Amsoshi


NA


SHEHU HIRABRI


08143533314KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘Danfodiyo, SAKKWATO BABI NA HUD’U


HABAICI A CIKIN WASU WAK’OK’IN ALHAJI MUSA ‘DANBA’U GIDAN BUWAI4.0 Shimfid’a


        A cikin wannan babi za a yi bayani tare da kawo misalai tun daga asalin kalmar habaici da ma’anarta da ire-irenta da dalilin da ya sa ake yin habaici da amfaninsa tare da yin sharhinsa a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.

4.1 Asalin Kalmar Habaici


Ra’ayin masana ya had’u a kan cewa, asalin kalmar habaici, Bahaushiyar kalma ce wadda za a iya danganta ta da maganganun hikima da azanci da gwaninta da nak’altar harshe da Hasuawa suka gada tun iyaye da kakanni. Saboda haka ba ta da alak’a da kowane harshe sai Hausa. Haka kuma ba a iya cewa ga lokaci da aka fara amfani da ita. Hausawa sun taso suna shirya habaicinsu da kansu a cikin wak’ok’i da maganganunsu na yau da kullum. Habaici ya k’ara samun gata ta hanyar makad’a da mawak’a da manazarta.

4.2 Ma’anar Habaici


Malamai masana da manazarta da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar habaici. Ga wasu daga cikinsu:

D’angambo, (1984: 42) cewa ya yi: “Habaici magana ce mai ‘boyayyiyar manufa, ba kasafai akan gane da wanda ake ba.”

Garba, (1998: 18) cewa ya yi: “Habaici magana ce mai d’aci da Bahaushe ke fad’a a sakaye domin ya sanya dabi’ar gyara kayanka a wanda ba ya zama sauke mu raba.”

Zaruk da wasu (2005: 47-48) cewa suka yi: “Idan aka ce habaici ko gugar zana duk ana nufin abu d’aya ne. Habaici shi ne yi da mutum a kaikaice. Habaici ya fi yawa inda kishi yake ko k’yashi. Galibi mutane suna d’auka cewa habaici salon mata ne, dalili kuwa shi ne a tsakanin mata kishi da gasa da ganin k’yashi suka fi yawa. Duk da haka za a iya cewa habaici ana samun sa a mata ana kuma samun sa a maza. Wasu maza idan suna gaba ko ta sana’a ko ta wani abu na cigaba sukan yi wa juna habaici.

Dunfawa, (2005: 20) cewa ya yi: ‘Habaici na nufin fad’a wa wani ko wasu aibin wani abu da suka yi, ko suke yi a fakaice ba tare da ambaton suna ko siffanta wanda ake yi wa ba wato ta yadda za ta sa a gane shi.”

K’amusun Hausa, (2006: 187) cewa ya yi: “Habaici na nufin suka mutum a fakaice ta hanyar magana.”

Yahaya, da wasu (2006: 42) cewa suka yi: “Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum. Shi ma zance ne na hikima da ake amfani da shi a yi da mutum a kaikaice. A wajen yin habaici ba a kan fito fili a bayyana wanda ake nufi k’uru-k’uru ba, sai dai akan yi amfani da wasu kalmomin sakaya kamar wanga ko wagga ko su wane da makamantansu.”

D’anhausa, (2012: 13) cewa ya yi: “Habaici magana ce da ake yi cikin hikima da nufin gaya wa wani sak’o amma ba kai tsaye ba, a fakaice wato a ‘boyayyar manufa. Akan yi magana da nufin wani abu da ake yi domin shi, amma shi habaici idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai yake gane wanda aka yi habaicin domin shi ba.”

Yahya, da wasu (2015: 75) cewa suka yi: “Habaici yana nufin magana ce mai d’aci da Bahaushe ke fad’a wa d’an uwansu a sakaye domin ya sanya shi ya gyara wani mummunan halinsa ko kuma domin fad’akarwa ga ‘yan uwa kowa ya shiga taitayinsa ko kuma kawai don ba da haushi.”

Yahya da wasu (2016: 218) cewa suka yi: “Habaici wani nau’i ne na zancen hikima da ake amfani da shi a yi da mutum a fakaice don ‘bata wa wani mutum rai ko yi masa k’aimi da kuzari ko yi masa fad’akarwa, ba tare da bayyana mutumin da ake nufi k’uru-k’uru ba, amma shi wanda ake nufi wani lokaci zai gane, sai dai sauran jama’a da wuya su fahimta idan ba wanda ya san abin da ake ciki ba.”

Ta la’akari da ma’anonin da malamai masana da manazarta suka bayar, a tawa fahimta ana iya cewa: Habaici suka ce da ake yi kaikaice cikin wasu ‘boyayyun kalmomi na hikima masu ban sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ‘bata rai ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya san abin da ke faruwa.

https://www.amsoshi.com/2017/06/22/313/

4.3 Ire-iren Habaici


A Hausa akwai ire-iren habaici kamar haka:

 1. Habaicin hannunka-mai-sanda

 2. Habaicin gugar zana

 3. Habaicin zagi a kasuwa

 4. Habaici mai karin magana


4.3.1 Habaicin Hannunka-mai-sanda


Habaici ne da ake yi domin jawo hankalin wani mutum ko nuni kan wani abu da ake so ya lura da shi ko ya gyara ko kuma don a sa mutum ya kama kansa. Misali, a wak’ar ‘Danba’u ta D.P.N. inda yake cewa:

Jagora: Ina horon wane,

Kullum ya kauce ya k’iya,

Wane ka bar neman shiga,

In ‘yan taron daba,

Yara:   siyasar ‘yan gurguzu,

Ai siyasar k’eta ce.

