(An introductory study of the forms functions and the qualities of the traditional music of the Hausa people)
Tattara Bayanai:
Abu-Ubaida Sani
08133529736
abuubaidasani5@gmail.com
1.0 Gabatarwa
An shirya wannan gajeruwar takarda ne a matsayin matashiya ko gabatarga ga kwas na Hausa da ake koya a jami’o’i da dama (a sashen koyar da harsunan Nijeriya) wato Traditional Music of Hausa People (Wak’ok’in Hausawa Na Gargajiya). Kasancewar wanda ya tsaya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa, ya kamata ne kowane kwas kada ya wuci farfajiyar da aka tanadar masa. Wannan ne zai sanya d’alibai su fahimci wurin da aka dosa ga kwas, yayin da bin tsarin hatsin bara lokacin karantar da wani kwas kan sa d’alibai su rasa abin kamawa. Farfajiyar wannan kwas shi ne wak’ok’in Hausawa na gargajiya. Abin da ake buk’ata d’alibai su sani cikinsa kuwa sun had’a da:
- Ire-ire ko nau’o’in wak’ok’in gargajiya na Hausawa
- Amfanin wak’ok’in gargajiya na Hausawa
- Yanaye-yanayen wak’ok’in gargajiya na Hausawa
A d’aya ‘bangaren kuma, “A bikin balbela, farar kaza ma na iya zuwa.” Saboda haka, yana da kyau a waiwaici ma’anar ita wak’a kanta, da samuwarta a k’asar Hausa, da kuma amfaninta. Wannan takarda za ta dubi wad’annan abubuwa guda uku, amma a tak’aice.
1.1 Ma’anar Wak’a
Wak’a ba sabuwar aba ba ce da ake da buk’atar dogon bayani game da ma’anarta. Masana da manazarta da dama sun bayyana ma’anar wak’a a rubuce-rubuce da suka gabatar a matakan ilimi daban-daban. Masana da marubuta da suka yi tsokaci kan ma’anar wak’a sun had’a da: Gusau, (1993) da K’aura, (1994) da Yahya, (1996) da Bunza, (1988) da Habibu, (2001) da Zurmi, (2006) da makamantansu.
Wak’a wani furuci ne (lafazi ko sak’o) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaitattun kalmomi cikin wani tsari ko k’a’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. (D’angambo, a cikin Habibu, 2001).
Shi kuma Alk’ali Haliru Wurno a wak’e ne ya bayyana nasa ra’ayi kan ma’anar wak’a kamar yadda Abdullahi, (2017) ya rawaito cewa:
Wak’a d’umi ne hira ko labari,
Zargi yabo zagi da kiznin sharri,
Koko kwad’ai ga mutum ya ba ka ka amsa.
Labar d’umi na wanda kay yi ga tsari,
Wani dunk’ulalle kay yi jeri-jeri,
A cikin nashad’i ko ganin ka k’osa.
Wak’e bayani na kad’anna da tari,
Wani bi ka sa gishiri ka yo mishi k’ari,
Had’ari na wak’e mai fad’in damassa.
Wak’a da wak’e Hausa sun d’auke su,
Sunansu wak’a ko’ina an san su,
Ka bid’o bayani babu sai dai kansa.
Wak’a fasaha ne da yac cud’e ka,
Kuma ba karatuna ba in an ba ka,
Ilimi dubu sai ka bid’o wani nasa.
A cikin d’umi wak’e kamar rana ne,
Kuko ya zam hadarin ruwan bazara ne,
Shi taho da sanyinai na ma’aunin nesa.
(Alkali Haliru Wurno ma’anar wak’a)
Sai dai wak’a a k’asar Hausa ba nau’i d’aya ba ce kawai. D’angambo, (2007) ya k’arfafa cewa: “Ya kamata mu tuna cewa akwai wak’ok’i iri biyu: rubutacciyar wak’a da wak’ar baka, wato wak’ar makad’a.” Gusau, (2003) cewa ya yi: “Wak’ar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa ga’ba-ga’ba bisa k’a’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amo kari da kid’a da amshi.”
