NA


SHEHU HIRABRI


08143533314KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘Danfodiyo, SAKKWATO 

BABI NA UKU


ZAMBO A CIKIN WASU WAK’OK’IN ALHAJI MUSA ‘DANBA’U GIDAN BUWAI3.0 Shimfid’a


Wannan babi zai yi bayani tare da kawo misalai a kan asalin kalmar zambo da ma’anrta da ire-irenta da dalilin da ya sa ake yin zambo da amfanin sa ga al’umma tare da yin sharhinsa a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.

3.1 Asalin Kalmar Zambo


An samu bambancin ra’ayi dangane da asalin kalmar zambo. Masana da manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da asalin kalmar. Abdullahi, (1995: 21) cewa ya yi: “Asalin zambo abu ne mai wuya a ce ga lokacin da aka fara samun sa a cikin wak’a kamar yadda ba a iya cewa ga rana ko lokacin da aka fara wak’a gaba d’ayanta. A nan ina ganin tun lokacin da d’an Adam ya fara bud’e baki da sunan yin wak’a ya k’irk’ira dabarar yin zambo don yi da wani ko musguna masa a kaikaice. Da haka dai zambo ya ci gaba da yawaita a cikin wak’ar baka ta Hasua har kawowa wannan lokaci da ya zama ruwan dare a cikin wak’ok’i.”

Yahaya da wasu (2006: 40) cewa suka yi: “Asalin kalmar zambo, Bahaushiyar kalma ce, ba aro ta an ka yi ba.” Dalilin da suka kafa shi ne, zambo dad’ad’d’en abu ne a cikin tarihin adabin Bahaushe na gargajiya.

Wasu na ganin asalin kalmar zambo daga harshen Larabci aka samo ta, wato “alzammu” mai ma’ana da Larabci zargi. Sannu a hankali kalmar ta tashi daga zammu ta koma zambo (Yahaya da wasu, 2006: 40).

Bunza, (2009: 132) cewa ya yi: “kalmar zambo ta fuskar furuci da rubutunsu da ma’anarsu ta fi kusa da kalmar zamba.”

3.2 Ma’anar Zambo


Masana malamai da manazarta da dama sun bayyana ra’ayi dangane da ma’anar zambo kamar haka:

Gusau, (1979: 39) cewa ya yi: “Zambo kalma ce wadda ake amfani da ita a matsayin kishiyar yabo, wato a siffanta wani mutum da wasu siffofi munana wad’anda za su walak’anta shi da jawo masa rashin martaba a idon ‘yan Adam tare da kau da kai cewa wannan mutum yana da wad’annan siffofi ko ba shi da su.”

Dangambo, (1984: 32) cewa ya yi: “Zambo zagi ne na kai tsaye, cikin zambo ana siffanta mutum da halayensa da d’abi’unsa da danginsa da iyayensa da dai duk wani abu da ya shafe shi wanda zai taimaka a gane da shi ake.”

Gusau, (1988:315) cewa ya yi: “Zambo wasu kalmomi ne na muni da ci wa mutum mutunci da ake amfani da su kai tsaye ga wanda ake buk’ata. A wajen zambo ana iya fitowa fili a fad’i wata fitacciyar siffa ta mutum wanda nan take ake saurin gane wanda ake nufi.”

Modibbo, (1989: 32) cewa ya yi: “Zambo dai shi ne fad’in mugun abu ga mutum, kuma zambo kishiyar yabo ne. akan ‘baci mutum da abin da yake na gaskiya, amma maras kyau ko kuma k’age.”

Abdullahi, (1995: 21) cewa ya yi: “Zambo magana ce da akan shirya a cikin wak’a domin muzanta mutum. Mawak’an Hausa na baka da marubuta suna amfani da zambo a cikin wak’ok’insu don musgunawa abokan hamayyarsu ko abokan hamayyar wad’anda suke yi wa wak’a, ta fitowa k’uru-k’uru su muzanta su ta siffanta su da wasu abubuwan munana marasa kyau kamar rowa rashin fara’a da dai sauransu.”

Shinkafi, (1998: 20) cewa ya yi: “Zambo siffanta mutum da wasu siffofi munana domin a muzanta shi ga idon mutane ko da ba ya da su. Zambo kishiyar yabo ne.”

Dumfawa, (2005:19) cewa ya yi: “Kalmar zambo tana nufin aibanta wani mutum ko wani abu dangane da sifarsa ko ak’idarsa ta yin amfani da wasu lafuzza na aibantawa ko muzantawa ko munanawa.”

K’amusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:489) an bayyana cewa: “Zambo na nufin k’aga wa mutum magana wadda za ta muzanta shi ta ‘bata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. Marok’a sun fi yin haka a cikin wak’a.”

Bunza, (2009: 132) cewa ya yi: “Kalmar zambo ta fuskar makusanciyar ma’ana tana da alak’a da habaici, ta fuskar furucinsu da rubutunsu da ma’anarsu tafi kusa da kalmar “zamba”. Zambo ya fi habaici zafi domin k’aga shi ake yi a lik’a wa wanda ake yi wa. Daga cikin kayan cikin zambo akwai:

 1. Wulak’anta wanda ake yi wa da wani abu na k’ask’anci ga irin matsayinsa.

 2. K’ara gishiri ga halinsa, ko wani aibi da aka san shi da shi. • K’ago abin da bai ji ba bai gani ba, a ce ya yi, ko ya ce ko nasa ne. 1. Yi masa muguwar fata.”


Zaruk da wasu (2011) cewa suka yi: “Zambo d’an uwan habaici ne. sai dai shi zambo ya fi habaici tsanani. Galibi idan an yi wa mutum zambo domin a tozarta shi a idanun jama’a idan za a yi wa mutum zambo akan d’auki wani hali nasa ko sifa a yi masa zambo da shi.”

D’anhausa, (2012) cewa ya yi: “Zambo ana yin sa ne musamman dan fad’akar da mutum ta hanyar ‘bata shi, wato fallasa shi domin a nuna ana sane da ire-iren miyagun d’abi’u da ke tare da shi had’e da ba shi shawara amma ba kai tsaye ba, ta cikin hikima wato rara-gefe idan an misalta shi da zambo.”

Yahya da wasu (2015: 17) cewa suka yi: “An bayyana zambo a matsayin kalma wadda ake amfani da ita a matsayin kishiyar yabo wato a siffanta wani mutum da wasu siffofi munana wad’anda za su wulak’anta shi da jawo masa rashin martaba a idon ‘yan Adam tare da kau da kai cewa wannan mutum yana da wad’annan siffofi ko ba shi da su.”

Yakasai (2012: 171) cewa ya yi: “Zambo salo ne da ‘yan siyasa musamman mawak’a suke amfani da shi domin su muzanta wani ko wasu k’ungiyoyin siyasa ta fuskar ambata tare da k’irk’iro wasu miyagun d’abi’u ko asali su danganta su ga wanda suke son su nak’k’asa domin mutane su kauce wa jefa masa k’uri’a lokacin za’be.”

Idan aka yi la’akari da wad’anna ma’anonin da suka gabata, a tawa fahimta ana iya cewa: Zambo suka ce da ake yi kai tsaye ta hanyar kawo hoton mutum, ko wani abu cikin surarsa ko halayensa ko kuma duk wani bayani wanda zai taimaka a fahimce da wanda ake kai tsaye domin a ‘bata masa rai tare da walak’anta shi da kuma kadar masa da k’ima da mutunci a idon jama’a.

 

https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada/

3.3 Ire-Iren Zambo


An samu bambancin ra’ayi dangane da ire-iren zambo. Barmo (2014: 15) da Modibbo (1989:32) sun bayyana ire-iren zambo kamar haka:

 1. Zambon halitta

 2. Zambon asali

 3. Zambon sarauta

 4. Zambon hali


Shi kuwa Tuluwa (2012: 75) ya kawo ire-iren zambo kamar haka:

 1. Zambon kama ko halitta

 2. Zambon asali

 3. Zambon matsayi

 4. Zambon hali


A nan an samu bambanci tsakanin zambo sarauta da zambon matsayi.

