Kundin Binciken Kammala Karatun Digiri Na Farko (B.A. Hausa) A Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Na
SHEHU HIRABRI
08143533314
BABI
NA ƊAYA
GABATARWA
Shimfiɗa
Nazarin adabin Hausa wani teku ne mai matuƙar girma wanda masana suka kasa gida
biyu, wato na baka da rubutacce; ko na gargajiya da na zamani. Masana da
manazarta da ɗaliban ilimi da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da
kowane fage. Ba fannin adabi kaɗai ba, har ma da sauran takwarorinsa wato ɓangaren
harshe da al’ada. Da yake hikima tana da faɗi, sai wannan bincike ya ga akwai
buƙatar ƙara fitowa da wani abu na adabi wanda ya danganci wata hikima da mawaƙa
ke amfani da ita, amma wannan aiki zai keɓanta ne ga wasu waƙoƙin Alhaji Musa
‘Danba’u Gidan Buwai.
Da yake binciken ya shafi waƙar baka ne, sai wannan aiki ya ga ya dace a yi
shimfiɗa kan ma’anar adabin Hausa wanda yake waƙa tana cikinsa ne tsundum.
Saboda binciken ya samu wurin zama ma’ana abubuwan da za a tattauna su fito
fili ga mai karatu.
Masana sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar kalmar adabi. Sai dai wani
abin gwanin ban sha’awa a nan shi ne, duka ra’ayoyin suna da makusanciyar
manufa da alaƙa ta ƙud-da-ƙud da junansu dangane da ma’anar.
Gusau, (2011:3) cewa ya yi: “Adabin Hausa, adabi ne wanda ya shafi hikimomi da
sarrafa harshe da kuma hanyoyi waɗanda suka shafi tafiyar da rayuwa ta yau da
akullum, kuma yakan zama mai yin darasi da hannunka-mai-sanda ko mai barbaɗa
gishiri a rayuwa.”
Galadanci da wasu (2011: 27) cewa suka yi: “A Hausa ma’anar ‘adabi ta yaɗu i
zuwa bayyana rayuwar al’umma ta fuskar al’adunsu, dabarunsu, harshensu,
abincinsu, makwancinsu da dai duk sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsu.
Saboda haka muna iya cewa, ‘adabi’ shi ne nazarin rayuwar al’umma. Ta nazarin
adabi za a iya sanin dabarun zaman duniya iri daban-daban.” A dunƙule dai adabi
ya ƙunshi halayen rayuwar al’umma da ayyukan fasaha da al’adu da ɗabi’u da
abinci da muhalli da waƙoƙi da wasanni da tarihi da makamantansu.
A taƙaice dai an yi wa wannan aiki tsarin gudanarwa na babi-babi domin sauƙaƙawa
wajen fito da abubuwan buƙata bisa ga tafarki daidaitacce. Babi na ɗaya ya ƙunshi
gabatarwa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar cigaba da bincike da
hanyoyi da muhali da muhimmancin da matsalolin bincike. A babi na biyu za a
kawo tarihin rayuwar Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai tun daga haihuwarsa har
zuwa rasuwarsa. A babi na uku za a kawo bayanai a kan zambo da rassansa tare da
sharhin zambo a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u. A babi na huɗu za a
kawo bayanai a kan habaici tun daga asalin kalmar har bayyana amfaninta tare da
yin sharhi a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u. A babi na biyar za a kawo
bayanin kammalawa tare da sakamakon bincike, sai manazarta da ratayen waƙoƙi su
biyo baya.
1.1 Bitar Ayyukan Da
Suka Gabata
A nazari da bincike irin wannan ya zama dole a yi waiwaye wanda Hausawa ke yi
wa kirari da ‘adon tafiya’ na wasu ayyukan da suka gabata. Bincike ya nuna
akwai aikace-aikace masu ɗimbin yawa da aka gudanar kan adabi a cikin kowane
reshe na adabin Hausa, musamman waƙa. Amma ba a sami wani aiki da ya yi daidai
da irin wannan aikin da aka sanya gaba ba, wato kan Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan
Buwai. Ayyukan da wannan bincike ya nazarta sun haɗa da:
Bello, (1976) a muƙalarsa mai taken: “Yabo da zuga da zambo a waƙoƙin sarauta.”
