu mutane da nake jin yana yawan ambaton su a cikin wak’ok’insa da kuma wasu wad’anda ya yi wa wak’a da kuma sauran mutane da ke zaune wuri d’aya da shi. Daga cikinsu akwai Alhaji Bala Musa Yabo da Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi da Muhammadu Galadima Horo (D’an’ige Horo) da Yusuf Bello D’ancad’i da Alhaji Audu na k’ofa (Sarkin bak’i) da Alhaji Hadi D’anmalam da Musa Damo da Alhaji Sanusi D’anwali da Alhaji Mani Sardaunan Illela da wasu daga cikin yaransa kamar waziri Shehu da Adamu Tozai da sauran mutane da dama. Sun fad’a min cewa Alhaji Musa ‘Danba’u mutum ne mai kyakkyawar huld’a tsakaninsa da jama’a. Kuma mutum ne wanda ba shi da girman kai. Yana da yawan son wasa da mutane manya da yara kuma yana girmama mutane manya da yara.

Wannan ni ma sheda ne domin mun had’u da shi a gidan mai martaba Sarkin Musulmi Muhammdu Maccid’o a ranar da aka yi nad’in sarautun sarkin yamma da sarkin Arewa da Jarma da Katuka da Durumbun Sakkwato. Na je wurin ‘Danba’u muka gaisa kuma ya kar’be ni hannu bibiyu.

 

2.4 Nad’ewa


        A tak’aice a cikin wannan babin an kawo bayanai kan tak’aitaccen tarihin makad’in da ake nazari a kansa watau Alhaji Musa ‘Danba’u tun daga haihuwarsa da iliminsa da iyayensa da aurensa da matansa da ‘ya’yansa da yaransa makad’a da marok’a da nasarorin da ya samu da nau’o’in wak’arsa da yawace-yawacensa da abubuwan da yake sha’awa da dangantakarsa da ‘yan uwansa makad’a da mawak’a da kuma sauran jama’a. Kai! Har rasuwarsa.

 

Post a Comment

1 Comments

 1. Allah gafartama musa dan ba'u da sauran al'ummar musulmi.

  ReplyDelete

Rubuta tsokaci.