 • Zambon kama ko Halitta: Zambo ne da mawak’a ke yi ta hanyar bayyana wata halitta da Allah ya yi wa mutum ko kuma su kalli wani abu da ya yi kama da halittar ya kira mutum da sunan wannan abin ko ya kwatanta su. Misali, a wak’ar Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai inda yake cewa:


Jagora: Ga wani d’an takara da doro,

Abu dai zuk’ui-zuk’ui,

Ke kuma bushiya ki ‘boye doronki,

Ba ki bakin komai.

Yara:    Wurin hwarauta banza ce.

 

Gindi:  ‘Ya’yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma PDP

 

 • Zambon Asali: Zambo ne da mawak’a ke yi wa mutum ta hanyar bayyana wani abu da ya shafi tushen asalin mutum ta fuskar tozartawa ko muzantawa. Misali kamar zambon da Audu Stim ya yi wa wani sharifi inda yake cewa:


Wane ba mu zagin babanai,

Don darajar kakansa,

Wurin uwa tai muka komawa

Mu yi mai gora,

Mun san asalin wance

Tasha tat tashi.

 

Gindi: Bafarawa Gwamnan Sakkwato,

Mai adalci mu muna tare da kai,

Gwamna muna bayanka.

 

Wani misali a cikin wak’ar ‘Danba’u inda yake cewa:

Jagora: Kowat taso tare da manya,

Ka san yana da tarihi,

Don haka manya sunka gaya mini,

Yara:    Danginsu Maguzawa ne.

 

Gindi:  D’antakarar zama gwamna,

Magatakarda wamakko,

Aliyu kar ka d’au reni,

Kuma kar ka d’au wulak’anci.

 

 • Zambon Matsayi: Zambo ne da ke da fuska biyu. A fuska ta farko mawak’a kan yi amfani da matsayin da mutum ya samu musamman lokacin da aka yi jayayyar sarauta ko mulki ko wani abu makamancinsu, sai su yi amfani da wannan matsayi su wa abokan hamayya zambo. Misali a wak’ar ‘Danba’u ta ciyaman d’in Gada Tanimun D’angaladima inda yake cewa:


Jagora:  K’ara hank’uri kar ka ji komai,

Hank’urinka shi na kai ka haka,

Hak ka yi ciyaman k’asar Gada

Ka kada biri sarkin k’walama,

Ci k’ungurguma a ci buzuzu,

Yara:    Na ce biri a yi a hankali

Wata ran cikinka ya ‘baci.

 

A fuska ta biyu mawak’an sukan yi zambo domin k’ok’arin ‘bata wani matsayi da wani mutum yake da shi a idon jama’a domin muzanta shi ko a ‘bata masa rai. Misali a wak’ar ‘Danba’u ta Aliyu Magatakarda Wamakko inda yake cewa:

Jagora: Aliyu kai ka gadi sarauta,

Ka yi nad’i daidai da sarauta,

Wanda duk bai gadi sarauta ba,

Yara ko ga nad’i sai mun gani.

Yara:    Wane nad’i nai ya cika girma,

Wanga uban huni sai ‘yan dako.

 

Gindi:   K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

 • Zambon Hali: Zambo ne da mawak’a kan yi ta hanyar amfani da mugun halin mutum sai a yi masa zambo a kai nai. Wani lokaci kuma sukan kwatanta halin mutun da na wata dabba mai irin halinsa sai su yi zambo su d’ora a kansa. Misali, ana iya wa mutum zambo ta hanyar rowa da sata da zina da kushili da k’arya da munafunci da zalunci da makamantansu. Haka kuma ana wa mutum zambo da halin dabba kamar biri da jaki da kusu (‘bera) da muzuru da bunsuru da kare da makamantansu. misali a wak’ar ‘Danba’u ta Matawallen Sakkwato Aminu Waziri yake wa abokin hamayya zambo da halin rowa inda yake cewa:


Jagora: Ga wani na neman Matawalle,

Kai k’wank’iro wa za ya nad’a ka,

Kowa ya san bai alheri,

Yara:    Bai iya kyauta ba a yaba mai,

 

Gindi:   D’an waziri ka k’ara shirawa

Aminu yau kai am matawalle.

 

Wani misali a cikin wak’ar Narambad’a ta mazan gabas tsayaye yana yi wa wani d’an sarki zambo da halin k’arya da rowa, inda yake cewa:

Jagora: Ka ga d’an sarki da kurruwa da hwad’i

Ga ya da k’arya ga ya da rowa,

Yara:    Ko ka girmama shi ba ya sarki.

 

Gindi:  Masu gari mazan gabas tsayayye

 

 

 

3.4 Dalilin Yin Zambo


Dalilai da dama ke sa a yi zambo, daga cikinsu akwai:

 1. Duk lokaci da aka yi jayayya ta siyasa ko sarauta ko neman aure ko nema wani muk’ami ko wani matsayi da makamantansu. Mawak’a da wad’anda ba mawak’a ba kan yi zambo ga abokan hamayya.

 2. Ana yin zambo domin a muzanta mutum ko wulak’anta shi ko cin zarafinsa. • Ana yin zambo domin a bayyana wani mugun hali ko d’abi’a da mutum ke da. 1. Ana yin zambo domin a huce haushi musamman in akwai wata adawa ko husuma a tsaknin wasu.

 2. Ana yin zambo domin tsoratarwa a kan wani abu da wani ke son ya yi ga wani mutum ko wani al’amari kamar sarauta ko siyasa ko wani abin da ya shafi zamantakewar al’ummar Hausawa.

 3. Ana yin zambo don samar da nishad’i da raha a cikin zukatan al’umma. • Ana yin zambo don a ‘bata wa mutum rai.


3.5 Amfanin Zambo


Duk da yake zambo suka ce da ake yi kai tsaye ta fuskar ‘batanci, amma kuma yana da amfani matuk’a. Daga cikin amfanin zambo akwai:

 1. Zambo yana hana yin shishigi watau mutum ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.

 2. Zambo wani ado ne da ke k’awata wak’a tare da k’ara mata armashi, ba wak’a kawai ba har sauran zantukan yau da kullum.

 3. Zambo na sa mutum ya san miyagun d’abi’unsa ko k’azafi ko wani abin da jama’a ke zarginsa da shi.

 4. Zambo na sa mutum ya daina wasu miyagun halaye ko d’abi’u

 5. Zambo na bayyana miyagun d’abi’un jama’a cikin hikima domin a k’aurace musu.

 6. Zambo kan taimaka wajen k’ara soke abokan hamayya.

 7. K’warewa wajen gina zambo a cikin wak’ok’i musamman na siyasa ko sarauta na k’ara wa mawak’i d’aukaka da farin jini ga jama’a.

 8. K’warewa wajen gina zambo a cikin wak’ok’i, na sa mawak’i ko marok’i ya samu alheri.

 9. Zambo wata taska ce ta adana adabin al’ummar Hausawa.

 10. Zambo na samar da nishad’i cikin raha da wartsakewar rayuwa.


3.6 Zambo A Cikin Wasu Wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai


A sama an kawo ma’anar zambo da ire-irensa da dalilan da ke sa a yi shi tare da bayyana amfaninsa. A nan kuwa za a kawo zambo a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u tare da yin sharhinsa a bisa mizanin nazari.

Kamar yadda Yahya( 1997) ya bayyana cewa: “Zambo wasu zantuka ne ake yi ta hanyar za’ben wasu kalmomi da za su ‘bata ko musguna wa wanda ake wa. Akan kwatanta kama ko d’abi’a ko hali na mutum da wasu siffofi don a wulak’anta shi. Kenan zambo yakan bayyana wanda ake wa shi a fili ba tare da wata wahala ba.

Za a ga irin wad’annan bayanan da Yahya, (1997) ya bayyana a kan zambo a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u. Haka kuma ‘Danba’u na amfani da hanyoyi biyu wajen gina zambo a cikin wak’ok’insa.

Hanya ta farko ‘Danba’u kan dubi abin da ke faruwa tsakanin wanda yake wa wak’a da abokin hamayyarsa sai ya gina zambo. Hanya ta biyu ‘Danba’u kan gina zambo ta hanyar bayyana wani abu da ke faruwa tsakaninsa (shi mai kid’i) da wani mutum sai ya gina zambo a cikin wak’a.