Marubucin ya yi bayanin matsayin kiɗa da waƙa da yadda waƙa ke shiga cikin
jinin ɗan Adam. Haka kuma ya kawo dangantakar makaɗan sarauta kuma, maƙalar ta
bayyana abubuwa uku waɗanda suka haɗa da yabo da zuga da zambo, ya kawo
ma’anoninsu da misalansu daga waƙoƙin da aka yi wa sarakuna. Daga nan sai ya naɗe
aikinsa.
Wannan aiki yana da nasaba da wannan bincike ta fuskar zambo. Sai dai maƙalar
ta keɓanga ne kawai a waƙoƙin faɗa. Shi kuma wannan aikin bincike bai keɓance
kowane ɓangare ba, yana magana ne a kan kowace irin waƙa amma ta Alhaji Musa
‘Danba’u.
Safiya, (1984) ta rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello
mai taken: “Habaici.” A cikin wannan aiki ta yi bayanin habaici da nau’o’insa
da yadda ake amfani da shi. Wannan aiki ba ɗaya ne da nawa ba, sai dai habaici
wani yanki ne a cikin nawa bincike domin za a fito da habaici a cikin waƙoƙin
Alhaji Musa ‘Danba’u. Amma duk da haka aikin zai ba da gudummuwa ta hanyar
samun nasarar wannan binciken.
Yahya, (1985) ya rubuta takarda mai taken “Hikimar mawaƙa.” Wannan maƙalar ta
haska min hanya da zan bi cikin hikima wajen nazarin gano hikimar da ‘Danba’u
ke bi wajen gina zambo da habaici acikin waƙoƙinsa, amma ba ɗaya ce da nawa
aikin bin cike ba.
Mazawaje, (1985) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya
mai taken: “Zambo da Habaici a Waƙar Fada.” Ya kasa aikinsa zuwa babi biyar. A
babi na biyar ya tsunduma a cikin aikinsa inda ya kawo bambanci tsakanin zambo
da habaici, sannan ya kawo zambo da habaici a tsakanin mawaƙan fada.
Idan aka yi la’akari da wannan bincike za a ga yana da alaƙa da wannan aiki.
Sai dai, shi yana magana ne a kan zambo da habaici a cikin waƙoƙin fada inda wannan
bincike ya keɓanta ga makaɗi ɗaya kuma aka faɗaɗa aikin a kan kowace irin waƙa.
Sai dai duk da haka ya ƙara share wa wannan aiki hanya domin samun nasarar
wannan aikin bincike.
Alkali, (1989) ya rubuta kundin neman digiri na biyu a Jami’ar Bayero, Kano mai
taken: “Cuɗeɗeniyar Adabi: Tasirin Adabin Baka a Kan Rubutattun Waƙoƙin Hausawa
Dangane da Habaici da Zambo Da Karin Magana.” Wannan aikin ya bambanta da nawa
aikin bincike domin aikin ya duba cuɗeɗeniyar da ake samu tsakanin zambo da
habaici a ƙarƙashin adabin baka da rubutacce. Shi kuwa wannan bincike zai yi
nazari ne a kan zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u.
Modibbo, (1989) ya rubuta kundin neman digiri na farko a jami’ar Usmanu
‘Danfodiyo mai taken: “Nazari da Sharhi Kan Yabo da Zambo na Waƙoƙin Musa Ɗankwairo
na Fada.” Wannan aikin ya yi nazari da sharhin yabo da zambo a cikin wasu waƙoƙin
Ɗanƙwairo na fada tare da kawo misalai a cikin wasu ɗiyan waƙa. Wannan aiki ba ɗaya
ne da nawa ba, domin ya yi nazari ne a kan yabo da zambo a cikin waƙoƙin fada
na Musa Ɗanƙwairo. Inda nawa aikin zai yi nazarin ne a kan zambo da habaici a
cikin kowace irin waƙa ta Musa ‘Danba’u. sai dai zai ƙara min haske wajen samun
nasaran nawa aikin bincike.
