Duk wanda ya san Alƙur'ani ya san cewa; Tauhidin da Alƙur'ani ya yi umurni da shi, kuma Manzanni suka zo da shi, suka kira mutane zuwa gare shi, shi ne kaɗaita Allah da bauta, a magana da aiki, a bayyane da ɓoye.
Allah ya ce:
﴿۞
وَٱعۡبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُوا۟ بِهِۦ شَیۡـࣰٔاۖ ﴾ [النساء ٣٦]
Kuma ya ce:
﴿وَمَاۤ
أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِیۤ إِلَیۡهِ أَنَّهُۥ لَاۤ
إِلَـٰهَ إِلَّاۤ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ ٢٥﴾ [الأنبياء ٢٥]
Ya ce:
﴿وَلَقَدۡ
بَعَثۡنَا فِی كُلِّ أُمَّةࣲ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُوا۟
ٱلطَّـٰغُوتَۖ﴾ [النحل ٣٦]
Allah ya aiko Manzanni da
yawa zuwa ga mutanensu, kowanne daga cikinsu cewa yake yi:
﴿یَـٰقَوۡمِ
ٱعۡبُدُوا۟ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَـٰهٍ غَیۡرُهُۥۤۚ﴾
"Ya ku mutanena, ku
bauta ma Allah, don ba ku da wani abin bauta wanda ba shi ba".
Don haka haƙiƙanin
Muslunci shi ne kaɗaita Allah da bauta. Ma'ana;
bayi su kaɗaita Allah da aiyukansu, na addu'a, roƙo, neman taimako, neman biyan buƙata, neman agaji, neman yaye bala'i, da
yanka, bakance, tawakkali, soyayya, tsoro da "raja'i", da sauran
aiyukan bayi na ibada, kada su yi su ma kowa sai ga Allah shi kaɗai,
ba tare da sanya masa kishiya da abokin tarayya ba.
Amma idan ka kalli aiyukan
Sufaye, na roƙon matattu, da neman
agaji a wajen waliyyai, da rataya zukata da shehunnai da duƙufa a ƙabarbura,
za ka tabbatar da cewa; lallai waɗannan
mutane ba su ma san amfanin zuwansu Duniya ba.
To wannan duka abubuwa ne da
suke nuni zuwa ga saɓawar Sufanci ga Addinin
Muslunci.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.