A wak’ar Alhaji Musa ‘Danba’u mai taken:

Ciyaman bugun ciyamomi:

Bala ba a jan ka d’an Musa.

Wadda ya yi wa ciyaman d’in Yabo Alhaji Bala Musa Yabo, inda yake cewa

Jagora: Wani ya sha karo da d’an Musa,

Ado na ji Bala ya kasai,

Can nig gane shi Dagawa,

Wawa ya d’au buhuhuwan lalle

Yara:   Ya ce za ya kasuwa muza.

Idan an lura, wannan d’an wak’a mawak’in ya bayyana wata gwagwarmayar da aka yi a lokacin za’ben ciyamomi inda Bala Musa ya samu nasarar lashe za’ben, sai ya yi amfani da galabar da ya samu sai ya wa abokin takararsa zambo da cewa ya sha karo da d’an Musa. Kuma an kasai. A nan kowa zai fahimci da wanda ake wato abokin takararsa, kuma don ya k’ara bayyana wanda yake wa zambo sai ya kawo sunan garin Muza saboda abokin hamayyarsa d’an garin Binjin Muza ne. Haka kuma a wani d’an yake cewa:

Jagora: Kansiloli daban-daban Audu,

Kansiloli daban-daban Ada,

Ga kowane yana ta k’iba,

D’an tsuntsun tsorolo tsomodo,

Yara:   Shi har yanzu bai yi gwa’bi ba.

 

A wannan d’an wak’ar mawak’in ya kawo siffar wani kansila wadda za ta sa a fahimci wanda ake wa zambo. Saboda ya nuna shi wannan mutum siriri ne kuma bai da k’iba.

Duk dai a cikin wannan wak’ar ya k’ara da cewa:

Jagora: Wani ciyaman na duba,

K’azami ne ku mun san shi,

Taro munka je da shi Legas,

Kwana ukku bai yi wanka ba,

Yadda ya mammatso ni sai nic ce,

Yara:    Tahi dan nan kana yi man wari.

A wannan d’an wak’a ya yi wa wani ciyaman zambo ne a kan wata halayyarsa ta zama da daud’a, domin idan aka gan shi kamar ba ciyaman ba, ga shi da rowa kuma ko kansa bai amfana ba.

 

 

Wak’ar Gwamnanmu Mun yi Mun K’are Ta Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko


Amshi: D’antakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka d’au reni,

Kuma kar ka d’au wulak’anci.

 

A cikin wannan wak’ar ‘Danba’u ya baje kolinsa ta hanyar gina zambo a d’iya da dama, kamar haka:

Jagora:  Tun sadda wane yai gwamna,

Martabar jaharmu ta hwad’i,

Mai ilimi da da marar ilimi,

Dole ne a samu bambanci,

Ku Sakkwatawa albishirinku,

Ga d’an uwanku nan d’anku,

Shi za ya takarar gwamna,

Ku daure ku ba shi goyon baya,

 

Yara:     In Aliyu ya zamo gwamna,

Martabar jaharmu ta tashi.

 

A wannan d’an wak’ar mawak’in ya kawo bayanai kai tsaye wad’anda ke sa a fahimci da wanda ake, kamar “gwamna da ilimi” a nan kowa zai fahimci gwamnan da ake magana wato gwamnan da ke jayayya da d’an takarar da ake yi wa wak’a. Haka kuma ya kawo maganar ilimi kasancewar gwamnan bai yi karatu mai zurfi ba daga firamari sai takardar kammala karatun pi’botal. Shi kuma wanda ake yi wa wak’a a k’asar Amurika ya yi karatunsa na digiri. A nan ya soki gwamna da cewa tun lokacin da wannan gwamnan ya fara mulki martabar jiharsu ta fad’i saboda ba ya da ilimin gudanar da mulki. Sannan ya yabi d’an takararsa da cewa idan suka za’be shi martabar jaharsu za ta dawo saboda yana da ilimin gudanar da mulki.

Haka kuma a cikin wani d’an wak’ar yake cewa:

Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,

Birni da k’auye na duba,

Kuma manya da yara na duba,

Duk inda ka ishe d’an abarba,

Yara:    Ya iya shirin munahucci.

 

Jagora: wannan

Yara:    Ya iya shirin azuranci.

 

A wannan d’an wak’ar mawak’in ya yi amfani da alamar wata jam’iya mai hoton abarba ya kira su da suna ‘yan abarba’ wanda kowa zai fahimci ‘yan jam’iyar da yake nufi. Ya soke su ta hanyar mamaki da cewa ‘yan birni da k’auye manya da yaransu duk sun iya munafucci da azuzanci.

Duk a cikin wak’ar ya k’ara da cewa:

Jagora: Ni ‘Danba’u hamdullahi,

Na yi godiya wajen Allah,

Siyasar su wane ta watse,

Yau shekara takwas suna mulki,

Girman sarakuna sun kasai,

Ga d’an talakka ya sha k’waya,

Wai za ya kori sarkinmu,

Kahin ya kori sarkinmu,

Allah ya biya buk’atunmu.

Yara:   Sai ga sakamako ya yi,

Shi ya rigayi hisshe shi.

 

A wannan d’an wak’ar mawak’in ya yi zambo ga wasu ‘yan siyasa abokan hamayyar wanda yake yi wa wak’a ta hanyar ayyana wasu abubuwa da suka faru tsakaninsu bayan sun yi mulki shekara takwas daga k’arshe suka samu rabuwar jam’iya. Haka kuma ya bayyana wasu rad’e-rad’in da ake yi cikin gari na cewa shi jagoran mai mulki ya ce sai ya tu’be sarkin garin daga karagar mulki. Wannan bayani da ya kawo k’arara za a fahimci da wad’anda ake wa zambo.

Haka kuma a wani d’an wak’ar yake cewa:

Jagora: A yanke mutum a yanke dabba,

Don tattalin bak’in tsahi,

Don a hau kujerar mulki.

Yara:   In lokacinka ya k’are,

Tsahinka dun na banza ne.

 

Jagora:  wawa

Yara:    In lokacinka ya k’are

Tsahinka duk na banza ne,

 

Jagora: Saga!

Yara:    In lokacinka ya k’are,

Tsahinka dun na banza ne.

 

A wannan d’an wak’ar, mawak’in ya yi zambo ne a kan wani shugaba wanda al’ummar garin ke zarginsa da yin tsafi domin ya samu mulki. Shi ne mawak’in ke cewa in lokacinka ya k’are tsafinsa duk na banza ne bai tasiri.

Haka kuma a cikin wani d’an wak’a ya k’ara da cewa:

Jagora: An tsai da wane takarar gwamna,

Kare mai bak’in jini da yawa,

Yara:    Du inda ya bi ya hurce,

‘Yan yara na yi mai yihu

 

Jagora:  Yihu kare

 

A nan ‘Danba’u ya yi amfani da wasu abubuwa da suke faruwa ga wannan d’an takara cewa magoya bayan wannan jam’iyar sun camfa shi da cewa bak’in jini gare shi ba su son sa a canza shi. shugabansu ya nuna sai shi, shi ne ‘Danba’u ke kira kare mai bak’in jini da yawa ma’ana a jam’iyarsa ma ba a son sa balantana ‘yan adawa sai ya siffanta shi da kare kasancewar kare bai da farin jini ga yara, duk inda suka gan shi k’aryarsa ta k’are, sai jifa. A nan kai tsaye za a iya fahimtar da wanda ake yi wa zambo, wato abokin takarar wanda yake yi wa wak’a kuma ya kira shi kare domin ya k’ara wulak’anta shi da rage k’imarsa a idon jama’a.

A wani d’an wak’a cewa ya yi:

Jagora: Ina d’an buga-buga wane?

Ya lek’a Gabas ya lek’a Yamma,

Ya lek’a Gusun ya lek’a Arewa,

Kullum wurin munahucci,

Ba Sakkwato noz ba da Sakkwato Sawuz,

Yara:   Ko Isa mun hi k’arhinka,

 

Jagora: Wawa,

Yara:    Ko Isa mun hi k’arhinka.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u na yi wa jagoran jam’iyar adawar wanda yake yi wa wak’a zambo lokacin da yake shige-shige domin ya koma jam’iyar da ke mulkin k’asar don su had’e su samu nasarar lashe za’be daga k’arshe dai bai samu nasara ba. Yana sukar su cewa ba su da kowa shi adda mutane. Shi ne mawak’in ke cewa ba Sakkwato Noz ba da Sakkwato Sawuz, ko a garinsu Isa sun fi k’arfinsa.