Waya, (1990) ya rubuta kundin neman digiri na farko a jami’ar Bayero, Kano mai
taken: “Habaici, Zambo da Karin Magana: Matsayinsu da Tasirinsu.” Wannan aiki
ba daidai yake da nawa bincike ba, domin ya yi nazari ne a kan matsayinsu da
tsasirinsu, inda nawa bincike zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa ‘Danba’u.
Bala da wasu (1993) sun rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu
‘Danfodiyo mai taken: “Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai Da Waƙoƙinsa.” Sun kasa
aikinsu gida biyar. A babi na biyu sun kawo tarihin mawaƙi, a babi na uku sun
tattauna a kan ma’anar waƙa da nau’o’inta. A babi na huɗu sun yi sharhin waƙoƙi
biyu, ta Magajin Rafin Sakkwato da waƙar Sarkin Daura Muhammadu Bashar ta
fuskar jigo da salo. Wannan aiki bai da alaƙa da nawa bincike sai dai binciken
namu ya keɓanta ne a kan Alhaji Musa ‘Danba’u. ma’ana mun yi tarayya wurin
nazarin waƙoƙinsa kawai. Sai dai kowannenmu abin da yake nazari daban. Su sun
yi sharhin wasu waƙoƙi kan jigo da salo. Ni kuma nawa aikin ya keɓanta ne kawai
a kan zambo da habaici.
Safara’u, (1994) ta rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello
Zariya mai taken: “Habaici da Matsayinsa ga Al’ummar Hausawa.” Wannan aiki ya
kawo ma’anar habaici da matsayinsa ga al’ummar Hasuawa. Shi kuma nawa aikin
bincike zai fito ne da zambo da habaici a cikin waƙoƙin ‘Danba’u Gidan Buwai.
Wannan aikin ba ɗaya ne da nawa ba.
Abdullahi, (1995) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo,
Sakkwato mai taken: “Dangantakar Waƙar Baka da Rubutatta ta Fuskar Zambo da
Habaici.” Ya kasa aikinsa zuwa gida huɗu. A babinsa na uku ne ya zube zuciyar
aikinsa, ma’ana dangantakar waƙar baka da rubutacciyar waƙa. Ni kuma nawa aikin
zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin ‘Danba’u. wannan aikin ba ɗaya
ne da nawa ba, amma zai ƙara mini haske sosai wajen samun nasarar nawa aikin.
Yahya, (1997) ya rubuta wani littafi mai suna: “Jigon Nazarin Waƙa.” Wannan
littafi ya taimaka min wajen sanin yadda ake nazarin waƙa kuma ya ba ni haske
sosai ta yadda zan gudanar da wannan aiki.
Zaruk da wasu (1997) sun rubuta wani littafi mai taken: “Hanyar Nazarin Hausa
Don Ƙananan Makarantun Sakandare.” A cikin wannan littafi sun yi bayani a kan
abubuwa da dama cikinsu har da adabi. Daga cikin adabi sun yi tsokaci a kan waƙa
kuma sun yi bayanin zambo da habaici ta fuskar ma’ana. Wannan littafi bai
tunkari irin matsalar da wannan aikin bincike ya tunkara ba amma zai ba da
haske ta yadda za a iya samun nasarar gudanar da wannan aikin bincike.
Garba, (1998) ya rubuta kundin digiri na biyu a Jami’ar Bayero, Kano mai taken:
“Azancin Magana A Waƙoƙin Makaɗan Baka.” Wannan aiki ba guda ne da nawa aikin
bincike ba sai dai zan samu haske na cigaba da nawa bincike.