Abu ne mai wuya a iya k’ayyade asalin lokacin da Bahaushe ya fara wak’a. Wannan kuwa na faruwa ne dalilin kasancewar a farkon rayuwar Bahaushe ba shi da ilimin karatu da rubutu. Ya samu wannan ilimi ne bayan cud’anyarsa da bak’in al’ummar Larabawa da kuma kar’bar addinin Musulunci da ya yi. Bayan ya koyi karatu da rubutu ta hanyar amfani da bak’ak’en Larabci domin rubuta Hausa (ajami), sai kuma ya fara rubuta wak’ok’i. Wannan na nuna cewa, tun kafin zuwan Musulunci da kuma hanyar rubutu Bahaushe na rera wak’ok’i da baka. Game da zuwan Musulunci k’asar Hausa kuwa, an samu bambancin ra’ayi tsakanin masana da marubuta. Wasu na ganin cewa addinin Musulunci ya shigo k’asar Hausa tun k’arni na goma sha biyu. Wasu ma sun ce tun k’arni na bakwai (Habibu, 2001). Amma akwai tabbacin Musulunci ya shigo k’asar Hausa tun zamanin sarkin Kano Ali Yaji. Wato shekarar 1349 zuwa 1385 (Birnin-Tudu, 2002).
1.1 Ra’ayoyi Game Da Asalin Wak’a
Akwai ra’ayoyi daban-daban da ke kirdadon asalin samuwar wak’a. Sai dai wad’annan ra’ayoyin sun kasance hasashe ne kawai. Wasu daga cikinsu ma sun kasance tamkar tatsuniya. An bibiyi irin wad’annan ra’ayoyin jama’a dangane da asalin wanzuwar wak’ok’in gargajiya, sannan aka tace su zuwa gidaje hud’u. Ga yadda suka kasance a tak’aice:
1.1.1 Masu Ra’ayin Banu Sasana
Wannan k’aulin yana ganin wak’a ta samu ne daga wani mutum “Banu Sasana” wanda wata fassara ta nuna cewa shi mutumin k’asar Hurasan ne, shi ne ya fara yin rok’o har ya zama shugaban masu rok’on duniya. Ba zaune yake a waje d’aya ba, yakan zagaya duniya ne. kalmar “sasana” na nufin marok’i a harshen Hurasanci. Wata fassarar na cewa shi ne Hassanu d’an Sabitu, mawak’in jahiliyyar Larabawa wanda daga bisani ya musulunta bayan bayyanar Annabi Muhammadu (S.A.W.). To wai zuriyar wannan Sasana ce ta kawo wak’ar Hausa.
1.1.2 Asalin Wak’a Daga Tsoffin K’asashen Afurka Ta Yamma
Wannan ra’ayi kuwa cewa ya yi, wak’a ta faro ne daga hasken da aka samu na tsarin tsoffin daulolin Afrika ta yamma, wato ana da Mali da Songhai. An danganta wannan zance ne da faruwar wak’a a k’asar Hausa saboda ganin cud’anyar da aka samu tsakanin sarakunan k’asashen, musamman lokacin mulkin sarki Askiya Muhammadu Ture (1493-1508) na Songyai. Sannan da ganin yadda wasu kayan kid’an na wad’annan daulolin suka yi kama da na k’asar Hausa, kamar su taushi da tambari da dundufa, in kuwa haka ne, to wak’a ba ta dad’e da zuwa k’asar Hausa ke nan ba.
1.1.3 Bautar Iskoki Da Dodanni
Ra’ayi na uku kuwa cewa ya yi, wak’a ta samu ne saboda k’angin bautar iskoki da dodanni, musamman ta hanyar kiraye-kirayen da ake yi musu. Za ta iya yuwawa masu wannan ra’ayi sun yi la’akari ne da yadda salon bautar iskoki da na dodannin yake. A yayin irin wannan bauta, akan yi kiraye-kirayen sunayen aljannu da wasu maganganun surkulle na tsafe-tsafe da dai makamantansu. Wannan tsari yana kama da wak’a.