Wad’annan bayanai da mawak’in ya kawo tare da ambata sunan garin wannan mutum ya bayyana wanda ake wa zambo kai tsaye.

A wani d’an wak’ar yake cewa:

Jagora: Kowa taso tare da manya,

Ka san yana da tarihi,

Don haka manya sun ka gaya mini,

Yara:   Danginsu Maguzawa ne.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa jagoran jam’iyyar da ke adawa da wanda yake yi wa wak’a zambo ta hanyar rad’e-rad’in da ke yawo cikin gari cewa asalinsu Maguzawa ne, wannan ya faru ne lokacin da ya fito takarar gwamna domin a sa mutane su k’yamace shi. shi ne a nan ‘Danba’u yake sukar sa da wannan kalmar ta Maguzanci. Har yake k’ara tabatar da abin, da k’ara masa gishiri cewa manya ne suka fad’a masa. A nan wannan kalmar ta Maguzanci ta bayyana wanda yake yi wa zambo.

Haka kuma a wani d’an wak’ar yake cewa:

Jagora: Ku k’ara shiri in za ku shirawa,

Ku ja d’ama in za ku shirawa,

An ce mahaukaci ya rantce,

Ya shedi ba ya kaffara,

Sai ya yi gwamna Sakkwato binni,

In kunka yarda yai gwamna,

Yara:  Irin ta dauri ta dawo,

Har yau muna cikin k’angi.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa zambo a kan d’abi’a shi ta rantsuwa musamman a wurin kamfe. Sau da yawa idan ya je kamfen yakan yi rantsuwa a cikin jawabansa, kusan kowane d’an gari ya san shi da wannan d’abi’ar. Wata rana a garin Wamakko wajen k’addamar da d’an takararsu, al’umma sun taru ga kafafen watsa labarai na jiha da na k’asa da na k’asashen waje irin su BBC da ‘BOA da makamantansu ya yi rantsuwa cewa ko kansila abokan hamayya ba za su ci ba balle gwamna. Shi ne ‘Danba’u ke yi masa zambo ta hanyar d’abi’arsa ta rantsuwa domin jama’a su fahimci da wanda yake.

Haka kuma a cikin wani d’an wak’ar ya k’ara da cewa:

Jagora: Mun san masu takarar gwamna,

‘yan takara zama mun san su,

Yan shaye-shaye mun san su,

Mun bar wane d’an wiwi ne,

Yara:    Can niga ganai cikin lungu,

Ya la’be ana yi mai moli.

 

A nan ‘Danba’u yana yi wa wasu ‘yan takara zambo ta hanyar bayyana wata d’abi’a ta shaye-shaye da wani d’an takara yake da ita. Wannan d’abi’a ce da kusan kowa ya san wannan d’an takarar. Shi kuma d’an takarar guda wanda ya kira d’an takarar zama shi kuma jam’iyarsa ba ta da k’arfi ko maza’barsa ba ya iya ci balantana ya ci za’be.

Haka kuma duk a cikin wannan wak’ar ta Gwamnanmu mun yi mun k’are yake cewa:

Jagora: Yanzu kowa ka cin amana jama’a,

A kwan a tashi ‘Danba’u,

Sai ka ganai cikin tarko,

Tarkon da ba ya hishe shi,

Ji wanda a cikin jama’a tai,

Sai ga shi yanzu ya bar su,

Wad’anga nan da ya samu,

Ya bid’o abara don ya raba musu,

Yara:   Sai ga abarba ta tsutsu.

 

Jagora: Da ya bid’o abarba don ya raba musu,

Yara:   Sai ga abarba ta tsutsa.

 

Jagora: Sakkwato mun canza musu suna,

Ba ‘yan abarba as sunansu ba,

Yara:  ‘Yan tukuwa d’iyan d’id’i.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani jagoran siyasa zambo da magoya bayansa ta hanyar sukar jagoran da ke cin amanar jama’a a cikin jagorancinsa kuma duk mai cin amanar jama’a sai ya shiga cikin tarko kuma tarkon da ba ya fita. Shi ne ‘Danba’u a cikin zambo yake nuna amanar da ya ci ta jama’arsa ma’ana yana cikin jam’iyar da aka za’be shi shekara takwas yana mulki cikinta amma yau ga shi ya fita ya d’auko wata jam’iya mai alamar abarba. A nan kai tsaye za a fahimci da wanda yake. Haka kuma ya kira ‘yan jam’iyya mai alamar abarba da suna ‘yan tukuwa d’iyan d’id’i. D’id’i sunan wata mahaukaciya ne.

A wak’ar Dr. Samaila Sambawa mai taken:

Amshi:  Yaro ya ja maka a karya,

D’an takarar gwamnan Kebi,

Dr Sama’ila Sambawa.

 

A cikin wannan wak’ar Danba’u ya yi amfani da zambo a d’iyan wak’ok’i da dama kamar haka:

Jagora: Jahar Kebbi ba wargi ce ba,

Kuna da d’inbin al’umma,

Ku za’bi mutum cincimtace,

Irin Sama’ila Sambawa,

Don kar ku yarda da jemage,

Ko yaushe kai nai soke yake,

Yara:   Ba za ya yarda da kowa ba.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d’aya. Ya yi amfani da salon jan ra’ayi ta hanyar yabon al’ummar Kebbi sannan ya tallata d’an takararsa, kuma ya soke abokin hamayyar Sambawa inda ya kira shi jemage. Jemage wani k’azamin tusntsu ne da ke kashi a baki kuma duk inda yake wurin bai shak’uwa kuma jemage bai da farin jini ga mutane. Ya kuma siffanta shi da wata mugunyar d’abi’a ta soke kai, Bahaushe na da tunanin duk mai yawan soke kai mugu ne kuma mugu bai cika yarda da mutane ba. A nan kusan kowa ya san da wanda ake wato shi ne abokin takarar Sambawa.

A wani d’an wak’ar kuma cewa ya yi:

Jagora: A Jahar Kebbi kowa ya waye,

Ba su koma za’benka ‘barawo

Ya kwashe kud’in talakawanai,

Ya je k’asar waje ya ‘boye,

Yara:    Har na ji mutane suna hwad’in

Olle raga muna nerori.

 

A nan zambon k’arara yake domin abokin takarar Sambawa an za’be shi a karo na farko a matsayin gwamna yanzu kuma a karo na biyu ne za su kara da Sambawa. Shi ne ‘Danba’u ke cewa al’ummar Kebbi sun waye, ma’ana sun gane ba su koma za’bensa. Sun fahimci ‘barawo ne ya kwashe kud’insu ya je k’asar waje ya ‘boye. Wai a kan tsananin yawan kud’in da ya sata har ya ji mutane suna fad’in olle raga muna nerori. Olle a harshen Yarbanci na nufin ‘barawo. A daidai wannan lokacin ana rad’e-rad’in cewa an kama gwamnonin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da kud’ad’e a k’asar waje. Shi ne ‘Danba’u ya yi amfani da wannan rad’e-rad’in ya gina zambo.

Haka kuma a wani d’an wak’a ‘Danba’u cewa ya yi:

Jagora: Mulkinka wane mulkin banza ne,

Mulkinka ba ya da tasiri,

Tun randa wane ya zam gwabna,

A jahar Kebbi kowa na kuka,

Talakawa sun damu da kai,

Na ji suna rok’on Allah

Yara:   Yada munka ga hwarkon mulkinka,

Ya Allah gwada muna k’arshe nai.

A wannan d’an wak’ar ba a buk’atar wani dogon bayani domin an fito da hoton wanda ake wa zambo k’arara ma’ana an ambaci muk’aminsa  wato gwamna kuma kowa ya san shi ne abokin hamayyar Sambawa.