 

A wani d’an wak’ar kuma cewa ya yi:

 

Jagora: Ina jin tsoron mutum,

Mai buk’atar gardama,

Ban so haka nan ba,

Wallahi Allah ya sani,

Ina kallon wane ya kama daji

Yara:  Wane dawo ga hanya,

Inda kowa ka murna ya hi kyau.

 

Gindi: D.P.N. ta yi daidai,

Da ‘yan Nijeirya,

Alheri yanzu kowa,

Buk’atatai yake.

4.3.2 Habaicin Gugar Zana


Habaici ne da ya shafi gugar zana. Akan yi shi ne a kaikaice ba tare da fitowa k’uru-k’uru ba, ta hanyar fad’in wasu daga cikin d’abi’un ko halayen mutum ko kuma a yi masa k’age. Misali a wak’ar Alhaji Musa ‘Danba’u ta D.P.N. inda yake cewa:

Jagora: Mu ba duba mukai ba,

Kuma ba tsafi mukai ba,

Rok’on Allah mukai,

D.P.N. dai ta hau,

Yara:   Mazanmu da matanmu,

Kowa ya zauna lahiya.

A nazarin wak’a, duk inda aka sami irin wannan magana akwai wanda ko wad’anda suke yin abin. Kenan ma’ana masu duba da tsafi. ‘Yan jam’iyar da ke adawa da D.P.N.

A wani d’an wak’a suke cewa:

Yaro: Mi ar ranak kilinge,

Ga harka duniya,

Ko ga shi cikin gida,

Yara: Kyalla shurewa takai,

 

Jagora: Yanzu ko ga shi cikin gida,

Yara:     Kyalla shurewa takai.

 

 

 

Gindi: D.P.N. ta yi daidai,

Da ‘yan Najeriya,

Alheri yanzu kowa,

Buk’atatai yake.

4.3.3 Habaicin Zagi a Kasuwa


Habaici ne wanda ake yi ta hanyar jefa magana kai tsaye ba tare da nuna wanda ake da shi ba, sai dai kowa zai rasa da wanda ake nufi. Amma a mafi yawan lokuta mai yin habaicin ya san da wanda yake. Shi ne Bahaushe ke cewa: “Kowa ya yi zagi a kasuwa, ya san da wanda yake.” Misali a cikin wak’ar ‘Danba’u ta PDP akwai inda yake cewa:

Jagora: “Yan siysa,

Ku yi hakk’uri,

Da Musa ‘Danba’u,

Kun san ku nawa ne,

Sannan ni naku ne,

Ko da kun k’i ni,

Mai kama ta kuka so,

In kuka k’i ni da d’a,

Yara:    Kun ganan da jika da goya.

 

Gindin Wak’a: Ya ‘yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma P.D.P.

4.3.4 Habaici Mai Karin Magana


Habaici ne wanda ake yi cikin sigar karin magana. Ma’ana ana amfani da karin magana wajen bayyana manufar da ake son a bayyana. Misali:

Cin d’ank’o har da su kaza.

Wani misali a cikin wak’ar ‘Danba’u inda yake cewa:

 

Jagora: Na gaya ma mutane,

D’auke dahi sai giwa,

Maza tahi kauce zomo,

Yara:   Ba ka iya wa kai nan?

 

Gindin Wak’ar: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

A wata wak’a kuma yake cewa:

Jagora: Wane bai da kirki sam-sam-sam,

Ya gama da dum masu biya tai,

Yanzu babu mai kud’i sai shi,

Na ce Allah na gode ma,

Yara:   Da na san bari ba shegiya ba ce.

 

Gindin wak’a: P.D.P. hasken Nijeriya,

Fati mai k’arfi da martaba.

4.4 Dalilin Yin Habaici


Akwai dalilai da dama da ke sa a yi habaici daga ciki akwai:

 1. Bayyana hasada

 2. Huce haushi

 3. Rowa

 4. Tsokanar fad’a

 5. Gargad’i da hannunka-mai-sanda

 6. Ramuwar gayya

 7. Kishi ko rashin jituwa (Yahaya da wasu 2006: 43).


4.5 Amfanin Habaici


Duk da kasancewar habaici suka ce da ake yi a kaikaice ta hanyar cin zarafi amma kuma, yana da amfani matuk’a. Daga cikin amfaninsa akwai:

 1. Habaici wata taska ce ta adana adabin Bahaushe.

 2. Habaici wani ado ne na harshe da ke k’awata wak’a tare da k’ara mata armashi, da kuma zantukan yau da kullum.

 3. Habaici na fad’akar da mutum ta hanyar sanin miyagun d’abi’u ko k’azafi ko wani abin da jama’a ke zargin sa da shi.

 4. Habaici na sa mutum ya daina wasu miyagun d’abi’u ko halaye.

 5. Habaici kan taimaka wajen k’ara soke abokin hamayya.

 6. Habaici na samar da nishad’i da raha a cikin zukatan jama’a.

 7. K’warewa wajen gina habaici a cikin wak’ok’i musamman na sarauta ko siyasa na k’ara wa makad’i d’aukaka da farin jini ga jama’a.

 8. Habaici na hana yin shisshigi watau mutum ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.

 9. K’warewa wajen gina habaici na sa makad’i ko marok’i ya samu alheri.

 10. Amfani da habaici a cikin wak’ok’i da zantuka na yau da kullum a cikin harshe yana k’ara bunk’asa harshe.


4.6 Habaici A Cikin Wasu Wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai


A sama an kawo ma’anar habaici da ire-irensa da dalilan da ke sa a yi shi tare da bayyana amfaninsa. A nan kuma za a yi sharhin habaici a cikin wasu wak’ok’in Alahaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.

Kamar yadda Yahya da wasu (2016: 218) ke cewa: “Habaici wani nau’i ne na zancen hikima da ake amfani da shi a yi da mutum a fakaice don ‘bata wa wani mutum rai ko yi masa fad’akarwa ba tare da bayyana mutumin da ake nufi ba, wani lokaci zai gane sai dai sauran jama’a da wuya su fahimta, in ba wanda ya san abin da ake ciki ba.”

