Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanayin Zuwan Mafayyaciya da Lokatak Da Dirka a Cikin Jimlolin Karin Harshen Sakkwatanci (4)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya
NA 
HARUNA ABDULLAHI UMAR

BABI NA UKU:  MAKAMANTAN WA’DANNAN JUMLOLI A A  KARIN HARSHEN SAKKWATANCI

3.0    SHIMFI’DA


Wannan babi shi ne babin da ya ke d’auke da nazari kan karin harshen Sakkwatanci, kuma a cikin sa ne za a ga ire-iren jumlolin da karin harshen Sakkwatanci yake da su. Wad’anda suka had’a da Sassauk’ar jumla a karin harshen Sakkwatanci, da kuma jumlar tambaya da ta umurni, tare da jumlar korewa duk  a  cikin karin harshen Sakkwatanci. Za a kawo su ne kamar yadda aka kawo na daidaitacciyar Hausa a babi na biyu. Kafin a yi duk wad’annan bayanan sai an waiwayi abin da masana suka ce game da karin harshen Sakkwatanci.

 

3.1    KARIN HARSHEN  SAKKWATANCI


Idan ana maganar karin harshen Sakkwatanci za a ga cewa karin harshen Sakkwatanci wani babban kaso ne da ya k’unshi karuruwan harsunan dukkansu.wasu masana na ganin cewa, karin harshe ya kasu kasha biyu wato Karin harshen gabas wanda ya k’unshi Kananci, Zazzaganci, Katsinanci da makamantansu. Da kuma karin harshen yamma wanda ya k’unshi Sakkwatanci, Kabanci, Zamfaranci, Arewanci, da sauran kare-karen harshen yamma. Saboda kasancewar Sakkwato ita ce uwa ga sauran karuruwan harsunan yamma. Saboda haka sai aka fahimci akan samu dangantaka ta fagen karin harshe da al’adu da auratayya, addini da kuma kasuwanci.

Hamma'ali, (1985), ya nuna cewa "Sakkwatanci Karin harshe ne na Sakkwato. An samo kalmar Sakkwatanci ne daga Sakkwato. Sakkwatanci Karin harshe ne na mutanen Sakkwato. Sai dai kuma ba ana nufin Jihar Sakkwato gaba d’aya ba. Wasu na ganin tsagwaron Sakkwatawa sune, wad’anda ke garuruwan da ke kusa da Sakkwato, wato Zamfarawa, Kabawa, Arawa. Musamman wad’anda aka kafa ko ciyar da su gaba, bayan jihadi.

Wasu na ganin cewa, Sakkwatanci Karin harshe ne na mulki. Dalilin da ya sa suke ganin Sakkwatanci a matsayin Karin harshe na mulki shine, saboda kasancewar Sakkwato cibiyar Daular Usmaniyya. Wadda bayan k’are jihadi ita ce ke fad’a a ji a k’asar Hausa, har zuwan Turawan Mulkin Mallaka.

 

3.2.1 SASSAUK’AR JUMLA A  KARIN HARSHEN SAKKWATANCI


Kamar yadda Sassauk’ar Jumlar daidaitacciyyar Hausa ta k’unshi yankin Suna da kuma abin da aka fad’i a game da suna; haka ma Sassauk’ar jumlar Sakkwatanci ta k’unshi yankin suna da kuma yankin abin da aka fad’i a game da suna. Misali wasu daga cikin jumlolin Sakkwatanci.

 

a-       Bala            ya      c         ci      abinci

 

 

 

Sn aik        maf     lokt      Aik    Sn kar’b

S                                     A           K

 

J                  Y Sn   +  YAfgsa

YAfgsn                  KN  +  Yn

YA                   Aik, YSn

KN                  maf, Lokat

Ysn                  Sn

Sn                  Bala

Maf                 ya

Lokat                   c

Aikat                  ci

Sn                   abinci

 

 

 

J

 

YSn                                  YAfgsn

 

Kn                            YA

Sn

Maf             Lokt      aik                   Sn

 

 

Bala                     ya                    c          ci                   abinci

 

b-      Musa           ya      s        sha     ruwa

 

 

 

Sn aik        maf     lokt      Aik    Sn kar’b

S                                     A           K

 

J                  Y Sn   +  YAfgsa

YAfgsn                  KN  +  Yn

YA                   Aik, YSn

KN                  maf, Lokat

Ysn                  Sn

Sn                  Musa

Maf                 ya

Lokat                   s

Aikat                  sha

Sn                   ruwa

J

 

YSn                                  YAfgsn

 

Kn                            YA

Sn

Maf             Lokt      aik                   Sn

 

 