Duk a cikin wannan wak’ar yake cewa:

Jagora: Wani ya ga alamun ya hwad’i,

Can nis same shi D’anwarai

Ya d’auko shatar babban mota,

An shak’e mai ita da albasa,

Yara:    Ya ce a kai mai a Ibadan,

Can za a kai ta a saisam mai.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya gina zambo ne ta hanyar yi wa abokin hamayya burga da kuma d’ebe tababa da nuna Sambawa zai sami nasara domin shi kansa abokin hamayya ya ga alamun fad’uwa shi ya sa ya raba hannu biyu domin ko ya fad’i zai ci gaba da sana’ar albasa tai. A nan kamar yadda k’amusun Hausa na Jam’ar Bayero (2006) ya bayyana cewa: “Zambo na nufin k’agawa mutum magana wadda za ta muzanta shi ko ‘bata masa suna.” Irin wannan ne ‘Danba’u ya yi ta hanyar k’aga wa abokin hamayyar Sambawa wanda ke rik’e da kujerar gwamna cewa an gane shi D’anwarai, D’anwarai wani gari ne kusa da Alieru wai ya d’auko shatar babbar mota an shak’e ta da albasa ya ce a kai mai Ibadan a sayar mai.

A wani d’an wak’ar kuma yake cewa:

Jagora: APP kun ‘bata shirinku,

Kun kada girman sarakuna,

Ga wanda ya gadi sarauta,

Sai d’ai ku k’wace rawaninai,

Yara:    Ku d’auka ku ba maginin laka.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani wanda ya ci za’ben gwamna a k’ark’ashin jam’iyar APP zambo ta hanyar kama sunan jam’iya k’arara da sukar su a kan sun kada girman sarakuna ta hanyar tu’be wani baban sarki a jahar Kebbi wanda ya gadi sarautar. Haka kuma ya soke sabon sarkin da aka nad’a ta hanyar kiransa ‘magini’ kuma ko maginin na laka. A nan abu ne a bayyane, inda gwamnatin jahar Kebbi ta tu’be babban sarki na jahar suka nad’a wani. Shi ne ‘Danba’u ya yi amfani da shi ya gina zambonsa.

https://www.amsoshi.com/2017/06/26/turken-yabo-cikin-wasu-wakokin-bage-dansala/

 

Wak’ar Yusuf Musa Illela Mai Taken:


Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa Ciyaman,

Kai ne suka sauna.

Wannan wak’ar ita ma ba a bar ta a baya ba domin ‘Danba’u ya yi amfani da zambo a ciki inda yake cewa:

Jagora: Koma ganin bushiya a birnin Illela,

K’ila ko ta tahiyatta,

Yara:   Tana nan Illela,

Don ko jiya mun ganat,

Ga ‘yan yara ga hannu.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa abokin takarar Yusuf Musa zambo ta hanyar fito da wata siffa ta k’irar jikinsa domin ya bayyana wanda yake yi wa zambo k’arara cewa yana da doro. Sai ya siffanta shi da bushiya domin kowa ya fahimci da wanda yake. Sannan shi kuma ya k’ara bak’anta masa rai.

 

 

Haka kuma ya k’ara de cewa:

Jagora: Duk bak’o ya shigo Illela,

Sai ka ji ya ce,

Garinga maye nika shakku,

Bak’in angulu,

Ka yi hurhura ka gama aski,

Yara:   Kai ka shafa muna lahiya,

A bar ce muna mayu.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u na yi wa wani mutum zambo a kan wani zargi da ake ma zuri’arsu da shi wato “maita”. Shi ne ‘Danba’u ya yi amfani da wannan zargin da ake yi musu ya yi masa zambo.

Haka kuma a wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Adamu Bakane,

Ka yi dangali bana ka huta,

Adamu Bakane,

Mai gida baban Shehu da Inuwa,

Yi zamannka ka huta,

K’attan banzan ga masu kuri Illela,

Yara:  K’yale su da ‘yan yara su ka ruga musu kashi.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa manya-manyan masu kud’in Illela zambo kasancewar sun taru a jam’iya d’aya shi kuma Adamu Bakane d’ai ne sai yaronsa guda kuma Allah ya ba su nasarar lashe za’be shi ne ‘Danba’u ya had’e su duk ya kira su da k’attan banza domin duk taronsu da dukiyarsu sun kasa cin za’ben k’aramar hukuma.

A wani d’an wak’ar yake cewa:

Jagora: Wanda Allah ya ba,

A bi shi shi ad daidai,

Wad’anda ba su buk’atak ka,

Ga su nan sun muzanta,

Yara:   Tun da ba su da komai

K’asa ga kuma ba su da kowa.

 

A nan ya yi wa ‘yan adawar ciyaman zambo cewa sun muzanta ba su da komai. Kuma ba su da kowa dan haka tun da Allah ya za’be shi to abi shi shi ad daidai.

A wani d’an wak’ar ya k’ara da cewa:

Jagora: Ar! Ga wani ya yi takarab bayis,

Ta ruhe da shi ya hwasa kuka,

Yanzu swata yaka nema,

Bakin dutse ka kai ka iske,

Yara:  Tun da d’an asali ba ya kasuwanci da k’azami.

A wanna d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa d’an takarar mataimakin ciyaman wanda ya fad’i za’be zambo ta hanyar muk’amin da ya nema wato bayis bai samu nasara ba. wad’annan kalmomi na takara da bayis k’arara sun bayyana wanda ake wa zambo,. Haka kuma ya k’ara sukar sa da wasu kalmomi masu zafi kamar swata da k’azami.

Haka kuma a cikin wani d’an wak’ar yake cewa:

Jagora: Buhun lalle yai kama da buhu bai yi buhu ba,

Shi buhun lalle yai kama da buhu ba yada  nauyi,

Da ina tsoron wane, yanzu na bar tsoron shi.

Yara:  Tun da bakin garkassu munka watce musu

kaya.

 

A nan ‘Danba’u ya yi wa wani babban mutum d’an siyasa na garin Illela zambo ta hanyar kiransa buhun lalle. Saboda shi buhun lalle ana kiran sa buhu matsawar dai an cika shi kamar yadda ake cika buhun hatsi ko na shinkafa. Amma ba matsayinsu d’aya ba, kuma nauyinsu da darajarsu ba d’aya ba. Haka kuma ‘Danba’u ya k’ara fito da zambo a fili cewa: “A da ina tsoron wane” ma’ana akan kud’insa da sauran abin da ya mallaka dun wanda zai yi jayayya da shi zai ji tsoro. Ya k’ara da cewa: “Yanzu na bar tsoron shi tun da bakin garkarsu munka watce musu kaya.” Ma’ana a bakin garkarsu aka kashe shi za’be. A nan a tak’aice ya yi wa wannan d’an siyasa zambo ne a kan gashi da girma da dukiya amma ba su amfane shi ba. duk zamansa babban jagora ya kasa cin rumfar gidansu.

Haka kuma a wani d’an wak’a duk a cikin wannan wak’ar yake cewa:

Jagora: Bambad’awan lokal,

Su wane sank’ira,

Ka da ka hwad’a ‘Danba’u,

Yara:   Wanga lokaci ba ka da k’arhi,

 

Jagora: Da kai nike kai wane,

Rak’umi d’an atololo bana ina za ka da kaya?

Yara:    Za ya je ‘bantala gindi,

Inda mata suke banza.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi amfani da matsayin wannan mutum ma’ana muk’aminsa na PRO ya fassara shi da bambad’awa lokal da kuma kalmar sank’ira domin ya bak’anta masa rai tare da bayyana shi ta hanyar da kowa zai fahimci da wanda ake. Haka kuma ya k’ara yi masa zambo ta hanyar siffarsa kamar tsawonsa, da idanunsa da wuyansa za a gansu kamar na rak’umi. Shi ne ya kira shi rak’umi. Haka kuma ya yi amfani da wata d’abi’arsa ta neman mata ya danganta shi da ‘bantalagindi. A yanayin tunanin Bahaushe idan ya ce ‘bantalangindi to yana nufin wurin da matan banza suka ke’banta suna holewa.