Za a ga irin wad’annan bayanan da Yahya da wasu (2016: 218) suka yi a cikin littafinsu mai suna Alun Nan Dai kan habaici a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai.

A wak’ar jam’iyar P.D.P. mai taken:

Ya ‘yan Nijeriya,

Siyasa ta tashi,

Ku dawo mu yi k’ok’ari,

Mu koma P.D.P.

A cikin wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici a wurare da dama a cikin d’iyan wak’a kamar haka:

Jagora: Na yi mamaki wane,

Don siyasa ta k’are,

Shi muddin yag ganan,

Ya canza man huska,

Ga siyasa ta dawo,

Ga mu mu ko mun dawo,

An ce a had’e,

Ba mu buk’ata ‘Danba’u,

Kowa ya tsaya wurinsa,

A buga a gani,

Yara:  A gane wa zai rinjaye.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa habaici ta hanyar wani abin da ya faru tsakaninsu, bayan wucewar siyasa da cewa, duk lokacin da ya gan shi ya canza mai fuska, yanzu kuma siyasa ta dawo, ya kira su ya ce a had’e, shi ne yake ba shi amsa cewa kowa ya tsaya wurinsa a buga a gani a gane wa zai yi rinjaye. A nan ya kira shi da wane ba wanda zai hak’ik’ance cewa ga wanda yake nufi, amma shi wanda ake wa ya sani, da kuma wanda ya san abin da ke tsakaninsu.

A wani d’an wak’a yake cewa:

 

Jagora: ‘Yan siyasa,

Ku yi hank’uri,

Musa ‘Danba’u,

Kun san ku nawa ne,

Sannan ni naku ne,

Ko da kun k’i ni mai kamata kuka so,

In kuka k’i ni da d’a,

Yara:   Kun ganan da jika na goye.

Bayan kammala d’an wak’ar sai ‘Danba’u ya ce: “Abin daga Allah ne.”

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wasu ‘yan siyasa habaici wad’anda ke jin haushinsa cewa su yi hak’uri da shi domin ko da sun k’i shi mai kama tai suka so, in suka k’i shi da d’a, sun gan shi da jika ya goya. Ma’ana da su so shi da kar su so shi ba abin da za su iya yi masa. Haka kuma duk abin da za su ba shi ya sami fiye da haka, don haka babu yadda za su yi da shi.

A wani d’an wak’a yeke cewa:

Jagora: Rak’umi na tafiya,

D’auke da kayanai,

Ya isko kunama yat taka,

Naj ji ya buga ihu,

K’asa akwai shaggu,

‘Yar abig ga ‘yar tcito,

Ga shi yanzu ta halban,

Yara: Har na gaza d’aukar kayan nan.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa habaici ta hanyar kwatance. Inda ya kwatanta wani babban d’an siyasa da rak’umi, da wani k’aramin d’an siyasa a matsayin kunama. Inda yake nuna wani babban d’an siyasa ya fad’a wa wani k’aramin d’an siyasa, k’aramin ya samu gagarumar nasara a kan babban d’an siyasan. Shi ne yake cewa rak’umi na tafiya d’auke da kayanai, ya isko kunama ya taka, sai nij ji ya buga ihu ya ce k’asa akwai shaggu, ‘yar abig ga ‘yar tcito ga shi yanzu ta halban har na gaza d’aukar kayan nan. A nan za a ga abin a dunk’ule yake ba kowa zai iya fahimtar wanda ake nufi ba.

Haka kuma a cikin wata wak’ar P.D.P. mai taken:

P.D.P. hasken Nijeriya,

Fati mai k’arfi da martaba.

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici a d’iyan wak’a daban-daban kamar haka:

Jagora: Kai ji wane yai tahiyar kura,

Yana gaba ya koma baya,

Inda yan nuhwa ba a kar’bai ba,

Ya dawo bai ishe kowa ba.

Yay yi shiru yar rik’e baki,

Nac ce duk mai koraj jama’a,

Yara: Sai ya bid’i mai ba shi shawara.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani d’an siyasa habaici ta hanyar kiran sa da wane yai tahiyar kura yana gaba ya koma baya inda ya nufa ba a d’aukai ba ya dawo bai ishe kowa ba. Ma’ana yana cikin jam’iyatai, ya fita ya koma wata jam’iya. Jam’iyar da ya koma ba su kar’be shi ba, ya dawo jam’iyyarsa ta farko suka k’i kar’bar sa. Wai sai ya yi shiru ya rik’e baki yana mamaki, sai yake cewa: “Kowa ke korar jama’a, sai ya bid’i mai ba shi shawara.” Ma’ana duk mai wulak’anta jama’a sai ya neme su, domin da yana da abokan shawara da haka ba ta faru ba. Nan canza jam’iyya zuwa wata jam’iya ga ‘yan siyasa abu ne wanda ya zama ruwan dare. Don haka zai yi wuya a gane wanda ake nufi kai tsaye, sai wad’anda suka san abin tun farko.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Mai k’ark’arin hawan icen kwakwa,

Idan ka hwad’o ka k’alle,

Kai cikin dubu nika tona ka,

Yara: Bak’ar magana wadda kai muna.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani d’an siyasa habaici da cewa mai k’ark’arin hawan iccen kwakwa, ma’ana mai son shiga jam’iya mai alamar kwakwa. Idan ka hwad’o ka k’alle. Ma’ana idan ya shiga jam’iyar, aka yi za’be suka fad’i. Kai cikin dubu nika tona ka, ma’ana cikin taron jama’a za su tona mai asiri. Bak’ar magana wadda kai muna. A nan ke nan akwai wata shawara da suka ba shi ya k’i ji har ya yi musu bak’ar magna. Shi ne yake yin k’arin bayani domin wanda suka yi haka ya san da shi ake amma wani ba zai fahimci da wanda ake ba.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Ku ji kyanwa mai saurin tafiya,

