Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai (5)

Amsoshi


 

NA


SHEHU HIRABRI


08143533314KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘Danfodiyo, SAKKWATO 

BABI NA BIYAR


KAMMALAWA5.0 Shimfid’a


Wannan babi zai yi bayanin kammalawa da yadda tsarin aikin ya kasance daga babi na d’aya zuwa babi na biyar, sannan za a kawo sakamakon bincike da nad’ewa. Haka kuma bayan nad’ewa, manazarta da ratayen wak’ok’in makad’a Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai za su biyo a k’arshen aiki.

https://www.amsoshi.com/2017/06/17/jigogin-wakokin-madahu-cikin-wakokin-masu-jihadi/

5.1 Kammalawa


Wannan aikin bincike mai taken: “Zambo da habaici a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.” Na d’auke da babi biyar. Babi na d’aya shi ne gabatarwa da ke k’unshe da shimfid’a da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike da muhallin bincike da kuma matsalolin bincike. A k’arshe aka biyo da nad’ewa.

A babi na biyu an kawo tak’aitaccen tarihin rayuwar Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai mai d’auke da haihuwarsa da iliminsa da iyayensa da matansa da yaransa da fara wak’arsa. Haka kuma an kawo jerin sunayen yaransa makad’a da marok’a da nau’o’in wak’ok’insa da abubuwan da yake sha’awa. An kuma bayyana dangantakarsa da sauran makad’a da kuma dangantakarsa da sauran al’umma. A k’arshe aka kawo nad’ewa da babin ke d’auke da ita.

A babi na uku an kawo bayanin asalin kalmar zambo da ma’anarta da ire-irenta tare da bayyana dalilin da ke sa a yi zambo. Haka kuma an kawo amfaninsa, sannan aka yi sharhin zambo a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u da kuma bayanin nad’ewa a k’arshen babin.

A babi na hud’u an tattauna habaici tun daga asalin kalmar da ma’anarta da ire-iren habaici da dalilan da ke sa ana yin sa tare da bayyana amfaninsa. Sannan aka yi sharhin habaicin tare da fito da shi a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai. A k’arshe an kawo nad’ewa.

Babi na biyar aka yi bayanin kammalawa tare da bayyana sakamakon bincike kamar haka:

 

5.2 Sakamakon Bincike


Kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Komai da ranarsa.” Wannan magana haka take, domin al’ummomi da dama sun d’auki zambo da habaici a matsayi hanya ta ‘batanci da cin zarafi, a haka su ma masana da manazarta suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anonin kalmomin biyu inda suka bayyana zambo a matsayin suka ta kai tsaye shi kuma habaici suka a kaikaice. Amma tare da haka sashen wannan aiki ya gano cewa zambo da habaici suna da matuk’ar amfani ga jama’a a wurare daban-daban kamar haka:

 1. Zambo da habaici dukkansu taska ce ta adana adabin Bahaushe.

 2. Zambo da habaici na hana yin shisshigi wato mutum ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.

 3. Zambo da habaici dukkansu ado ne da ke k’awata harshe musamman a cikin wak’a da kuma zantukan yau da kullum.

 4. Zambo da habaici na fad’akar da mutane ta hanyar sanin miyagun d’abi’u ko k’azafi ko wani abu na daban da jama’a ke zargin sa da shi.

 5. Zambo da habaici kan taimaka wajen k’ara soke abokin hamayya.

 6. Zambo da habaici na bayyana miyagun d’abi’un mutum cikin hikima domin a kauce masa.

 7. Zambo da habaici na samar da nishad’i ga mai sauraro. Yakan iya kasancewa hannunka-mai-sanda ga wanda ake wa.

 8. Zambo da habaici kan taimaka wajen mai da martani musamman ga sarakuna da masu mulki ta hanyar wani zalunci da suke yi wa talakawansu.

 9. Zambo da habaici a cikin wak’ok’i ko maganganu yau da kullum na k’ara bunk’asa harshe.

 10. Zambo da habaici na taimakawa wajen huce haushin wanda ba a iya mayar wa raddi kai tsaye.

 11. K’warewa wajen yin zambo da habaici a cikin wak’ok’in siyasa da na sarauta na k’ara wa makad’i d’aukaka da farin jini ga wanda ba shi ake yi wa ba. Wanda aka yi wa kuwa, an tsira gaba ta har abada.

 12. K’warewa wajen yin zambo da habaici kan sa mawak’i ko makad’i ko marok’i ya samu alheri.

 13. Muhimmancin zambo da habaici ga al’umma har ya kai ga samun gurbi a cikin adabi da ake nazarin su a k’ananan makarantu da kwalejoji da kuma manya-manyan jami’o’i.


https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-4/

 

5.3 Nad’ewa


Wannan babi an yi bayanin kammalawa ne tare da bayyana yadda tsarin aikin yake, sannan an kawo sakamakon bincike inda aka gano muhimmancin zambo da habaici ga al’ummar Hausawa.

 

Post a comment

1 Comments

Rubuta tsokaci.