Wak’ar Sarkin Yamman Sakkwato  Mai Taken: Alhaji Aliyu Magatakardan Wamakko

K’i sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

A wannan wak’ar Alhaji Musa ‘Danba’u ya gina turken zambo a d’iyan wak’a a wurare daban-daban kamar haka:

Jagora: Aliyu kai ka gadi sarauta,

Ka yi nad’i daidai da sarauta,

Wanda duk bai gadi sarauta ba,

Yara ko ga nad’i sai mun ganai,

Yara:   Wane nad’i nai ya cika girma,

Wanga uban huni sai ‘yan dako.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani basarake abokin hamayyar sarkin Yamma a gefen siyasa wanda aka nad’a su lokaci d’aya zambo a kan gadon sarauta, kasancewar shi sarkin yamma d’an gidan sarauta ne. ya gadi sarautar kuma an nad’a shi. shi kuma wanda yake yi wa zambo ba inda ya gadi sarauta kuma sarautar da aka yi masa ba a ta’ba yin ta a Sakkwato ba shi aka fara yi wa ita. Shi ne yake yin zambo cewa wanda duk bai gadi sarauta ba yara ko ga nad’i nai za a gane bai gadi sarauta ba, saboda haka nad’insa ya cika girma kamar gammo. A nan za a fahimci wanda ake yi wa zambo kasancewar bai gadi sarauta ba kuma ba a ta’ba yin sarautar ba sai gare shi.

A wani d’an wak’ar yace:

Jagora: I tak’amarka Alu daidai kake,

Tak’ama sai dai d’an sarki,

Jan biri in dai ya yi tak’ama,

Yara:   Tabbata hwadaman nan ya gani,

Yana nuhwa ya kare geron wani.

 

A wannan d’an wak’ar ma ya yi zambo ne a kan gadon sarauta cewa Alu ya gadi sarauta shi kuma bai gada ba. kamar dai yadda aka yi bayani a d’an wak’ar da ya gabata. Sai dai a wannan d’an wak’ar ya k’ara kawo siffar wanda yake yi wa zambo ta yadda za a k’ara fahimtar sa, ta hanyar launin jikinsa tare da danganta shi da biri don k’ara bak’anta masa rai.

Haka kuma a wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Ran Juma’a na kwan mamaki,

An yi sarautu Sakkwato bunni,

Mai kurin shi ad da mutance,

An yi nad’i kowa ya watce,

Mai jama’a ya kwashi abinai,

Sai nib biya garkar wani sarki,

Ni ishe ‘yan banga sun taru,

Yara:   Da haka ‘yan sholi d’ai d’an nig gani.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani basarake da aka nad’a su tare da Alu zambo ta hanyar wani abin da ya faru a ranar da aka nad’a sarautar bayan kammala nad’i. Da ma akwai jayayyar siyasa tsakaninsu duk da kasancewarsu jam’iyarsu d’aya amma shi wanda ake wa zambo koyaushe yana bugun gaban cewa ya fi Alu mutane sannan kuma shi a tare da gwamna shi kuma Alu ya samu sa’bani da gwamna ga shi mataimakin gwamna amma komai ba a yi da shi ta hanyar gudanar da mulki. Wannan rashin kulawar da ake wa Alu shi ya ja ra’ayin al’ummar garin suke k’aunar sa saboda tausai, ranar nad’i bayan watsewa sai jama’a suka yi gidan Alu. Shi ne domin ya k’ara bayyanar da wanda yake, saboda ‘yan banga ke gadin gidansa, haka kuma a sashen gidansa akwai dabar ‘yan shaye-shaye babba kasancewar hukuma ba ta zuwa wurin kamun ‘yan shaye-shaye.

A wak’ar jam’iyar P.D.P. mai taken

Ya ‘yan Nijieriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari

Mu koma PDP

 

Ita ma wannan wak’ar ba a baro ta a baya ba wajen gina turken zambo kamar inda yake cewa:

Jagora: Babu mai cin bashi,

Cikin siyasar PDP

In kana son ka shigo

Cikin siyasar PDP,

Ka biya bashin banki,

Ka je mu je tare da kai,

Kar tafiya ta yi nisa,

Yara:   Ka je ka goga mai la’bo.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani babban jigon siyasa na fatin da ke adawa da PDP, mai kud’i ne kuma d’an kasuwa ne wanda ake rad’e-rad’i a cikin gari cewa ba kud’insa ne yake kasuwanci da su ba, banki ne ya ba shi bashi. Shi ne ‘Danba’u yake yi masa zambo da wannan kalma ta bashi domin kowa ya fahimci wanda yake wa zambo.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Ko cikin mata,

Wance ‘yar jidalin mata ce,

Kullun habshi takai,

Kamar karyar zango,

Yara:    An yi an k’are,

Ke bak’in jidali ya hwarma.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wata mata ‘yar siyasa zambo a kan halayyarta ta fad’a da mutane musamman a fagen siyasa har ma ‘yan siyasa na amfani da ita wajen cin zarafin abokan adawa.

Haka kuma a cikin wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Wanda duk ke kwakwa,

Ba mutumen kirki ne ba,

Yara:    Da d’an k’waya,

Sai d’an dara,

Sai ko d’an daga.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa ‘yan wata jam’iya mai alamar icen kwakwa zambo ta hanyar kiran su ‘yan kwakwa, tare da zagin su da rashin kirki da miyagun d’abi’u na shaye-shaye da caca.

A wani d’an wak’ar kuma yake cewa.

Jagora: Ashe wane barazanarka,

Aikin banza ce,

Ba ya da kowa,

Garinsu koran,

Shi d’ai ne,

Yara:   Mun ji labarin ko gidansu,

An ce ya sai da.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani mai goyon bayan jam’iyar da ke adawa da PDP zambo ta hanyar nuna cewa barazanar da yake yi aikin banza ce saboda bai da kowa ma’ana ba ya da mata ba ya da d’a, kuma bai da mutum d’aya da yake a k’ark’ashinsa, k’uri’arsa kad’ai ya mallaka. Sai ya k’ara bayyana shi ta hanyar da kowa zai fahimci shi da cewa har gidansu an ce ya sai da kuma gaskiya ne dai-dai lokacin ya sai da gidansu.

Haka kuma a wani d’an wak’a yana cewa:

Jagora: Ga wani d’an takara da doro,

Abu dai zuk’ui-zuk’ui,

Ke kuma bushiya ki ‘boye doronki,

Yara:    Ba ki bakin komai,

Wurin hwarauta banza ce,

 

Jagora: Na ga baki bakin komai,

Yara:    Wurin hwarauta banza ce.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an takara zambo ta hanyar wata halitta da Allah ya yi masa ta doro sai ya siffanta shi da bushiya kasancewar ta a dunk’ule da doro da cewa a wurin hwarauta banza ce don yara ka kama ta don ba ta iya gudu kamar zomo ko kurege kuma ba ta iya tashi sama kamar tsuntsaye saboda haka shi ma kayar da shi za’be ba wani abu ne mai wuya ba.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Bana duna bak’in kare,

Dubara ta k’are,

Kai kare d’auke k’afarka,

Na ga gungu ‘yan yara,

Yara: Kar su ‘bata ma tsari.

 

Jagora: In kai kare  d’auke k’afarka,

Na ga gungu ‘yan yara,

Yara:   Kar su ‘batama tsari.

 

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa zambo a kan wata halitta da Allah ya yi masa ta launin jikinsa wato bak’i ya kuma danganta shi da kare don ya wulak’anta shi. Duna na nufin mutum mai bak’i da yawa. Wannan kalma ta duna ita ta bayyana wanda yake wa zambo.

 

A wak’ar Aliyu Magatakarda Wammako mai taken:

K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya gina zambo a d’iyan wak’a da dama kamar inda yake cewa:

Jagora: Mugun madambaci kake Ali,

Baba da ka tattako, ka bugi bakin dogo,

Ya tahi ba ban kwana,

Yara:   Bar maganar guntu,

Shi hadda ciki nai ya hude.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wasu abokan hamayyar Alu da suka sha kaye a za’ben 2007 zambo ta hanyar fad’uwa za’be, tare da bayyana k’irar halittarsu ta yadda kai tsaye za a fahimci su. Inda ya kira babban jigon da dogo shi kuma wanda jigon ya tsaisuwa takara, ya kira shi guntu. Masu wad’annan siffofin a Sakkwato ba ‘bace suke ba, domin da an ce dogo kusan kowa ya san da wanda ake.

A wani d’an wak’a kuma yake cewa.