Shinkafi, (1998) ya rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu
‘Danfodiyo mai taken: “Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali
(1975-1960).” Wannan aiki ya yi bayani a kan waƙoƙin Narambaɗa musamman waƙoƙin
sarauta inda ya yi bayanin abubuwa da dama har da zambo da habaici. Wannan
aikin ba ɗaya ne da nawa aikin ba. Sai dai zai ƙara min haske wajen samun
nasaran nawa bincike.
Maidubu, (1999) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Bayero, Kano mai
taken: “Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai Rayuwarsa da Ayyukansa.” Wannan aiki
ba ɗaya ne da wannan aikin bincike ba domin wannan aikin ya kawo tarihin
rayuwarsa da ayyukansa da kuma bayanin wasu waƙoƙi. Ni kuma nawa aikin zai keɓanta
ne a kan zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin ‘Danba’u, duk da haka za a sami
hasken da zai haska ga wannan aikin bincike.
Halima, (2000) ta rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu
‘Danfodiyo mai taken: “Dabarun Zambo A Cikin Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo.”
Wannan aiki ya bayyana dabarun da makaɗin ke amfani da su wajen yin zambo a
cikin waƙoƙinsa. wannan aikin ba iri ɗaya ne da nawa bincike ba domin nawa
bincike zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa
‘Danba’u Gidan Buwai.
Yahya, (2002) ya rubuta maƙala mai taken: “Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo
Cikin Nazarin Waƙa.” Wannan maƙala za ta taimaka min ƙwarai ta hanyar fito da
siffar zambo da habaici a sauƙaƙe a cikin waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan
Buwai.
Ɗalhat, (2002) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo mai
taken: “Habaici Da Dangantakarsa Ga Al’ummar Hausawa.” Wannan aiki, ba fuska ɗaya
suka duba da wannan bincike ba. Sai dai ya yi maganar habaici kuma habaici wani
yanki ne a cikin wannan aikin bincike. Sai dai shi ya yi nazarin habaici da
dangantakarsa da Hausawa, shi kuwa wannan aikin bincike zai yi nazarin zambo da
habaici ne a cikin wasu waƙoƙin ‘Danba’u.
Dunfawa, (2005) ya rubuta maƙala mai taken: “Zambo da Habaici A Cikin
Rubutattun Waƙoƙin Addini.” Duk da yake wannan maƙala ta yi nazari ne a kan
rubutattun waƙoƙin addini, shi kuma wannan aikin bincike zai yi nazari ne a kan
waƙoƙin baka na Alhaji Musa ‘Danba’u za a ga hanyar jirgi daban da ta mota sai
dai dukansu sun yi tarayya ne a wajen nazarin zambo da habaici, amma za ta
haskaka min ƙwarai da gaske wajen samun nasarar gudanar da wannan aikin
bincike.
Yahaya da wasu (2006) sun rubuta wani littafi mai suna: “Darussan Hausa Don
Manyan Makarantun Sakandare.” Wannan littafi ya yi bayanai a kan abubuwa da
dama. Daga cikin abubuwan da suka tattauna har da ɓangaren adabi. A ɓangaren
adabi kuma sun tattauna a kan zambo da habaici. Wannan littafin zai taimaka
wajen samun nasarar wannan aiki, amma ba su da wata doguwar alaƙa, kowane cin
gashin kansa yake.
Mujallar Makrantar Hausa, (2007) ta yi rubutu a kan wasu waƙoƙin Ɗandago tun
daga tarihin rayuwarsa da yadda yake tsara waƙa har zuwa kan yadda yake
yabo da zambo da habaici. Mujallar da wannan bincike kowane zaman kansa yake,
amma duk da haka, za ta ƙara ba da haske wajen samun nasarar binciken.