1.1.4 Farauta A Matsayin Asalin Wak’a
Ra’ayi na hud’u wanda shi ne aka fi yarda da shi cewa ya yi, wak’a ta faru ne sakamakon hasken kirare-kiraren da ake na farauta da na noma da kuma na yak’e-yak’en da suka haddasu a tsakanin k’abilun Hausawa. Don haka wak’a ta faru ne kenan daga farauta da kirare-kirarenta, ta dad’a da noma da yak’e-yak’e. A lokacin noma da yak’i da ma sauran lamura da suke buk’atar jarumta da k’arfin guiwa, akan yi kirari da kalaman zuzutawa da kambamawa domin samar da k’arfin guiwa ga wad’anda ake yi wa. Masu ra’ayin suna ganin, daga irin haka ne aka yi ta samun ci gaba da sauye-sauye cikin tsarin kalamai da salon da ake furtawa, har dai ya kai ga an samar da wak’ok’i na hak’ik’a.
1.2 Sauyi A Duniyar Wak’a
Wani babban lamari ya ‘bullo duniyar wak’a yayin da Bahaushe ya samu ilimi da damar fara amfani da kayan kid’a na zamani domin rera wak’ok’insa. Amfani da fiyano da sutudiyo ya canji kalangu da ganga da dundufa da makamantansu na dangin kayan kid’an gargajiya da Bahaushe ya saba amfani da su. Wannan sabon lamari ya samar da muhawara tsakanin masana wak’ok’in Hausa. Wasu dai suna da ra’ayin cewa, duk wak’ar da aka sa mata kid’a, to ta tashi daga rubutacciya. Saboda haka za a kira ta ne wak’ar baka kai tsaye. Wasu kuma suna kallon cewa, sabon salo da wak’ok’in suka zo da shi, sun fi k’arfin a kira su wak’ar baka kawai. Idan aka yi haka, hak’ik’a ba a yi wa wak’ar baka ta asali adalci ba. Domin ita ba sai an rubuta ba ake rerawa. Ma’ana ana rattabo ta ne kawai kai tsaye.
Wani bambanci da ke tsakanin wak’ok’in da ake samarwa a sutudiyo da na baka shi ne, a wak’ok’in baka ba a samun amsa amo da daidaiton baituka kamar yadda yake samu a wak’ok’in zamani na sutudiyo. A wannan ‘bangare (k’afiya da daidaiton baituka) wak’ok’in zamanin sun fi kama da rubutattun wak’ok’i. A tak’aice dai, wak’ok’in sai suka kasance tamkar jemage; ba su ga tsuntsu ba su ga dabba. Wato dai siffofinsu ba su tsaya ga wak’ok’in baka ko rubutattu ba kad’ai. Za ta iya yuwawa, wannan ne dalilin da ya sa kafar intanet na Hausa mai suna amsoshi (www.amsoshi.com) ya kira irin wad’annan wak’ok’i da Wak’ok’in Zamani. Domin kuwa, duk inda aka zaga aka zago, dole ne a yarda wak’ok’in sun samu ne a zamanance. Sannan zamani yana tasiri ga wak’ok’in da su kansu mawak’an.
1.3 Amfanin Wak’a
Hak’ik’a wak’ok’i suna taka muhimmiyar rawa wurin fad’akarwa tare da wa’azantarwa ga al’umma bayan d’umbin nishad’antarwa da akan samu daga wak’ok’i. Ba za a ta’ba mantawa da gudummuwar rubutattun wak’ok’i ba a lokacin jihadin jaddada addinin Musulunci k’ark’ashin jagoranci Shehu Usmanu D’anfodiyo (Yahya, 1987; Zurmi, 2006). A zamanin yau kuwa, ‘bangarorin rayuwa da dama sukan rasa armashi idan babu wak’a. Bello, (2017) ya zayyano wasu daga cikin fannonin rayuwa da wak’a ke taka rawar gani gare su. Sun had’a da: siyasa, da ilimi da tarihi da makamantansu. A tak’aice, amfanin wak’a sun had’a da:
- Wak’a babbar hanya ce ta jawo ra’ayin al’umma a lokutan siyasa domin za’ben wani d’an takara. Mawak’a na da babban gurbi wurin tallata ‘yan takara ta hanyar kurara su da fito da ayyukansu na alkairi fili tare da kushe abokan takararsu.
- Wak’a babbar hanya ce ta tallata haja ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban. Masu shaguna da kamfanoni da ma wasu nau’ukan kasuwanci iri-iri kan nemi mawak’a su tallata hajarsu.