Jagora: Wad’ansu maza, sun yi rantsuwa kuma sun k’ara,

Sun ce maka d’an Barade ba ka zama gwamna,

Allah ya yarda yau Alu ka zama gwamna,

Bamaguje kai kuma ya za ka yi zancen kononka,

Yara:    Du hatcin Sakkwato kaf ba su cire mai kahwara

 

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani babban jigo na siyasa a jam’iyar da ke adawa da Alu a kan wata d’abi’arsa ta rantsuwa musamman awajen yak’in neman za’be inda yake rantsuwa cewa ba gwamna ba ko kansila jam’iyarsu Alu ba ta ci. Mai wannan d’abi’ar a Sakkwato kowa ya san shi, haka kuma ya k’ara kiran sa da kalmar Bamaguje wadda da yawan masu adawa da shi sukan jefi shi da ita. Dalilin da ya sa ake kiransa Bamaguje shi ne Bagobiri ne saboda  irin rigimar da Usmanu Bini Fodiyo ya yi da Gobirawa a kan Musulunci.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Wane Sakkwatawa sun d’aukai mutumen kirki,

Dab baya ya yi lalata,

Ya tafka abin kumya.

Yara:     Dan nan daraja tai ta hwad’i,

 

Jagora:  Mun gane shi mutumci madara ne,

Da ya zube a k’asa,

Yara:    Ban san wani mai kwasa tai ba.

 

A wannan d’an wak’ar, makad’in ya yi wa wani d’an siyasa zambo wanda Sakkwatawa suka kar’be shi hannu biyu-biyu suka goya masa baya ya ci za’be har sau biyu, daga baya sai ya juya masu baya a kan wata ‘yar matsala har dattijawan garin suka rok’e shi wata alfarma domin a samu zaman lafiya a garin ya yi amfani da k’arfin mulki ya k’i. Daga nan su kuma suka juya masa baya wannan matsala ta yi sanidiyar fad’uwa za’be daga baya ya yi bid’a shiri abin ya ci tura. Shi ne ‘Danba’u ke yi masa zambo da cewa Sakkwatawa sun d’auke shi mutumin kirki daga baya ya yi lalata, daraja tai ta fad’i don haka shi mutumci madara ne idan ya zu’be bai kwasuwa.

A wani d’an wak’a kuma yake cewa:

Jagora: Ji wane d’an hwad’in rai wai bai bid’ar sanata,

Shugaban k’asa yaka so,

Bana ya yi ‘bakan-’bakatantam,

Bai yi president ba,

Kuma nan ga jiha tai ya hwad’i,

Ba zama Sakkwato,

Yara:    Sai dai ya tsaya Kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

A wannan d’an wak’ar zambo a fili yake ba ya buk’atar dogon sharhi. Amma a tak’aice ga al’adar siyasa Nijeriya, idan gwamna ya yi mulki a zangon na biyu ya k’are, zai nemi kujerar sanata, shi wannan gwamna ya k’i neman kujerar sanata sai ya nemi kujerar shugaban k’asa bai samu nasara ba kuma d’an takararsa na gwamna bai samu nasara ba. shi ne ‘Danba’u ke yin zambo da kiran sa d’an fad’in rai wai bai bid’ar sanata shugaban k’asa yake so daga k’arshe ya k’ara bayyana wanda yake wa zambo ta hanyar ambatar sunann garinsu da cewa ba zama Sakkwato, ambatar Sakkwato. Ya bayyana kai tsaye wanda ake nufi.

Haka kuma a wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Mai jamai’as siyasa,

Bana ya hwad’i ina magana,

D’an Sakandare ya kasai,

Ya shiga sabbatu,

Yara:   Bana ko magana tai ya noce.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa zambo ta hanyar wak’ar da wani makad’i ya yi masa inda yake kiran sa mai jami’ar siyasa k’asar ga kowa iya ta sai ya ambaci sunan wannan wanda yake wa wak’a, ya ce shi ya koya masa. Wannan kalamin da makad’in ya yi na mai jama’ar siyasa sai ya zama sara a wannan lokaci. Shi ne ‘Danba’u ke mai da martani ta hanyar zambo cewa mai jama’ar siyasa ya fad’i ina magana? D’an sakandare ya kasai. Mai jama’ar siyasa a Sakkwato sananne ne.

A wak’ar Tanimu D’angaladiman K’yad’awa mai taken:

Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimu na Alhaji Yakubu.

A wannan wak’ar Alhaji Musa ‘Danba’u ya fito da zambo a cikin d’iyan wak’ar wurare da dama kamar haka:

Jagora: Ranar za’ben Gada ‘Danba’u,

Ban gani ba labari naj ji,

Wad’ansu maza sun ji azaba,

Wani ya bar hula da agogo,

Wani kau ya mance gilashi nai

Wasu kau sun d’auko k’ahwahunsu,

Yara:    Can sun ka mance kubuttansu.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi amfani da wasu abubuwan da suka faru a ranar da aka yi za’ben ciyaman a Gada. An yi gwagwarmaya sosai kuma an samu tashin hankali bayan kammala za’be. Tanimun ya samu nasara sai aka fara yi wa ‘yan adawa kuwa daga k’arshe aka biyo manyan ‘yan adawa da gudu to a nan fa wasu suka yadda hula, wasu agogo, wasu gilashi wasu a guje ba takalma. Shi ne ‘Danba’u ke yin zambo cewa ranar za’ben Gada wasu maza sun ji azaba. Wani ya bar hula da agogo wani ya mance gilashi nai wasu ko sun hawo k’afafunsu can sun ka mance kubuttansu. Kubuttai na nufin rufaffen takalmi na roba. A nan a Gada kowa ya san wad’anda wannan abin ya faru a kansu.

A wani d’an wak’a kuma yana cewa:

Jagora: K’ara hank’uri kar ka ji komai,

Hank’urinka shi nak kai ka haka,

Hak ka yi ciyaman k’asar Gada,

Kak kada biri sarkin k’walama,

Ci k’urgurguma a ci buzuzu,

Nac ce biri  a yi a hankali,

Yara:   Wata ran cikinka yana ‘baci.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa abokin takarar Tanimun zambo a kan nasarar da aka samu a kansa. Shi ne yake cewa ka kada biri sarkin kwalama. A nan ya kira shi biri ne domin a wulak’anta shi tare da muzanta shi a idon duniya. A nan kowa ya san wanda ake wa zambo wato wanda Tanimu ya kasuwa za’be.

Haka kuma a wasu d’iyan wak’a yake cewa:

Jagora: Nai rok’o ‘Danba’u wajenka Tanimun na k’ara,

Dauda k’iri nike kallo ka ba shi wuri nai ya dace,

Na so a hidda d’an gwadda mai ja,

Yara:    Mun gane bai muna alheri.

 

 

 

 

Jagora: A in kun yi mitin kuma kun k’are,

Don Allah kira Dauda K’iri,

Ka san aikin nai dattijo,

A ba shi babban aikinai,

Tunda wurinai ya saba,

A hid da wanga hwarin doki,

Yara:    Don na ga bai muna alheri.

A wad’annan d’iyan wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani mai rik’e da muk’ami lokal gwammen a Gada zambo ta hanyar siffar jikinsa mai launin ja ko fari inda ya kira shi da jar gwadda da kuma farin doki. Sannan ya bayyana halayarsa ta rowa tare da kawo wasu bayanai ta hanyar kawo sunan Dauda K’iri domin ya k’ara fito da abin fili kasancewar Dauda K’iri aka cire aka sa shi tare da yi wa Dauda K’iri rok’o cewa a maisam mai muk’aminsa a fid da wancan farin doki tun da bai masu alheri.

A wak’ar Ciyaman d’in Shagari, Alhaji Muhammadu Galadima Horo mai taken:

Dogo kana halin kyauta,

Alhaji D’an’ige d’an dattijo,

Mamman ciyaman Shagari,

A wannan wak’ar ma ‘Danba’u ya yi zambo a cikin wasu d’iyan wak’a kamar haka:

Jagora: Na san karo da kai,

Ba ya da dad’i,

Kai ji wane ya sha kaye,

Don na gane shi can malisa,

Yara:   Ya tara leda yana k’ullin magi,

 

Jagora: wawa

Yara:    Ya tara leda yana k’ullin magi,

Jagora: saga

Yara:    Ya tara leda yana k’ullin magi.