Dangambo, (2007) ya rubuta littafinsa mai suna: “Gadon Feɗe Waƙa.” Wannan
littafi ya yi bayanin waƙa ciki da wajenta tun daga jigo, salo da zubi da
tsari. Wannan littafi ba ɗaya ne da nawa aiki ba sai dai yana da amfani ƙwarai
ga wannan aikin bincike.
Bunza, (2009) ya rubuta littafi wanda ya raɗa wa suna: “Narambaɗa.” A cikin
wannan littafi a babi na shida da ya kira ‘keɓaɓɓo Kananan Jigogin Sarauta’
inda a ciki ya kawo zambo da habaici ya yi bayaninsu a dunƙule. Kuma ya kawo
misali a cikin wasu ɗiyan waƙoƙin sarauta. Littafin ba ɗaya ne da wannan aikin
bincike ba domin ya yi magana ne a kan waƙoƙin Narambaɗa kawai. Inda wannan
aikin bincike zai yi magana a kan zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin
‘Danba’u. Sai dai ya zama min hanya ta sanin yadda ake gane zambo da habaici a
cikin waƙoƙi da yadda ake sharhin zambo da habaici a cikin ɗiyan waƙa.
Usman, (2009) ya rubuta maƙalarsa mai taken: “Zari: Kiɗa Sana’ar Ƙira Don Zuga
Maƙera.” Cikin wannan maƙalar ya fito da zambo da habaici a cikin wasu ɗiyan waƙa.
Wannan aikin ba ɗaya ne da wannan aikin bincike ba, sai dai zai yi ƙarin haske
dangane da wannan bincike.
Shagari, (2011) ya rubuta kundin digirinsa na farko a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo,
Sakkwato mai taken: “Waƙoƙin Jam’iyyar P.D.P Na Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan
Buwai.” Wannan aikin ya keɓanta ne a cikin wasu waƙoƙi biyu kacal na siyasa
kuma na jami’iyyar P.D.P. don haka aikin ya bambanta da nawa. Alaƙarsu kawai
ita ce an yi su a kan makaɗi ɗaya.
Muhammad, (2013) ya rubuta maƙalarsa mai taken: “Habaici A Adabin Al’ummar
Hausawa.” Wannan aikin ya yi nazarin habaici tare da bayyana hikimarsa ga
al’ummar Hausawa. Wannan aiki ya bambanta da nawa domin nawa aikin zai fito ne
da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u.
Atuwo da Bunza, (2014) sun rubuta maƙalarsu mai taken: “Sulhun Tankiya a Cikin
Waƙoƙin Baka da Rubutattu na Hausa.” Inda suka yi amfani da waƙoƙin baka da
rubutattu daga cikinsu har da waƙar ‘Danba’u ta haɗin kan Nijeriya, inda suka
yi amfani da waƙar suka yi sulhun tankiyar a cikin hikima. Wannan maƙalar da
nawa bincike kowane zaman kansa yake. Alaƙarsu kawai ita ce sun yi tarayya a
wurin nazarin waƙoƙin mutum ɗaya.
Gusau, (2014) ya rubuta littafi mai suna: “Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na
Biyu.” Wannan littafi ya kawo zubin waƙoƙin makaɗan baka cikinsu har da waƙoƙin
‘Danba’u waɗanda suka haɗa da waƙar Magajin Rafin Sakkwato Alhaji Shehu da ta
Isa Ɗunɗaye da ta Isiyan ‘Danba’u da ta Janjunan Gidan Buwai da ta Sarkin
Arewan Sakwkato da waƙar haɗin kan ‘yan Nijeriya. Aikin ya bambanta da wannan
bincike sai dai kawai dukkansu sun yi tarayya a cikin waƙoƙin mutum ɗaya.
Yahya, da wasu (2015) sun rubuta littafi wanda suka raɗa wa suna: “Sai Alu:
Sharhi Kan Waƙoƙin Da Aka Yi Wa Dr Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman
Sakkwato.” Wannan littafi ya kawo zubin waƙoƙin na mawaƙa daban-daban kuma an
yi sharhinsu sannan an yi bayani kan jigo/turken zambo da habaici a ciki amma
duk da haka ya bambanta da aikina domin an yi amfani da waƙoƙin baka da
rubutattu da ba za a rasa waƙar Musa a ciki ba.
