NA
HARUNA ABDULLAHI UMAR
BABI NA BIYU: JUMLA DA IRE-IRENTA A HARSHEN HAUSA
2.0 SHIMFI’DA
Wannan babin na biyu shi ne babin da yake k’unshe da jumlar Hausa tare da ire-irenta. Saboda haka shi ne babin da za a kalli yadda ire-iren jumlolin Hausa suke. Kafin nan za a kawo ma'anar jumlar ta hanyar ra'ayoyin masana.
MA'ANAR JUMLA
Jumla kamar yadda masana suka bayyana ta ita ce, zance mafi tsari da cikakkiyar ma'ana. Wadda ta k’unshi jerin kalmomi daban-daban bisa k’a'idar harshe. Kowace jumla tana k’unshe da muhimman ‘bangarori guda biyu, wato yankin suna, da yankin bayani. Don tabbatar da gaskiya ko me ake nufi da jumla an dubi wasu k’amusoshi Ingilishi. A cikin wani k’amus an bayyana jumla da cewa.
Runnie (1975). “Jumla rukunin kalmomi ne, wanda yake k’unshe da yankin aikatau da kuma fa'ili/ma'aikaci wanda ke bayyana wani bayani ko tambaya ko maganar motsin rai ko umurni. Zai iya zama sark’ak’k’e da gangar dogarau ko had’ad’d’e wanda yake da fa'ili/ma'aikaci fiye da d’aya ko kuma yankin aikatau d’ai-d’ai”.
Rundell (1982), Shi ma cewa ya yi, “jumla ta k’unshi wasu taron kalmomi wad’anda suka had’u, suka bayar da cikakken bayani”.
Robinson (1978) Ya ce, “Jumla wani babban ‘bangaren nahawu ne, wanda ya k’unshi yankuna da ganguna, wad’anda za a iya amfani da su don bayyana wani bayani ko tambaya ko kuma umurni”.
A nan ma'anonin da masana suka bayar ya nuna cewa, kalmomi su ne gimshik’an da ake harhad’awa a samu cikakkiyar jumla mai ma'ana. Tun da yake kalmomi ne ke had’uwa su gina jumla zai yi kyau a ba da tak’aitaccen bayani dangane da ire-iren jumlolin Hausa, ta hanyar lura da yanayin zubin kalmomin cikinsu.
IRE-IREN JUMLOLIN HAUSA
- Sassauk’ar Jumla
- Jumlar Tambaya
- Jumlar Umurni
- Jumlar Korewa
Yanzu za a d’auki kowace jumla domin a nuna yadda tsarinta yake.
SASSAUK’AR JUMLA
Sassauk’ar Jumla ta k’unshi yankin suna da kuma abin da aka fad’i a game da suna. Wannan batu ana iya tak’aita shi kamar haka:
J Suna aikau + Abin da aka fad’i a game da suna. Wannan yanki na abin da aka fad’i a game da suna ya k’unshi aikatau da suna kar’bau (Aikatau + Suna kar’bau). Wannan tsarin shi zai ba da fasalin nan na S.A.K a matsayin tsarin gudanar da sassan sassauk’ar jumla. Irin wannan gundarin tsarin na S.A.K shi ne ake samu a harshen Ingilishi da wasu harsunan masu dimbin yawa.
Masana da yawa sun kawo wannan tsarin na S.A.K, kuma sun yi bayaninsa. Akwai kuma wasu ayyukan wad’anda a kan tsarin S.A.K, na Hausa suke. Misalin Sassauk’ar jumlar Hausa shi ne:
(a) Bala ci abinci
Sn aikau Aik Sn kar’b
(b) Musa sha ruwa
Sn aikau Aik Sn kar’b
(c) Musa kama Zaki
Sn aikau Aik Sn kar’b
(d) Ali kashe Kare
Sn aikau Aik Sn kar’b
(e) Bala ya a ci abinci
Sn aik maf lokt Aik Sn kar’b
S A K
J Y Sn + YAfgmsn
YAfgsn KN + YA
YA Aik, YSn
KN maf, Lokat
Ysn Sn
Sn Bala
Maf ya
Lokat a
Aikat ci
Sn abinci
J
YSn YAfgmsn
Kn YA
Sn
Maf Lokt aik Sn
Bala ya a ci abinci
(b) Musa ya a sha ruwa
Sn aik maf lokt Aik Sn kar’b
S A K
J YSn + YAfgSn
YAfgsn KN + YA
YA Aik, YSn
KN maf, Lokat
Ysn Sn
Sn Musa
Maf ya
Lokat a
Aikatau sha
Sn ruwa
J
YSn YAfgsn
Kn YA
Sn
Maf Lokt aik Sn
Musa ya a sha ruwa
(c) Musa ya a kama Zaki
Sn aik maf lokt Aik Sn kar’b
S A K
J YSn + YAfgSn
YAfgsn KN + YA
YA Aik, YSn
KN maf, Lokat
Ysn Sn
Sn Musa
Maf ya
Lokat a
Aikatau kama
Sn Zaki
J
YSn YAfgsn
Kn YA
Sn
Maf Lokt aik Sn
Musa ya a kama Zaki
(d) Ali ya a kashe Kare
Sn aik maf lokt Aik Sn kar’b
S A K
J Y Sn + YAfgSn
YAfgsn KN + Yn
YA Aik, YSn
KN maf, Lokat
Ysn Sn
Sn Ali
Maf ya
Lokat a
Aikatau kashe
Sn Kare
J
YSn YAfgsn
Kn YA
Sn
Maf Lokt aik Sn
Bala ya a kashe Kare
JUMLAR TAMBAYA
Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake gina wa don a yi tambaya. Saboda haka Hausa tana da tsarin da take bi wajen ginin jumlar tambaya. Hanyar da Hausa take bi wajen ginin jumlar tambaya ita ce, dole ne 'kalmar tambaya', ta zo a farkon jumla. A Hausa ana da kalmomin tambaya kamar haka: Ina,? waa,? yaushe,? k’ak’aa,? yayaa,? mee,? Ga misalin su. a cikin jumla:
a- Ina Maryam ta a tafi ?