- Wak’a hanya ce ta ilimantarewa da fad’akarwa. Jama’a sukan samu ilmummuka daban-daban tare da wayewar kai daga wak’ok’in da suke saurara. Wannan ya had’a da bayanai game da cututtuka, da yanayin siyasar k’asa da makamantansu.
- Wak’a hanya ce ta samun abin masarufi da dogaro da kai ga mawak’a da dama.
- Wak’a na samar da nishad’i da annashuwa.
- Kafa ce ta adana tarihi da al’adu. Akwai wak’ok’i da suke d’auke da tarihin muhimman mutane cikin al’umma ko wasu muhimman lamura da suka faru. Irin wad’annan wak’ok’i za su kasance tamkar taska na adana wad’anan muhimman tarihai har zuwa lokaci mai tsawo nan gaba.
- Wak’a na tallafa wa wasu ‘bangarorin adabin Bahaushe na baka da rubutattu.
- Wak’a hanya ce ta tallatawa tare da yad’a harshe zuwa ga wasu al’ummu da duniya baki d’aya.
- Wak’a ta kasance babbar hanya da al’umma za su iya bayyana kukansu ga gwamnati ko wata majiya a matsayin k’ungiya ko d’aid’aikun jama’a.
1.4 Kammalawa
Duk da dusashewar al’adun gargajiya da dama a dalilin tasirin zamani, wanda ciki har da wak’ok’in gargajiya, dole ne a yarda cewa wak’ok’in gargajiya na da mutuk’ar amfani ga ‘bangarorin rayuwar Bahaushe daban-daban. Daga ciki akwai koyar da tarbiyya da hannunka mai sanda da ilimantarwa da fad’akarwa da nishad’antarwa da adana al’adu da kalmomi da dai sauransu.
https://www.amsoshi.com/game-da-mu/
Manazarta
Abdullahi, S. M. (2017). “Kud’i A Idan Mawak’an Hausa Na Baka Da Rubutattu, Wak’ar Kud’i Ta Alhaji Audu Wazirin D’anduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja” Kundin digiri na farko da aka gabatar a Sashen Harunan Nijeriya, Jami’ar Usamnu D’anfodiyo Sakkwato
Bello, S. A. (2017). “Tasirin Wak’a A Cikin Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Wak’ok’k’in Aminu Ladan Abubakar.” Takardar da aka gabatar a taron masoya Aminu Ladan Alan Wak’a, a makarnatar Ado Gwaram, Kano
Birnin-Tudu, S. Y. (2002). “Jigo da Salon Rubutattun Wak’ok’in Fura’u na K’arni na Ashirin.” Kundin babban digiri na uku (Ph. D.) wanda aka gabatar a Sashen Harrunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo, Sakkwato.
Bunza, A. M. (1988). “Nason Kirari Cikin Rubutattun Wak’ok’in Hausa na K’arni na 20.” Mak’alar da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Dangambo, A. (2007). D’aurayar Gadon Fede Wak’a. Zaria: Amana publishers LTD
Gusau, S. M. (2003). Jagora Nazarin Wak’ar Baka. Kano: Benchmark.
Habibu, L. (2001). “Bunk’asar Rubutattun Wak’ok’in Hausa a K’arni na Ashirin (20).” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato.
K’aura, H. I. (1994). “K’awancen Salo a Tsakanin Rubutattun Wak’ok’in Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa.” Kundin kammala digiri na biyu (M.A.) wanda a aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo, Sakkwato.
D’angambo, A. (1980). “Hausa Wa’azi Verse From CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style. A Ph. D. thesis submitted to the University of SOAS, London.
Yahya, A. B. (1987). “The ‘Berse Category of Madahu With Special Reference To Theme, Style and the Background of Islamic Soures and Beliefs.” A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu D’anfodiyo University, Sokoto.
Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Wak’a. Kaduna: Fisbas Media Service.
‘Yar’aduwa, T. M. (2010). Jagoran Nazain Rubutaccen Adabin Hausa. Ibadan: HEBN publishers PLC.
Zurmi, A. D. (2006). “Tsoratarwa a Cikin Wak’ok’in Wa’azi na Nana Asma’u.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato.
Kafar Intanet
www.amsoshi.com
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.