Bagudu, (2015) ta rubuta maƙalarta mai taken: “Gyara Hali da Tarbiya: Nazarin
Waƙoƙin Daka Na Mata A Garin Sakkwato.” Wannan maƙala ta fito da hanyoyin gyara
halaye da tarbiya a cikin waƙoƙin daka na mata, haka kuma ta fito da turken
(jigo) habaici a cikin ɗiyan waƙoƙi da dama. Wannan aiki ba fuska ɗaya suka
duba da nawa aikin bincike ba, sai dai ta fito da habaici a cikin waƙoƙin daka
na mata, habaici wani yanki ne a cikin nawa aikin bincike sai dai za a fito da
shi ne a cikin wasu waƙoƙin Musa ‘Danba’u.
Junaidu da ‘Yar’aduwa, (2015) sun rubuta littafinsu mai suna: “Harshe da Adabin
Hausa a Kammale.” Wannan littafi ya yi bayanin abubuwa da dama da suka shafi
harshe da adabi a cikin adabi ya kawo habaici. Wannan littafi ba ɗaya ne da
nawa aikin ba, domin nawa aikin zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin
‘Danba’u.
Yahya, (2016) ya rubuta wani littafi mai taken: “Salo Asirin Waƙa.” Wannan
littafi ya yi bayanin salo tun daga ma’anarsa da nau’o’insa da yadda yake zuwa
a cikin waƙa. Wannan littafi yana da bambanci da wannan aikin bincike sai dai
zai taimaka min ta hanyar sanin yadda ‘Danba’u ke amfani da salo wajen yin
zambo da habaici a cikin waƙoƙinsa.
Yahya, da wasu (2016) sun rubuta wani littafi wanda suka kira: “Alun Nan Dai:
Sharhi Kan Waƙoƙin Da Aka Yi Wa Alhaji (Dr) Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin
Yamman Sakkwato).” Wannan littafi ya kawo waƙoƙi masu yawan gaske kuma sun ɗauke
su ɗaya bayan ɗaya sun yi sharhin kowace daga cikinsu ta hanyar fito da
jigogi/turaku manya da ƙanana tare da bayyana salailan da ke cikin waƙoƙin. A
gaskiya wannan aikin ya ba ni haske sosai ta hanyar da zan gudanar da nawa
bincike cikin sauƙi.
Gusau, (2016) ya rubuta wani littafi mai suna: “Makaɗa da Mawaƙan Hausa.”
Wannan littafi ya ba da tarihin mawaƙa ne, da makaɗan baka a taƙaice cikin mawaƙan
da ya kawo har da Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai. Wannan littafi ya fitar da
ni wani ruɗu da manazarta suka sa min na rashin samun daidaituwa a kan
tsayayyar shekarar da aka haifi Alhaji Musa ‘Danba’u. bayan hira da na yi da
wazirinsa Alhaji Shehu waziri ya sheda min shekara da aka haife shi wadda kuma
ta bambanta da sauran shekarun da manazarta suka bayyana a cikin ayyukansu. Sai
na sami wannan littafi wanda ya ƙara tabbatar min da abin da wazirin Alhaji
Musa ‘Danba’u ya sheda min. Na ji daɗi ƙwarai da gaske da ya walwale mini
wannan ruɗu da nike fama da shi. Amma duk da irin namijin ƙoƙarin da wannan
littafi ya yi min wajen walwale sarƙaƙiyar da ni shiga sun bambanta domin Gusau
ya yi aikinsa na littafi kan makaɗa da mawaƙa da yawa. Aikina kuwa
‘Danba’u kaɗai zai taɓo da waƙoƙinsa da ke ɗauke da zambo da habaici.