K’ark’arin takai dai ta ci kifi,

Dur radda k’aya tal lak’e miki,

Yau kowa bai tagaza miki,

Sai dai ki mace ‘yar damk’on uwa,

Yara: Don mun kula ‘barnarki tai yawa.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani d’an siyasa habaici a kaikaice ta hanyar ‘boye sunansa ya kira shi da kyanwa mai saurin tafiya, k’ark’arin takai ta ci kifi. Ma’ana wani d’an siyasa ne ke k’ok’arin shiga wata jam’iya ko kuma tsayawa takara a wata jam’iya. Duk rad da k’aya ta lak’e miki yau kowa bai tagaza miki, ma’ana dur randa aka yi za’be ya fad’i ko suka fad’i k’arya tai k’are domin kowa bai taimaka masa sai dai ya mace, domin rashin kunyarsa ya yi yawa. A nan sai dai hasashe kawai ga mai saurare amma ba za a iya cewa ga wanda ake nufi ba. Don haka habaici ya amsa kirarinsa cewa habaici masu fad’a kowa amsa da shi ake.

A wak’ar Tanimu D’angaladiman Kyad’awa mai taken:

Dogo kana da shirin Yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakubu.

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici a d’iyan wak’a daban-daban kamar haka:

Jagora: Ni munahukin Gada na san shi,

Don bak’in jininai ya yi yawa,

D’azu ya wuce mu muna hira,

Sai nij ji yara suna ihu,

Wada nij ji ana kard’a-kard’a,

Nac ce gudun ga na aura ne,

Yara: Shi bai yawo a cikin Gada,

Kuma bai shiri da mak’wabtansa.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani mutum habaici ta hanyar gugar zana inda ya fito da wasu ‘yan halayensa a kaikaice ta yadda ba a iya gane wanda ake nufi kai tsaye, sai ya danganta shi da yadda mutane ke gudun munafuki da yadda kare ke samun barazana ga yara, idan sun had’u. Don haka shi munafuki za a ga ba a cika yarda da shi ba, kuma mutane ba su ra’ayinsa.

A wani d’an wak’a suna cewa:

Yaro: Kowa da abin da yake sauna,

Kowa da abin da yake tsoro,

Kusu kyanwa yaka jin tsoro,

Jagora/Yara: In ga kura a cikin gari,

Aura ba za ya hitowa ba.

Jagora: A in ga kura a cikin gari,

Aura ba za ya hitowa.

A wannan d’an wak’a sun yi wa wani d’an siyasa habaici ta hanyar nasara da gogansu ke samu ga wanda yake wa habaici cewa kowa da abin da yake tsoro kusu (‘bera) kyanwa yaka tsoro. Aura (kare) kura yaka tsoro. Shi kuma wanda ake wa habaici, Tanimun yake tsoro. A nan za a ga abin a ‘boye yake ga mai sauraro ko karatu sai in an bayyana.

A wak’ar Matawallen Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ma ya yi habaici a cikin ta kamar haka:

Jagora: Ko a siyasa in ta tashi,

Mai jama’a shi ne aka za’be,

Kai wane kar ka fito a gane ka,

Bak’in jininka kare ya ‘baci,

Yara: Ko da ka je ka buga fosta,

Ko a gida wani ba ya lak’a ta.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa wanda ke son ya yi takara habaici cewa ko a siyasa in ta tashi mai jama’a shi ne aka za’be, kai wane kar ka fito a gane ka. Ma’ana ko ya fito ba a za’ben sa domin ba ya da jama’a saboda bak’in jinin da yake da shi, kamar yadda kare ke da bak’in jini ga yara. Don haka ya ji yana maganar zai buga fosta to ko ya je ya buga fosta ko a gida mutane ba su lak’a ta. A nan ya kira shi da wane kuma masu son su fito takara suna da yawa don haka zai yi wuya a gane wanda ake nufi.

A wani d’an wak’ar makad’in ya k’ara da cewa:

Jagora: Abin da duk kura ka buk’ata,

Ba haka sarkin fawa ka so ba,

Kura kwad’anki har ya ‘baci,

Ita dai kullum ta ci nama,

Yara: Dur randa ta shiga ba daidai ba,

Sai ta sha kashi ga mutane.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani habaici a kaikaice ta hanyar amfani da sunan sarkin fawa da kura da cewa abin da duk kura ka buk’ata ba haka sarkin fawa ka so ba. A nan za a iya cewa maigida ne da yaronsa. Maigida shi ne sarkin fawa, yaron shi ne kura. Shi sarkin fawa duk lokacin da da ya yi yanka yana son ya sayar ya sami riba, ita kuma kura bid’a takai ta mamaye sarkin fawa. Ma’ana shi maigidan yana hasashen hanyar da za a bi a sami nasara, shi kuma yaron zagon k’asa yake wa maigidan saboda kwad’ayin samun abin duniya har yake son ya zalunci maigidan. Du randa ta shiga ba daidai ba sai ya sha kashi ga mutane. Ma’ana duk randa ya kuskura maigidan ya gane sai ya ci kwakwarsa d’anya.

A wak’ar Attahiru Bafarawa mai taken:

Kada ka ji tsoron maza,

Rik’a zakin duniya,

Bai san tsoro ba,

Bafarawa Attahiru.