Musa                    ya                    s         sha                  ruwa

 

c-       Musa           ya      k     kamma   Zaki

 

 

 

Sn aik        maf     lokt      Aik    Sn kar’b

S                                     A           K

 

J                  Y Sn   +  YAfgSn

YAfgsn                  KN  +  Yn

YA                   Aik, YSn

KN                  maf, Lokat

Ysn                  Sn

Sn                  Musa

Maf                 ya

Lokat                   k

Aikat                  kama

Sn                   Zaki

 

 

 

J

 

YSn                                  YAfgsn

 

Kn                            YA

Sn

Maf             Lokt      aik                   Sn

 

 

Musa                    ya                    k         kamma           Zaki

 

d-      Ali              ya      k     kashe    Kare

 

 

 

Sn aik        maf     lokt      Aik    Sn kar’b

S                                     A           K

 

J                  Y Sn   +  YAfgsn

YAfgsn                  KN  +  Yn

YA                   Aik, YSn

KN                  maf, Lokat

Ysn                  Sn

Sn                  Ali

Maf                 ya

Lokat                   k

Aikat                  kashe

Sn                   Kare

 

J

 

YSn                                  YAfgSn

 

Kn                            YA

Sn

Maf             Lokt      aik                   Sn

 

 

Ali                       ya                    k        kashe               Kare

 

3.2.2 JUMLAR  TAMBAYA


Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake yi domin tambaya. Saboda haka Sakkwatanci yakan canja wasu daga cikin kalmomin na tambaya, amma kuma wasu basu canjawa, kamar yadda daidaitacciyar Hausa take fad’insu haka Sakkwatanci shi ma yake fad’insu. Ga wasu daga cikinsu.

  • Ina Maryam tat tahi ?

  • Waa aŋ   ka   aika ?

  • Yaushee za  a  dawo  wa aiki ?

  • K’ak’aa za  a  yi  ?

  • Yayaa Audu   yah  hwad’i  jarabawa ?

  • Mii Ali  yas  saye ?

  • Wa sunka  zo  d’azu ?


 

3.2.3 JUMLAR  UMURNI


Jumlar umurni kamar sauran jumloli ita ma jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci daidai take da jumlar umurni ta daidaitacciyar Hausa. Haka ma takan zo da kalma d’aya rak, a matsayin jumla, kuma ta ba da ma'ana cikakkiya, kalmar da take zuwa da ita, itace kalmar aikatau. Ga kad’an daga cikin misalan jumlar umurni a karin harshen Sakkwatanci.

  1. Ali tashi !

  2. Kabiru rubuta !

  3. Musa Karanta !


Haka jumlar ya kamata ta kasance amma saboda wasu dalilai sai ta koma kamar haka:

Misali:

Tashi !

Rubuta !

Karanta !

 

3.2.4 JUMLAR  KOREWA


Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci ita ma daidai take da jumlar korewa ta Daidaitacciyar Hausa. Sai dai kuma ita wannan jumlar ta korewa ta d’an bambanta da ta daidaitacciyar Hausa a wasu bak’ak’en haruffa na Sakkatanci da suka sa’ba da na daidaitacciyar Hausa. Ga wasu daga cikin su:

  1. Baa Ali     yas     sayee ba.

  2. Rabi ba      ta       tahi    makaranta    ba.

  3. Baa kud’d’i                 banki.

  4. Agwagwa ba      ta       tashi   sama  sosai.

  5. Baabu ruwa            a        randa.

  6. bai dace   a        hana  bara   ba.

  7. Kaada kaa    tahi/kar        ka a    tahi.


 

  1. 3 NA’DEWA


Wannan babi wato babi na uku inda aka bayyana karin harshen Sakkwatanci a bisa ra’ayoyin masana da kuma ire-iren jumlar Hausa karin harshen Sakkwatanci, tare kuma da kawo wasu misalai daga ciki. A sassauk’ar jumlar Hausa ta karin harshen Sakkwatanci an yi bayani cewa ita ma jumlar ta k’umshi yanki biyu wato yankin suna da kuma yankin abin da aka fad’i a game da suna, haka ita ma jumlar karin harshen Sakkwatanci tana bias tsarin S.A.K, kamar haka sassauk’ar jumlar daidaitacciyar Hausa. Jumlar tambaya ta karin harshen Sakkwatanci ita ma kamar jumlar tambaya take ta daidaitacciyar Hausa, jumla ce da ake yi domin tambaya. Jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar umurni take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne akan umurni. Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar korewa take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne a kan korewa sai dai ta bambanta da ta daidaitacciyar Hausa kad’an.

 

 

 

 

 

 

Post a Comment

0 Comments