1.2 Hujjar Ci Gaba Da
Bincike
Hujjar
ci gaba da wannan bincike ita ce a iya inda Allah ya kai ganina, kuma ya ba
hannu damar taɓawa domin yin bitar ayyukan da suka gabata wajen nemo wani
bincike wanda ya yi canjaras, ma’ana ya yi daidai da irin wannan aiki a
matsayin wani littafi ko kundi ko maƙala ko mujalla da za a iya nazari a
ilmance ta wannan ɓangaren ba a samu ba. Wannan dalilin shi ya tilasta ni
cike wannan giɓin da aka bari.
Kasancewar irin shaharar da Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai ya yi a fagen gina
zambo da habaici a cikin waƙoƙinsa, wanda ake hasashen kafin rasuwarsa babu
wani mawaƙin baka da ya yi fice a ƙasar Sakkwato da ya kai shi a wannan ɓangare
ma’ana mai yawan amfani da zambo da habaici a acikin waƙoƙinsa, wasu waƙoƙinsa
kusan kashi saba’in cikin ɗari (70%) duk zambo ne da habaici musamman waƙoƙin
siyasa da na sarauta, amma kuma babu wani bincike da aka gudanar a kansa.
Wannan ya ƙara min ƙwarin guiwar fitowa da wannan a matsayin nazari a cikin
adabin Hausa ta ɓangaren waƙar baka domin muhimmancinsa.
1.3 Hanyoyin Gudanar Da
Bincike
A duk lokacin da za a gudanar da bincike dole ne a samu hanyoyi na ilimi da za
a bi domin gudanar da shi. Saboda haka, a ƙoƙarin gudanar da wannan aikin
bincike za a bi duk hanyar ilimi da ta dace domin gudanar da binciken kamar ɗakunan
karatu manya da ƙanana domin samun littattafai da muƙalu da kundayen da za su
ba da haske wurin gudanar da binciken. Haka kuma za a kusanci manyan masana da
malamai musamman na wannan fanni domin samun ƙarin haske da shawarwari domin a
samu nasarar gudanar da binciken.
A ɓangaren waƙa ita ma za a sanya waƙoƙi waɗanda za a sami zambo da habaici ƙarara
ta hanyar kawo hoton yadda mai nazari zai fahimci abin cikin sauƙi. Haka kuma
hira da yaran Musa da waɗanda suka san shi da kuma sauran na kusa da shi da
kuma sauran abokan hulɗa saboda samun bayanai a kansa da kuma walwale zare da
abawar wasu dunƙulallun maganganu da ke cikin waƙoƙinsa. idan an bi waɗannan
hanyoyi babu shakka za a samu nasarar gudanar da wannan aikin bincike.
1.4 Muhallin Bincike
Muhallin wannan bincike shi ne waƙoƙin Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai da
adabin baka. Harshen Hausa na da rassa guda uku da suka haɗa da Adabi da Harshe
da Al’ada. Wannan aikin bincike zai keɓanta ne a fagen adabi. Shi ma adabi an
kasa shi gida biyu, wato:
1.
Adabin baka/gargajiya
2.
Rubutaccen adabi/na zamani
Wannan aikin zai keɓanta ne a kan adabin baka. Adabin baka yana da rassa guda
uku kamar haka:
1.
Zube
2.
Waƙa
3.
Wasan kwaikwayo
Wannan bincike zai keɓanta ne a akan waƙar
Waƙa ta kasu gida biyu:
1.
Waƙar baka
2.
Rubutacciyar waƙa
Wannan bincike zai keɓanta ne a kan waƙar baka ta Alhaji Musa ‘Danba’u, haka
kuma ko a cikin waƙoƙinsa, za a yi nazarin waɗanda ke ɗauke da zambo da habaici
kawai.