A wannan wak’ar akwai habaici a ciki inda yake cewa:

Jagora: Ga d’ammanin Haji ‘Danba’u,

Idan an je a wurin buki,

Idan masu kud’i sun had’u,

To da sun je kyauta sukai,

Wani mai kud’i ya barkace,

Yara: Rabon guraye yakai.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani mutum mai kud’i habaici ta hanyar gugar zana da wani halin rowa da cewa ga d’ammanin Haji ‘Danba’u idan an je wurin buki, idan masu kud’i sun had’u da sun zo kyauta sukai, wani mai kud’i ya barkace rabon guraye yakai. Ma’ana rowa gare shi bai iya kyauta amma gaba yake wurin rabon abinci. A nan wanda ake wa habaicin ya san da shi ake. Haka kuma duk wanda ya je wurin bikin ya ga lokacin da mai kud’in ke rabon abinci zai fahimci da wanda ake. A nan ma’anar da Yahya da wasu (2016: 218) cikin Alun Nan Dai suka bayyana a sama ta fito fili.

A wani d’an wak’a ya ce:

Jagora: Bafarawa Attahiru,

Ga mota za ya ban,

Katan keke ya hana.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani mutum wanda ya hana a ba shi kyautar mota habaici da cewa Bafarawa ga mota za ya ban kata keke ya hana. A nan wanda ya hana Bafarawa ya ba shi mota ya san da shi ake kuma Bafarawa ya san da wanda ake domin ya san abin da ya faru, amma kuma wanda bai san abin da ke faruwa ba, ba zai gane ba.

A wak’ar jam’iyar D.P.N. mai taken:

D.P.N. ta yi daidai da,

‘Yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa,

Buk’atatai yake.

A wannan wak’a ‘Danba’u ya baje kolinsa wajen habaici a cikin d’iyan wak’a da dama kamar haka:

 

 

 

Jagora: Mu ba duba mukai ba,

Kuma ba tsahi mukai ba,

Rok’on Allah muke,

D.P.N. dai ta hau,

Yara: Mazanmu da matanmu,

Kowa ya zauna tahiya.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wasu ‘yan siyasa habaici. Irin wannan habaici da ya zo a cikin wannan d’an wak’a shi ake kira habaicin zagi a kasuwa. A nazarin wak’a duk inda aka samu irin wannan magana akwai wanda ko wad’anda suke yi abin ke nan ma’ana masu duba da tsafi. Su rok’on Allah sukai, su kuma ‘yan wata jam’iya su ke duba da tsafi amma dai ba su ce musu suna yi ba, shi ya sa ake wa habaici kirari da maso fad’a kowa tamkar da shi ake.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Ni mamaki nake,

Mai duba shi da boka siyasa guda akai,

Mai duba ya buga yace su za su ci,

Boka ya yi tsahi da ‘yan kaji bakwai,

Kuma Allah yai hani tona sirinai aji,

Yara: To du a gama ta sai sun yi kunya duniya.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wasu ‘yan siyasa habaici a kaikaice ta hanyar gugar zana inda ya d’an k’yafato wasu ‘boyayyun halayensu wad’anda ba su fito fili jama’a suka sani ba, na duba da tsafi, domin ‘Danba’u da kansa a cikin layi na biyar a cikin wanann d’an wak’ar cewa ya yi: “Kuma Allah yai hani tona sirinai a ji.” Sai yara suka cika da cewa: “To du a gama ta sai sun yi kunya duniya.” Ma’ana ba kowa ya san suna tsafi ba amma duk a gama ta sai asirinsu ya tonu.

A wasu d’iyan wak’a ya k’ara da cewa:

Jagora: Ina horon wane,

Kullun ya kauce ya k’iya,

Wane ka bar neman shiga,

Inda ‘yan taron daba,

Yara: Siyasar ‘yan gurguzu,

Ai siyasar k’eta ce.

 

Jagora: Ina jin tsoron mutum,

Mai buk’atar gardama,

Ban so haka nan ba,

Wallahi Allah ya sani,

Ina kallo wane ya kama daji,

Yara: Wane dawo ga hanya,

Inda kowa ka murna ya hi kyau.

Jagora: Mutane ku yi hankali,

Da sarkin ‘banna kare,

Yana iya canye awakinku,

In ta zaburo,

Yara: Ya ko runtce ido,

Ya dawo ya ce ba shi ba ne.

A irin wannan habaici da ya zo a cikin d’iyan wak’ar da suka gabata a sama shi ake kira habaicin hannunka-mai-sanda. Habaicin hannunka-mai-sanda habaici ne da ake yi domin jawo hankalin wani ko nuni a kan wani abin da ake so ya lura da shi ko ya gyara ko kuma don a sa mutum ya kama kansa. Za a ga d’iyan wak’ar uku da suka gabata dun hannunka-mai-sanda ne ake yi.

A d’an wak’a na farko yana yi wa wani mutum habaici ta hanyar yi masa hannunka-mai-sanda inda ya ambaci kalmar horo kai tsaye cewa ina horon wane kullun ya kauce ya k’iya. Ma’ana yana hana shi shiga abin da bai da amfani ya k’i, ya k’ara da cewa wane ka bar neman shiga inda ‘yan taron daba, siysar ‘yan gurguzu ai siyasar k’eta ce. A nan d’an wak’ar ya fito da gargad’i fili ba sai an yi dogon bayani ba.

A d’an wak’a na biyu shi ma yana jawo hankalin wanda ake wa habaici ta hanyar bayyana damuwa game da wanda ake fad’a wa gaskiya amma yana gardama. To ga shi an nuna masa hanyar gaskiya ya kauce mata, ya kama hanyar k’arya. Duk da cewa ya kama hanyar da ba ta k’warai ba. ma’ana ya shiga jam’iyyar da ba D.P.N. ba, saboda soyayya da yake masa ya k’ara kiran sa da cewa wane dawo ga hanya inda kowa ka murna ya fi kyau. Ma’ana jam’iyar D.P.N.