b- Waa za a aika ?
c- Yaushee za a dawo aiki ?
d- k’ak’aa za a yi ?
e- Yayaa Audu ya a fad’i Jarabawa ?
f- Mee Ali ya a Saya ?
g- waa da waa suka zo d’azu ?
JUMLAR UMURNI
Jumlar umurni cikakkiyar jumla ce, sai dai kuma ta k’unshi kalma d’aya rak. Haka kuma jumlar umurni a Hausa tana d’auke da wani tsari na musamman, inda Jumlar takan zo da kalma d’aya rak, a matsayin jumla cikakkiya, mai ma'ana. Kuma kalmar da take zuwa da ita, ita ce kalmar aikatau. Ga yadda abin yake:
- Tashi !
- Rubuta !
- Karanta !
Ga yadda ya kamata jumlar ta kasance, amma saboda wasu dokokin nahawu sai suka sa aka ajiye sauran kalmomin.
Misali
Kai ka tashi !
Kai rubuta !
Kai karanta !
JUMLAR KOREWA
Jumlar Hausa ta korewa tana d’auke da wasu kalmomi na musamman da harshen Hausa ya aminta da su domin su zama sharad’i, kafin a gina jumlar korewa ta amsu. Sannan da wad’annan kalmomin ne za a iya nuna irin korewar zance da ake samu a cikin jumla. Kalmomin ana amfani da su ne wajen nuna korewar zance a cikin jumla ta hanyar bin wasu k’a'idoji da aka shimfid’a. Ta amfani da su ne za a iya fahimtar korewar da aka samu a cikin jumla. Kalmomin korewa su ne:
- Ba (baa ------- ba)
- Ba (ba --------- ba)
- Ba (baa)
- Ba (ba)
- Ba (baabu ----)
- Ba i (ba i----)
- Kaada/kar ----)
Ga misalin ka`an daga cikin jumlar korewa:
Ali ya a sayaa
- Ba (baa ------- ba) Baa Ali ya sayaa
Rabi ta a tafi makaranta
- Ba (ba --------- ba) Rabi ba ta a tafi makaranta
akwai kud’i a banki
- Ba (baa) Baa kud’i a banki
Agwagwa ta tashi sama sosai
- Ba (ba) Agwagwa ba ta tashi sama
Akwai ruwa a randa
- Ba (baabu ----) Baabu ruwa a
- Kaada/kar ----) Kaada ka a tafi/kar kaa tafi.
NA’DEWA
Wannan babi wato babi na biyu ya bayyana ma'anar jumlar Hausa a bisa ra’ayoyin masana, tare da bayyana ire-iren jumlar Hausa da ake da su tare kuma da ba da wasu misalai daga cikin kowace jumla. Misali:
A sassauk’ar jumla an nuna cewa, wannan jumla, jumla ce da ta k’umshi yankin suna, da kuma yankin abinda aka fad’i game da suna. Haka kuma ita ce jumlar da ke bisa tsarin S.A.K. Jumlar tambaya kuma, ita ce jumlar da ake gina wa don yin tambaya. Jumlar umurni kuwa ita ce jumlar da ta k’umshi kalma d’aya rak. Jumlar korewa kuwa, ita ce jumlar da ke d’auke da wasu kalmomi na musamman da harshen Hausa ya aminta das u domin su zama sharad’I, kafin a gina jumlar korewa ta amsu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.