1.5 Muhimmancin Bincike
Muhimmancin wannan aikin bincike shi ne domin samun takardar shedar kammala
digirin farko a Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato. Ba tare da rubuta aikin
ba, wanda yake yana daga cikin sharuɗɗan da ba a kammala digiri sai da shi, ya
zan dole a yi shi. Yin sa ke sanya a karɓi digirin, rashin yin sa kuma, kan
sanya a rasa digiri. Ƙaruwar ilimi ga mai gudanar da aikin bincike. Fitowa da
basirar da Allah ya yi wa Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.
1.6 Matsalolin Bincike
Babu
shakka manazarta masu bincike sukan haɗu da matsaloli daban-daban idan ba a sa
haƙuri ba, sai a kasa kai ga nasara, ko kuma ana iya kammala binciken amma babu
ƙaruwa da aka samu. Daga cikin matsalolin bincike akwai:
1.
Rashin kuɗi: Da yawa mai bincike zai samu littafi da zai taimaka masa
wajen gudanar da bincike, amma ba ya da zarafin sayen shi. Kuma babu shi a ɗakunan
karatu, kuma mai shi ba zai ba da aro na tsawon lokaci ba. Wani lokaci duk da
kuɗin da za a gurza maka ba ka da. Wani lokaci kuma ko aron ba za a ba ka ba.
Haka kuma masu irin wannan bincike, sau da yawa sukan haɗu da matsalolin
yankewar guzuri a lokacin da suke bincike ta hanyar zuwa wajen ganawa da waɗanda
binciken ya shafa, ko ake bincike a kansu, da su kansu kuɗin da ake buga aikin
da su, wani lokaci a neme su ruwa a jallo a rasa.
2.
Mai bincike yakan ci karo da matsaloli ta hanyar dokokin da ake aza
masa a ɗakunan karatu manya da ƙanana, wani lokaci za ka tashi daga Sakkwato
har Zariya ko Kano tare da takardar neman ba ka dama ka yi bincike amma a
gindaya ma wasu sharuɗɗa waɗanda matsawar ba ka yi haƙuri ba sai ka kasa samun
abin da kake nema. A ɗakunan karatu na makarantar da kake karatu kakan nemi
wata alfarma a hana ka.
3.
Wata matsala da mai bincike ke haɗuwa da ita, ita ce zai ci karo da
ayyuka masu magana a kan mutum ko abu ɗaya amma bayanin kowane ya bambanta da
na wani kuma kowane ya ce ya samo shi ne daga tushe.
4.
Haka kuma masu riin wannan bincike na waƙa sukan ci karo da matsaloli
wurin ganawa da mawaƙa ko kuma yaransu da suka gaje su. Kasancewar ba su zama
wuri ɗaya, a yi ta nemansu abin ya ci tura wani lokaci har mai bincike ya ji
kamar a canza mai wani taken bincike.
5.
Wata matsalar bincike ga masu nazarin waƙa ita ce, ta hanyar neman waƙoƙin
da tattara su da rubuta su musamman waƙar baka. Yana da matuƙar wahala hasali
ma wata waƙa za ta ƙawata ma aikinka ka tashi gari da gari ka je inda wanda
anka yi wa waƙar bai da ita. Haka kuma ka je wajen mawaƙin shi ma bai da ita.
Haka za ka yi ta yin wahala wani lokaci ka samo wani lokaci kuma ka rasa.
1.7 Naɗewa
A wannan babi an
tattauna manya-manyan muhimman tubalai na gina kowane bincike da manazarci zai
gudanar a kowane ɓangare na ilimi a ciki ne zai kawo hoton yadda binciken zai
gudana daga farkon babi na ɗaya har zuwa ƙarshe a matsayin gabatarwa da bitar
ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike tare da kawo hanyoyin da
ake bi wajen gudanar da bincike da kuma bayyana inda muhallin bincike zai keɓanta.
Haka kuma an bayyana muhimmancin bincike da irin taimakawa da yake yi wurin
cigaban ilimi. Haka kuma an kawo matsalolin da aka haɗu da su wurin gudanar da
bincike.
[…] Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai […]
ReplyDelete