Shi ma d’an wak’a na uku gargd’i ne yake yi ta hanyar habaicin hannunka-mai-sanda da cewa mutane su yi hankali da sarkin ‘barna kare. A nan yana kira ne ga mutane kaikaice su yi hankali da wani mutum wanda ya kira kare domin bai da amana, ana iya ba shi hakkensu ya cinye.

A wad’annan d’iyan wak’ar da suka gabata, za a ga abin a dunk’ule ba za a iya cewa ga wanda ake nufi ba.

A wani d’an wak’a ya ce:

Jagora: Bak’in kwad’ayin wane,

Ya kai shi d’aukar arkane,

Yara: Ga jirgin Makka,

Ya taka motar D’andume.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani habaici ta hanyar gugar zana ya kawo wani halinsa na kwad’ayi, sai ya kira shi da wane ta yadda ba za a iya gane wanda ake nufi ba kai tsaye.

A wani d’an wak’a ya k’ara da cewa:

Jagora: Na san kissa kare,

D’auke k’ahwa da ya yi,

Ba ciyo ne takai ba,

Yara: Tsoro yaka yi,

A korai da manyan dutsuna.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani mutum habaici a kaikaice ta hanyar kwatance inda ya kwatanta abin da kare ta hanyar kissa da cewa, na san kissa kare d’auke k’afar da ya yi ba ciyo ne takai ba. ma’ana wani mutum ne ya bar zuwa wajen da suke zama. Shi ne d’auke k’afar da ya yi. Me ya sa ya bar zuwa wurin, sai ya ce: “Saboda bai da lafiya.” Shi ne yake cewa ba ciyo ne takai ba, ma’ana k’arya yakai lafiyarsa lau. Dalilin da ya sa ya bar zuwa wurin shi ne yake cewa: “Tsoro yaka yi a korai da manyan dutsuna.” Ma’ana kada a yi masa wulak’anci. A nan za a ga abin a dunk’ule ba za a iya bayyana wanda ake nufi ba.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: In tafiya tai tsawo,

Kai amali ka tsarsuwa,

Jaki sarkin kud’a,

Yara: Duk yada ka so ya kai,

Inda zango bai zuwa.

A wannan d’an wak’a ‘Danba’u ya yi wa wani habaici ta hanyar kasawa a kan neman wata buk’ata sai ya kwatanta abin da rak’umi da jaki da nuna cewa idan tafiya ta yi tsawo sai amali. Ma’ana rak’umi yana iya tafiya daga k’asa zuwa wata k’asa amma jaki bai iyawa. Shi ne ‘Danba’u ke kwatanta tafiya wasu ‘yan siyasa da nuna gwarzonsa shi ne amale. Shi ke iya wa tafiyar shi kuma wancan abokin adawa shi ne jaki duk yadda ake so yakai wani wurin ba zai iya ba.

A wani d’an wak’a kuma yake cewa:

Jagora: Ni na san ungulu,

Kolo rage tak’ama,

Tak’amar banza shi kai,

Yara: Yana iya tahiya,

Da ya iske mushe yai ta ci.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa habaici ta hanyar ‘boye sunansa ya kira shi da ungulu (kolo) kuma ya d’an zoji wata d’abi’arsa ta tak’ama da cewa tak’amar banza ce tunda yana tafiya ya iske mushe ya sauka ya yi ta ci. Ma’anar mushe shi ne cin hak’in mutum ba da son ransa ba, don haka tak’amarsa ta banza ce tunda azzalumi ne.

A wani d’an wak’a suke cewa:

Yaro: Mi ar ranar kilinge,

Ga harkad duniya,

Ko ga shi cikin gida,

Yara: Kyalla shurewa takai,

 

Jagora: Yanzu ko ga shi cikin gida,

Yara: Kyalla shurewa takai.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa habaici a kaikaice ta hanyar ‘boye sunansa ya yi amfani da wani suna na daban wato kilinge da cewa mi ye ranar kilinge. Kilinge na nufin wuk’a wadda ta sallace ma’ana marar kaifi wadda ba ta iya yankan komai. Kyalla kuma na nufin babbar akuya lafiyayya. A nan abin da yake nufi shi ne, miye ranar wannan mutumin da ya ‘boye sunansa a cikin jam’iyyar siyasa tunda bai iya amfana mata komai.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Ni na san,

Maitatsine,

Wuyal lamari garai,

Don Allah dai mutane,

Ku bar yarda da shi,

Yara: Ko an yi shiri da shi,

Watce tsarin nan yakai.

A wannan d’an wak’ar, ‘Danba’u ya yi wa wani d’an siyasa habaici ta hanyar yi wa jama’a hannunka-mai-sanda game da shi, cewa su bar yarda da shi domin ko an k’ulla harka da shi ‘bata tsarin yake.

A wak’ar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko mai taken:

D’antakarar zama gwamna,

Magatakarda Wamakko,

Aliyu kar ka d’au reni,

Kuma kar ka d’au wulak’anci.

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici a cikin wasu d’iyan wak’a, kamar inda yake cewa:

Jagora: Ni na tabbata kana da basira,

Na sani kana da tunani,

To amma fa ka k’ara kulawa,

Angulu munahukin Allah ne,

Yara: In ka ganai wurin yak’i,

Shi ba da gaske ya zo ba.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani habaici ta hanyar yi wa d’an takara hannunka-mai-sanda cewa ya san yana da basira kuma ya san yana da tunani, to amma fa ya k’ara kulawa, sai ya ‘boye suna, sai ya kira shi da angulu munafukin Allah ne in ka ganai wurin yak’i shi ba da gaske ya zo ba. ma’ana duk yadda yake nuna goyon bayansa kada ya amince masa. Ba da gaske yake ba.