Jagora: Ka gama da tsohon kolo,

Wane ya bar gidanai,

Yara:    An ce yanzu kulun,

Yana loja kwance.

 

A wad’annan d’iyan wak’a ‘Danba’u ya yi wa abokin takarar D’an’ige zambo da cewa ya sha kaye, kuma an gama da shi ya kira shi tsohon kolo, sannan ya soke shi da wurin zamansa, wato loja sannan ya kira shi wawa da saga. A nan kalamun shan kaye da kuma zama loja sun bayyana wanda ake wa zambo. Domin an san wanda ya sha kaye kuma kowa ya san ya daina zama garinsu garin da ya koma akwai wata loja nan ne wurin zama nai kullum.

A wasu d’iyan wak’a suke cewa:

Yaro: Wani ciyaman na nan mai rowa,

Da du, ya gane ni ya sha toka,

Wani mai idanun ‘yabin,

Yara: Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.

 

Jagora: Ina mai idanun mussoshi,

Yara:    Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.

 

A wani d’a yake cewa:

 

Jagora:  Wani ciyaman ne,

Sarkin rowa,

Sai son a zo a yi mai wak’a,

To ba ni yin aikin banza,

Yara:    Na daina yin wak’a kyauta.

 

Jagora:  Wawa,

Yara:    Na daina yin wak’a kyauta.

 

Jagora: Saga!

Yara:   Na daina yin wak’a kyauta.

A wad’annan d’iyan wak’a ‘Danba’u da yaransa sun yi wa wani ciyaman zambo ta hanyar halinsa na rowa tare da bayyana siffofinsa ta yadda kowa zai iya fahimtar da wanda ake kamar inda yake cewa mai idanun ‘yabin kuma ya yi kan ‘yan jarirai. A wani layin wak’a ‘Danba’u ya bayyana ‘yabin a karin harshen Sakkwatanci da cewa mussa (ma’ana kyanwa) ke nan shi wannan yana da irin idon kyanwa, kuma yana da k’aramin kai kamar na jarirai. A nan sun yi amfani da nau’o’in zambo iri biyu na hali da kuma na halitta.

A wak’ar ciyaman d’in Gwadabawa Alhaji Musa Lumu mai taken:

Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji LumunMusa ciyaman zarumi.

Ita ma wannan wak’ar ba a bar ta a baya ba domin akwai zambo a cikinta kamar inda yake cewa:

Jagora: K’asar Gwadabawa,

Mu mun yi babban arziki,

Don mun ije kunkuru mai idanu tsatstsaye.

Yara:   Kai bari d’an tulluk’i ba a yi komai da kai.

 

A wani d’an wak’a yake cewa:

 

Jagora: Wane an kashe shi sai ya tcira man tcegumi

Mai babban gaba mi gami na ni da kai?

Yara:    Ka isko ni gida ka ce za ka tungatci da ni.

 

A wad’annan d’iyan wak’ar ‘Danba’u ya yi wa d’an takara da Musa Lumu ya kasuwa zambo ta hanyar halitta da Allah ya yi masa inda ya siffanta halittarsa da kunkuru tare da bayyana yadda idanunsa suke da kuma yanayin k’irar jikinsa wato d’an tulluk’i kuma mai babban gaba tare da ambatar an ije shi da an kashe shi, tare da bayyana wani sa’bani da ya faru tsakaninsu inda yake cewa ka isko ni gida ka ce za ka tungatsi da ni. Bayan kammala d’an wak’ar sai ‘Danba’u ya ce: “Ba ka fad’a da Musa Lumu shi da yak kashe ka sai ‘Danba’u da am macce.”

Haka kuma a wani d’an wak’a suke cewa:

Yaro: Haji ‘Danba’u akwai tambaya ta ni da kai,

Yaran Musa akwai tambayata ni da ku,

Marok’an Musa akwai tambayata ni da ku,

Shin don Allah ina mai hwad’in sai ya bugan?

Wani d’an kutu’bi bak’i mai idanun raguna,

To na zage ka,

Yara/jagora: Komai kakai man sai ka yi,

Jagora: Wane yau na zage ka,

Yara:    Komai kakai man sai ka yi.

A wannan d’an wak’ar sun yi wa wani mutum wanda sa’banin siyasa ya had’a su zambo ta hanyar bayyana abin da ya faru tsakaninsu tare da kawo hoton sifarsa wato kutu’bi bak’i mai idanun raguna ta yadda kowa zai fahimce shi, sannan daga k’arshe kai tsaye suka ce sun zage shi komai zai yi ya yi.

A wak’ar Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi mai taken:

Sardaunan Hamma’ali zaki

Malami Maigandi bi da arna,

A wannan wak’ar ita ma ‘Danba’u ya yi zambo a cikinta kamar inda yake cewa:

Jagora: Hamma’ali na tafi yawo,

Ga wani nai muna kurin banza,

Ya ce shi aka wa Sardauna,

Sai nac ce kauce da nesa,

Yara:   Kusun kusumi ba ya kyau da sarki.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani mutum wanda ya yi neman sarautar Sardaunan Hamma’ali bai samu ba. zambo ta hanyar halittarsa wato siffar jikinsa inda ya kira shi da kusun kusumi ba ya kyau da sarki. Da ya kai k’arshen d’an wak’ar sai ya ce ana sarki babu kyau babu kyawun kama?

A wani d’an wak’ar yana cewa:

Jagora: Cikin ‘yan sarki na Hamma’ali,

Akwai wani sata yakai da rana

Shi wannan ya zame muzuru,

Yara:   ‘Yan kaji bai bari su girma.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an sarkin Hamma’ali wanda a masarautar shi ne kawai bai goyon bayan Sardauna. Shi ne ‘Danba’u ke yi masa zambo ta hanyar k’irk’iro sata ya lak’a masa domin a wulak’anta shi a ci zarafinsa tare da bak’anta masa rai da siffanta shi da muzuru. Duk d’an sarkin da ke jiran sarauta aka kira shi ‘barawo ai an nakasa shi. A nan kusan ‘yan Hamma’ali duk sun san d’an sarkin da ake nufi.

A wak’ar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko mai taken:

Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu Sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

Wannan wak’ar ita ma akwai zambo a cikinta. A cikin wasu d’iyan wak’a kamar haka:

Jagora: Su wane sun ci amana Allah,

Yanzu amana ta kama su,

Sun yi gidaje gadan-gadan,

Gahwa gidaje daidai jin dad’i,

Yara:    Ba a da dama zaunawa ciki.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wasu manyan ‘yan siyasa da suka fad’i za’be a jahar Sakkwato, suka kasa zama garin zambo ta hanyar bayyana manya-manyan gidaje da suka yi amma ba su iya zama garin saboda bak’in ciki da kuma tsoron kada a yi musu wani abu. Wad’annan ‘yan siyasa a jahar Sakkwato sanannu ne.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Wane giyam mulki ta d’ibai,

Hay ya je Gada ya sha wallah,

Ya ce ko hullatai ya aje k’asag ga,

Sai tai gwamna Sakkwato.

Yara:    Mai bundigar iskan ga talo-talo,

Bana ya hau dokin rantsuwa.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani mai mulki zambo ta hanyar wata halayyarsa, ta rantsuwa da kuma wani jawabi da ya yi a garin Gada wurin kamfe inda yake cewa duk wanda ya tsaisuwa takara gwamna sai ya ci za’be. Shi ne yake danganta maganarsa da bindigar iska wato maganar banza kuma ya kira shi talo-talo kuma ya hau dokin rantsuwa.

3.7 Nad’ewa


A wannan babi an yi bayani a kan zambo tun daga asalin kalmar da ma’anarta da ire-iren zambo daga ra’ayoyin masana da manazarta daban-daban, tare da kawo dalilan da ke sa a yi shi. haka kuma an bayyana muhimmancin ko amfanin da ake samu ta hanyarsa. Daga k’arshe an kawo sharhin zambo a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai ta hanyar fitowa da abubuwan da masana da manazarta suka bayyana a matsayin zambo. Haka kuma an nazarci wasu wak’ok’insa da ke d’auke da zambo aka kawo misalai a wurare daban-daban.