A wani d’an wak’a kuma cewa ya yi:

Jagora: Ga magatakarda ga Muntari,

To amma fa ku k’ara kulawa,

In dai abin rabo ya samu,

A dank’a ma masu imani,

Yara: Don kada a bai wa kuraye shiya,

In sun had’e shi an huta.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wasu habaici ta hanyar hannunka-mai-sanda ga d’an takarar gwamna da mataimakinsa da cewa su k’ara kulawa in dai abin rabo ya samu a damk’a ma masu imani, ke nan wad’anda aka saba ba abin rabon suna zalunci, a canza su idan kuma aka ci gaba da ba su ba za su yi adalci ba canye shi za su yi. A nan za a ga an yi suka a kaikaice ta yadda ba za a iya gane da wa ake ba.

A wak’ar Dr. Aliyu Magatakarda mai taken:

Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamna Sakwkato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici a cikin wasu d’iyan wak’a kamar haka:

Jagora: Ka ga mutum-mutumi da kamar mutum,

Da ka ganai ka ga tsumma ne kurum,

Bai hana komai bai tare komai,

Ka yi shi don ya tsare ma gona,

Yara: Bai hana tsuntsu ‘bata ma ita.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani mutum habaici da cewa ka ga mutum mutumi da kamar mutum. Mutum-mutumi na nufin karare ko itace da aka had’awa, a sa masa riga da hula a cikin gona matsayin mai tsaro musannan ga yara da tsuntsaye. Ma’ana ga mutum cikakke da ka gan shi ka ga kamilin mutum wanda ke iya yin abin kirki, amma bai iya komai ba, tsumma ne kawai, ma’ana girman ne kawai, bai da wani amfani ga jama’a, da shi da mutum-mutumi duk d’aya. To in ka aje shi ne domin ya tsare ma gona, bai hana tsuntsu ‘bata ma ita ma’ana idan an aje shi domin ya magance wata matsala, to aikin banza aka yi domin ba zai iya ba, kunya kawai za a ji. A nan za a ga abin a dunk’ule ba za a iya gane wanda ake nufi ba.

A wani d’an wak’a ya k’ara da cewa:

Jagora: Allah waddan gurun kolo,

Da d’ai bai saba kashin kunya ba,

Shi bai saba kashin kunya ba,

Ba ka sani sai ka je gaisai,

In ya yi ma kyauta ka duba,

Ka dubi girmanai ka ga kyauta,

Yara: Abin akwai abin ban kunya ‘yan uwa.

A wannan d’an wak’ar makad’in ya yi wa wani babban mutum habaici ta hanyar raina kyautar da yake yi, da cewa idan ya yi ma kyauta ka dubi kyautar ka dubi girmansa ka dubi kyautar abin akwai kunya. A nan ‘Danba’u ya danganta girmansa da gurun kolo. Kasancewar gurun kolo bai da amfani domin ba a ra’ayinsa. Shi ma girmansa bai da amfani domin bai iya kyautata ma jama’a. Sai dai ya yi abin a kaikaice ta yadda ba za a iya gane wanda ake nufi ba.

 

A wak’ar Alhaji Aliyu Magatakardan Wamakko mai taken:

K’ara shirawa

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro Magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya gina habaici a d’iyan wak’a daban-daban kamar haka:

Jagora: Mun sani Allah shi ka ba da mulki ya ba ka,

Don kak ka bi shawarar buhun kowa,

Mai so a k’i wa kowa komai,

Yara: D’an Barade Alu,

Kai ta wa mutane adalci.

https://www.amsoshi.com/2017/06/21/206/

A wannan d’an wak’ar makad’in ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d’aya ya yi wa wani mutum na tare da gwamna habaici kuma, ya yi wa gwamna hannunka-mai-sanda da cewa Allah shi ka ba da mulki kuma ya ba shi, kada ya bi shawara buhun kowa mai son a k’i wa kowa komai, d’an Barade Alu kai ta wa mutane adalci. A nan yana k’ara ba gawamna shawara cewa kada ya bi shawara wani mutum da yake tare da shi mai rowa wanda ba ya son a yi alheri.

A wani d’an wak’a kuma yake cewa:

Jagora: In ka ji k’i gudu ‘Danba’u,

Sa gudu ne ab bai zo ba,

Ranaz za’benka d’an Barade na wamakko,

Wad’ansu maza hay Yamai suna ‘boyo,

Yara: Kahin a yi za’be sun tcere.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wasu mutane habaici ta hanyar tserewar da suka yi ranar za’be ganin cewa ba su da nasara, kafin a gama za’be a k’idaya (k’irga) sai suka tsere suka tafi Yamai a k’asar Nijar. Shi ne yake sukar su cewa duk wanda ya ce ba ya gudu to wanda ke sa gudu ne bai zo ba, da mai sa gudu ya zo ma’ana ruwan k’uri’ar da suka ga ana yi wa Alu, sai ga shi sun tsere da kafafunsu sun bar k’asa sukutum saboda kunya da gudun wulak’anci. A nan wad’anda ake wa habaici sun san da su ake, kuma duk wanda ya san lokacin da suka tsere sun san da wanda ake amma wanda duk saurare kawai yake bai san abin da ke faruwa ba, bai iya gane wanda ake wa habaicin.

 

A wasu d’iyan wak’ar kuma ga abin da yake cewa:

Jagora: Na gaya ma mutane d’auke dahi sai giwa,

Yara: Maza tahi kauce zomo ba ka iyawa wa kai nan?

 

Yaro: Da ma hank’urin kwaram sai goga,

Wuyau ta sai k’arfe,

Jure fari sai tofa,

Baba ruwa da kada ba a zuwa wanka,

Sai dai a tsaya kallo.

Jagora/yara: Wani ya shiga zai wanka,

Da ya shiga bai kai wajje ba.

A wad’annan d’iyan wak’ar suna jifar tsuntsu biyu da dutsi d’aya suna gwarzanta gogansu suna sukar abokin hamayyarsa kaikaice a kan kasawar da ya yi. D’auke dafi sai giwa, gogansu ne giwa. Maza tafi kauce zomo, abokin hamayya ne zomo, ba ka iya wa wa kai nan?

A d’a na biyu inda aka ce da ma hank’urin kwaram sai goga, gwarzonsa ke nan, jure fari sai tofa, ruwa da kada sai kallo wani ya shiga zai wanka da ya shiga bai kai wajje ba. A nan duk habaici ne kaikaice ake wa abokin hamayya na kasawar da ya yi.

A wak’ar Sardaunan Hamma’ali mai taken:

Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

A wannan wak’ar ma makad’in ya yi habaici a cikin ta inda yake cewa:

Jagora: Na sauka kware don in ga ciyaman,

Na tahi ofis sai nig gaisai,

Sai ya ce a ba ni kud’d’in mai,

Da ya ce a ba ni kud’in mai,

Ni yi jira ba a mik’a min ba,

Ni mamaki ya kama ni,

Ga rijiya ta ba da ruwanta,

Yara: Sai guga ta hana a d’ebo.

Sai jagora ya ce: “Ke guga ‘yar bak’in ciki,” a nan dai ya ba da bayanin abin da ya faru da kansa a k’arshe sai ya yi suka kaikaice rijiya ta ba da ruwanta sai guga ta hana a d’ebo. Ma’ana ciyaman shi ne shugaba kuma shi ke da iko a kan komai na k’aramar hukumar, ya ce a ba shi kud’in mai amma wanda an ka ce ya ba shi ya hana. A nan ciyaman shi ne rijiya. Wanda aka ce ya ba shi kud’i shi ne guga.

A wak’ar Dr. Sama’ila Sambawa mai taken:

Yaro ya ja maka a k’arya,

D’an takarar Gwamnan Kebbi,

Dr. Sama’ila Sambawa.

A cikin wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici a cikin wasu d’iyan wak’ar kamar haka:

Jagora: Du ya da aura ya kai k’arhi,

Ba ya shiga d’akin kura,

Idan ba da bindiga ya zo ba,

Ko da da bindiga ya zo ma,

Kare ba ya i mata wa ash shi.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani habaici da cewa duk yadda aura (kare) ya kai k’arfi ba ya shiga ramin kura. Ma’ana duk yadda wanda ake wa habaici yake ganin yana da k’arfi, to ya sani bai yi k’arfin sambawa ba in ba da bindga ya zo ba, ma’ana sai ya yi gagarumin shiri, kuma ko da ya yi gagaruma shiri, ba ya iya wa da shi. Ma’ana wanda ake wa habaici duk yadda yake ganin yana da jama’a to bai iyawa da Sambawa.

A wani d’an wak’a yake cewa:

Jagora: Wani ya ci tuwonsa na shinkahwa,

Ya d’auki Pure water ya sha,

Sai ya gano bawan Allah,

Mai cin tuwon dussa kullum,

Ya ce ya hana masa dussatai,

Ku al’umma na tambaiku,

Shin wannan shi ne adalici?

Yara: Wannan ya yi babban zalunci,

Ko ba a ce masa komai ba.

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wani mutum habaici kaikaice cewa wani ya ci tuwonsa na shinkafa ya d’auki pure water ya sha, ma’ana yana bisa babban aikinsa sai ya gano bawan Allah mai cin tuwon dussa kullum. Ma’ana shi wanda ke bisa k’aramin aikin da ko cefane ba ya yi masa ya ce ya hana masa dussatai. Ma’ana ya kore shi daga aiki. Ku al’umma na tambai ku shin wannan shi ne adalci? Sai ya ba da amsa da kansa cewa wannan ya yi babban zalunci koba a ce masa komai ba. A nan za a ga abin a dunk’ule yake. A tak’aice ambatar wani ke nuna habaici a cikin d’an wak’ar domin ba a fayyace ba.

A wak’ar ciyaman d’in Gwadabawa Alhaji Musa Lumu mai taken:

Gwabron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

 

A wannan wak’ar ‘Danba’u ya yi habaici inda yake cewa:

Jagora: Bak’ar akuya wance ke ad da k’allallen k’aho,

Ban layya da ke kuma ba mu yin suna da ke,

Yara: Mu ba mu sayen ki bari masu yin tsahi su sai.

 

A wannan d’an wak’ar ‘Danba’u ya yi wa wata mace habaici ta hanyar ‘boye sunanta da cewa: “Bak’ar akuya wance ke ad da k’allalen k’aho ban layya da ke kuma ba mu yin suna da ke mu ba sayen ki bari masu yin tsafi su saye ma’ana ba su buk’atar ta a jam’iyyarsu, domin halayyarta da d’abi’unta kamar yadda ba a buk’atar a yi layya da dabba mai k’allalen k’aho kuma ba a yin suna da ita. Don haka duk mai halayya irin tata ba a buk’atar ta a siyasa. A nan yana da wuya a fahimci wadda yake nufi. Rashin gane waddea ake nufi ya tabbatar da habaicin da ake bayani a kai.

4.7 Nad’ewa


Wannan babi an yi bayanin habaici tun daga asalin kalmar da ma’anarta da ire-irenta, daga ra’ayoyin masana da manazarta daban-daban tare da kawo dalilan da ke sa a yi habaici. Haka kuma an bayyana muhimmanci/amfani da ake samu ta hanyoyinsa. A k’arshe an kawo sharhin habaici a cikin wasu wak’ok’in Alhaji Musa ‘Danba’u Gidan Buwai ta hanyar fitowa da abubuwan da masana suka bayyana a matsayin habaici. Haka kuma an yi nazarin wasu wak’ok’insa da ke d’auke da habaici aka kawo misalai a wurare daban-daban.